Almizan : A Takaice kai Tsaye: Na M.M Awwal, Ta GSM,0803 451 4691 ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 10 Shawwal, 1426                 Bugu na 691                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
A Takaice kai Tsaye: Na M.M Awwal, Ta GSM,0803 451 4631

INA MALAM BABAYO MUSA?

Malam Babayo Musa Jos NNPC Depot Makurdi, na ji kana cewa ku IZALATUL BIDI'A WA IKAMATUS SUNNA ce jirgin tsiranku, amma na ga a jikin jirgin da ka ce ba ruwanka da shi, akwai kalmar La'ilaha illallahu Muhammadur Rasulullahi a kansa. To naka jirgin tsiran, wace kalma ce a kansa? Kuma ai ga shi nan ma an rusa naka jirgin tsiran. To ya kamata ka zo ka hau wanda yake babu wanda ya isa ya rusa shi.

Daga Mustafa Usman Kaduna 0803 637 6252

MALAMAN FADA ALLAH YA ISA!

Ba kowa ne ya jefa kasar nan a cikin kangin da take ciki ba sai Malaman fada. Gaskiya kun ci amanar Shehu Danfodiyo. Mu dai Allah ya isa!

Daga Bashir Ustaz Unguwar Kanawa Minna jihar Neja 0802 787 1944

EDITA INA NEMAN KARIN BAYANI

Assalamu alaikum. Edita ina neman karin bayani game ga jawabin watan Ramadan da kuka sa a makonni hudu da suka gabata. Shin jawabin na bana ne, ko kuwa?

Daga Yusuf Mai Gyran Rediyo Bici jihar Kano 0803 637 1635

Malam Yusuf ba mu sa jawabin Ramadan ba, sai dai mun sa hudubar Manzon Allah da ya yi shekaru fiye da 1400 da suka gabata a kan Ramadan. Amma in kana maganar bayanin da Malam Zakzaky ya yi ne kan azumin Ramadan, to wannan ya yi shi ne bayan ya ida tafsir a Larabar karshe kafin Ramadanan bana. -Editan shafi.

HABA SHAIKH DAHIRU USMAN BAUCI!

Assalamu alaikum. Shaikh Dahiru Bauci ka san fa kai Shehi ne, ya kamata ka ji tsoron Allah ka daina zigzag da kalankuwa a kan cancantar khalifancin Imam Ali (AS) da sauran Sahabbai. Don na ji a tafsirinka na ran 21 ga watan Ramadan 1426 kana ta waskiya, alhali ka san komai.

Daga Adamu Zawal 0803 538 7890

INA ABOKINA HORSE POWER?

Assalamu alaikum. Ina abokina Muhammad Horse Power, ALMIZAN ba ta aiki da jita-jita, idan da gaske ne ba ka sani ba, Allah ya ganar da kai.

Daga 0806 532 2274

BUHARI DA GOWON KUN BA NI KUNYA

Gaskiya tsaffin Shugabannin kasar nan, Janar Muhmmad Buhari, da Janar Yakubu Gowon, kun ba ni kunya, da kuka kwashi jiki ku kai wa Obasanjo gaisuwar ta'aziyyar rasuwar matarsa, Stella da mutu a Sifen, amma ba ku ce komai ba game da mutane 117 da suka rasu a hatsarin jirgin saman 'Bellview' da aka yi a garin Lisa.

Daga Abdullahi Mai Turare Bauci

INA GAI DA JAGORANA

Assalamu alaikum. Ku mika min gaisuwata ga Shaikh Ibraheem Zakzaky (H). Allah ya ja zamanin Malam, amin.

Daga Safiyanu Aliyu Tanko 0803 538 7890

SHEKARAU KWANANKA NAWA?

Assalamu alaikum. Haba Shekarau kwananka nawa? Saura kwana nawa ka sauka? Da me za ka je wa Allah idan ka yi fada da shi? Ya kamata dai ka sani ba a fada da Allah a ci riba!

Daga Tahir Ibrahim T/Wada Zariya 0806 532 2274

ALLAH YA JA ZAMANIN ALMIZAN

Assalamu alaikum. Allah ya ja zamanin ALMIZAN. Allah ya saka maku da alherinsa. Mu kam a Adamawa kowane mako muna samun ALMIZAN.

Daga Abubakar AMB Yola 0803 451 4631

GWAMNAN ZAMFARA YAYA DAI?

Assalamu alaikum. Gwamnan Zamfara, Alhaji Ahmad Sani yaya dai, don na ga da wuya ka share sati biyu ba ka fita kasashen waje ba, amma sai na ji yanzu ka daina fita, ko dai kana jin tsoron irin abin da ya faru ga Gwamnan Bayelsa kada ya faru gare ka ne?

Daga Shehu Kaurar Namoda jihar Zamfara, mazaunin Kormo Abuja 0804 337 3137

MUTUWAR STELLA OBASANJO MA AYA CE

Zuwa ga 'yan uwa Musulmi na Nijeriya, musamman masu kokarin yin fada da Harkar Musulunci a Nijeriya karkashin jagorancin Malam Ibraheem Zakzaky, don giyar dimokradiyya tana kwasar ku, ya kamata dai ku sani Stella Obasanjo ta fi ku shan giyar dimokradiyya, amma yanzu ina take? Hattara dai musulmi! Don haka mutuwar Stella aya ce.

Daga Aliyu Musa, Ali Yamalti 0803 678 8569

INA YI WA MALAM ZAKZAKY FATAN ALHERI

Assalamu alaikum. Ina fatan alheri ga Malam Zakzaky, saboda kokarin da yake yi na fadakar da al'ummar musulmi kan abubuwan ya kamata su yi. Ina fatan an yi muzaharar Kudus lafiya. In Allah ya so kwanan nan zan kawo wa Malam Zakzkay ziyara.

Daga Nasiru Ibrahim Shehizzaman Jagoran Palasdinawa Koki Kano 0802 358 9589

ALLAH YA JI KAN MUSULMIN DA SUKA RASU A PAKISTAN

Assalamu alaikum. Girgizar kasar da aka yi a kudancin Asiya babbar musiba ce a duniya. Allah ya ji kan musulmin da suka rasu. Mu kuma Allah ya kare mu

Daga 0806 541 8587

INA MUSULMIN NIJERIYA?

Assalamu alaikum. Musulmin Nijeriya ya rage naku! Kusan shekaru bakwai kenan ana dimokradiyya da sunan za a gyara barnar da soja suka yi. To yanzu wane sauyi aka samu? Ya kamata dai mu sani cewa wallahi adalci da sauyi na alheri yana cikin kiran Malam Ibraheem Zakzaky. Mai rabon shan romo a duniya da lahira shi ne zai shigo cikin da'awar Malam Zakzaky (H) a yi gwagwarmaya da shi.

Daga Muhammad Aruwa K/Guga Katsina 0803 692 0810

MU SIFFANTU DA KYAWAWAN DABI'U

Sanin kowa ne cewa daya daga cikin abubuwan da suka kawo yaduwar Musulunci da ci gabansa shi ne kyakkyawar dabi'a ta Manzon Allah (S). Wannan ya tabbata a cikin Alkur'ani, inda Allah yake cewa, "Da ka kasance mai fushi mai kaushin zuciya da sun watse daga gefenka." Don haka mu ma a yau in har muna so mutane su fahimce mu, ya zama wajibi a kanmu mu nuna musu kyawawan halaye da dabi'u na gari. Imam Ja'afar (AS) yana cewa; "kirki da kyawawan dabi'u suna kawo walwala da nisan kwana." Don haka yana da kyau a gare mu mu siffantu da kyawawan dabi'u.

Daga Salisu Mika'ilu Birnin Kudu (saintmanager@yahoo.com)

SHAWARATA GA LIMAMIN A DAIDAITA SAHU

Asslamu alaikum. Ni dai shawarata ga Limamin A Daidaita Sahu a nan ita ce, ya kamata ya yi waiwaye ya duba abin da ya faru ga magabatansa wadanda suka yi yinkurin ganin bayan 'yan uwa musulmi da suke kira da 'yan Shi'a a Kano. Domin ba ta yi musu da kyau ba. Ya kamata ya duba Limamin ta-zarce, Limamin guguwa bala'i, da Gwamnan da ya gabace shi, Kwankwaso. Dukkansu zai ga yadda kwangilarsu ta kaya.

Daga Musa El-Husain (musahsn@yahoo.com)

OBASANJO DA ATIKU SU HADIYE JUNANSU MANA

In Obasanjo da Atiku ba sa jituwa sai me ya faru? Su hadiye junansu mana, in da gaske ne. Ba kulob daya suke ba? Allah Ya raba mu da shirme!

Daga Adamu Zawal 0803 538 7890

INA MASU SHIRIN AUKA WA 'YAN UWA?

Assalamu alaikum. Ina masu shirin auka wa 'yan uwa da sunan Daidaita Sahu? Ku sake shiri don mu mun san a matsayinmu na masu fafutikar dawo da martabar addini dole ne za mu fuskanci matsaloli daga bangaren makiya Allah. Amma wannan ba zai hana mu aikata namu bangaren ba, don dama sunna ta riga ta gabata a haka. Sannan ba kuma za mu iya gane ko su waye a daya bangaren ba har sai sun fito sun bayyanar da kansu.

Daga Prof Nomagic (profnomagic@yahoo.com)

GWAMNA KURE KA BIYA MU HAKKINMU

Gwamnan jihar Neja, Alhaji Abdulkadir Kure ka ji tsoron Allah kamar yadda kake riya kana yin shari'ar Musulunci a wannan jihar, ka yi kokarin bai wa ma'aikata hakkokinsu. Ka kuma taimaka ka biya su albashi kamar yadda sauran jihohi suke biya. Saboda abin da ake biyan su yanzu ba ya isar su tafiyar da rayuwarsu.

Daga Masu Kishin Suleja jihar Neja (marininvest2000@yahoo.com)

YARIMA RASHIN RUWA YA YI TSANANI A GUSAU

Assalamu alaikum. Don Allah Gwamnan jihar Zamfara, Alhaji Ahmad Sani, ka tausaya wa musulmi albarkacin wannan watan, domin rashin ruwan sha ya yi tsanani a garin Gusau da kewaye. Ka ba Dagutunka, Mista Italco dama, ya sako mana ruwa.

Daga Dansani Bakura, (dansanibakura@yahoo.com)

ALMIZAN NI MA NA BUDE I-MEL DINA

Assalamu alaikum. Dalilin da ya sa na turo muku wannan sakon shi ne don in jinjina muku da kuma in sanar da ku cewa ni ma na bude I-mel dina sabo. Don haka zan ci gaba da hulda da ku kamar yadda sauran masu hulda da ku ke yi in har Edita ya amince da haka.

Daga Al-Mustapha Abdulmumini Magaba Karamar Hukumar Funakaye jihar Gombe (charmingaccurate@yahoo.co.uk)

Malam Mustapha muna jiran ji daga gare ka.

-Editan shafi

HABA BUKAR ABBA IBRAHIM

Assalamu alaikum. To Gwamnan jihar Yobe, Alhaji Bukar Abba Ibrahim, ka yi mulki a jihar Yobe har sau uku ba ka tsinana mana komai ba, amma yanzu mun ga fastocinka a matsayin kana neman Shugaban kasa a 2007. Ka sani karya kake yi, kujerar Shugaban kasa ta fi karfinka, sai dai ka koma ka ci abin da ka tara.

Daga 0803 970 3978

MUNA GOYON BAYAN AHMADI NAJAD

Assalamu alaikum. Muna goyon bayan kalaman da Shugaban kasar Iran, Dakta Ahmadi Najad ya yi a kan haramtaciyyar kasar Isra'ila. Dakta Najad kar ka damu Allah yana bayan mai gaskiya.

Daga Salisu Potiskum jihar Yobe 0804 226 3254

NUHU RIBADO YAYA MUKA JI SHIRU?

Nuhu Ribado yaya muka ji shiru ne? Ina maganar binciken da ka ce Hukumarka ta EFCC za ka yi a kan Obasanjo? To ya kamata dai ka san cewa a lokacin Obasanjo mai kaki ne da 'Yar'aduwa aka fara sata a Nijeriya.

Daga Adamu Zarto Kusfa Zariya jihar Kaduna 0802 833 7498

INA MUSTAFA GADON KAYA YA KOMA NE?

Assalamu alaikum. Wai don Allah ina Alhaji Mustafa Umar Baba Gadon Kaya ya shige ne? Ko ya tashi daga Kano ne? Na kwashi lokaci mai tsawo ban gan shi a wajen wani taro da ake yi a Kano ba. Wai don Allah in ba ya Kano yanzu ina ya koma? Don ni gaskiya ina son wakokinsa.

Daga Ado NEPA Kofar Wambai Kano 0802 437 9973

GARE KU 'YAN WASAN HAUSA

Assalamu alaikum. Nasihata ga 'yan wasan kwaikwayo na Hausa ita ce, yada addinin Musulunci shi ya fi masu a kan neman kudi da kuma yada al'ada.

Daga M.G. Hamman Yola jihar Adamawa 0804 318 4034

MA'AIKATAN ALMIZAN BA MA'ASUMAI BANE

Assalamu alaikum. Malam Adamu ka san cewa ma'aikatan ALMIZAN ba ma'asumai bane, za su iya yin sabo, balle kuma kuskure? Bai kamata don ka samu kuskure a ALMIZAN ka kira ma'aikatan makaryata ba, bayan kuma ba ka nemi uzirinsu ba. Don Allah ka daina cin mutununcin mutane, ka ji. Ai mu da ALMIZAN da ma'aikatanta sai addu'a da fatan Allah ya kare su daga sharrin masu sharri, amin.

Daga Muhammad Aruwa Kofar Goga Katsina 0803 692 0810

SAI AN SHARE YAHUDAWA ZA A SAMU ZAMAN LAFIYA

Assalamu alaikum. Gaskiya ina goyon bayan Shugaban kasar Iran, Dakta Ahmadi Najad kan a share Yahudawa daga doron kasa. Domin zaman lafiyar duniya ba zai samu ba, sai in ba Yahudawa. Kuma za mu ba da gudummawarmu wajen hakakkar da wannan burin a karkashin jagorancin Malauna Sharafuddini Malam Ibraheem Zakzaky (H), Allah ya kara masa lafiya.

Daga Muhammad Mai Sobo Katsina 0802 559 4697

ALLAH YA JI KAN MUSULMIN DA SUKA RASU

Assalamu alaikum. Allah ya ji kan musulmin da suka rasu a cikin hatsarin jirgin saman 'Bellview' amin.

Daga Ibrahim Suleja jihar Neja 0806 549 4863

'YAN SALAFIYYA BA DA KU MUKE BA

Assalamu alaikum. 'Yan Salafiyya ba da ku muke ba, mu da gwamnatin kafirci muke yi, kuma insha Allah za mu yi nasara a kanta.

Daga Dauda Mai Leda Kaduna 0803 287 3662

NA CIKIN JIRGIN NAN SUN GA TASHIN HANKALI

Assalamu alaikum. Babban tashin hankali ne a ce kana cikin jirgin sama ya kama da wuta da kai a sama, ko kuma ya fado. Allah ya kiyaye gaba, ya ji kan musulmin da suka rasu a hatsarin jirgin saman 'Bellview.'

Daga Awwal Z.M Ayagi Azamiyya 0806 541 8587

AHMADI NAJADI KA CANCANCI YABO

Assalamu alaikum. Ina jinjina ta musamman ga Shugaban kasar Iran, Dakta Ahmadi Najad, saboda kalaman da ya yi na cewa ya kamata a shafe Isra'ila daga doron kasa.

Daga Danjuma Ado Yola jihar Adamawa 0802 525 3218

KUN SAN HALIN DA JOKOLO KE CIKI KUWA?

Assalamu alaikum. Sarakunan Arewa, kun san halin da tsohon Sarkin Gwandu, Alhaji Mustafa Haruna Jokolo ke ciki kuwa? Ku tuna fa a dalilinku ya shiga wannan halin da yake ciki.

Daga Adamu Zarto Kusfa Zariya jihar Kaduna 0802 833 7498

KU DAINA TAYAR DA JIJIYAR WUYA

Kasashen Turai ku daina tayar da jijiyar wuya saboda haramtacciyar kasar Isra'ila don kuwa wata rana za ta rushe.

Daga Muhammad Bello Maiduniya Lafiya jihar Nassarawa 0806 245 0055

OBASANJO KA FARA GANI KENAN

Obasanjo ka fara gani kenan. Ka ga irin mutuwar da azzalumai ke yi.

Daga Abubakar U/Sunusi Kaduna 0802 881 1123

MUNA TARE DA AL'UMMAR IRAN

Assalamu alaikum. Shin wai don Allah menene bambanci tsakanin maganar da Dakta Ahmadi Najad ya yi na cewa a share haramtaciyyar kasar Isara'ila daga taswirar duniya da kuma barazanar da Amurka ke yi a kullum a kan shirin nukiliyar Iran? Ko dai don saboda haramtaciyyar kasar Isra'ila 'yar lele ce? To mu dai muna tare da al'ummar Iran.

Daga Bilyaminu Kiru jihar Kano 0806 566 6555

INA YI MAKU BARKA DA SALLA

Assalamu alaikum. Ina yi maku barka da salla da sauran al'ummar musulmin duniya. Allah ya maimaita mana, amin.

Daga Yaluna U/Mu'azu Kaduna 0803 588 1599

KU HADA KAI MUTANEN IRAKI

Haba mutanen Iraki hada kai ya kamata ku yi ku kori Amurka da kwayenta daga kasarku, ba gwagwarmyar neman mulki ba.

Daga Usman Abubakar Jauro Gombe 0805 914 7801

MALAMAN NIJERIYA KADA WURI YA KURE MAKU

Malam Nijeriya kada fa wuri ya kure maku. Ku yi bayani game da juyayin masallacin Kudus. Ko kuwa dai shi ma masallacin na 'yan Shi'a ne? Ko kuma su ma Palastinawan 'yan Shi'a ne? To ku sani komai dadewa gaskiya za ta bayyana.

Daga Muhammad Aruwa Kofar Guga Katsina 0803 692 0810

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


 Shafin Gamji | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International