Jarida don Karuwar Musulmi
Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki ISSN 1595-4471
Juma'a 10 Shawwal, 1426
Bugu na 691
Tunatarwa | | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari Tattaunawa | Labarai |
Wa zai mulki jihar Katsina a 2007?
A siyasa irin ta dimokradiyya kuge da kuma dundufarta na bugawa a ko'ina a duk fadin kasar. Masu mulkin da ke bisa, yanzu ne suka yi rabi, amma har an fara nazari da hasashe da kuma tattauna waye zai dare kujera a 2007? Daga Shugaban kasa har kasa maganar kenan. Kulle-kulle kuma sai ci gaba suke yi. Ana ta gyara makamai a ga ya za a yi amfani da su domin cimma abin da aka sa a gaba? Katsina wuri ne da ya yi fice a iya kullin irin wannan siyasa a kasar nan. A cikin gida sun iya bindigar kasa da farmaki irin na macijin cikin saura. Yanzu abin da aka fi yawan zama a kansa shi ne zaben Gwamna na 2007 a jihar ta Katsina. Tuni dare ya zama rana ga wasu, ana tattauna ya za a yi nasara? Me ke matsalolin? Ya za a yi maganinsu? Wa da wa za a ga bayansu kafin lokacin? Wannan shiri ya kama daga wadanda suke son hawa da wadanda suke son dora wasu da kuma 'yan "in wane ya hau mune za mu wataya, don haka za mu yi bangar wane ya ci." Wani abin takaici ya zuwa yanzu duk masu kamfen din karkashin kasa ba wadanda ke yi a bisa akida da manufar cewa, "Kawo ci gaban Katsina ko kyautata ma talaka ko warware wata matsala da ta dami jihar." Kamfen din yana tafiya ne a kan ko dai "an bata mani rai sai na dau fansa," ko kuma "mu bari mu hau don mu da'yan 'group'" dinmu mu dana," ko "bari in yi gumza domin a ji ni a zo a sasanta da ni in samu wani abu," ko kuma wadanda wasu suka turo domin su amshi gwamnatin su ma. A iyaka binciken ALMIZAN daga wadanda suka yi fosta ko wadanda suka turo wasu na masu kamfen ko masu mitin din cikin dare, har yanzu babu wani mai wata manufar da na kawo a sama, watau a takaice, wani shiri a tsare ko a magance na kai "Katsinawa tudun an warke." Kakabin farko a kan wanda zai tsaya Gwamna a 2007 ya fara ne da cewa wai "dole ne a wannan karon a ba dan yankin Karaduwa!" Babu wata huja ta jihar ta bunkasa. A'a lokaci kawai ya yi da za a ba dan Karaduwa, ko da kuwa wanene. Ja'iri ne ko Liman? Oho! A dai ba dan Karaduwa. A bisa wannan ake ta da tsimin Karaduwawa. Ba wani dalili, sai dai kawai ka ji, an ce "sai Karaduwa!" Ana neman a bautar da su a tunani, a sanya su kurkukun "sai Karaduwa," maimakon akalla su ce Allah ya yi mana zabi na alheri daga ko'ina ina ne. Guguwar Karaduwa na kada marasa 'yancin tunani a can yankin. Wasu rundunar kuma cewa suke, "sam dan cikin ganuwa ya gama mulkinmu." Dalili kawai shi ne wani dan cikin ganuwa ya taba yi, kuma ga wani yana sama, don haka ya kamata a sami wani dan wajen ganuwa ma ya yi. Masu wannan gangami su ma har suna yayata nasu ra'ayin. Abin har ya ginu a siyasar ganuwa da wajen ganuwa. Na ga wani rubutu wai 'hujjoji da illar sa dan ganuwa ya sake mulki.' Duk rubutun babu wata hujja wadda aka bayar a dimokradiyyance idan dan takara yana neman ya rubbaci mutane su ba shi kuri'unsu. Ko 'yar karyar nan ta wadata ruwan sha da kafa maku injinan janareto kowa ya ga haske har da rana babu. Abin da ake cewa shi ne ya kamata, kuma ya kara kamata. Abin ma har da dadin dadawa, kamata ya yi a ce dan wajen ganuwa ya dana. Ana ta kashe tunanin wasu da kumfar baki "an gama mulki daga cikin birni!" Wa za a ba a wajen ganuwa? Oho! Ya yake? Oho! Ina zai kai su? Oho! Jimlar dai ita ce "mu ma a ba mu!" A bayanan da nake da su, mutanen yankin Daura sune ba su dauki Gwamna ya fito daga cikinsu wani abin ko a mutu ko ai rai ba. Sai dai wasu da suka fito daga Kananan Hukumomin da aka ce duk suna cikin "Daura Senetorial" ne suke son su ce masu su ma 'yan uwansu ne a siyasa, don haka wai takarar tasu ce, suna neman su ba su goyon baya. A bincikena 'yan asalin Daura na hakika sam ba su dauki lamarin wani kayan gabas ba. Wata kungiyar kuma da suke son ganin ko ta yaya sai mulkin ya tsaya a cikinsu sune 'yan cikin ganuwa. Ga alama suna neman abin ya zama kamar wani gado ne. Suna jin kamar wani alami ne, mulkin sai su. Su ke kusa da NEPA ta jiha, suna garin da ya fi gine-gine a duk fadin jihar. Ko mitin za a yi, ina ne za a yi cikin birni? Dan wane ne da din gidan wane, ya za a yi wani ya zo ya mulke mu? Babu wata hujja ta fita daga wasu matsalolin da Katsina ke ciki. In ka matsa ma dan birni da tambaya, yana iya ce maka, "ai idan aka ba dan wani wuri, har raba gidan sarautar nan yana iya yi. Kuma wanda ka ga ai bai dace ba ko?!" Wa ne daga birnin? Ina za ya da su? Duk kar ka yi wannan zancen, dan birni kawai! Wannan shi ne magagin da ake shayar da su - da 'birni'. Mafi yawa daga dirgar mulkin tana fitowa ne daga jam'iyyar PDP. Sune suka fi 'yan takara. Su suka fi hamasa da kumaji a tsakani da cikinsu. Kullen-kullen ya fi kamari a tsakiyarsu. ANPP kuwa ta zama a jihar kamar wadda kanjamau ya kai kasa. Sune ya kamata su zama kamar jam'iyyar hamayya mai yin magana idan sun ga ana wani abin da ba daidai ba. "A jihar ta Katsina ANPP ta zama summun bukumun, kamar suna a wata duniya wadda ba talabijin ko rediyo," a ta bakin wani. Daga wadanda ke wakiltarsu a Majalisu, sunan mutum biyu kake ji. Sune Sanata Abu Ibrahim da Hamisu Gambo a matsayin wadanda suka san cewa "wakilci a Abuja fa, ko da magudi ya kai mutum, to an yi karya da mutane kuma mutanen nan na bukatar shi." Sauran wakilan tsakaninsu da su sai da a tsohuwar fostar da aka buga lokacin yakin neman zaben 2001. Wasu daga wakilan ANPP din ma a majalisu an gano suna halin 'dan salula' har daya an kore shi daga jam'iyyar. Shi ne dan majalisar jihar na Karamar Hhukumar Daura. Ba wani jigo a ANPP da ke zaune a jihar balle ya ce yana tare da jama'a, har zai iya yin wani katabus. 'Yan siyasar da zababbun suna ma jama'arsu shiga ramin kurege, a shiga ta nan a fita ta can. Kafin ka ankara, lokacin da za ka hangi kura, lamarin ya zama hira. Magoya bayansu na ikirarin cewa shugabanninsu ko wadanda suka yi ma wahalar siyasa, yanzu sun mai da su sune makiyansu na farko. Suna ikirarin cewa kan mage ya waye, kuma suna jiran su dawo masu da neman a sake amfani da su, a lokacin za su yi masu sakiyar da babu ruwa. Sai sun yi masu je ka huda. Jama'ar gari kuwa, wadanda suna ganin akalla a samu jam'iyyar hamayya ta rika magana, suna ganin ANPP ya kamata ta zama, amma ba ta yi. An ce rashin tsari ya sa ko kudin hayar ofis nasu na jiha sai da aka kai rana suka iya biya. Bincike ya nuna mani ANPP suna neman ta fadi gasassa ne, ba wahala, ba kashe kudi, ba wani tsari na a taimaki jama'ar jiha; a fatansu rigima ta dabaibaye PDP, a samu fashewa da munafunci a tsakaninsu, su kuma su tsinci dame a kala. Wasu 'yan PDP su yi fushi, su kuma sai dan takararsu ya ci. Buhari ya daga hannunsa ya ce ga nawa, sai a tafi da tunnin mutanen a bisa rikicin PDP da kuma makantaccen son Buhari. Da wannan shi kenan sai su samu mulki. Binciken ALMIZAN ya tabbatar cewa wasu da suka fadi zabe a ANPP a 2001, cikin su har da wanda ya yi takarar Gwamna, Injiniya Nura Khalil, sun rika tona ainihin yadda suke da gaskiyar kamanninsu. Da kuma tafiya ta yi nisa, mabiya na ta godiya ga Allah cewa gara da ba a yi ba. A yanzu ba wanda ya san gobe sai Allah. Tabar buki ta fi ANPP kwarijini a Katsina. 'Ya'yanta na cewa, "za mu farfado da ita domin mu fuskanci 2007. Za a gyara ta a mikar da ita, kuma za a yi siyasa kafin 2007. Za mu shirya sosai domin 2007. Idan ANPP za su gyaru kafin 2007 saboda zaben 2007, wannan ya nuna suna son mai da mutanen jihar kwarawa kenan. Lokacin da PDP na masu mulkin yadda suka ga dama, sun yi gum suna son su kuma dawo su yi amfani da su domin su amshi mulki ya dawo wajensu. Wani abu mai kamar wuya, wai "bera ya yi ma mage limanci." Hasashe ya nuna wata sabuwar jam'iyya na iya tasowa ta fito da mutumin da 'yan siyasa ke so kuma ta zo na biyu a tasiri a zaben Gwamnan, bayan jam'iyya mai ci. Kamar kowane Gwamna mai tafiya, Alhaji Umaru Musa 'Yar'aduwa shi ma yana cikin zullumin tunanin wa zai gaje shi? Yana tunanin ya mutuncinsa zai kasance in ba shi a gidan gwamnati? Wa zai kare masa shi, wa zai rufa masa asiri, wa zai rika tasiri a kansa ko da kuwa yana daga inda yake ne? Gwamnan yana da matsaloli da kuma makiya. Bayan dawowarsa ta biyu ya yi baram-baram da wasu dattawa, bangaren Amadi Kurfi, Aminu Makera da kuma bangaren su Lawal Kaita da Iro Danmusa. Da dattijan bangan siyasa irin su Alhaji Audu 'Yan Doma da Balukuki (Karami). Dukkaninsu ba wani sirri, suna adawa da sukar gwamnatin da Gwamnan. Su ma da ire-irensu ba sa magana, ba sa cewa kanzil, suna fadin a tafi a haka. Suna jiran ko dai sai a 2007 za su koya masa hankali, su kalubalance shi cikin duk wanda ya fito, ko kuma sai ya bar mulkin su fara magana. Wannan da wasu dalilai ya sa tunanin cewa a kyale kujerar ta tafi haka. Sam ba ta ma yiwuwa bindiga a ruwa. Wannan ya sa kullum ana nazari da bajewar wa za a ba? Yaya yake? Ko zai iya rike alkawari? Da dai sauran tambayoyi. Bincikenmu ya gano daga duk wadanda suka fito neman takara a Katsina, lamarin da sauran jan aiki, wai samun ruwa a fako. Domin kamata ya yi ko da a dimokradiyyance, ya dace kafin a kalle ka a ce wannan shi ne Gwamnanka, ka san shi ciki da waje da kuma ya yake hatta ga iyalansa zuwa ga abokai. Ya yake a da can, ya yake jiya da yau? Hatta iyalinsa ya yake tafiyar da sarautar mulkinsu? Sannan ka san me aka dankara maka ko aka zaba maka. Bincikenmu ya gano masu bukatar wannan matsayi a aji uku suke. Aji ukun sune wadanda suke son su dare, tsakaninsu da Allah nema suke. Da kuma wadanda suke neman in tafiya ta yi nisa a san da su, a kuma yi masu sakayya. Na ukunsu sune wadanda ke son dora yaransu, domin su rika karanta masu da kuma fassara musu, tare da yi masu zagin inda za su bi. An ruwaito wani hamshakin Attajirin jihar na cewa shi ba zai tsaya takara ba, amma gaskiya dole ya taka rawa a kan waye zai mulke shi. An ce ya ce zai kashe ko nawa ne domin ganin cewa wanda zai shiga gidan gwamnati yana da tasiri a kansa. Ya zuwa yanzu wasu sun fito har sun nuna cewa lallai 2007 da su za a fafata. Wadanda fastocinsu ke shawagi a bangwayen Katsina sune; Alhaji Umaru Maiwada Suleiman, wani tsohon jami'in 'yan sanda da ya yi ritaya a 2002 a matsayin DIG. Alhaji Abdu 'Yandoma, wani tsohon Sanata da aka yi waje da shi a zaben 2001, yanzu kuma wakilin kamfen na Atiku a Katsina. Alhaji Abdulmumini Aminu, wani tsohon Gwamna kuma tsohon Shugaban Hukumar kwallon kafa ta NFA zamanin Abacha. Alhaji Aminu Bello Masari, Kakakin majalisar wakalai na yanzu. Wadannan su suka fi yawan fastoci da suka cika duk garin. Akwai wadanda kuma a gefe aka ce suna da 'yan kwamitocinsu na yin abubuwa karkashin kasa, irin su Sanata Abu Ibrahim, Sanata na yankin Funtuwa a yanzu. Alhaji Murtala Ibrahim Safana, wani babban Jami'i a Hukumar Tsara Birane ta Abuja, Alhaji Isma'ila Mamman Kurfi, wani tsohon Sanata da aka yi wancakali da shi a zaben 2001, Alhaji Ibrahim Idah, wani tsohon ma'akacin banki kuma Jami'i a "Vision 2010" na Abacha, Injiniya Mahmud Kanti Bello, Sanata a wannan karni daga yankin Daura. Alhaji Tukur Ahmad Jikamshi, tsohon mataimakin Gwamna a 1999-2001, Injiniya Nura Khalil, tsohon dan takarar Gwamna a ANPP 2001, Alhaji Lamis Shehu Dikko, Shugaban bankin Intercity a yanzu. Har ila yau akwai mutane irin su Alhaji Zakari Ibrahim, Talban Katsina, tsohon shugaban Hukumar Raya Kamfanoni da Masana'antu, da Dakta Jabir, wani Darakta da ke aiki da Carter Foundation a yanzu, sai Alhaji Bilya Sanda, dan kasuwa kuma daya daga cikin jiga-jigan Jami'ar Musuluci da ke Katsina. Akwai kuma wadanda ake rade-radin cikin su Alhaji Umaru Musa 'Yar'aduwa ke duba yiwuwar mara ma baya. Sunayen suna da yawa, amma wadanda suka fi karfi sune; Mataimakin gwamnan jihar, Alhaji Abdullahi Garba Aminci. An ce saboda saukin kansa da kuma biyayya ga Gwamnan. Da Alhaji Tanimu Kurfi, Shugaban bankin gidaje na kasa a yanzu, Alhaji Murtala Ibrahim Safana, ma'aikaci a Hukumar Raya Birnin Abuja. Injiniya Muttaka Rabe Darma, Kwamishinan matasa da wasanni na jihar, Alhaji Abba Sayyadi Rumah Sakataren gwamnatin jihar Katsina a yanzu. Akwai kuma 'yan takarar da ka iya bayyana don raba gardama. Sunayen wadanda ke a wannan sashe suna da yawa, kuma wasu ko bayyana ba su yi ba. Amma dai suna gefe suna karantar yadda hali da yanayi zai kama. Daga sunayen da ake rade-radi akwai na Wazirin Katsina, Dakta Sani Abubakar Lugga. Sai kuma na Sardaunan Katsina, Alhaji Ibrahim Kumasi. A cikin wadannan jerin, wasu daga cikinsu ana da bayanan da suka nuna ko kansiloli ba su cancanta a zabe su ba, balle su nemi takarar Gwamna. Wani an ce 'yan siyasa sun yi masa shigo-shigo ba zurfi. Dan abin da yake da shi duk ya kadar tun kafin a je ko'ina. An ce da ya ga ya shiga wani yanayi, sai ya koma yi wa 'yan uwansa 'yan siyasa yarfe da kage. Daga jerin da na kawo wasu an ce sun dau jama'ar jihar kamar wasu kwarawa ne, ba su san su ba, ba su tare da su, ba su zama tare da su. Amma niyyarsu lokaci guda za su zo Naira ta yi aiki. Suna ba da misali da cewa yanzu ba zabe ake ba saye ake. Kuma in dai a wannan zamanin kudi na tasiri, to "sai sun yi." 'Yan wannan ajin sun mai da mutum bai da wata daraja ko daukakar da Allah ya yi masa, a'a shi da kimarsa na sayarwa ne, kuma za su zo su saye shi. Akwai wani wanda ake ganin zumudinsa na jin shi mai jini a jika ne zai hana ya yi aikin. Da kuma halinsa na bai cewa bai yi, zai tattara komai a kan zai iya, kuma zai yi; amma daga karshe ba a yin komai. Wani neman ganin sai "ya rama" zai hana a yi aikin. An ruwaito wani har sambatu yake, yana cewa "in na yi Gwamna sai na rushe kaza, sai na kama wane." Binciken da na yi domin nazarin wannan rubutu, ya gano cewa lallai da sauran jan aiki a gaba a kan mulkin siyasar dimokaradiyya a Katsina. Kuma akwai rikici a kasa kwance mina-mina, kowa yana dasa bom dinsa a inda yake jin cewa dan uwansa zai taka domin ya tashi ya wargaza shi. A rubutu ne gaba zan ya bayani ne sosai dalla-dalla a kan yiwuwar 'yan takarar, da yi masu fidar rago ku gan su a fili domin sanin su waye ke son mulkar ku? |
Shafin Gamji | Tafsirin Alkur'ani | Hadisai | Crescent International |