Jarida don Karuwar Musulmi
Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki ISSN 1595-4471
Juma'a 10 Shawwal, 1426
Bugu na 691
Tunatarwa | | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari Tattaunawa | Labarai |
Amerika da kawayenta
Sun firgita!
|
Sai dai abincin wani gubar wani, wannan magana ta Shugaban Iran din ta firgita Amerika da 'yan kanzanginta, domin kowannensu a rude suke suna ganin kamar Iran na neman ta hallaka su kenan. Gidan talbijin na BBCWORLD ya nuno Firayin Minista na kasr Birtaniya, Mista Tony Blair yana cewa " a ce wani Shugaban wata kasa ya fito ya furta cewa za su share wata kasa. Wannan wani abu ne da ba za a amince da shi ba." Haka kuma ita ma mai magana da yawun Shugaban kasar Amurka, Sakatariyar harkokin waje ta Amerikan, Misis Condoleeza Rice, tun lokacin da Ahamadinajad ya yi wadannan kalamai, duk wanda ya gan ta zai gan ta a firgice tana nuna cewa wadannan kalamai na Shugaban ba su dace ba, kuma su ba za su kyale ba. Shi kuwa Shugaban haramtacciyar kasar Isra'ila, Ariel Sharon, kira ya yi ga Majalisar dinkin da ta kori kasar Iran din daga Majalisar tare da sanya mata takunkumi. Manazarta na ganin wadannan kalamai na Shugabannin Turai ta yamma na kara nunawa a fili cewa dukkansu suna karkashin Yahudawan ne, bilhasali ma Yahudawan ne ke juya su, shi ya sa ma ba su taba yin tir da kisan gillan da Shugaban kasar Isra'ila yake yi wa Palasdinawa ba. Domin duk wanda ya yi nazarin jawaban Ahmadinajadi zai gane cewa shi fa ya dirar wa Yahudu ne, amma sai ga shi su wadannan ne suka fito suna ta babatu a kan lamarin, domin an taba Uwargijiyarsu, Isra'ila. Kuma ga duk mai bin al'amuran yau da kullum zai fahimci cewa su wadannan kasashe na Amerika suna neman wata hanaya ce wacce ta halasta masu su kai hari a Kasar ta Iran. Wannan kuwa za a iya amincewa da haka in aka yi la'akari da yadda suka matsa wa kasar a kan batun makamashin Nukilya wanda dukkansu sun mallaka, amma suna ganin bai kamata ita Iran ta mallake shi ba. Wadannan kalamai dai da Shugaba Ahmadinajad ya yi sune cewa tabbas za a ci gaba da gwagwarmaya da Yahudawa 'yan mamaya har sai an kawar da Haramtacciyar gwamnatin Isra'ila daga baki dayan Palasdinu. Mahmood Ahmadinajad ya fadi haka ne yayin da yake gabatar da wani jawabi a taron da aka yi wa take da 'Duniya ba tare da Yahudawan Sahayoniya ba,' wanda aka gabatar a ranar Larabar makon shekaranjiya a Tehran babban birnin kasar ta Iran. Ahmadinajad, har ila yau, ya kara nuni da cewa shirin yaudara da haramtacciyar kasar Isra'ila ta fito da shi na janyewa daga yankin Gazza don ta nema wa kanta halascin ci gaba da zama a inda ta mamaye bai rudar al'ummar musulmi ba, domin kuwa kowa ya san Yahudawa 'yan mamaya ne, kuma wajibi ne su fita daga Palasdinu gaba daya. Shugaba Ahmadinajad ya ci gaba da nuna cewa a yanzu Yahudawan Sahayoniya suna son su ga cewa sun lalata wannan hadin kan da ke tsakanin Palasdinu ta hanyar shigo da yaudara, saboda haka ya yi kira ga al'ummar kasar da su kasance masu taka-tsantsan don kada su fada tarkon makiya. Haka nan kuma a lokacin jawabin nasa, Shugaban kasar ta Iran ya tabo hakkin Palasdinawa na cewa wajibi a kai lokacin da za su gudanar da zabe 'yantacce a kasarsu inda za su zabi tsarin da suke so da kuma Shugaban da zai jagorance su da kansu. Wannan taro dai ya sami halartar wakilai daga kungiyoyin gwagwarmaya na Palasdinu daban-daban da kuma wasu daga cikin manyan jami'an gwamnatin kasar Iran da sauran jama'a. Daga bisani bayan da Yahudawan suka rude suka fara mayar da martani ga Shugaban nan Iran, Shugaban ya kara fitowa fili ya sake tabbatar da wadancan kalamai nasa, inda ya nuna shi fa gaskiya ya fada kuma tana nan zaunanniya. Haka kuma a wani kaulin na Shugaba Najadi ya nuna cewa wadannan kalamai nasa tamkar kalaman al'ummar kasar Iran ne. Ya kuma ce Turawan Yamma suna da damar fadin abin da suka ga dama, amma surutansu duk na banza ne. A wani abu mai alaka da wannan, dubun-dubatar Iraniyawan ne suka fito tituna a makon da aka gabatar da Ranar Kudus ta duniya, wato ranar Juma'ar karshe ta Ramadan da ta gabata, suka fito tituna suna nuna goyon bayansu ga Palasdinawan. A wannan gagarumar Muzahara da suka gabatar, Iraniyawan sun rinka tafiya da daga kwalaye tare da furta kalaman la'anta ga Isra'ila da Amerika, suna cewa "Mutuwa ga Isra'ila, Mutuwa ga Yadudanci, mutuwa ga Amerika." Sannan suka rinka tafiya suna jan tutar Isra'ila a kasa, sannan daga bisani suka banka mata wuta. Komawa babban shafinmu Komawa saman wannan shafin
| |
| Tafsirin Alkur'ani | Hadisai | Crescent International
| Tafsirin Alkur'ani | Hadisai | Crescent International
|