Almizan :Infaki nau’i ne na ibada ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 22 Zulkidah, 1426                 Bugu na 697                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Rahotanni

Infaki nau’i ne na ibada

- Malam Kasimu Umar Sakkwato

Daga Musa Muhammad Awwal

H

An bayyana cewa bayar da dukiya a hanyar Allah, infaki, wani babban nau’i ne daga cikin ibada wacce bawa kan yi don neman yardar Ubangijinsa.

Malam Kasimu Umar, Wakilin ’yan uwa na garin Sakkwato ne ya bayyana haka a Kaduna a matsayinsa na babban bako mai jawabi a wajen wani gagarumin taro da aka gabatar don tattara kudade a shirin da Kadunan ke yi na dumfarar babban bukin kaddamar da Asusun AM, wanda ke tafe ba da jimawa ba.

Malam Kasimu, wanda kuma yake shi ne Shugaba na wannan Asusu, ya kuma jawo hankalin ’yan uwa cewa su sani bayarwa fisabilillah ne ke kara wa dukiya albarka. Kuma ta yin haka ake samun sabati a kan abin da ake yi.

Saboda haka sai Malamin ya yi kira gare su cewa su fito su taimaka wa addinin Allah da duk abin da suka mallaka, musamman a wannan lokacin da Harka Islamiyya ke da matukar bukatar kudi don aiwatar da muhimman abubuwan da ke gabanta.

Shugaban Asusun, ya kuma yi wa ’yan uwa matashiya da cewa babu inda Harka za ta je ta samo kudade in ba daga ma’abotantata ba. Wannan ne, in ji shi, ya zama wajibi ga duk wani mai bin Malam Zakzaky bil hakki ya fito ya bayar don taimaka wa aikin Allah.

Da ya juya ga wannan yanki na Kaduna kuwa, Malam Kasimu cewa ya yi, ai kamata ya yi a ce wannan yanki ne ya fi bayar da kaso mafi tsoka, musamman don ganin Malam Zakzaky ya fito ne daga wannan yankin ne.

Shi ma a nasa jawabin, mai masaukin baki, Malam Muhammad Mukhtar Sahabi, muhimmancin bayar da dukiya don Allah ya nuna, inda ya nuna cewa dan uwa na samun sabati ne ta hanyar bayarwa don Allah.

Saboda haka sai ya yi kira da cewa wajibi ne kowa ya fito ya bayar da dukiyarsa don Allah ba tare da wani jinjina ko waigen baya ba.

Bayan da aka kammala jawabai ne sai aka ci gaba da batun kaddamar da neman kudi, inda aka fara da kiran da’irori, halka-halka da kuma daidaikun mutane. Nan take dai aka tara sama da Naira N303,592.00.

A daren wannan rana ne kuma aka gabatar da wani gagarumin majalisin mawaka wanda Mustafa Gadon Kaya ya shugabanta, inda a nan ma aka tara dubunnan Nairori.

Wani abin burgewa game da wannan taron da ALMIZAN ta ci karo da shi, shi ne, yadda iyalan Shahid Sabi’u Imam da ya yi shahada sakamakon harbin sa da ’yan sanda suka yi, bayan sun kammala muzaharar juyayin shahadar Shaikh Ahmad Yassin a Kaduna, suka yi wa wani dan uwa da ya yi wa Shahid din lancin na Naira 2,000, lancin na Naira dubu 20.

’Yan Hizbah sun yi wa ’yan uwa raunuka

Daga Ali Kakaki

Wasu ’yan Kungiyar JTI da suke cikin kayan Hizbah sun dirar wa ’yan uwa Musulmi, Malam Rabi’u da Malam Ahmad Ola da ke Dawakin Dakata da duka har suka ji masu raunuka.

Wannan lamari, da wasu da dama da muka zanta da su suka bayyana shi da cewa na rashin sanin ya kamata ne, ya faru ne a daidai lokacin da Malam Husaini Abubakar Bauci yake irin zage-zagen da suka saba yi a kan Malam Zakzaky da Shi’a a unguwar Dawakin Dakata da ke Karamar Hukumar Nasarawa da sunan wa’azi.

ALMIZAN ta samu zantawa da Malam Bashir, Wakilin Halkar Tudun Wada kan faruwar lamarin, ya kuma tabbatar mana da cewa yanzu haka raunukan da ’yan Hizbah suka ji wa ’yan uwan biyu sun fara warkewa.

Malam Bashir ya tabbatar wa da ALMIZAN cewa a yayin wannan zage-zagen da suka kira wai da sunan wa’azi, an ga motoci biyu kiran fijo masu dauke da lambar gwamnati a wannan wurin.

Sai dai da muke zantawa da shi, daya daga cikin shugabannin Hizbar a Kano ya ce ba mutanensa suka yi wannan dukan ba.

Sadaukar da rai
don Allah ne zai tabbatar da zaman

lafiya

In ji Malam Muhammad Turi
Daga Ali Kakaki

Malam Muhammad Mahamud Turi ya bayyana cewa gane cewa tafarki na sadaukar da rai saboda Allah (T), wato shahada shi ne hanyar tabbatar da zaman lafiya da kuma izzar Musulmi da Musulunci a wannan zamanin da kafircin duniya yake yakar Musulmi da Musulunci da sunan yaki da ta’addanci.

Malam Muhammad Turi ya yi wannan bayani ne a lokacin da yake jawabi ga dimbin al’ummar Musulmi jim kadan bayan kammala sallar Juma’a kamar yadda ya saba gabatarwa a duk Juma’a a masallacin Juma’a na Fagge.

Malam Turi ya ce, shi Shahidi matsayinsa a wajen Allah matsayi ne na musamman, kuma wanda Allah ya azurta shi da samun wannan babban matsayi ya rabauta a rayuwarsa ta duniya da kuma gobe kiyama. “Bawa ba shi da wata hanya da zai samu daukakar da zai samu a wannan zamanin kamar ya yi shahada a tafarkin Allah (T).”

A cikin jawabin nasa, Malam Muhammad Turi ya tabo irin kurari da kulle-kullen da ake yi wa ’yan uwa Musulmi almajiran Malam Zakzaky a gidan gwamnati da kuma wasu hukumomi a garin Kano, har ma da ware kudi aka ba wasu mutane suna zage-zage a unguwanni wai da sunan suna wa’azi, har ma suna barazanar za su kawo hari, amma har yanzu shiru kake ji.

Malam Turi ya kara da cewa, “akwai lokacin da muka samu labarin sun riga sun gama shirye-shirye suna gab da zuwa, amma muna ta sauraro, amma sun kasa zuwa.”

Haka kuma Malamin ya ce; shi akwai likafaninsa na Mu’assasatu Shahada har ya yi kura ya fara baki, “sauraro muke, amma har yanzu shiru kake ji,” in ji shi.

Ya ci gaba da cewa akwai wauta a cikin abin da ita gwamnatin Kano take niyyar yi, “saboda ko ba komai za ku taimaka wa Amurka da Isra’ila ne dangane da burinsu wajen hada fada tsakanin Musulmi.”

ALJAZEERA ta ci mutuncin al’ummar Iraki

In ji Dakta Ibrahim Jafari

Bayan wata ganawa da Firaministan kasar Iraki, Dakta Ibrahim Ja’afari ya yi da babban Malamin addinin Musulunci a kasar, Ayatullah Ali Sistani ya bayyana cewa abin da tashar talabijin ta ALJAZEERA ta yi wa Malamin cin mutunci ne ga al’ummar Iraki.

Wannan mai da martani na Firaministan na Iraki, wanda ya fito jaridarsa mai suna AL-BAYAN, ya nuna cewa wannan tamkar cin mutuncin al’ummar kasar ta Iraki ne.

A wata hira da tashar talabijin ta AL-JAZEERA ta watsa da wani masanin tarihi dan asalin kasar Syria, Fadel Alrubaiyi, ya nuna babban Malamin addinin na kasar Iraki, Ayatullah Ali Sistani a matsayin wanda ya taimaka wa Amurkawa shigowa kasar ta Iraki.

Haka nan kuma ya kara da cewa yana kiran Ayatullah Sistani da ya koma masallaci ya bar sha'anin siyasa, wanda wannan ma tamkar wani harafi ne na wulakanta matsayin babban Malamin, in ji Firaministan na Iraki.

Tun bayan wannan shiri da aka watsa dai al’ummar kasar suka rika fitowa kan tituna suna Allah wadai da wannan abu, sannan kuma suna nuna rashin amincewarsu kan abin da masanin ya fada.

Saboda haka ne ma a wannan Asabar din shi Firaministan kasar Iraki, Dakta Ibrahim Ja’afari ya kira tashar da ta nemi gafarar abin da ta aikata, kuma ta nisanci maimaita irin haka a nan gaba.

Hamas ta sami gagarumar nasara
A zaben Kananan Hukumomi

Rahotanni da ke fitowa daga yankin gabar yammacin Kogin Jordan na Palastinu na nuna irin gagarumar nasarar da Kungiyar Jihadin Musulunci ta Hamas ta samu a zaben Kananan Hukumomi da aka gabatar a karshen wannan makon.

Tuni dai har jami’an haramtacciyar kasar Isra’ila sun fara bayyana tsoronsu kan irin wannan nasara da suka ga kungiyar tana samu.

A wata hira da aka watsa ta kafar watsa labaran haramtacciyar kasar, Silvan Shalon, Ministan harkokin wajen kasar ya yi kira ga Shugaban gwamnatin Palastinu, Mahmood Abbas da ya tabbatar da an hana kungiyar ta Hamas yin takara a zaben da za a gudanar a ranar 25 ga watan Janairu mai kamawa.

Jami’an na haramtacciyar kasar Isra’ila sun ci gaba da bayyana cewa lalle in aka bar kungiyar ta Hamas ta tsunduma a cikin zaben za a koma shekaru 50 da suke wuce ne.

Masana dai na ganin irin wannan nasara da kungiyoyin addini suke samu tamkar wata manuniya ce da ke hikiyar irin yadda kafircin duniya ke ta komawa baya, sannan ruhin addini yake tasowa.

Bapalastiniya ta fasa wa Yahudawa kwai

Wata yarinya ’yar Palastinu ’yar shekara 15 da haihuwa a wani taro a Kuala Lumpa ta fasa kwai kan yadda haramtacciyar kasar Isra’ila ke ci gaba da azabtar da Palastinawa a sansanonin su da ke kasashe daban-daban a duniya.

Wannan yarinyar mai suna Najma Jalamneh dai ta gabatar da wani jawabi ne a wani taro na tabbatar da zaman lafiya da aka a Kuala Lumpa babban birnin kasar Malysia a makon jiya.

Yarinyar a jawabin ta mai tsananin kashe gwiwa ta bayyana yadda sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila ke kashe yara kanana, tare da rusa gidajensu, da kuma kona dukkanin amfanin gonarsu wanda a kansa ne suka dogara.

Najmah ta ci gaba da bayyana cewa; a wannan taron na zaman lafiya a duniya da ake gabatarwa su basu ganin wata ma’ana a cikinsa, domin kuwa kamar yadda ta bayyana su ba su taba zama cikin kwanciyar hankali ba tun daga lokacin da aka haife su.

Najmah ta ci gaba da bayyana cewa tana jin mamakin yadda ake nuna ’yan gwagwarmayar Palastinawa a matsayin ’yan ta’adda alhali kuwa su al’umma ce wadda aka zalunta.

Wannan taro na duniya na zaman lafiya dai wanda ya samu halartar masana da ’yan siyasa daga bangarori daban-daban na duniya sai a ranar Asabar din nan da ta gabta aka kammala shi.

‘Juyin Musulunci a Iran ya kawo hadin kan daliban ‘Hauza’ da Jami’a’

Na’ibin Limamin Juma’a a birnin Tehran, kuma Shugaban Hukumar fayyace maslahar tsarin Musulunci a Iran, Ayatullah Hashemi Rafsanjani ne ya jagoranci sallar Juma’a da aka gabatar a babban masallacin Juma’a da ke Jami’ar Tehran a makon da ya gabata.

A lokacin da yake gabatar da hudubobin sallar Juma’ar tasa, Ayatullah Hashemi Rafsanjani, ya fara ne da kiran al’umma zuwa ga tsoron Allah kamar yadda aka saba, sannan kuma ya yi magana kan rayuwar Imam Ridha (AS) ya taka saboda munasabar ranar haihuwarsa wanda ta zo a makon da ya gabata.

Haka nan kuma Ayatullahi Rafsanjani, ya yi magana kan abubuwan da suka faru a makon da ya wuce, ciki ya ambaci shahadar wani babban Malami, Ayatullah Dastgaib, daya daga cikin Limaman Juma’a da aka kashe a shekarun farko bayan juyin Musulunci a Iran.

Haka nan kuma Ayatullah Rafsanjani, ya yi jawabi kan rayuwar Ayatullah Dakta Mufattah, shi ma wanda munafukai suka kashe bayan juyin Musulunci, Rafsanjani ya nuna cewa Mufattah shi ne babban wanda ya yi yunkurin ganin an sami daidaito tsakanin dalibai masu karatun addini da kuma ’yan Jami’a.

A wani bangare na hudubar tasa, Ayatullahi Hashemi Rafsanjani, ya yi magana kan zaben ’yan Majalisa na kasar Iraki, inda ya nuna cewa babu shakka wata nasara ce da al’ummar kasar suka sake samu, sabanin yadda ’yan mamaya, Amurka da kawayenta suke son su gani. Sannan ya yabi Maraji’ai na addini, musamman ma Ayatullah Ali Sistani wajen irin yadda suka iya hado al’umma, tare da tabbatar da natsuwa a lokacin hayaniya.

A karshe Rafsanajani ya soki Amurka kan irin yadda take ci gaba da tuhumar Iran kan sa hannu cikin lamurran cikin gidan Iraki, inda ya ce wannan wani abin dariya ne kawai ga dukkanin mai hankali.

Hajjin da babu bara’a ga azzalumai ba Hajji kammalalle bane

In ji Marigayi Imam Khumaini

Sabanin yadda wasu daga cikin Musulmi suke zato aikin Hajj wata ibada ce, sannan kuma a lokaci guda dama ce da Allah Ta’ala ya bai wa bayi saboda tattauna matsalolinsu na siyasa da zimmar kawo gyara cikin rayuwar al’umma a baki daya.

A cikin umurnin da Allah Ta’ala ya yi game da aikin Hajji ya nuna a fili cewa daya daga cikin hadafin wannan aiki na ibada shi ne saboda al’umma su shaida wasu amfanoni.

Cikin amfanoni da za a iya samu baya ga ibada ta aikin Hajji akwai fuskar tattalin arziki, zamantakewa, da kuma bangaren siyasa.

Marigayi Imam Khumaini (RA) ya kasance yana fadi game da aikin Hajji cewa; hajjin da babu bara’a ga azzalumai ba Hajji kammalalle bane.

A wata ganawa da Jagoran juyin juya hali na Musulunci ya yi da tawagar jami’ai masu gudanar da aikin Hajji, ya nanata wannan ma’ana na cewa kamar yadda ya kamata al’umma su amfana da gefe na ma’ana cikin wannan ibada, haka kuma ya kamata kada su yi sakaci da bangarensa na siyasa.

Yanzun haka dai al’ummar Musulmi a kasashe daban-daban sun fara tafiya birni mai tsarki saboda wannan ibada ta shekara-shekara.

Izala ba ta rabu gida uku ba

In ji sabon Sakataren Kungiyar

Sabon jami’in hulda da jama’a na Kungiyar Izalatul Bidi’a Wa Ikamatu Sunna, Alhaji Aminu Abubakar Funtuwa ya yi watsi da jita-jitar da ake ta bazawa a ’yan kwanakin nan na cewa Kungiyar ta dare gida uku. Sakamakon kin halartar taron sulhu da Dakta Ahmad Gumi ya kira da wasu shugabani kungiyar suka yi a farkon watan Shawwal.

Alhaji Aminu Abubakar Funtuwa, wanda yake ganawa da ALMIZAN a farkon makon ya ce, “wannan magana ba gaskiya bane. Mu mun san kungiyar Izala tana nan a dunkule wari daya, kuma ana tafiya tare.”

Ya ce ko a ranar Asabar din nan da ta gabata, ta kira wani gagarimin wa’azi na kasa baki daya, wanda kuma ya hada hancin duk kusan Malaman da ke cikin kungiyar, “in ba a tare ake tafiya aba ai za ka ga wasu sun zo wasu ba su zo ba. Amma duk wani Malami wanda muke ji da shi ya halarci wannan taron wa’azin,” ya jadadda.

Alhaji Aminu Abubakar Funtuwa ya hakikance cewa wannan zance wani suruto ne kawai da wasu mutane da ba sa yi wa Musulmi da kuma Kungiyar Izala fatan alheri suka kirkira suke kuma watsa shi domin su raba kan mutane, “sun kirkiri wannan jita-jitar ne don su kawo rikici ko kuma su kawo tashin hankali a cikin wannan kungiyar tamu. Don haka mu wannan labarin na cewa kungiyar Izala ta rabu gida uku wani zance ne da mu ba mu san shi ba.”

Sabon jami’an watsa labaran na kungiyar Izala ya ce ba ma wai Izala ta rabu gida uku ba, hatta bangaren Jos ma da suka bangare, sunan nan suna ta kai kawo wajen ganin sun dawo an ci gaba da tafiya tare. “Hatta bangaren Filato muna nan mun kai kawo wajen ganin mun jawo su a jika, don dai mu ci gaba da tafiya tare kamar yadda aka faro wannan tafiyar shekaru sama da 25 da suka gabata.”

Wani bincike da ALMIZAN ta yi ta gano cewa jama’a suna ta yada jita-jitar cewa Izala ta kasu gida uku, inda wasu suke cewa akwai bangaren Jos, na Kaduna da kuma na Dakta Ahmad Gumi, musamman saboda kin halartar taron sulhun da Dakta Gumi ya kira da wasu shugabannin Izala bangaren Kaduna da ake ganin sun fi kusa da shi suka yi. Sai dai su shugabannin kungiyar suna ta kore wannan batun. A cikin jawaban da suka gabatar ma a wajen taron wa’azin kasa da suka yi a makon jiya, kusan duk wanda ya yi wa’azi a wajen taron yana jadadda diyaucin wannan kungiyar ne.

Alhaji Aminu Abubakar Funtuwa ya ce, ba wani abu mai kama da rashin jituwa tsakanin su Shaikh Yusuf Sambo da kuma Dakta Ahmad Gumi, “ba wata baraka tsakanin Izala da kuma Dakta Ahmad Gumi. Mutane su ke hadasa yawancin rigingimin da ake samu a cikin wannan addinin namu na Musulunci.”

Sabon jami’in hulda da jama’ar na Izala ya yi watsi da wani labari da wata jarida (ba ALMIZAN) da ta buga a makon jiya, da yake cewa wasu matasa sun yi zanga-zanga a wajen taron wa’azin kasa da aka yi a Kaduna suna nuna bara’arsu ga shugabanninsu. Ya ce shi bai san inda wannan jaridar ta samo wannan labarin ba. “A samunmu mu dai mun masata da Malaman Izala a nan kamar yadda ake, babu wata baraka a tsakansu, da Malamai da matasan tsintsiya madaurinki daya ne.”

Da yake tsokaci game da inda aka kwana game da batun sulhunta Kungiyar Izala, Alhaji Aminu Abubakar Funtuwa ya ce, har yanzu suna nan suna ta kai kawo wajen sun jawo mutanen Jos a jika domin a hade a ci gaba da tafiya. “Ka san komai yana da lokacin da zai kawo karshe. Mu dai a shirye muke mu hade a ci gaba da tafiya kamar yadda aka faro ta. In dai za a tsare hakin Musulunci kamar yadda ya kamata a shirye muke a ci gaba da tafiya.”

Alhaji Aminu Abubakar Funtuwa ya yi kira ga Musulmi da babbar murya su hade da juna su bar wani zance rabe-rabe. “Lokacin da ya yi kamata Musulmi su san cewa wannan rabe-raben da ake yi su a je shi gefe guda, mu tsaya mu fuskanci abin da yake gabanmu. Muna matukar bukar hadin kai, kasar nan tamu ta shiga wani mummunan hali, kowa ya san halin da ake ciki. Mu hada kai mu fuskacin abin da yake gabanmu. Mu daina zama muna sukar juna. Idan ba mu hada kai waje daya ba za mu rushe. Idan kuwa muka hada kai waje daya ba za mu fuskaci wata matsala ba,” ya karkare.

ISLAMIC FORUM ta yi taronta a Kano

Daga Al-Hausain Dakace

Kwanakin baya ne sananniyar Kungiyar nan, ISLAMIC FORUM OF NIJERIYA ta gudanar da taron ta a makarantar koyan harshen larabci da ke Kano (SAS), karkashin Shugabanta na kasa, Alhaji Dakta Aminu Dantata, wanda aka fi sani da Aminu Dogo.

Kafin a fara bayanan nasarorin da ISLAMIC FUROM din ta samu da kuma yadda take tallafawa al’ummar Annabi wajen samar masu da guraban aiki da kuma makarantu, sai da Shugaban ya yi takaitaccen bayani mai muhimmanci.

Kafin nan sai da ya fara yi wa bakin da suka zo maraba da zuwa; “ina maraba ga dukkan jama’ar da ta halarci taron.” Sannna kuma sai ya yi addu’ar Allah ya dada karfafa wa wannan kungiya gwiwa. Ya kara da cewa da yardar Allah al’ummar Musulmi za su ci nasara a kasar nan.

Alhaji Aminu Dogo ya ci gaba da cewa, “Kungiyar ta ISLAMIC FORUM tana nan daram-dakam, kuma za ta ci gaba da aikace-aikacenta da ta saba.”

Bayan Shugaban ya kammala jawabinsa ne, sai babban Sakataren kungiyar ta ISLAMIC FORUM, Dakta Usman Jibirin mai ritaya ya yi takaitaccen bayanin nasarorin da kungiyar ta samu, inda ya ce sun samarwa da matasa shiga aikin soja na NDA da ke Kaduna kimanin mutane 7, sojan ruwa kuma mutane 2, sojan sama 3.

Har ila yau babban Sakataren ya ci gaba da cewa, a aikin dan sanda kuwa sun sami nasaran shigar da matasa 10 da kuma aikin soja da ke Zariya kimanin mutane 13, sai kuma mutane 2 a aikin kwastan, sun kuma samarwa da matasan guraben karo ilimi daga manyan Jami’o’in da ke kasar nan kimanin mutanen 12, da kuma dibar wadansu aiki masu tarin yawa a bankunan kasar nan.

Kazalika babban Sakataren na ISLAMIC FORUM ya ce sun gabatar da wani taro a Gusau ta jihar Zamfara don wayar da kai tsakanin Musulmai da kiristoci, wanda ya sami halarta Sultan na Sakkwato, Alhaji Muhammad Maccido da dai sauran muhimman aikace aikace da kungiyar ta gudanar a fadin kasar nan.

Babban Sakataren ya kuma yaba sosai ga Shugaban kungiyar ta ISLAMIC FORUM, Alhaji Dakta Aminu Dantata game da yadda yake bai wa kungiyar taimako da kuma hadin kai don ganin ta ci gaba da kuma ba da shawarwar masu ma’ana da yake yi. Haka kuma ya yaba wa Alhaji Aliko Dangotte a kan yadda shi ma yake tallafawa da kudadansa.

An kuma tabbatar wa al’ummar Musulmi a wajen taron cewa ISLAMIC FORUM kofar a bude take ga dukkan al’ummar Musulmin da yake bukatar shiga, kuma kungiyar ba ta da nasaba da wata kungiya ta siyasa, ko kuma wata manufa ta dabam, “lila Musulunci,” in ji babban Sakataren na ISLAMIC FORUM.

’Yan fashi da makamai sun matsa kaimi a Kano

Daga Al-Husain Dakace

Yanzu haka dai ’yan fashi da makami sun matsa kaimi sosai wajen aikata yin fashi da makami ta yadda masu kudi manya da matsakaita kai har ma da ma’aikatar jihar ba sa iya kyakkyawar gudanar da barci sakamakon matsa kaimi da ’yan fashin suke yi na kai hare-hare ba ji ba gani.

Bayan harin da suka kai a Unguwar Gwale da ke cikin birnin Kano a gidan Ferfesa Ayagi, inda aka tabbatar wa da ALMIZAN cewa sun yi matukar barna tare da yin awan gaba da kudade masu tarin yawa, baya ga mummunan dukan tsiya da suka yi wa Farfesan sun kuma haura wasu unguwannin.

A unguwar Gyadi Gyadi kuwa, dirar mikiya ’yan fashin suka yi a gidan Kwamishinan aikin gona na jihar Kano, Alhaji Ibrahim Garba, inda suka yi awon gaba da kudade masu tarin yawa, an kuma shaida wa ALMIZAN cewa sun dauki lokaci suna yin abin da suka ga dama a gidan, kuma babu wani dauki da Hukumar ’yan sanda suka kawo masu.

A kasuwar Kantin Kwari kuwa, ’yan fashin dirar mikiya suka yi ofishin Shugaban Kungiyar ’yan kasuwar, Alhaji Bature Abdul’aziz, inda suka daddaure masu gadin gaba daya, sannan suka shiga cikin ofishin suka yi awon gaba da tsabar kudi har Naira 50,000. Bayan fitarsu sun kuma yanka daya daga cikin masu gadin yankar rago.

A unguwar Kwana Hudu kuwa, ’yan fashin gidan Alhaji Abdul Rahaman Siraji suka shiga, amma Allah ya sa ba su same shi ba, amma sun yi awan gaba da muhimman kayayyaki masu dan karen tsadar gaske, amma daga baya an samu nasarar damke wasu daga cikinsu.

Irin wannan tasar da ’yan fashin ke yi ba ta tsaya a cikin garin Kano ba, hatta kwanakin baya dira ’yan fashin suka yi a Karamar Hukumar Dambatta da ke jihar ta Kano, inda nan ma suka wawushe makudan kudade masu tarin yawan gaske.

A wata sabuwa kuma, wadansu da ba a san ko su wanene ba a unguwar Gandun Albasa sun kashe wani almajiri da ake kira Namanu a cikin shagon da yake kwance kuma an tabbatar da cewa kusan duk shekara ya kan zo unguwar.

Jaridar ALMIZAN ta lura cewa mafi yanwancin wadannan muggan aika-aika da ’yan fashin suka gudanar duk sun yi su ne bayan wucewar watan Ramadan mai albarka.

Yayin da wasu ke yin kira ga gwamnatin Malam Ibrahim Shekarau da cewa ya kamata ta kara tsaurara tsaro sosai ko mutanen jihar sa samu su sarara, musamman masu hannu da shuni.

An yi kira ga Harisawa da su yi aiki don Allah

Kwamandan Harisawa masu ba da kariya ga Harka Islamiyya, Malam Abubakar Maina Bukar Potiskum ya yi kira ga Harisawan da su yi aikinsu don Allah. Malamin ya yi wannan kiran ne a wata ganawa da ya yi da Harisan yankin Gombe jim kadan da ya kawo ziyara yankin na Gombe.

Tunda farko Malam Abubakar Maina, ya ankarar da Harisanwa cewa su sani fa Allah ne yake son su shi ya sa ya zabo su daga cikin sauran ’yan uwa don yin aiki na musamman, wanda kuma ya fi kowane aiki wahala, duk kuwa da cewa babu wanda aka tilastawa, ko kuma aka yi masa alkawarin wani albashi mai tsoka. Kowa shi ne ya ji zai iya sadaukar da lokacinsa dama ransa don ganin addinin Allah ya daukaka.

Don haka ya bukaci Harisawan da su mance da duk wani abin da wani zai fada walau na yabo ko na suka, “domin dama ba suna yi bane don a yaba musu. Idan kuma don kushe zai sa ku dakata, to ku sani kuna taimakawa makiya.”

Ya ci gaba da cewa, “domin makiya kullum suna ta kirkiro sababbin hanyoyi don ganin sun kawo cikas ga wannan gwamnarmaya.” Ya ce, “suna iya gwada wannan ka ga idan wancen ya dakata wancen ya dakata, sai abubuwa ba su gudana ba sai su kara kaimi in sun ci nasara a wannan Da’irar, sai su yi gaba, cam ma su cinna irin wannan wutar,” in ji shi.

Har ila yau ya gargadi Harisawan da suke yada gulmace-gudlmace da su ji tsoron Allah, domin duk mutumin da ya yi sanadiyyar fitinuwan wani, to Allah zai kama shi da azaba mai radadi.

Daga karshe ya ba da shawarwarin yadda ya kamata Harisawan su rika shirya wasu shirye-shirye nasu don ganawa da junansu. To sai dai ya nuna musu cewa kada su yawaita shirye-shirye domin hakan zai sa wasu su kasa zuwa, amma idan aka sa sau biyu asati kowa zai zo cikin marmari.

Daga karshen zaman ’yan uwa Harisawa sun yi tambayoyi ga Malam Abubakar Maina Bukar, inda ya ba su amsoshi kamar yadda ya kamata. Harisawa da dama ne daga cikin gari da kuma kewaye suka halarci zaman da aka yi.

Kafin wannan ganawa da Harisawan, Malam Maina ya yi wa dumbin jama’a da suka taru a babban masallacin Juma’a na Gombe wa’azi a matsayin goron salla.

Inda ya yi kira ga ’yan uwa da su kara jan damara ba wai su yi sako-sako ba. Ya ce alamar karbar azumi shi ne dorewa da ayyukan alheri. Ya kuma nemi jama’a da su kara yin riko ga Ahlul baiti (AS) don riko da su shi ne mafita, inda ya kawo hadisin Manzo (SAW) da suke magana a kan falalar yin rikon da Iyalan gidan Manzon Allah. “Manzon Allah ya ce; ‘na bar muku littafin Allah da makusantana.” Ya kara da cewa babu mafita a yau matukar ba gwagwarmaya mutum ya kama karkashin jagorancin Malam Ibraheem Zakzaky (H) ba.

Jama’a da dama ne suka saurari wa’azin wanda kuma mawakan gwagwarmaya suka karawa taron armashi, inda kowa ya tashi yana annashawa.

Majalisar jihar Sakkwato za ta bincike Bafarawa

Majalisar gwamnatin jihar Sakkwato ta kafa wani kwamiti na gaggawa na mutane bakwai wadanda za su yi wa Gwamnan jihar, Alhaji Attahiru Bafarawa bincike kan zargin halasta kudin haram, mallakar gidaje a birnin London da kuma cin dukiyar baitulmali ba tare da bin ka'ida ba.

Yayin da yake gabatar da jawabi a wajen kaddamar da kwamitin, mai magana da yawun Majalisar jihar Sakkwato, Alhaji Lawali Labbo ya bayyana cewa kwamitin zai yi bincike ne sannan ya ba da shawara kawai.

Ya ci gaba da nuna cewa babu yadda Majalisa za ta nade hannunta alhalin tana jin tuhumce-tuhumce masu girma irin wannan da ake yi wa Gwamnan jihar.

Shugaban kwamitin binciken, Ahmad Halliru Binji ya bayyana farin cikinsa na kafa kwamitin, sannan ya bayyana cewa za su yi bakin kokarinsu wajen aiwatar da wannan aiki kamar yadda ake bukata.

Sauran mambobin kwamitin sun hada da Bello Atto Gwaranyo, Aliyu B. Ibrahim, Umar Mode, Harande Tsamiya da Garba N. Sanda.

A ziyarar da kai Majalsair dai a kwanakin baya, bayan wasu jerin zarge-zarge da aka yi masa a wasu jaridun kasar nan, Gwamnan Attahiru Bafarawa ya bukaci Majalisar da ta bincike shi, ya kuma ce idan har aka same shi da laifi zai sauka daga mukaminsa.

Nijeriya dai ta yi suna kan cin hanci da almundahana tare da cin dukiyar baitul mali daga bangaren jami'an gwamnatocinta, inda ko a makon shekaran jiya ma sai da Majalisar dokokin jihar Bayelsa ta yi tsige Gwanmna jihar, Diepreye Solomom Peter Alamieyeseigha aka gurfaranar da shi a gaban kotu bayan ya tsero daga London inda ake tuhumarsa da laifin hallata kudaden haram.

An fara daidaita sahun mata a Kano

Daga Aliyu Saleh da Ali Kakaki

Hukumar A DAIDAITA SAHU da gwamnatin jihar Kano ta kafa ta fara daukar matakai a kan shigar rashin mutunci da mata suke yi a Kano, inda ta fara shirya tarukan fadakarwa, kara wa juna sani da kuma wayar da kan mata domin dawo da su kan hanya madaidaiciya.

A wajen wani taron fadakarwa da ta shiriya wa matan a ranar Lahadin nan da ta gabata a karkashin jagorancin matar Gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau, Hajiya Zainab Ibrahim a dakin taron na laburarin Murtala Muhammad da ke Kano, an nuna muhimmancin yin shigar da addinin Musulunci ya yi na’am da ita, tare da yin Allah wadai da shigar rashin mutunci.

A taron mai taken SUTURA-MUTUNCI, wanda aka watsa shi kai tsaye da gidajen rediyo da talabijin na jihar, ya kunshi jawabai nasihohi tambayoyi, da kuma faretin da mata suka yi cikin shigar Musulunci da Allah da Manzonsa suka yi umarci duk wata Musulma ta yi.

A lokacin da take jawabi a wajen taron, wata fitacciyar Malama mai wa’azi a Kano, Malam Maryam Abubakar Abba, ta nuna fa’idojin yin shigar mutunci da kuma illar da ke tatter da shigar rashin mutunci.

A kasidar tata mai shafuka 13, mai taken ‘Fa’idojin Suturar Mutunci da Illar Rashin Yin Ta, Malam Maryam Abba, ta yi tsokaci mai zurfi ga iyaye da su tashi tsaye wajen tilastawa ’ya’yasu yin shigar mutunci ko sa samu tsira a duniyarsu da lahirarsu. “Hakika shigar mutunci tana da alaka da addini da kuma al’ada, domin mun san cewa Musulunci shi ne ya umurci mace da ta suturce jikinta,” ta ce.

Malam Maryam Abba, ta bayyana cewa, saboda yadda mutanenmu suka tashi suka ga addinin Musulunci a idan suke, sai suka nemi mai da shiga mutunci wace ita ce Musulunci ya yarda da ita tamkar wata shiga ta al’ada, har suke yi mata fassara da sunan shigar al’ada. Ta ce, “na yi kokarin sauya kalmar mutunci zuwa Musulunci don a cikin Alkur’ani da Sunna akwai cikakken bayanin irin shigar da ya kamata ko ya wajaba Musulmi su yi da kuma fa’idar yin haka da illar rashin yin hakan.”

Malamar, ta bayyana abin da ake nufu da sututar mutunci, inda ta ce, “sutarar mutunci (ita ce wace) mace za ta yi ba tare da an ga wani abu na daga jikinta ba sai da larura.” Ta jawo hankali mazaje da su yi wa idanunsu linzami wajen kaffa-kaffa da kallon matan da Allah ya hane su su kalla, wadanda suke yawo a cikin gari ba tare da sun yi shigar mutunci ba, “idan mutace ta ki yin shigar mutunci, kai Allah bai yarda maka da ka kalle ta ba, face kallon farko wanda ido ya fara ba tare da niyya ba.”

Ita kuwa Dakta Fatima Batul Muktar, kira da ta yi ga mata da su shiga cikin taitayinsu wajen irin shigar da Musulunci ya yarje masu su rika yi. Ta yi kira ga iyaye da su rika kula da kai kawon ’ya’yansu, idan za su fita su tabbatar sun yi shigar mutunci kafin su fita daga cikin gidajensu. Ta dora alhakin yawancin shigar rashin mutuncin da mata ke yi a wuyan matan shugabannin da ake da su.

A nata jawabin, uwargidan Gwamnan Kano, Malama Zainab Ibrahim, cikin farin dogon hijibi, ta gode wa wadanda suka shirya wannan taron. Sannan ta tabbatar da cewa sai wadda imani ya rashi ne take iya yarda ta yi shigar da addinin Musulunci ya umurci Musulmi su yi. Ta yi kira ga mata da su guji buya bayan hijabi suna aikata alfasha, “idan kin sa hijibi a jikinki sai kuma ki sa a zuciyarki.”

Malamai da dama ciki har da Shaikh Ibrahim Khalil da kuma Dakta Bala Muhammad, Darakta-Janar na Hukumar A Daidaita Sahu ne suka yi jawabai masu ratsa zukata a wajen wannan taron wanda Hukumar ta ce za ta rika shirya makamancinsa a kai a kai don wayar da kan mata nauyin da ya hau kansu kafin su fita cikin al’aumma.

Jama’a da dama da muka zanta da su a wajen da kuma wadanda suka yi karin bayani a wajen wannan taron, wanda ya zo kwanaki biyar bayan fara aiki da dokar hana daukar mata a kan baburan acaba a duk fadin jihar Kano, sun bayyana jin dadinsu da yadda aka shirya shi. Sannan sun nemi gwamnati ta kafa wata dokar da za ta tilasta wa mata yin shigar da addinin Musulunci ya yarje masu su yi.

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


 Shafin Gamji | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International