> Almizan:Kisan gilla ga Yahudawa almara ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 22 Zulkidah, 1426                 Bugu na 697                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Babban Labarinmu

Kisan gillar Yahudawa a yakin duniya almara ce

In ji Shugaban kasar Iran

Shugaban kasar Iran, Dakta Ahmadinajad ya kammala wata ziyarar aiki ta tsawon kwanaki uku wace ya fara da garin Hamidan. A lokacin da yake gabatar da jawabi gaban dimbin al'ummar da suka tare shi a garin ya yi magana kan ayyukan raya yankin.


Haka nan kuma a wani bangare na jawabin nasa, Shugaba Ahmadinajad ya nuna matukar mamakinsa kan yadda Yahudawa suke yayata maganar kisan gillar da suke cewa an yi masu a lokacin yakin duniya na biyu, sannan kuma da yadda ba sa yarda kowa ya yi ‘munakasha’ cikin wannan lamarin.

Dakta Ahmadinajad ya ce, wannan ba shi ne zai kawo warware matsalarsu ba. Hanyar samun zaman lafiya shi ne kawai kamar yadda Jagora Ayatullah Khamnai ya bayyana cewa Palastinawa da ke sansanoni daban-daban na duniya su dawo kasarsu, sannan su gabatar da wata kuri'ar jin ra'ayi, inda za su zabar wa kansu abin da suke so.

Har ila yau Dakta Ahmadinajad ya sake nanata abin da ya fada a farkon makon shekaranjiya a kasar Saudiyya na cewa in dai da gaske Amurka da kawayenta na Turai suke yi, sun damu da halin da haramtacciyar kasar Isra'ila ke ciki to su yanki wani bangare na kasarsu, su ba ta don ta kafa kasarta. Kuma ya ce in har suka yi haka, to, Iran za ta yi shiru ta daina kalubalantarta.

Tuni dai kamar yadda aka saba har Amurka da ’yan korenta sun fara mai da martani kan wannan magana ta Ahmadinajad. Sauran al'ummar Musulmi da kasahensu kuwa, sai nuna farin cikinsu suke yi game da irin yadda a yanzu Dakta Ahmadinajad yake bayyana abin da suke so su fadi.

A wani labarin kuma, kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya shiga sahun kasashen duniya wajen yin tir da furucin da Shugaban Iran, Dakta Ahmadinejad ya yi na nuna kyamar Isra´ila. A cikin wani kuduri da ya zartar, kwamitin ya ce haramun ne wata membar kwamitin ta yi barazana ga ’yanci da wanzuwar wata kasa.

A kwanakin baya ne Shugaba Ahmadinejad ya kwatanta Isra´ila da wata cutar kansa, sannan ya ce kamata ya yi a mayar da kasar ta Bani Yahudu a wani yanki da ke tsakanin Jamus da Austria.

Hakazalika Shugaban ya yi suka da yadda ake ba da muhimmanci ga kisan kare dangi da gwamnatin Nazi ta yi wa Yahudawa a lokacin yakin duniya na biyu.

A halin da ake ciki ma’aikatun harkokin wajen biranen Berlin da Vienna sun ba da takardun sammaci ga jakadun Iran da ke kasashensu don nuna adawa da furucin na Shugaba Ahmadinejad.

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


  | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International