Almizan :Kashe Mumini babban al'amari ne ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 10 Shawwal, 1426                 Bugu na 691                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Tunatarwa:Tare da Shaikh Ibrahim Zakzaky

Kashe Mumini babban al'amari ne

SHAIKH ZAKZAKY
Malam Ibraheem Yaqoub Zakzaky H.

Mai karatu yau muna dauke ne da ci gaban jawabin da Malam Ibraheem Zakzaky ya gabatar a wajen taron Yaumu Shuhada na bana, wanda aka gabatar a filin kofar shahidai (Doka), Zariya. Kuma yau muna mako na uku kenan da soma kawo maku wannan jawabi. In dai ana biye da mu mun tsaya ne daidai inda Malam yake bayanin irin makircin da ake shiryawa da aiwatar da su ga wannan Harka ta hanyoyi daban-daban. Yau ma dai Musa Muhammad Awwal ne ya rubuto mana daga kaset. A sha karatu lafiya. Za mu dan koma baya kadan.

BA MU KI SU DA SHIRIYA BA

Aka sami wani Basaraken gargajiya, (a'a ku kyale shi ku daina tsine masa. Ku fadi abin da yake yi ne mara kyau, sai mutane su gane). La'alla ya tuba. Ba ku ji na ce wani maye ya tuba ba? Ai mu ba da su muke fada ba. Mu muna abinmu saboda Allah ne. Su suna yi saboda nasu daban. Ba mu ki su da shiriya ba. Fatanmu Allah Ya shirye su, Ya yafe masu, Ya sa kuma da mu da su makomarmu Aljanna. Ba ma fatan wani ya shiga wuta. In ka tsine wa mutum kamar ka ingiza shi wuta kenan.

Shi kenan aka ba su kudade da adduna, aka kai masu sababbin adduna, aka ba su kudi mai yawa. Ana ba kowanne wanda ya yarda zai yi wannan aiki, a ba shi adda da Naira dubu goma. Aka rarraba wa mutane kudi aka ce ga wanda za su far wa. Suka yi ta fafatawa kuwa.

In sun yi kukan kura suka ce wayyehoho! Sai su arna, ba su da imani! Wayyehoho! Sai su matsiyata shegu, 'yan banza! Da ma kabbarorinsu kenan nan ai. Sai su je kai hari, irin wannan dai. A takaice ba labarin waki'ar Sakkwato zan ba ku ba, wani abu ne da jaridu sun farfada a makwanni daban-daban na abubuwan da suka faffaru.

Amma dai a takaice abin da suka yi kenan, suka yi ta kai hari gidajen 'yan uwa. Sun kona gidaje daban-daban kimanin sittin da 'yan kai. Akwai bayani cikakke da aka rubuta na duk abubuwan da aka yi. Sun rugurguza gidajen wadansu, har da makaranta. Sun rusa makaranta. Kuma ban san ko nasara zan suka yi ba? To sun yi nasara wajen kashe mutum shida, in nasara ce a wajensu. Wannan cikin artabu da suka yi kenan cikin kimanin wata biyu.

Sun yi wannan yunkurin, tun bayan Ashura suka kashe mutum guda. Bayan nan da kwana uku suka kashe mutum biyu. Bayan nan suka yi yunkuri, su kashe daya nan, su kashe can, har dai a karshe suka kashe mutum shida.

YADDA AKE YIN HUKUNCI GA WANDA YA YI RIDDA A SHARI'AR MUSULUNCI

To ban san ko su wadannan da ake ba su adda da dubu goma za su yi tunani ba. Ban san ko kuma gargajiyan da ake yin amfani da su, a ba su kudin su bayar, su ma za su yi tunani ba. Amma mu kaddara ranku ya sawwala maku cewa wadanda kuke kashewa sun yi sabo, sun yi ridda a fahimtarku. Sun fita daga addinin Musulunci, a fahimtarku, mu kaddara haka kuka fahimta. To sai mu ce maku ba inda shari'a ta ce maku ku kuma aikinku shi ne ku je ku kashe su, domin shari'a rubutacciya tana nan kan cewa ko da mutum ya yi ridda ana hukunta shi ne, ba ana kashe shi bane. Akan kawo shi ne a kawo masa hujjoji na cewa ya yi ridda. A ce, to me ka ce? In ya ce Astagfirullah na tuba, shi kenan.

Hatta in ya nace ya ce yana nan a kan bakarsa kan kalmar ridda da ya yi ko aikin ridda da ya yi, aka kuma yanke masa hukunci na kisa, to ana ba shi damar tuba na kwana uku. Wato bayan an kai shi kotu ta yanke masa hukunci na cewa ya yi ridda saboda fadin wani abu ko aikata wani abu, shi kuma ya tsaya kan bakarsa daram a kan cewa yana nan a kan abin da ya yi daidai ne. To za a ce masa kotu ta same ka da laifin ridda kuma ta yanke maka hukuncin kisa, amma za a ba ka damar kwana uku ka tuba.

To har bayan kwana ukun in aka zo za a kashe shi, ko da an daga takobi, in ya ce ya tuba, za a janye. Wannan shari'a ce. Ku karanta, haka take a rubuce. Kuma ba wani sabanin Mazhaba a kan abin da nake fadi, ballantana wani ya ce ai a Mazhabarku kenan.

BA WAI MUNA JIN TSORON KAR KU YI KISAN BANE

To ina ka sami cewa za ka iya zuwa kai ka kashe mutum kawai a kan kai ba ka ma san shi ba, ba ka ji ma ta bakinsa ba? Kuma an taba yin hukunci a hukunta mutane a dunkule? Kamar mu kaddara akwai kungiyar mutane, sai aka sami wani mutum a cikinsu ya fadi wata magana, to kowa ya fadi wannan maganar kenan ( a cikinsu)? Ba shi wanda ya fadi maganar shi kawai za a dauko ba?

Mu kaddara wani ya kuke yana wa'azi, sai ya fadi wata kalma, kuma kalmar nan ta zama mugunyar kalma wadda a nazarin masu hankali da masu ilimi wannan maganar ta fid da shi addinin Musulunci, to kuma ta fid da duk wanda yake sauraron sa? Mu kaddara in ka ji kalma mummuna, ko da a rediyo ne, kai ma ka zama wannan? Ai ka ga shi ne ya yi laifi, shi za ku kamo shi kadai. Sannan shi ne za a yi wa hukunci a kotu, ba kowa da kowa bane. Ba a taba hukunta mutanen gari ko kabila ko al'umma ko 'yan wata kungiya ba. Wannan shari'a kenan. To ku ina kuka sami hujjar kuna iya zuwa ku kashe mutum?

Ina fadin wannan ne wala'alla za ku yi hankali. Ba wai muna jin tsoron kar ku yi kisan bane, muna so ku yi hankali ne kar ku je ku ga abin da yake ba makawa, ba ku kuma da maguda, ba ku da matsera in kun gan shi, shi ne sakamakon Allah gobe kiyama.

To in wanda ka kashe mumini ne, to da nassin Alkur'ani Allah (T) yana cewa; "waman katala mu'uminan muta'ammidan fajaza'uhu jahannama khalidan fiha, wa gadiballahu alaihi wa la'anahu wa a'adda lahu azaban alima." Ma'ana wanda duk ya kashe mumini da gangan, sakamakonsa jahannama, zai dawwama cikinta, kuma Allah ya yi fushi da shi ya tsine masa, ya yi masa tanadin babbar azaba. Nassin Alkur'ani Malam! Ina kai ina LA'ILAHA ILLALLAHU, in ta zo gobe kiyama?

Wannan ita ce maganar da Manzon Allah ya dinga nanata wa wani wanda ya kashe wani bayan ya ce LA'ILAHA ILLALLAH. Yana cewa, "Ya Rasulullah ai ya fada don ya kare kansa ne." Har yake ce masa ka tsaga zuciyarsa ne ka ga cewa ba da gaske yake yi ba? Har ya ce ya yi burin ina ma bai musulunta ba.

BABBAN AL'AMARI NE KASHE MUMINI

Akwai ruwayoyi iri-iri da suka zo dangane da irin wannan, amma na wanda ya fi shahara shi ne na wani mutum mai suna Muhallib Bin Jufama, wanda aka ce ya kashe wani haka nan bayan ya ce LA'ILAHA ILLALLAH, Manzon Allah ya fusata yana gaya masa haka nan. Har sai ya ce Ya Rasulullah nema mani gafara. Aka ce Manzon Allah ya daga hannu ya yi addu'a, amma mutane abin da suka ji, wani abu ne daban. Amma dai sun dauka Manzon Allah ya yi masa addu'a ne. Amma kunnuwansu abin da ya ji masu, wallahu a'alam. Su dai sun ji kamar Manzon Allah ya ce ne Allah kar ka gafarta masa. Kuma sai ba da jimawa ba ya mutu.

Aka dauke shi aka tona kabari aka sa shi, ana sa shi sai kasa ta tunkudo shi. Aka sake tona wani kabarin aka sa, sai kasa ta sake tunkudo shi. Sai aka gaya wa Manzon Allah bayan da aka yi haka nan da shi sau uku. Sai ya ce ku je ku sami tsakanin inda dutse ya rabu, a kan dutse. Ku sami sarari inda dutse da dutse suka rabu ku jefa shi ku cike da kasa da duwatsu. Haka aka yi.

Sannan bayan da aka dawo, Manzon Allah ya ce da su, akwai mutanen da suka yi laifi fiye da na Muhallib, ya koya maku darasi ne. Akwai mutanen da suka yi laifi fiye da na Muhallib kasa ta karbe su. Ai kasa ta karbi Fir'auna, kodayake ta bullutso da shi, amma akwai Hamana da su Namarudu da sauransu, kasa ta karbe su, ko? Na shi Fir'auna Allah ya bar shi ya zama aya har ya zuwa mutanen yanzu, har ya zuwa mutane masu zuwa.

Akwai mutanen da suka yi barna fiye da na Muhallib kasa ta karbe su, amma ta bullutso da shi ne don ta koya maku darasi. Babban al'amari ne kashe mumini.

Sannan kuma wannan da fatawar kanka da ganin daman kanka ba da shari'a ba, ba hujja ta shari'a ba. Domin wadanda akan kashe da hujja na shari'a, in ma hukuncin na ridda ne, yakan zama ya ba Malami tsoro. A zamanin da musulmi ke da iko, an taba yanke wa wani Malami hukuncin kisa, aka ce sai da aka yi wata tara Malamai na fadar ra'ayinsu daban-daban. Kowanne ya fadi ra'ayinsa, wani yana ganin lalle ba za a kashe shi ba. Da za su tsaya su ga cewa lalle ba za a kashe shi ba, sai a sake shi. Amma shi ya tsaya a kan batunsa shi ba ridda ya yi ba, kuma yana nan a kan matsayinsa, su kuma suna ganin lalle wannan abin ridda ne, ya tuba, ya ce, a'a. Da aka tsaya kiki-kaka, sai da aka yi wata tara ana ja in ja tsakanin Malamai.

To wannan kuwa ba ka san mutum ba, kana kallon gini ne kawai ba ka san waye a ciki ba. Mata ne, yara ne, tsofaffi ne, ka cinna wa gidan wuta kana yanka ihu, ba ka san ma wa kake kashewa ba, har da dabbobi da kaji wadanda su ba su yi maka komai ba.

Ala'ayyi halin, muna gaya maku ko za ku wa'azantu, amma ba mun ce maku muna jin tsoron kisanku bane. Amma ku naku in abin ku yi kisan ne, to ba ku cuce mu da komai ba, kun cuci kawunanku ne wala'alla za ku yi tunani.

To ala'ayyi halin dai sun yi wannan yunkuri nasu. A daidai lokacin da suke yin na Sakkwato sai muka ji labarin an fara shiri a sauran wurare. A wasu sauran garuruwa an fara shirya irin wadannan, cewa za a yi mai gaba daya ne, an fara da Sakkwato ne. Suna jiran a gama na Sakkwato ne su fara sauran. Har ma wasu suka ce ai ba sai an gama na Sakkwaton ba, a fara na sauran wurare kawai. Sai ga shi Allah (T) ya kawo karshen na Sakkwato din. To ban san ko sauran garuruwan ko za a ci gaba ba? Ko akwai masu kwadayin dubu goma da adda?

To don ku sani, su wadanda suka yi kisan na Sakkwato, bala'i na ta fada masu. Muna da tabbacin wanda ya kashe wani dan uwa da ake cewa Ibrahim Mai Dori, shi ne ya soka masa wuka a ciki. To shi kuma ko da kudin da aka ba shi ne na ladan kisan, ya sayi babur yana acaba da shi. Shi kenan sai su kuma 'yan AREA BOYS da suka fi karfinsa su biyu suka ce ya kai su wani wuri za su biya shi. Suka je da shi bayan gari suka soka masa wuka a daidai inda ya soki Ibrahim Mai Dori, suka dauke babur din.

Kuma ana da labarin wadanda gidansu ya kama da wuta ba a san asalin inda wutar ta fito ba. Muna da labarin wadanda suka yanke jiki suka fadi. Har wasu na cewa, "addu'ar 'yan Buraza ta." To ita ta! Kuma nuna nan muna yin ta insha Allah.

WANNAN YANA IYA ZAMA DARASI GA MASU YUNKURI

Ka ga shi wannan bai ci ribar abin da ya samu ba sam, ga shi shi ma ya mutu. Kun ga wancan kashe shi ya yi, shi za a je gobe kiyama yana da hujja, an kashe shi ne. Shi kuwa wannan, na'am kana iya cewa an kashe shi ne, to amma ya yi shahada ne fisabili mene? An karbi babur, babur din da ya samu na kudin da ya yi kisa aka biya shi lada.

Wa ya sanar da kai kuma ko ayar "Waman Katala Mu'uminan Muta'ammidan….." ba za ta yi aiki a kansa ba? Ka ga "fa jaza'uhu jahannama" kenan. "Khalidan fiha" kenan. "Wa gadiballahu alaihi" kenan. "Wa la'anahu" kenan. "Wa a'adda lahu azaban alima" kenan. Ka ga gobe kiyama mummunan karshe, a nan ba babur din. Wannan yana iya zama darasi ga masu yunkuri.

Akwai wani dan uwa da ya yi shigar burtu, shi ma sai ya zama dan tauri. Ya shiga cikin 'yan taurin, sai suka ga ba su gane shi ba, sai suka ce kai daga ina kake? Ya ce, "daga Kano nake, ni ma na ji an ce ana wannan aiki ne ana karkashe wadanga mutane, shi na nac ce bari in zo in sami rabona." Sai suka ce, "ka ji abin da zan gaya ma, ka yi ta kanka. Wallahi 'yan Burazan nan kwana su kai suna salla, suna addu'a. Yanzu haka ma Bagargajiyen da ya sa mu, ji ake shi na kururuwa cikin dare. Mu ma duk tsoro ya kama mu. Saboda haka san ka san inda ka nufa kawai tun da wuri. "

Duk dai labaran da muke ba ku muna da tabbaci. In da abin a ce za mu yi husuma da su ne a gaban kotu mai adalci, muna da bayanai. Amma don kafa hujja, ko da ba za mu iya samnun adalci ba, muna so mu rubuta wadannan mu ce ga shi abin da muka yi, mu ga ita Hukuma in ba ta da hannu, me za ta yi? Saboda haka duk wani musulmi da ka gan shi yana hankoron fada da musulmi dan uwansa, to don ya sani, yana taimaka wa Yahudawa ne, kuma shirinsu ne. Hatta wannan shiri na Sakkwato muna da tabbacin nasu ne. Tunda har ma sun ce sun ware dala miliyan 100 domin yaki da taddanci a Nijeriya. Abin da suke kira ta'addanci shi ne Musulunci. Kuma wannan shi ne yanzu suke ta fama yin a ko'ina da ko'ina a duniyar musulmi yanzu. Duk an far wa musulmi da kisa ta kai tsaye da ta cikin gida da ta kuma wadansu hanyoyi daban-daban.

Kuma har ila yau, sune wadannan da suke wadannan kashe-kashe da suke cewa wai 'yan ta'adda musulmi ne suka yi, domin su dora wa shi musulmin din sunan dan ta'adda, su suke ta'addancin. Su suka zunguri dogayen ginin nan guda biyu na Manhatan da ke New York, suka ce 'yan Alka'ida ne, Osama Bin Laden ne da ke Afghanistan. Suka je suka karkashe mutane wadanda ba a san adadinsu ba a cikin Afghanistan; har yanzu suna kisa.

Sune suka kai harin Madrid a tashar jirgi, wanda ba wanda zai iya zuwa tashar jirgi ya dasa bom a tasha din in ba ma'aikacin tashar ba, tare da taimakon Hukuma. Hukuma ta dasa wannan bom din, ta kashe mutanenta, ta ce 'yan Alka'ida ne.

Sune suka dasa bom shekara daya da ta wuce, bara 1 ga watan Satumba. Suka je suka yi garkuwa da wasu yara, sun rurrufe idanunsu wai su 'yan ta'adda ne. Suka karkashe mutane da yawa. Yadda za ma a tabbatar da wannan shi ne, ba su wadanda aka ce wa 'ya ta'addan ne suka yi kisan ba, a'a, sojojin Rasha ne wadanda (Shugaban Rasha) Puttin ya tura, su aka ce suka yi mafi yawan kisan, tsakanin 'yan kananan yara. 'Yan kananan yara a firamare wadanda aka tube su tsirara, zuwa Malamansu da sauran mutane, suka kashe kimanin 300. Kuma har yanzu, ko jiyan nan ina kallo, su iyaye mata na wadannan yaran sun je sun ga Puttin duk fuskokinsu a bace, suna ganin gwamnati ta san wani abu, tana kuma wani rufa-rufa da ba ta gaya masu ba, domin gwamnati ita ta kashe wadannan mutanen, ba wadanda aka kira 'yan ta'adda ba.

Su kuma 'yan ta'addan nan ba a ma san ko su waye ba. Suka ce 'yan Alka'ida ne wai an kashe mutum 10, kuma ba a ga gawar ko mutum guda ba. Ba wani ka-ce-na-ce, 'yan sandansu ne, ma'aikatan KGB ne, su suka yi wannan shigar suka yi wannan aika-aikar da suka yi. Sannan kuma suka ce 'yan Ceceniya ne, Basayeb ne suka yi, sai ga shi an yi hira da Basayeb ya ce, lalle 'yan KGB ne suka yi. Har suka shiga babatu, don menene talabijin din Amurka zai yi hira (Interview) da Basayeb? Alhali mujirimin ya yi wannan barnar.

A biyo mu mako na gaba don ci gaba insha Allah.

"Saboda haka duk wani musulmi da ka gan shi yana hankoron fada da musulmi dan uwansa, to don ya sani, yana taimaka wa Yahudawa ne, kuma shirinsu ne. Hatta wannan shiri na Sakkwato muna da tabbacin nasu ne. Tunda har ma sun ce sun ware dala miliyan 100 domin yaki da ta'addanci a Nijeriya. Abin da suke kira ta'addanci shi ne Musulunci. Kuma wannan shi ne yanzu suke ta fama yin a ko'ina da ko'ina a duniyar musulmi yanzu."

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


 Shafin Gamji | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International