Jarida don Karuwar Musulmi
Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki ISSN 1595-4471
Juma'a 10 Shawwal, 1426
Bugu na 691
Tunatarwa | | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari Tattaunawa | Labarai |
Wa zai hukunta Bush?Daga Hasan MuhammadA shekarar da ta gabata ne dai wata kungiyar lauyoyi ta kasa-da-kasa da ke da hedikwatarta a Canada ta gabatar da wasu kararraki a kan Shugaban Amurka George Bush, inda ta zarge shi da laifin ba da goyon baya da taimakawa wajen azabtar da mutane. |
Wannan kuwa ya faru ne lokacin da Bush din ya kai ziyarar aiki kasar ta Canada cikin watan Nuwamba. Su dai wadannan koke-koke da aka yi a kan Bush sun ta'allaka ne a kan yadda ake cin zarafin daurarraru a kurkukun Abu Ghraib da ke can Iraki da ma wasu zarge-zargen na cin zarafi a can Guantanamo ta kasar Cuba, cikinsu kuwa har da wani dan karamin yaro wanda ake tsare da shi a can din sama da shekara hudu da suka
gabata.
Ire-Iren wadannan zarge-zargen na cin zarafin fursunoni yayin da ake binciken su
ya sake tasowa ne cikin watan Afrilun da ya gabata ne lokacin da aka nuna hotunan wasu tsararrun da suke cikin wani mawuyacin hali na galabaita da kuma muzantawa a hannun sojin Amurka da ke Iraki, wato a kurkukun Abu Ghraib. Babu shakka wadannan hotuna sun girgiza duniya, amma abin takaici sai aka buge da hukunta wasu kananan hafsoshi da kuma kananan sojoji.
Haka kuma dai irin wannan hanya ake bi wajen bincikar tsararru a can Guantanamo da nufin a tilasta su su amince cewa sun aikata wani laifi, kamar a ce suna da alaka da kungiyar Alka'ida, ko wata kungiya da ake alakanta ta da ayyyukan ta'addanci. Daga cikin wadannan hanyoyi akwai tozarta daurarrun ta hanyar cinna
musu karnuka, wulakanta Alkur'ani mai tsarki, kasantuwar mafi yawan wadanda ake
tsare da su din musulmi ne, ko kuma a hana musu abinci ko yin barci. Bugu da kari kuma suna amfani da wata hanya ta tozartarwa da sunan bincike, wato a ce sai an yi wa mutum binciken kwakwaf alhalin yana kwabe zindir, wato ta hanyar bincika cikin bakinsa, ko duburarsa, ko marainansa, ko farji. Ana kuma yin wannan cin zarafin ne hade da zagi na cin mutunci.
Sai dai abin takaici sai gwamnatin kasar Canada ta yi amfani wai kariya ta diflomasiyya ta hana a tuhumi Bush da wadannan laifuka da ake zargin sa, matakin da wani Jojin kasar mai suna William Kitchen ya yi watsi da shi. "Babu shakka wannnan ba hujja bace," a cewar Farfesa Michael Mandel, wani Lauya, yana mai cewa; "an gabatar da wadannan zarge-zargen bisa ka'ida da hujjoji masu karfi. Ita kanta gwamnatin ba ta karyata wadannan zargin ba saboda ba yadda za ta yi ta ce ba ta san su ba. Kuma ita kanta kariyar diflomasiyyar da aka fake da ita ba ka'ida bace, domin ko kadan ba ta shafi zarge-zargen ba. Abin tababa kawai shi ne a wacce kotu ya kamata a gabatar da su."
Ya ce, "ko da ma Bush yana da wannan kariyar, to, ai ta wucin-gadi ce, domin ba zai iya tsallake ta ba shi da sauran jami'an gwamnatinsa a kasar ta Canada a yayin da suka bar gwamnati. Kodayake dama dole za a tsammaci gwamnatin ta Canada za ta fake da wannan batun," in ji shi.
Paul Martin dai ya gayyaci Bush ne zuwa Canada alhalin yana sane da irin katobarar da Bush din ke aikatawa, wanda hakan ya saba wa dokokin kasa-da-kasa, duk kuma da cewa ya san bai halasta masa ba a matsayinsa na mai laifi ya shiga kasar ta Canada. Bugu da kari kuma ga masifa da bala'in da ya jefa Iraki a ciki ta hanyar kaddammar da haramtaccen yaki a kasar.
Wani Lauya da ke garin Vancouver mai suna Gail Davidson, wanda shi ne ya gabatar da wadannan zarge-zarge da ake yi wa Bush ya ce; "muna da tarin hujjoji na kishiyantar wannan mataki. Ba mu ga wata hujja ta hana shari'a ta yi aikinta, domin batun cewa akwai wata kariya ta diflomasiyya bai ma taso ba, domin ba ya bisa ka'ida."
A shekarar da ta gabata din ne dai a wata shari'a da aka yi a boye ba tare da
manema labarai ba, inda wani babban Antoni-Janar ya zartar da cewa Bush na da kariya ta diflomasiyya wanda hakan zai iya hana wa a kama shi a hukunta shi a Canada, kuma
ya haramta buga duk wani abu da yake da alaka da wadannan zarge-zargen da ake yi masa.
Sai dai a makon da ya gabata ne wata kotun koli ta soke wancan haramci da aka sa na hana buga batun, kamar yadda wata jarida mai suna COUNTERPUNCH ta ruwaito;
"wannan ba karamar nasara bace," in ji Davidson, yana mai cewa; "saboda ta tabbatar da cewa haka zai bai wa mutanen Canada dama su bi diddigin lamarin da ma sauran al'ummar duniya baki daya don a tabbatar an yi amfani da doka ta yadda Bush ba zai kubuta daga munanan laifukan da ya tafka ba."
Ya ci gaba da cewa; "ga dukkan alamu dai tsarin shari'a na Amurka ya gaza ya hukunta shi alhali akwai hukumomi na duniya masu wannan ikon. Don haka ya rage wa Canada ta tabbatar da aiki da wannan doka,"
Davidson da Howard Rubin da Jason Gratl da kuma Micheal Vonn, wadanda suke wakiltar kungiyar kare hakkin dan Adam, sun shiga kotun ne da karfin gwiwar cewa lalle sai a dage wannan haramci na buga batun, kuma suka yi nasara bayan mintuna 50 ana tafka muhawara.
Yanzu haka dai an sake sa ranar 25 ga Nawambar bana a matsayin ranar da za a ci gaba da sauraron wannan karar a babbar kotun koli da ke garin Vancouver.
Haramtacciyar kasar Isra'ila ta kaddamar da hare-hare ta sama a yankunan Palasdinawa, bayan ta kaddamar da wani harin ta kasa kwanaki biyar kafin a gudanar da ranar Kudus ta duniya.
An ba da rahoton cewa mutane biyar ne suka samu raunuka kuma akalla sun rusa wani gini duk a can Arewacin Gazza.
Wadannan hare-haren sun zo ne sa'o'i bayan da kungiyar Islamic Jihad a Gazza ta ba da sanarwar ta harba rokoki don ramuwar gayyar kisan wani babban Kwamandanta.
Ita dai Kungiyar Islamic Jihad ta ce ta harba rokoki 20 daga Arewacin Gazza bayan da aka kashe Luay Saadi a wani hari da Isra'ila ta kai garin Tulkaram na Yamma da Kogin Jordan.
A wata sabuwa kuma wani babban jami'in Hamas ya nemi Hukumar gudanarwar Palasdinu da kada ta kuskura ta amince da shawarar Isra'ila na cewa kada a bar Hamas din ta shiga zaben 'yan Majalisa da za a yi a watan Junairun badi.
Wani Shugaban Hamas din a garin Nablus, Shaikh Yasser Mansour ya ce, a matsayinta na wata Harka mai adawa da mamaya, Hamas na da 'yancin shiga wannan zaben da za a yi.
Ya ce Isra'ila na ta faman fadi-tashin ganin, sai an haramta wa Hamas shiga zaben ne ta hanyar bayyana ta da cewa wai kungiya ce ta ta'addanci.
Mansur ya kara da cewa Hamas ba za ta ba da kai bori ya hau ba, kuma sai ta shiga zabukan da za a yi.
Shafin Gamji | Tafsirin Alkur'ani | Hadisai | Crescent International |