Almizan :Editoci ku tsare gaskiya ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 22 Zulkidah, 1426                 Bugu na 697                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Babban Labarinmu

Editoci ku tsare gaskiya

In ji Gwamnan Bauci

Gwamnan jihar Bauchi, Alh. Adamu Mu’azu, ya hori Editocin kafafen watsa labaran kasar nan da su tsare gaskiya da adalci a yayin gudanar da ayyukansu.


Ya kuwa yi wannan tsokacin ne sa’ilin da yake jawabi ga taron shekara biyu-biyu na kungiyar Editocin da ake kira da Turanci Nigeria Guild of Editors, wanda aka yi a Bauchi ranar Litinin da Talatar nan da suka gabata.

“A yau a Nijeriya, ya zama al’ada ga jaridu da mujallu su buga labarin batanci ga shugabannin gwamnati ta hanyar amfani da karerayi, kirkire da zargi mara tushe da sauransu," Gwamnan yana mai kokawa ga Editocin.

Gwamna Adamu Mu’azu ya kara da cewa, “sau da dama kuma sai ka ga Jami’in Gwamnatin da aka ci wa mutunci ba a ba shi damar daidaita labarin ba. Wani abin takaicin wannan al’amarin ma shi ne cewa a yayin da labarin batanci ke samun muhimmanci a shafin farko don sayar da jaridar ko mujallar, sai ka ga hakIkanin bayanan da aka bayar da ke karyata batancin an sakala su a can wani wuri da ba kowa zai lura da shi ba kamar shafi na uku ko na bakwai.”

A nan sai Gwamnan ya katse takardar jawabin da yake karanta wa Editocin, ya ba da misali da labarin da wata mujalla ta buga, inda ta ce gwamnatin jihar ta kashe kudI Naira na gugar Naira har miliyan 800 don buga kalandu da sauran takardun kirgen kwanan wata.

Ya ce, “duk Editan da ya buga wannan labarin bai san aikinsa ba, ko kuma ya yi biris da ka’idojin aikin, don kuwa ya kamata ya tuntubi sashen gwamnati da abin ya shafa don ya ji ta bakinsu.”

Har ila yau Gwamnan ya ce sau da yawa sai ’yan jarida su ce wai ba su samu ganin wanda labarin ya shafa ba, “to me zai hana a dakatar da labarin har sai an ji ta bakinsa?” Gwamnan ya tambaya.

Daga nan kuma ya roki Editocin cewa su yi wa Allah da Annabinsa kar su raba Nijeriyar nan. A cewarsa daga take-taken da yake gani a jaridu, ana ta rura wutar hargitsa siyasar kasar nan ne.

Ya kuma ce, “ra’ayin jawo shugabanni kasa ko ta halin-kaka ya kai wani mikidari mai ban tsoro, wanda ke sa mutanen kwarai tsoron neman mukaman siyasa. Abin da muka tsammata daga wannan muhimmiyar sana’a taku shi ne sa ido da ba da rahotannin gaskiya cikin adalci.”

Da yake mai da martani, Shugaban kungiyar, wanda kuma aka sake zaben sa a karo na biyu, Malam Baba Halilu Dantiye, ya gode wa Gwamnan saboda samun damar halartar taron kungiyar da karbar bakuncin taron.

Daga nan ya tabbatar wa Gwamnan cewa kungiyar Editocin za ta rika sa ido sosai a kan membobinta, don ganin sun tsare ka’idojin aikin jarida da suka hada da tsare gaskiya da adalci a cikin labarai da rahotanni.

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


  | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International