Almizan :PDP na zargin gwamnatin Shekarau da jefa Sarkin Kano a siyasa ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 22 Zulkidah, 1426                 Bugu na 697                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Babban Labarinmu

PDP na zargin gwamnatin Shekarau da jefa Sarkin Kano a siyasa

Daga Ali Kakaki alikaki2001@yahoo.com


o.
i

   

Jam’iyyar PDP ta jihar Kano, ta nuna damuwa tare da zargin gwamnatin jihar Kano karkashin Malam Ibrahim Shekarau, Limamin A Daidaita Sahu da yaudar Sarkin Kano, Alhaji Dakta Ado Bayero har ta jefa shi cikin harkokin siyasar da ake yi a jihar.

Yayin da yake jawabi a yayin da ya ziyarci fadar Sarkin Kano, a kwanakin baya, Shugaban jam’iyar PDP na jihar Kano, Sanata Mas’ud Doguwa, ya bayyana cewa jam’yyarsu ta PDP sun lura da hikima da dabara ta gwamnatin jam’iyyar ANPP take yi na yaudarar wannan masarauta don yi musu kamfen na siyasa wanda a ra’ayin mafiya yawan jama’ar jihar nan sun nuna rashin gamsuwa da mafiya yawan tsare-tsare na tafiyar da gwamnatinsu.

Ya ce, “a fahimtarmu (PDP) wannan ya sa gwamnati ta shirya wa Mai Martaba zagaye na Kananan Hukumomi, wanda ta kira shi da suna daban-daban (A Daidaita Sahu) da fassarori kala-kala wadda ba su dace da manufofi da tarbiyyar wannan masarauta ba.”

Shugaban na PDP ya kara da cewa; “don haka muke rokon Ubanmu Sarkin Kano da ya duba wannan al’amari da wannan shiri da aka saka shi a kai (A Daidaita Sahu) domin duk manufofin siyasa ne, kuma dalilin siyasa ya sa aka shigar da Mai Martaba ciki, bayan kuma mun tabbata Mai Martaba Uba ne ga kowa.”

Mas’ud L. Doguwa ya ci gaba da cewa, “Allah ya taimaki Sarki, jam’iyyar PDP tana tabbatar maka da ci gaba da yi wa masarautar nan ladabi da biyayya domin samun tabbataccen zaman lafiya, mun tabbata Sarki Uba ne ga kowa, ya kuma dauki kowa dansa, yana kuma yi wa kowa adalci.”

Lokacin da yake mayar da jawabi ga korafe-korafen da ’ya’yan jam’iyar PDP suka yi masa, Sarkin Kano, alhaji Ado Bayero cewa ya yi, “ina kira ga dukkan ’yan jam’iyyu kowace irin jam’iyya ce, da Musulmi da Kirista bisa sharuda na addinanmu mu zauna lafiya da juna, kada siyasa ta bata tsakanin jama’a. Muna addu’a cewa Allah ya tabbatar da zaman lafiya a kasar nan.”

Haka zalika Sarkin ya ce, Shugabanci na Allah ne, Allah shi yake bai wa wanda ya ga dama, a yi kokari a dauka cewa shugabanci na Allah ne.

Sai dai kuma tun kafin wannan ziyara ta ’ya’yan PDP, ALMIZAN take jin bayanai iri-iri a bakuna daban-daban kan cewa wai gwamnatin jihar Kano ta ware wasu makudan kudade ga masarautar Kano domin ta kaddanar da wannan shiri na A Daidaita Sahu a Kananan Hukumomi 44 da ke fadin jiha.

Yanzu haka dai wannan ziyara ta ’ya’yan PDP ta haifar da cece-kuce tsakanin magoya bayan jam’iyyun biyu da ke jihar.

Duk iya kokarin da ALMIZAN ta yi domin ganin Kwamishinan yada labarai na jihar Kano, Dakta Tijjani Muhammad Naniya a kan wannan takaddama abin ya ci tura.

...Abin da ya sa muke goyon bayan shirin

“Kamar yadda muke ambatawa kullum, wannan shiri na A Daidaita Sahu muna goyon bayansa, kuma in Allah ya yarda za mu ci gaba da goyon bayansa. Muna gode wa Allah cewa burinmu ya soma cika domin an fara ganin abubuwan ban sha’awa daga rahotannin da muke samu daga Hakimai da Digatai da masu Unguwanninmu.”

Sarkin Kano, Alhaji Dakta Ado Bayero kenan a lokacin da yake jawabin kaddamar da shirin A daidaita Sahu na Karamar Hukumar Karaye a ranar Asabar din makon jiya ’yan kwanaki bayan ziyarar korafi kan yawon kaddamar da shirin da ’ya’yan PDP suka kai masa a fadarsa.

Sarkin na Kano ya ci gaba da cewa, “hakika wannan shiri na A Daidaita Sahu ya soma ratsa jini da tsoka na al’ummarmu, har ma da makwabtanmu; a bisa ga wannan dalili ne muka ga ya dace mu fito mu zagaya jama’armu a Kananan Hukumomi don kaddamar da kwamitin A Daidaita Sahu.”

Alhaji Ado Bayero ya kara da cewa, “wanan ziyara da muke yi ta dace da manufofin gwamnatin jihar Kano, wadda ta damu matuka da gyaran dabi’u na al’ummarmu.”

Haka kuma Sarkin ya ce, “kamar yadda muka sha ambatawa a baya, wannan jiha ta Kano madubi ce ga sauran jihohin Arewa har da sauran jihohin Nijeriya baki daya, saboda haka duk abin da Kano ta yi ku sani fa sauran jihohinmu na Arewa da ma sauran jihohi na kasar nan za su yi koyi da mu. Saboda haka wajibi ne jama’ar Kano mu fi kowa da’a da sanin ya kamata.”

Shi ma da yake nasa jawabin a madadin Gwamnan jihar Kano, Dakta Bashir Shehu Galadanci, mai bai wa Gwamna shawara a kan Alarammomi da Tsangayoyi na Allo da Makarantun Islamiyya, cewa ya yi shirin A Daidaita Sahu yana daga cikin manyan manufofin wannan gwamnatin, sannan yana tattare da kokarin gwamnati na tabbatar da shari’ar Musulunci a wannan jiha ta Kano.

Yanzu haka dai Sarkin Kano ya kaddamar da shirin a Kananan Hukumomin Dala, Gwale, Doguwa, T/Wada da kuma Garun Malam, Kura, Kumbotso, D/Kudu, Ajingi, Gaya, Kano Muncipal, Tarauni, Rogo da kuma Karaye, inda a kowace Karamar Hukuma yake nanata cewa, “muna goyon bayan shirin A Daidaita Sahu.”

Komawa babban shafinmu        Komawa saman wannan shafin


  | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International