Almizan :Harisawan Kaduna sun samu yabo daga jama'a ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 22 Zulkidah, 1426                 Bugu na 697                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Babban Labarinmu

Harisawan Kaduna sun samu yabo daga jama'a


Daga Aliyu Saleh

Harisawan Kaduna sun samu yabo daga jama’ar garin sakamakon ayyukan taimakon jama’a da suke yi, da suka hada da gayaran makabartu, kwalabatoci da kuma hanyoyin da bololi suke neman kwace su daga jama’a.

Da muke zantawa da shi a ranar Asabar din nan, Alhaji Muhammad Sani Abdullahi T/Wada Kaduna, ya bayyana cewa, “mu dai ba mu da abin da za yi masu sai dai addu’a. Wallahi dare da rana muna yi wa wadannan mutanen addu’a, saboda tsakanin da Allah mu dai abubuwan da suke yi mana ba za mu ce komai ba sai dai mu ce Allah ya saka da alheri.”

Alhaji Muhammad Sani Abdullahi, wanda yake mahauci ne ya ci bayyana mana ra’ayinsa a gaban rumfarsa da ke kusa da titin Zango jikin Bashama cewa; “a gaskiya duk wanda yake zaune a T/Wada daga shekara 20-30 da suka wuce, ya san cewa akwai hanyoyin da mutane ba za iya wucewa a kasa ma balle a kan abin hawa, amma yau mun wayi gari sakamakon ba da lokaci da karfinsu da kuma abin da suka mallaka da wadannan mutane suka yi duk an gara mana hanyar.”

Ya ce, ka duba nan Layin Kosai, idan ka gangara wajen gadar Audu na Audu da ba ta biyowa, amma an wayi gari sakamakon aikin da mutanen nan suke yi da mota da masu tafiyar kasa suna wucewa ta wajen hankalinsu kwance. Ka duba hanyar Zango, hanyar da a toshe take, amma yanzu sun gyara mana ita. Ka duba makarba duk ranar Asabar sai sun je sun yi mana aiki. Akwai abin da ya fi wannan mu a rayuwarmu. Kai mu dai babu abin da za mu yi sai dai godiya. Allah ya saka masu.”

Alhaji Muhammad Sani Abdullahi ya yi kira ga al’ummar Musulmi kwata da su taimakawa Harisawan da kayan aiki, “tunda su sun sadaukar da lokacinsu, mu kuma mu taimaka masu da kayan aiki. Mu dai ba ma biyansu ko taro, don Allah suke yi mana wannan taimakon. Allah ya saka masu da alheri.”

Shi ma wani matashi, Anas Ibrahim Muhammad Garba da ke Layin Fulani T/Wada Kaduna, ya bayyana matukar gamsuwarsa da wannan aikin alherin da ake yi masu, “muna yi masu godiya sosai da sosai, gaskiya saboda Allah T/Wada akwai wuraren da ya kamata a ce gwamnti ta gyara su, amma sai wadannan mutanen duk da cewa su ba gwamnati bane, amma sun yi mana wannan aikin saboda Allah.”

Ya ci gaba da cewa, “Gaskiya mutanen nan suna yin abubuwansu yadda ya dace da addini, ba suna yin abubuwan da suke yi bane don neman wani abu daga wajen mutane ko gwamnati. Saboda haka muna yi masu godiya kwarai da gaske, kuma Allah ya saka masu da alheri.”

Shi kuwa Alhaji Musa Ibrahim Ali Ingawa da muka gan shi a bakin sana’arsa ya bayyana cewa, “game da wadannan mutanen da suke yi mana gyaran makabarta, gaskiya suna kokari dari bisa dari, kuma muna yi masu fatan alheri game da ayyukan da suke yi. Muna ba su goyon baya a kan abin da suke yi mana.”

Ya ce, tunda wannan wajen da suke gyarawa makwancin kowa ne, ya kamata sauran al’umma su ma su rika fitowa suna tafiya tare da Harisawan domin a yi wannan aikin tare, “domin ko ba kowai idan mutum ya fito aka yi wannan aikin da shi zai samu lada. Domin wajen da suke gyara duk makwancinmu ne.”

Shi kuwa Alhaji Muhammad Sani Jaggaba, 45, ya yaba da irin ayyukan da Harisawan suke yi ne, “domin wannan wajen da suke gyara ai duk gidan kowa ne. Duk inda muka ci kasuwar nan can za mu koma. Ya kamata gwamnati ta tashi tsaye ta taimakawa wadannan matasan da suke yin wannan aikin tsakaninsu da Allah.”

Malam Yakubu Muhammad, 30, ya ce, “gaskiya wadannan bayin Allah babu abin da za mu ce masu sai dai mu ce masu Allah ya saka da alheri.” Ya yi suka ga gwamnati da ta yi biris da kula da sauke da nauyin da ya hau kanta, abin da ya sa wadannan matasan suke yin wannan aikin, “mu dai mun zabe su ne domin su yi mana aiki, amma zaluncin da suke yi mana ya yi yawa. Ya kamata shugabanni su san cewa da mulkin nan da kuma duniyar nan za a bar ta fa.”

Da muke zantawa da shi a makabarta, Malam Aliyu Bakin Ruwa, ya bayyana mana cewa su dai wadannan aikice-aikicen da suke yi suna sauke wajibin da ya hau kansu ne, sakamakon umarnin yin hakan da Malaminsu, Malam Ibraheem Zakzaky ya ba su a lokacin da suka yi bukukuwan cikarsu shekaru 10 da kafuwa. “Don haka muna yin wannan aikin ne domin cika umarnin da Malam Zakzaky ya ba mu, ta haka sai mu samu yardar Allah da muke nema.”

Da al’ama dai wannan aikin da aka fara shi tun daga 2000 yana yi wa jama’a tasiri, ya kuma kara dangon zumunci tsakanin Harisawan da al’ummar da suke rayuwa a cikinsu, wannan ne ma ya sa, kamar yadda Malam Aliyu yake shaida mana jama’a suke sayan kayan aiki suke ba su domin su ji dadin gudanar da wannan aikin alherin da suka faro, “ka ga kayan aikin nan duk jama’a ne suka saya suka ba mu don mu ji dadin gudanar da wannan aikin da muke yi.

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


  | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International