Jarida don Karuwar Musulmi
Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki ISSN 1595-4471
Juma'a 10 Shawwal, 1426
Bugu na 691
Tunatarwa | | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari Tattaunawa | Labarai |
Kasar Iraki:Fagen jihadi ko dandalin wasan kwaikwayon siyasa (4)?
Daga Mujtaba Adam Tehran, Iran, (nigeria3000@yahoo.com)
Me kasar Saudiyya za cewa faduwar mutum-mutumin Saddam Husain a bakin Hotel din Palasdinu ranar da sojojin Amurka suka shiga birnin Bagadaza? (wanda kafafen watsa labarun duniya suka nuna). Haka yana nufin faduwar nasu mutum-mutumin da ya dade yana yi wa al'ummar musulmi dodorido ne? Sarakunan kasar Saudiyya ba su zaci cewa mahaukaciyar guguwar siyasa mai karfi wacce ta fi ta Katrina na nan tafe ba bayan faduwar Maigadin kofar gabas -Harisu Bawwabatul-Sharqiyya- kamar yadda suke kiran Saddam Husaini. Saboda yana fada da Parisawa! Kamar yadda mahaukaciyar guguwar Katrina ta yaye fuskar Amurka ta nuna wa duniya cewa har yanzu bambancin launin fata bai kau ba, haka nan guguwar da ke kada wa a Iraki za ta yayewa kasar Saudiyya zani a kasuwa. Idan ma har ba ta riga ta yaye ba. Ministan harkokin cikin gidan Iraki, Jabir Alzubaidy da ya mai da wa Sa'ud Al-Faisal martani ya fadi wani bangare na gaskiya da ya ce: "Da akwai wata kasa guda sukutum wacce sunanta na iyalai daya ne. Ba mu son mu fadada magana a kan haka, amma muna sane da cewa da kawai 'yan Shi'a miliyan hudu a kasar Saudiyya wadanda ake mu'amala da su a matsayin 'yan kasa masu daraja ta uku. Da 'yan Isma'iliyya miliyan daya da ake mu'amala da su a matsayin 'yan kasa masu daraja ta hudu. Amma duk da haka ba mu son tsoma baki a cikin harkokin cikin gidan Saudiyya. Su fara bai wa mata 'yancin tukin mota tukunna a matsayin matakin farko na bai wa mata 'yancin da muke da shi a kasar Iraki!" Jaridar Alquds 3/10/2005. Wani dalilin da ke sa Saudiyya ke kin yin Allah wadai da ayyukan ta'addanci a Iraki ba zai rasa alaka da abin da jaridun kasarta ke bugawa ba. Ga karin haske a kan haka. Jaridar ALWATAN ta Saudiyyar ta buga labari a ranar 3/10/2005 kamar haka: "Jaridar ALWATAN ta sami labari daga wata majiya ta musamman cewa jami'an tsaron kasar Syriya sun mika wani saurayi dan kasar Saudiyya da yake kokarin shiga cikin kasar Iraki ga ofishin jakadancin Saudiyya da ke Damascus. Da akwai tabbacin cewa mahukuntan kasar Syriya sun mika wa Saudiya wasu 'yan kasa biyu da su ma suke kokarin yin kutse zuwa kasar Iraki ta hanyar Syriya. Da akwai alaka a tsakanin kasashen biyu ta bangaren tsaro ta yadda jami'an Saudiyya ke zuwa domin su karbi 'yan kasarta masu yin kutse." Jaridar ALMADINAH mallakin Saudiyya ta ranar 3/19/2000 ta buga hirar da ta yi da Ministan harkokin wajen Iraki Hoshyar Zibary, wacce a ciki ya fadi cewa: "Da akwai 'yan kasar Saudiyya 100 da ake tsare da su a gidajen kurkukun Iraki. Dukkansu sun shiga cikin kasar ne da zimmar shiga Kungiyar Alka'ida." Ko kuma rahoton kungiyar leken asirin SAUDIYYA-MUKHABARAT da yake cewa: "Da akwai 'yan kasar 350 da suka shiga Iraki wadanda sune kaso 12 na dukkan 'yan kasashen waje da ke yaki a Iraki. Mutane 53 daga cikinsu sun mutu wajen kai hare-hare." www.alhaqaeq.net. Ko rahoton da jaridar ALHAYAT mallakin Saudiyya da ake bugawa a London, wanda ke cewa: "Wata majiya mai karfi ta tabbatar da cewa wasu mutane 15 'yan kabila daya sun kutsa cikin Iraki ta hanyar kasashen makwabta. Labarin wasu daga cikinsu ya iske iyalansu cewa sun mutu. Wasu kuwa ba a san makomarsu ba." www.daralalhayat.net. Wannan adadin na 'yan kasar Saudiyya masu kai kunar bakin wake a kan fararen hular Iraki ne ya sa Abdurrahman Rashid ya rubuta kasida mai taken SHIN ADADIN MUTANE 300 KADAN NE? Ya kuma ci gaba da yin wasu tambayoyin kamar haka: "Ya aka yi aka dauki wannan adadin mai yawa na 'yan kasar Saudiyya da Masar da Jordan da Lebanon da Sudan da sauran kasashen Larabawa saboda su zama masu kisa da barna a kasar Iraki? Wadanda suka dauki wadannan mutanen da shigar da su cikin Iraki suna da ikon su dauki kamarsu saboda su rusa al'ummarsu. A hakikanin gaskiya wadannan mayakan ba su kadai bane abin tsoro, da ko shakka babu matsala ce ga al'umma idan ba yau ba, to gobe. Babban abin tsoro shi ne tunanin da ke samar da irin wadannan mutanen da daukar su a matsayin mayaka." www.ahli.iraq.com. Zainul Abidin Al-Rikaby a cikin kasidarsa da jaridar SHARQUL AUSAT ta buga a ranar 30 ga watan Yuli 2005 ya gano bakin zaren ayyukan ta'addanci da ya ce: "Duk wani aikin laifi da ke faruwa a doron kasa, to sai an fara shirya shi a cikin kwakwalwa kafin a zartar da shi. Tunanin aikata ta'addanci yana farawa ne a cikin kwakwalwa kafin motoci masu makare da bama-bamai da mutane masu kai harin kunar bakin wake su kai harin. Saboda haka duk yadda aka yi kokarin gano dalilin ayyukan yin amfani da karfi da ta'addanci, to, dalilinsa daya ne, shi ne; tunani." Idan har Saudiyya za ta yi furuci da cewa da akwai ayyukan ta'addanci a Iraki, to, dele ne ta yi furuci da cewa 'yan kasarta ne suka fi yawa wajen kashe fararen hula. Idan kuwa ta yi furuci da haka, to, dole ne ta sa katuwar alamar tambaya a kan tunanin da ake cusa musu a makarantu da kuma masallatai. Da akwai alamar tambaya mai girman gaske a kan duk wani abu da yake da alaka da tarbiyya a wannan masarauta ta zuriyar Sa'ud, wacce daga nan ne mutane 15 daga cikin 19 da suka kai harin 11 ga watan Satumba suka fito. Tarihi shi ne shaida cewa babu wata mazhaba kwaya daya ta Musulunci, wacce ta kafu da karfin takobi in ba Wahabiyancin mutanen Najadu ba. Babu wata mazhaba kwaya daya ta musulmi da ba ta furuci da 'yar uwarta a matsayin musulma, idan ba mazhabar gwamnatin Saudiyya ba. Su kadai ne ke yi wa kawunansu kallon Annabawan da Allah Ya aiko a karni na 18 saboda su kawar da bidi'a da shirka da kafirci a tsakanin musulmi! Idan babu kira me ya ci gawayi? Idan babu wankin kwakwale da sunan addini, me zai sa wannan adadin mai yawa na 'yan kasar Saudiyya su rika kashe musulmi a kasar Iraki? Su rika tarwatsa kawunansu a tsakanin masu salla da rusa masallatai? Yin amfani da tsohuwar nazariyya da ke cewa talauci ne ke mai da mutane 'yan ta'adda ta kau a kan 'yan kasar Saudiyya. Domin su ba sa cikin talaucin da zai sa su yanke kauna daga rayuwa balle su ji dadin tarwatsa kawunansu a cikin fararen hula. Hasali ma wani rahoto da jaridar ALQURDHA ta buga a ranar 3/10/2005 ya ce: "'Yan kasar Saudiyya da ke shiga Iraki domin kai hare-hare suna zuwa da kudaden da suka kai dalar Amurka 10.000 zuwa 15 000." Shakka babu, da akwai shakku mai yawa a kan cewa masu jihadi ne kadai ke kashe fararen hula a Iraki. 'Yan sandan garin Basara sun kama sojojin Birtaniya biyu sanye da jallabiyyar Larabawa da makamai da bama-bamai a hannunsu suna shirin tarwatsa wani ofishin 'yan sanda, watakila kuma da masallacin Shi'a, saboda su kara ruruta wutar rikicin mazhaba a kasar da ke gab da fadawa cikin yakin basasa. Dambaruwar siyasa da ta addinin kasar Aljeriya ma ya tabbatar da cewa kungiyoyin leken asirin Yammacin Turai, musamman Faransa da ma gwamnatin sojan kasar suna da hannu wajen kashe fararen hula da dama ba kungiyar 'Salafiyyya Lil Da'awa Wal Qital' bace kadai ta yi wa al'ummar Aljeriya kisan kiyashi ba. Sai dai abu daya da babu shakku a cikinsa shi ne cewa; babu ma'aikacin wata kungiyar leken asiri ta Yammacin Turai da zai kai harin kunar bakin wake a kan fararen hula. Za su iya tarwatsa motoci masu bama-bamai daga nesa, ko su yi shigar Larabawa su bude wuta a kan fararen hula, amma ba kunar bakin wake ba. Mai akida ne kadai zai iya yin kunar bakin wake, amma ba dan leken asiri ba. Su kuwa 'yan kasar Saudiyya suna yi wa Iraki kallon kofar shiga Aljanna ta hanyar kashe Kurdawa da 'yan Shi'a da Ahlus Sunnan da suka shiga cikin siyasa. Kabilancin Larabci kuwa da Sarakunan Saudiyya ke yi wa Iraki kuka a kansa a yau, da a baya shi ne abin da suke gaba da shi. Gaba ce wacce ta dace da manufofin Amurka, domin kuwa kasar Masar karkashin Gamal Abdun-Nasir da ta daga tutar kishin Larabci a shekarun hamsinoni da sittinoni tana kawance da Tarayyar Soviet. Tarihin yin amfani da addini domin kare manufofin da ba masu tsarki ba dadadde ne daidai da dadewar Zuriyar Sa'ud a kan mulki. A wannan lokacin ne babban Muftin Saudiyya, Shaikh Bin Baz ya rubuta littafi na musamman a kan sukar kishin Larabci "Naqdu Qaumiyyatul-Arabiyya," wanda Gamal Abdun-Nasir na Masar ke jagoranta. A fadar Muhammad Mas'ary (dan kasar Saudiyya mai hamayya da tsarin mulukiya) a cikin kasidarsa mai taken "Ha'qaiq anil Wahabiyya"ya ce: "Shaikh Bin Baz (Allah Ya gafarta masa ) ya rubuta wannan liffafin ne saboda ya taya Sarakunan kasarsa fada da Jamal Abdun-Nasir. Fatawar da ya bayar a cikin wannan littafin na haramcin neman taimakon kafirai domin yin wani aiki, hannunka mai sanda ne ga Abdun-Nasir da ya gayyato Injiniyoyin kasar Rasha saboda su gina wa Misirawa madatsar ruwan tekun maliya." Muftin na Saudiyya da ya kafirta akidar kishin Larabci ta Nasiriyya, sannan kuma ya haramta wa Masar yin hulda da Tarayyar Soviet bai ce uffan ba yayin da Sarki Abdul-Azizi Ali Sa'ud ya gayyato Injinoyin sojan Amurka (a lokacin Shugaba, Franklin D. Rosevelt) suka gina filin jirgin sama a garin Dhahrain. Bai kuma ba da wata fatawar ba wacce ta haramta wa Sarki Abdul-Aziz din kulla yarjejeniyar tsaro da gwamnatin Amurka karkashin shugabancin Harry S.Truman a 1947. Ga shi kuwa a karkashin wannan yarjejeniyar ne Amurka ta rika aike wa da kwararrun sojojinta domin su bai wa takwarorinsu na kasar Saudiyya horo da kuma sayar wa da kasar kayan yaki. Muftin na Saudiyya bai kuma haramta wa sarakunan na Saudiyya bai wa Amurka damar kafa cibiyar horo ta soja ba a kasar Saudiyya a 1992. Sabanin haka ma, babban Muftin ya fitar da wata fatawa a cikin shekarar 1999 wacce take akasin wacce ya ba da a kan Jamal AbdunNasir. Wannan karon ya halatta wa Sarki Fahad Ibn Abdul-Aziz neman taimakon sojojin kafiran Amurkawa saboda su fitar da musulmin sojojin Iraki da suka mamaye kasar musulmi ta Kuwaiti. Ga Nassin Fatawar Babban Mufitin Na Saudiyya. "Amma abin da ya faru a kan gwamnatin Saudiyya na neman taimakonta da sojojin da suka kunshi musulmi da wadanda ba musulmi ba saboda kare kasar Kuwaiti daga zaluncin Shugaban kasar Iraki, ya halatta, kai ya zama wata larura. Tana kuma da uzuri a kan haka, kuma abar yi wa godiya ce a kan abin da ta yi." Mujallar IQRA'A 23/8/1990. Za mu ci gaba insha Allah. |
Shafin Gamji | Tafsirin Alkur'ani | Hadisai | Crescent International |