Almizan :Ku kara hakuri da ni kan yakin da nake yi a Iraki ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 22 Zulkidah, 1426                 Bugu na 697                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Babban Labarinmu


Ku kara hakuri da ni kan yakin da nake yi a Iraki

Gorge Bush yana rokon Amurkawa


Shugaban kasar Amurka, Gorge W. Bush ya kirayi al’ummar kasar da su kara karfin zuciya kan lamarin Iraki, sannan ya raya cewa ana ci gaba da samun nasara duk da yanayi mai wahala da sojojin kasar ke kara shiga wanda ba a yi tsammani ba.

Bush ya gabatar da wani jawabi ne daga ofishin Shugaban kasa da ake kira 'Oval office' a ranar Lahadin nan da ta gabata, inda yake kiran al’ummar kasar da su kara hakuri da shi kan yakin da ya ce yana yi na samarwa Iraki ’yanci.

Bush yace ba lallai ne yan Amurka su yadda da dukkanin abin da yake tunani ba amma dai yana son a akalla kada su sami karayar zuciya kan abin daya sa a gaba.

Duk da yake dai jawabin Bush a ofishin Oval abu ne da ba a saba gani yana yi a kodayaushe ba, amma daga watan Nuwamba wannan shi ne karo na biyar da Bush din ya yi irin wannan jawabin duka kan lamarin Iraki.

A cikin jawabin nasa, Bush, ya tabbatar da cewa an yi kura-kure wajen mamayar Iraki, sannan kuma ya nuna cewa akwai sauran jan aiki a gaba.

Masana na ganin cewa wannan kamar wani juyawa ne daga irin yadda Bush din ya saba yin magana cikin girman kai da halin tabbas, zuwa yanzu wani hali na rungumar kaddara da kuma fuskantar hakika.

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


  | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International