Jarida don Karuwar Musulmi
Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki ISSN 1595-4471
Juma'a 10 Shawwal, 1426
Bugu na 691
Tunatarwa | | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari Tattaunawa | Labarai |
Babi na uku:
Ma'asumancin Manzon Allah (2)
"K o da na gaya wa Mu'awiyah wannan zance, sai kuma ya ce: 'Na fi gaban haka, na fi gaban haka. Wani abu ni zan bari da za a rika tunawa da ni?' Mu'awiyah ya ci gaba da cewa; 'Dan uwanmu Abubakar ya yi mulki, ya shuka adalci, kuma ya aikata abin da ya aikata, amma yana mutuwa aka manta da shi, sai wadanda idan suka tuna da shi sai su ce Abubakar. Haka nan kuma dan uwanmu Umar ya yi mulki mai tsanani na shekaru goma, amma yana mutuwa aka manta da shi, sai idan an tuna da shi ake cewa Umar. Sai kuma dan uwanmu Usman ya yi mulki, ya aikata abin da ya aikata, shi ma sun aikata masa abin da suka aikata, amma yana mutuwa suka manta da shi, da abin da aka yi masa. "Mu'awiyah ya kammala da cewa; 'amma su kuwa 'yan uwan Hashim, a kullum suna kururuwa sau biyar a rana suna cewa, 'mun shaida Muhammad Manzon Allah ne.' To, wane tunawa za a yi wa mutum kamar haka? Sai dai kawai idan ya mutu a turbude shi a cikin kasa." Hakika Allah ya kunyata Mu'awiyah Bin Abu Sufyanu, domin dukkan kokarin da ya yi na ganin an manta da ambaton Manzon Allah (SAWA) bai yi nasara ba. Ya yi amfani da duk wani abin da yake da shi domin samun wannan dama, amma duk bai yi nasara ba. Mu'awiyah, Allah yana kallon dukkan abin da ka aikata, domin shi ne ya gaya wa Manzonsa (SAWA) cewa; "MUN DAUKAKA AMBATONKA." Allah ya cika haskensa duk kuwa da irin makarkashiya da munafunci, da kuma cogen da ka yi a cikin addininsa. Ka yi mulkin yammaci da gabashi, amma kana mutuwa aka manta da kai. Duk wanda ya tuna da kai, idan har ya san gaskiyar abin da ka aikata, yana tunawa da irin aika-aikar da ka aikata ne domin ka ruguza Musulunci. Za a rika tunawa da Muhammad Dan Abdullahi (SAWA), kuma dan uwa ga Banu Hashim, daga karnoni zuwa karnoni, daga al'umma zuwa al'umma, har lokacin da Allah zai tabbatar da addininsa a bayan kasa, da mutanen da za su gaje ta. A duk lokacin da aka ambace shi, za ka ji ana yi masa salati, tare da Iyalan gidansa tsarkaka. Wannan abu ya tabbata, kuma zai ci gaba da tabbata har karshen duniya, duk kuwa da makarkashiyar Mu'awiyah, da 'yan uwansa Banu Umayya. Maimakon makircinsu ya rage wa Manzon Allah da Iyalan gidansa daraja, sai ma darajarsu ta kara daukaka. Tabbas, Mu'awiya za ka gamu da Allah a ranar kiyama, dangane da abubuwan da ka kirkira a cikin addininsa, kuma zai yi maka hukuncin da ya dace kai. Idan kuma muka waiwayi dansa, Yazidu Bin Mu'awiyah, mai abin kunya, mashayin giya, wanda ke takama da sabon Allah a fili, za mu ga cewa ya yi gadon halayya irin na Mahaifinsa Mu'awiyah, da Kakansa Abu Sufyanu. Da a ce bai yi gadon wadannan munanan halaye ba, da Mahaifinsa Mu'awiyah bai dora shi a kan shugabancin musulmi ba. Dukkaninsu, sun san halayensa a lokacin da yake raye, musamman dan Husaini Bin Ali, Shugaban Samarin Aljanna (AS). Babu kokwanto cewa, Mu'awiyah ya tafiyar da rayuwarsa, sannan ya karar da dukiyar da ya tara wajen kokarin rusa Musulunci. Mun ji yadda ya yi kokarin binne ambaton Manzon Allah (SAWA). Da bai yi nasara ba kuma ya shirya yaki da dan uwan Manzon Allah, Ali Bin Abi Talib. Sannan kuma ya sunnata wata tsinanniyar sunna ta la'antar Ali Dan Abi Talib, har ma ya umurci Gwamnoninsa na kowane sashe, su rika la'antar Ali da sauran Iyalan gidan Manzon Allah (SAWA) a kan mumbarorin salla. Ya yi haka ne a kokarinsa na la'antar Manzon Allah (SAWA). A cikin littafin Al-Aqd-Al-Farid, juzu'i na 2, shafi na 301, Ibn Abd Rabbih ya ruwaito cewa, Mu'awiyah ya sunnata la'antar Imam Ali a kan mumbarorin salla, kuma ya rubuta wa dukkanin Gwamnoninsa a lokacin, ya ba su umurnin su ma su rika la'antar Imam Ali a lokacin salla, kuma suka yi hakan. Har Ummul Salama, matar Manzon Allah, ta rubuta wa Mu'awiya wasika, tana ce masa; "Kana la'antar Allah da Manzonsa a kan mumbarorin salla, domin kana la'antar Ali da masoyansa! Na rantse da Allah, kuma na shaida cewa Allah da Manzonsa suna kaunar Ali." Amma duk da wannan wasika da ta aika masa, bai daina la'antar Ali ba. Za mu ci gaba insha Allah. |
Shafin Gamji | Tafsirin Alkur'ani | Hadisai | Crescent International |