Almiza:Musakan jihar Zamfara sun koka ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 10 Shawwal, 1426                 Bugu na 691                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Rahotanni

Musakan jihar Zamfara sun koka

H

Musakan jihar Zamfara sun bayyana takaicinsu a kan yadda aka kwashe su zuwa Kaduna suna yi wa Gwamna Zamfara kamfe na tsaya wa takarar Shugaban kasa, amma aka wulakanta su a can suka tagayyara babu ko kudin abinci.

Wani Shugaban kungiyar musukan na wata Karamar Hukumar a jihar ta Zamfara da ya bukaci a sakaya sunansa ne ya bayyana wa jaridar ALMIZAN irin takaicinsa kan irin halin da suka shiga a Kaduna lokacin da suka je wajen wani taron kara wa juna sani da kuma yi wa Yarima kamfe da aka yi a jihar Kaduna kwanakin baya.

Shugaban kungiyar musakan ya zargi Shugaban musakan jihar Zamfara, Alhaji Ibrahim Sani Bakura da cewa an kwashe su daga gidajensu da yarjejeniyar za a ba su wani adadin kudi a can Kaduna don su ci abinci, sannan an tanadar masu ingantaccen wurin kwanciya, "amma muna zuwa can sai muka ga akasin haka."

Ya ce, "mun je Kaduna, wasu ba su taba sanin can ba balle su san inda za su. Mun wahala sosai. Sannan wani babban abin takaici tun zuwanmu ba mu sake sa Shugaban musakan Zamfara a ido ba, sai can mu ga wasu 'yan Majalisa da wasu manyan ma'aikata, amma ba wani tasiri, don ba su amfana mana komai ba," in ji shi.

Saboda haka, musakan suna kira ga jagororin nasu na jiha da na kasa cewa don Allah su daina yin amfani da sunayensu don cimma wasu bukatu nasu, kuma idan an ba su wasu hakkoki na jama'arsu, to, su rinka adalci.

A cewarsa, su tuna fa sai sun yi bara su sami abinci, an hana su bara, kuma an je an tagayyarar da su ba alfanu tun daga gidajensu har Kaduna. "Nan gaba kenan sai ku sake yi mana dadin baki ku kwashe mu zuwa Abuja ku je ku yi mana fiye da haka," ya ce.

Amurka ba ta da manufar alheri a kan

musulmi

In ji Malam Kasim Umar
Daga Yakub Almafary

"Akwai ban mamaki da ban takaici ganin yadda al'ummar musulmi suka rikirkice suka kidime wai a kan hasashen da kasar Amurka ta yi na cewa ai nan da shekaru 15 Nijeriya za ta wargaje."

Malam Kasim Umar Rimin Tawaye, Wakilin 'yan uwa Musulmi na Sakkwato ne ya bayyana wannan takaicin nasa lokacin da yake wata hira da Wakilinmu dangane da wannan rahoton da kasar Amurka ta bayyanar.

Malam Kasim Umar ya ci gaba da bayyana cewa babu shakka akwai wadansu makirce-makirce da gadar zare da ita Amurka ta sha kulla wa Nijeriya tuntuni har zuwa yau din nan da take wannan hasashen, "kamar lokacin aukuwar makirce-makircen ya kusa kuma tana ganin za su jefa kasar nan cikin wani mummunan hali, shi ya sa ta fitar da wannan rahoton," in ji shi.

Malamin kuma ya kara da cewa, sai dai kuma al'ummar musulmi ya kamata su sani, ita Amurka sharrinta ga dukkan al'ummar musulmin duniya ba daya bane, sannan a kullum cikin kulle-kulle take a kan yadda za ta jefa musulmin duniya cikin bala'i don ba ta da manufar alheri a kansu.

Ya ce, "to yaya za mu yi tsammanin Amurka ta aikata ko ta fadi alheri ko ta jawo wani alheri zuwa ga musulmi tunda Musulunci da musulmi sune manyan makiyanta dare da rana?"

Saboda haka Malam Kasim ya yi kira da kakkausar murya ga al'ummar musulmi cewa a kan wannan rahoton na Amurka bai kamata su harzuka su tayar da hankalinsu ba. "Ba haka ya kamata mu hangi wannan hasashen ba. Ai abu ne sassauka. Da a ce talakawa sun san hakkin kansu da ba su ma kula da maganar ba."

Malam Kasimu Umar ya ce, "abin da ya kamata mu yi shi ne, mu koma ga Allah da addininsa dari-bisa-dari, kasar sai ta tarwatse da sunan addini, sai addinin Allah ya maye kasar. Amma abin da Amurka take so a nan shi ne a mika mata kai a ce mata, to, menene mafita? Sai ta zo ta sami shiga gadan-gadan. In da can da an fito bautar Ingila, yanzu kuma sai a koma bautar Amurka da hujja!"

Ya ce, "abin da muke tsammani daga Allah shi ne addinin Musulunci zai mamaye kasar nan ko Amurka ta so, ko ba ta so ba. Kuma wannan hasashen nata na banza ne, kuma zai tafi a banza. Karshe guguwar addinin da za ta kada za ta je har can ta tarwatsa ta," in ji shi.

Hasken Ahlul Baiti ya fi karfin dushewa

In ji Malam Abubakar Nuhu T/Mafara
Daga Yakub Almafary

An bayyana cewa hasken Allah idan ya bayyana, to, ya fi karfin dushewa ga kowa, haka kuma lamarin addinin Musulunci. Yayin da duk gaskiya ta bayyana, to ta fi karfin wani mai kokarin rufewa, balle har ya iya rufe ta din.

Wakilin 'yan uwa musulmi na garin Talata Mafara ta cikin jihar Zamfara, Malam Abubakar Nuhu ne ya yi wannan bayanin lokacin da yake wani jawabi a harabar masallacin Juma'a da ke garin.

Malamin ya ci gaba da bayyana cewa, idan muka dubi al'umarin bayyanar Manzo (SAW) da sakon da aka aiko shi da shi da kuma lura da irin halin da Iyalan Gidansa Tsarkaka (AS) suka shiga, "tun a rayuwarsa da bayan wafatinsa, yayin da makiyansa sun yi iya yin su don su dushe haske da darajojinsa, amma ina! Allah ya ki. Duk da karfin mulki na zalunci da suke jin suna da shi, amma bai hana haskensa da darajojinsa su watsu a duniya ba."

Malam Abubakar Nuhu ya ci gaba da cewa, Imam Ali (AS) yana da wasu darajoji hudu wadanda babu mai irin su duk a sahabbai. "Fuskarsa ba ta taba sujada ga gunki ba, Manzon Allah (S) ne surikinsa, Shugabar mataye gaba daya; Fatima (AS) ita ce matarsa, sannan Hasan da Husaini (AS) Shugabannin Samarin Aljanna ne 'ya'yansa." Ya ce, "hadisi ya zo kan cewa ba domin haihuwar Imam Ali (AS) ba, da Fadimatuz-Zahra (AS) ta rasa mijin da za ta aura a duniya."

Haka kuma Malam Abubakar ya bayyana cewa Imam Ali (AS) ya sami wadannan darajoji, daukaka da fifitashin da Allah ya yi ne birbishin dukkan sahabbai a sanadiyyar biyayyarsa ga Manzon Allah (S).

Ya ce tabbas Imam Ali ne ya fi kusanci ga Manzon Allah (S), "ya girma a gidan Manzo (S), ya sha ruwan wahayi da tarbiyya da ruwan ilimi daga wajen Manzo (S), sannan kuma yana ganin girman jagoranci da sakon da Allah ya aiko Manzo (S) da shi ga talikai."

Madrasatul Fodiyya Kaura-Namoda ta raba kyaututtuka

A kwanakin baya ne Madrasatul Fodiyya Islamiyya da ke garin Kaura-Namoda a jihar Zamafa ta yi bikin ba da kyaututtuka ga hazikan dalibanta, wadanda suka ba da kokari a fannoni daban-daban na karatun shekarar bana.

Da yake jawabi a wajen taron, Shugaban makarantar, Malam Labaran Ishak Alkasim, ya bayyana asalin sunan Fodiyya kanta da dalilin assasa makarantar, inda yake cewa sunan ya samo asali ne daga sunan Shehu Usman Danfodiyo, kuma Malam Zakzaky ne ya ba ta suna Fodiyya don kamanta ayyuka irin na Shehu Danfodiyo.

Kuma ya tabo asalin kafuwar ita kanta wannan Fodiyyar ta Kaurar-Namoda da cewa an fara karatu ne da dadewa, "yanzu tana da dalibai sama da 150 da kuma Malamai masu ba da gudummawa 21.

Bayan Malamin ya kare bayaninsa ne, sai aka saurari karatu daga bakin dalibai. Sun dai yi karatun ne a bangaren Alkur'ani da Hadisi, sai Seera, Tahzibi da kuma Arabiyya. Karatun ya kayatar kwarai da gaske.

Bayan nan sai aka shiga raba kyaututtuka daban-daban, inda aka ba da kyauta ga daliban da suka nuna kwazo da hazaka, da kuma daliban da suke zuwa makaranta a kan lokaci, da kuma ga daliban da ke da tsafta, kuma an ba da kyauta ga dalibin da ya fi saura tarbiyya da kuma kyauta ga masu hidima ga makaranta.

Da yake jawabi a wajen taron, Malam Aliyu Adamu Takakume, ya jawo hankalin al'umma da su tashi tsaye su ba yaransu tarbiyya ta kwarai don kada su tsaya gwamnati ta ba yaransu tarbiyya.

Malamin ya kara da cewa sata kawai azzaluman mahukunta suka sa gaba, don haka ya ce jama'a kada su sake zaben su. Ya ba da misali da kudin da Janar Ta-zarce ya sata. Ya ce in a ce za a raba wa mutanen Nijeriya ne ko da yau aka haifi jinjiri, to zai samu miliyan daya.

Daga karshe Malamin ya jawo hankalin iyayenmata da su tashi tsaye su ga sun ba yaransu tarbiyya ta kwarai, don kuwa makaranta ta farko ita ce uwa mace. "In ka ga yaro ya tashi da tarbiyya daga uwa ne."

An dai kare taron ne da rufe taro da addu'a daga bakin Na'ibin Limamin masallacin Juma'ar garin, Malam Altine Kaura-Namoda.

Ba mu gamsu da zaben da PDP ta yi ba

In ji Alhaji Ibrahim Taiwo

Wani dan jam'iyyar PDP a jihar Kaduna, Alhaji Ibrahim Taiwo Gadar Gayan, ya bayyana rashin gamsuwarsu da zaben shugabannin jam'iyyar PDP na jihohi da aka yi a karshen makon nan.

Alhaji Ibrahim Taiwo, ya bayyana rashin gamsuwar tasa ne a lokacin da yake zantawa da ALMIZAN jim kadan bayan an bayyana wadanda suka lashe zaben shugabannin jam'iyyar da aka yi a duk fadin kasar nan.

Ya ce, "mu ba su gaya mana za a yi zabe ba, a matsayinmu na wadanda muka tsaya takara a jam'iyyar, muna sa ran da an yi zabe da ma da mu muka ci, amma da yake ba su gaya wa kowa ba, sai suka bayyana wadanda suka lashe zabubbukan da aka yi. Kamar yadda aka yi na da, na yanzu ma haka aka yi."

Alhaji Ibrahim Taiwo, ya tabbatar da cewa ba wani zabe da aka yi, an dai yi nadi ne kawai. "Wa ya yi zabe? Su suka nada kansu. Ba abin da za mu ce sai dai mu ce an danne mu, an hana mu motsawa. Da an kyale mu, da mun kai gaci. Amma ba yadda za mu yi da su."

Sai dai duk da haka ya tabbatar da cewa ba su da shirin ficewa daga cikin jam'iyyar ta PDP duk da wannan abin da ya kira da danniyar da aka yi masu. Ya ce, "ba za mu janye ba, muna nan tare da su. Idan har muka janye ba mu yi wa magoya bayanmu da kuma jam'iyyarmu ta PDP adalci ba. Muna nan cikin PDP kamar yadda su ma suke cikin PDP, sai dai za mu san matakin da ya kamata mu dauka a nan gaba," in ji shi.

Alhaji Ibrahim Taiwo, wanda ya tabbatar da cewa ana yi masu wannan danniyar ne sakamakon goyon bayan da suke yi wa Alhaji Falalu Bello, ya ce, amma duk da haka masu neman yi masu makarkashiya ko kafar ungulu ba za su kai gaci ba. "Muna bukatar a yi adalci. PDP ta kowa da kowa ce. Ba ma son a ce an yi nadi, mun fi son a zabi wanda ya cancanta, amma ba a yi nadi ba."

Ya ce, wadannan shugabanin da aka 'nada' 'yan PDP ba za su amfana da su ba, kuma ba sa yin na'am da su. "Sai dai su a tsakaninsu ne za su amfana, amma ba mutanen PDP da na Nijeriya ba. Mu dai ba ma murna da wannan 'ta-zarcen' da aka yi a jam'iyyar PDP a jihar Kaduna," ya jadadda.

Alhaji Ibrahim Taiwo, ya yi hannunka mai sanda ga masu mulkin, inda ya bayyana cewa; shi dai mulki na Allah ne, duk wani magudi ba zai hana wanda Allah ya nufa ya zama Shugaba ya zama ba. "Ka manta da Obasanjo ne? Ba yana kurkuku aka fito da shi ya zama Shugaban kasa ba? Mandela shekarunsa nawa a kurkuku? Amma daga bisani ba ya fito ya zama Shugaban kasa ba? Don haka mulki na Allah ne. Wannan magagin barci kawai suke yi. Duk abin da suke yi ba zai hana wanda Allah yake so ya zama wani abu ba."

Da yake tsokaci game da yanayin mulkin Karamar Hukumar Igabi, Alhaji Ibrahim Taiwo, ya koka matuka a kan yanayin jagorancin yankin. Ya ce tunda aka zabi Alhaji Sulaiman Husaini ba wani abu da ya yi wa yankin.

Alhaji Ibrahim Taiwo ya zargi Shugaban Karamar Hukumar Igabi da yin mulkin danniya, babakere da kashe-mu-raba. Ya ce, "Alhaji Sulaiman Husaini ya manta da wadanda suka zabe shi, ya dauka mutum daya ne kawai ya zabe shi ba mutanen Igabi ba. Mu mutanen wannan yankin sai dai mu jira Allah ya yi mana canji mafiya alheri kawai."

Ya koka matuka da yadda Shugaban Karamar Hukumar ta Igabi ya yi watsi da bukatun jama'ar yankin ya rungumi mutum daya kawai yana sa shi yana hana shi, "ya dauke shi kamar Ya Rasulullahi. Mu dai mutanen Igabi mun yi zaben tumun dare," ya fada.

Ya yi kira ga daukacin jama'ar Karamar Hukumar Igabi da su saki kowa su kama Allah, su daina ganin wani zai yi masu arziki ba Allah ba. "Su kuma kama sana'a kada su dogara da siyasa, siyasa ba komai bace. Su daina tunanin sai da wane za su rayu. Idan kuma zabe ya zo su tashi su yi zabe na kirki, kada su sake kwata 'yar gidan jiya," ya karkare.

Alhaji Ibrahim Taiwo

26 ga Nuwanba za a bai wa Sarkin Borgu sanda

Daga Musa Muhammad Awwal

Wata sanarwa da ta fito daga bakin Sakataren Masarautar Borgu da ke cikin jihar Neja, Alhaji Muhammadu S. Dantoro, Marafan Borgu, ta bayyana cewa a halin da ake ciki dai gwamnatin jihar Neja ta sanya ranar Asabar 26 ga watan Nuwambar nan a matsayin ranar da za a yi bikin bai wa Sarkin Borgu, Kitoro III, Sanata Alhaji Halliru Dantoro sandar girma a matsayin Sarkin Borgu na 16.

Sanarwar, wacce aka raba wa manema labarai, ciki har da ALMIZAN, ta kuma ce za a yi wannan gagarumin biki ne a filin taro na Sabuke, wato Sabuke Square da ke babban birnin na Karamar Hukumar Borgu da misalin karfe 10:00 na safe.

Gwamnan jihar Neja, Alhaji Abdulkadir Kure ne zai mika wa Sanata Alhaji Halliru Dantoro wannan sanda a matsayin Sarki mai daraja ta daya.

Sanarwar ta ci gaba da bayyana cewa ana sa ran halartar dukkan tsofaffin Shugabannin kasar nan, Gwamnoni masu ci da na da, Sanatoci, Ministoci, Jakadun kasashen waje da ke nan kasar, Sarakuna, Oba-Oba na Yarabawa, Eze-Eze na yankin gabashin kasar nan, tare da sauran al'ummar kasar na masoya.

Alhaji Muhammadu S. Dantoro, ya kuma shaida wa manema labarai cewa shirye-shirye dai sun yi nisa inda daukacin al'ummar kasar Borgu suka hada karfi da karfe domin ganin cewa wannan biki ya gudana cikin tsari mai kyau da kwanciyar hankali. Sanata Alhaji Halliru Dantoro, Kitoro III

Jihar Zamfara ce a gaba wajen zaman lafiya

In ji 'Yan Doton Tsafe

Alhaji Habibu Aliyu, 'Yan Doton Tsafe, ya bayyana cewa jihar Zamfara ce a gaba wajen zaman lafiya a tsakanin al'umma a duk fadin kasar nan.

Sarkin na Tsafe, ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kaduna kwanan baya.

Alhaji Habibu ya ce, jihar ta Zamfara ta sami wannan nasara ce saboda irin biyayyar da al'ummar jihar ke yi wa shugabanninsu. Ya ce, "mutanen jihar nan mutane ne da suke bin shugabanninsu kuma da bin dokoki na kasa."

Saboda haka sai 'Yan Doton ya yi kira ga jama'ar tasa da su ci gaba da samar da irin wannan zaman lafiya, wanda ya ce, shi ne ginshikin komai na rayuwa. "Wanda kuma alhamdu lillahi ina ganin ma akwai lokacin da aka ce jihar Zamfara ta fi kowace jiha a Nijeriya zaman lafiya. Ba komai ya kawo wannan ba, sai taimakon Allah," in ji shi.

Game da taimakon al'umma kuwa, 'Yan Doton Tsafe cewa ya yi, su sun gode wa Allah a jihar Zamfara domin gwamnatin jiharsu ta Ahmad Sani ta fito da hanyoyi don taimaka wa jama'a, "an yi kwamitin zakka da wakafi da jiha, an kuma yi na kowace masarauta, wanda yake kowane Sarki shi ke shugabantar wannan kwamitin," ya ce.

Alhaji Habibu Aliyu ya ci gaba da cewa; ta wannan kwamiti, gwamnati take bayar da kayayyaki domin bayarwa ga jama'a don samun abin neman kwabo. Ya ce tana bayar da injinan nika, markade da sufe, "ana bayar wa ga mabukata musamman marayu domin su dogara da kansu."

Haka kuma Sarki ya bayyana cewa wannan kwamiti na Zakka da wakafi yana raba kudi ga gajiyayayyu domin samun abin masarufi.

Game da batun aikin gona kuwa, 'Yan Doton cewa ya yi, gwamnatin jiha Zamfara a tsaye take domin ganin ta bunkasa aikin noma ta hanyoyi da dama. "Yanzu misali a bara a masarautata, Tsafe kawai, na sami mota 54 ta taki wadda gwamnati ta ba mu muka bayar bashi. Amma a bana na samu mota 135 na taki muka raba wa manoma," in ji shi.

Sarkin ya ce, kuma an yi kyakkyawan shiri domin samun ganin an biya wannan bashi. Ya ce za a biya ta hanyar bayar da amfanin gona ne. Bayan da kuma akwai shirin 'inshora' a cikin wannan harkar, wadda shi manomin da ke cikin wannan shirin ba zai yi asara ba.

Game da batun sayen kayan amfanin gona daga hannun manoma kuwa, 'Yan Doton Tsafe cewa ya yi, "gwamnati ta yi kyakkyawan shiri a kan wannan. Gwamnati ta shirya, maimakon mutum ya biya bashin da aka ba shi da kudi yana iya biya da amfanin gona, kamar dawa, gero, masara da sauransu. Za a amshi kowane buhu a kan N4,000 sabanin farashin kasuwan da bai kai N2,000 ba.

Dubun 'yan fashi a Zamfara ta cika

Daga S. Samaru

A cikin makon jiya wasu matasan Fulani kimanin su tara da dattawa guda uku dubunsu ta cika bayan sun fita aikin dare, a yayin da suka aikata fashi da makami tare kuma da fyade a wani kauye da ake kira Marbe cikin Karamar Hukumar Tsafe a jihar Zamfara.

Kama wadannan matasa ya biyo bayan mutum daya da aka kama mai suna Abubakar; shi kuma ya tona asirin sauran.

Su dai wadannan matasa ana zargin su da fashin makudan kudade daga wasu maza ne tare kuma da yi wa wasu mata fyade su uku, ciki har da mai juna biyu, wadda a sanadiyyar wannan fyade cikinta ya zube.

Su dai wadannan matasa sun karyata wannan zargi da 'yan sanda suka yi masu. Wasu daga cikin su sun ce Abubakar ne kawai ya ambaci sunansu.

Shi dai Abubakar shi ne aka ce shugabansu, shi kuma ya ce bai san hawa ba balle sauka da asuba zai yi sahur aka kama shi wai sun yi fashi.

Wani daga cikinsu mai suna Sani ya gaya wa manema labaru cewa ita bindigar toka da aka same shi da ita ta ardo ce da ya ba shi don yana masa kiwon shanu yana ba shi lada.

Shi kuwa Ardo mai kimanin shekaru sittin, shi ma ya karyata wannan zargi da ake yi masu. Ya kara da cewa ita bindigar da ake magana ta fi shekara goma a hannunsa yana bai wa yara suna masa kiwon shanu; cikin yaran kuma har da shi Sanin.

Shi kuwa Mataimakin Kwamishinan 'yan sanda na jihar Zamfara, Mark A. Idakwo, a zantawarsa da manema labaru a ofishinsa da ke Gusau, cewa ya yi suna nan suna bincike, kuma bincikensu ne zai tantance wadanda ba 'yan fashi bane daga cikinsu. Kuma suna nan suna kai gwauro suna kai mari sai sun gano wadanda suka ari takalmin kare suka bai wa hanya kashi daga cikinsu.

Mataimakin Kwamishina, Mark, da aka tambaye shi cewa ba ya ganin wadannan za su iya guduwa kamar yadda ya faru a baya da wasu, sai ya ce, ko alama, in Allah ya yarda ba zai faru ba. Kuma sun dauki duk matakin da ya dace don kaucewa aukuwar hakan.

Daga karshe ya mika godiyarsa ga Gwamnatin jihar ta Zamfara da kungiyar 'yan sintiri da al'ummar jihar Zamfara da suke ba su goyon baya.

Amurka na amfani da cusa wa fursunoni cuta don tatsar bayanai a Guantanamo

Bayanin da ya fito daga Sami Alhaj, wani fursuna da ke tsare a sansanin ihunka-banza na Guantanamo da ke Cuba ya tabbatar da cewa sojojin Amurka na amfani da cusa wa fursunoni kwayoyin cuta don su takura su wajen tatsar bayanai.

Sami Alhaj ya kara da bayyana cewa a kowace rana mutum ya yi kusa da wuraren da fursunoni ke daure da sarkoki zai rika jin nishi na tsananin rashin lafiya na fursunonin da suka kamu da wata rashin lafiya sabuwa, wadda a da can ba su da ita. Sannan kuma babu wani himma da Amurkawan suke nunawa wajen kawo Likita don duba su ko tanadar magunguna na sha. Sami Alhaj ya kawo misalin wani fursuna dan asalin kasar Marocco da aka kama, wanda ya samu karaya a lokacin da ake kokarin kawo shi Guantanamo tun shekara ta 2001 har yanzun yana nan a cikin wannan halin na azaba.

Alhaj ya ce da yawa suna fama da ciwon hakori saboda matsalolin da suke ciki, kuma babu wani kulawa da suke samu, saboda haka nan haka suke ganin dare kamar yadda suke ganin rana babu barci.

Har yanzun da yawa daga cikin fursunonin da aka kame tun shekaru hudu da suka gabata ba su san me ya sa aka kama su, ballantana ma a gurfanar da su gaban kuliya, don haka nan su ba su san ranar ganawa da masoyansu ba.

Sami Alhaj shi ma yana cikin ma'aikatan tashar Aljazeera wadanda suka shiga wannan bala'in na ta'addancin Amurka.

Harkar Musulunci za ta bude tashar Talbijin da Radiyo ta hanyar tauraron dan Adam

Daga www.harkarmusulunci.8m.net

Shaikh Ibraheem Yaqoub Zakzaky ya gabatar da wani jawabi a karshen wani taron karawa juna ilmi na tsawon kwanaki biyu da aka gabatar daga ranakun 4-6 ga watan Nuwamba na wannan shekara a Zariya.

A lokacin da yake gabatar da jawabinsa, Shaikh Ibraheem Zakzaky ya bayyana yadda ya kamata a yi amfani da kudaden da ake tarawa na Harkar Musulunci, inda ya nuna cewa kungiyoyi a halin yanzun suna gudanar da ayyukansu ne ta hanyar tattara gudummuwa daga 'ya'yan kungiyoyin nasu, wadanda a mafi yawan lokuta ma'aikatan gwamnati ne.

Sannan sai Shaikh Zakzaky ya nuna cewa a halin da wannan kasa ke ciki a yanzun, mafi yawan ma'aikata ba wani abin kirki suke samu ba a kowane wata a matsayin albashinsu, wadansu lokutan ma sukan share watanni ba a yi albashi ba, sannan su kansu ba sa iya rike lalurarsu zuwa wata daya kamili da albashin nasu.

Haka nan Shaikh ya bayyana cewa wadanda suke rike da kudi a kasar sune 'yan siyasa wadanda ba zai yiwu a iya samun wani abu daga gare su ba, saboda haka nan ya wajaba mu da kanmu mu samar da yanayi na shigar kudade don aiwatar da ayyukanmu na yau da kullum.

A wani bangare na jawabin nasa, Shaikh Zakzaky ya bayyana shirin Harkar na fito da wata tashar talbijin da radiyo wadanda za a rika watsa su ta hanyar tauraron dan Adam.

Haka kuma ya nuna muhimmanci samar da wata jarida ta harshen Turanci wadda za ta rika kai wa sassan da ba sa jin harshen Hausa a kasar. Sannan kuma ya nuna cewa yanzun haka dai za a fara nazarin farko na aiwatar da shirin ta hanyar tuntubar kwararru kan abubuwan bukata don cimma wannan buri.

Shaikh ya bayyana takaicinsa kan yadda wasu tashoshi ke watsa abin da suka ga dama da sunan mahanga ta addini, sannan ya nuna lalurar harkar Musulunci ta sami kafa nata tashar wadda za ta rika fadin nata mahangar.

Shaikh ya rufe taron daga karshe da addu'a.

An tuna da cika shekaru 41 da korar marigayi Imam Khumaini (RA) zuwa gudun hijira Turkiyya

Kimanin shekaru 41 da suka gabata, a ranar 4 ga watan Nuwamban shekara ta 1964 jami'an tsaron Sarki Shah na Iran da aka hambarar suka tafi birnin Qum, inda marigayi Imam Khumaini (RA) ke zaune suka kama shi sannan suka fitar da shi daga kasar zuwa gudun hijirar farko kasar Turkiyya.

Tun cikin daren ranar hudu ga watan na Nuwamba ne dai jami'an tsaron na hambararren Sarkin kasar, Shah, suka tafi gidan marigayi Imam da ke can birnin Qum, inda suka kama shi sannan suka nufi filin jirgin saman Mehrabad da ke Tehran da shi sannan suka saka shi a jirgi suka kore shi daga kasar.

Sarki Shah hambararre na Iran ya tsorata ne kwarai da gaske kan yadda kiran marigayi Imam Khumaini (RA) ya rika samun karbuwa a wancan lokacin tsakanin dukkanin bangarori na al'ummar kasar, saboda haka nan sai ya fara ganin babbar barazana ne kiran Imam zai kasance gare shi.

Babban abin da ya fi tayar wa Shah hankali a wancan lokacin shi ne irin yadda marigayi Imam ya kalubalanci shirinsa na kwaskwarimar mallakar filaye (Land reforms), don haka ya firgita ya ga cewa in dai yana son shirin ya tabbata, to dole ne sai Imam ba ya kasar, kamar yadda yake zato.

Imam a wannan shekara ya mai da babban ranar idi ta kasa da ake kira da 'noruz' a matsayin ranar juyayi, saboda juyayin irin yadda Shah ya mayar da kasar zuwa ga dogaro da kasashen waje.

An gudanar da manya-manyan gangamomi a dukkanin manyan biranen kasar saboda tunawa da wannan muhimmiyar rana ta tarihi a kasar Iran.

Ayatullah Sayyid Ali Khamna'i ne ya jagoranci sallar idin bana a Tehran

Jagoran al'ummar musulmi Ayatullah Sayyid Ali Khamna'i ne ya jagoranci dimbin al'ummar musulmin da suka halarci sallar idin karamar salla da aka gabatar a babban masallacin idi na marigayi Imam Khumaini (RA) da ke Tehran.

A lokacin da yake gabatar da huduba bayan sallar idi kamar yadda aka saba, Ayatullah Khamna'i ya fara ne da jawo hankulan al'ummar musulmi kan muhimmancin ci gaba da riko da kyawawan dabi'un da aka koya a lokacin ibadar watan Ramadan mai alfarma.

Haka nan kuma Ayatullah Khamna'i ya bayyana cewa idi a hakika shi ne ranar da mutum bai sabi Allah Ta'ala ba a ciki, kamar yadda ya zo a wata ruwaya ta Amirul muminin (AS). Saboda haka ya nuna cewa duk da yake dai musulmi za su yi farin ciki a wannan ranar, kuma za su sanya mafi kyawun tufafinsu, amma ya kamata a sani cewa babban abin da ake nufi da idi shi ne ci gaba da rashin saba wa Allah.

Sayyid Ali Khamna'i ya kawo wata kissa ta wani cikin manyan sahabban Imam Ali (AS) wanda ya je gidansa ranar salla, sai ya tarar da shi yana cin wani abinci kaskantacce. Saboda haka sai ya tambayi Imam Ali (AS) cewa yau ne ranar idi, amma ga shi ba ka kasance kana yin mu'amala kamar yadda sauran jama'a suke yi ba na cin abinci mafi dadi da dai sauran su ba. Sai Imam Ali (AS) ya ba shi amsa da cewa "Idi ita ce ranar da aka gafarta maka zunubai."

A wani bangare na jawabin Sayyid Ali Khamna'i ya tabo maganar mamayar da aka yi wa ofishin jakadancin Amurka da ke Tehran ne a shekara ta 1979, inda ya nuna cewa bayan wannan mamayar an iya tattara littafai mujalladi fiye da 100 kan bayanan irin yadda Amurka take makarkashiya ga Iran da sauran kasashen musulmi.

Sannan ya ce al'ummar Iran tare da dogaro da kansu da kuma tawakkali ga Allah Ta'ala ba sa tsoron dukkanin wani mahuluki.

Ayatullah Khamna'i ya mai da martani kan hayaniyar jawabin Ahmadi Najad

Jagoran juyin-juya-halin Musulunci a Iran, Ayatullahil Uzma Sayyid Ali Khamna'i ya mai da martani kan irin yadda kasashen yamma da haramtacciyar kasar Isra'ila suka rika yawaita hayaniya kan jawabin Shugaban kasar Iran Dk. Ahmadi Najad.

Ayatullah Khamna'i ya bayyana cewa kimanin shekaru goma da suka gabata ma Shugaban kasar wancan lokaci na Iran, ya yi magana kan kashe Ishaq Rabin, tsohon Firaministan haramtacciyar kasar Isra'ila, inda shi ma ya janyo mummunar hayaniya daga bangaren Yahudawa da kuma dukkanin kasashen da ke tare da su na wancan lokacin.

Sayyid Ali Khamna'i ya bayyana takaicinsa da rashin jin dadinsa kan yadda wasu kasashe suke tsananin tasirantuwa da zaluncin Yahudawan sahayoniya a duniya.

A wani bangare na jawabin nasa, Ayatullah Khamna'i ya bayyana irin yadda Amurka da wasu daga cikin kafafen yada labarai suke kokarin alakantar da wannan jawabi na Ahmadi Najad da lamarin mallakar makashin nukiliya na Iran. Sannan ya nuna cewa ai ba karfin nukiliya ne yake kifar da wata gwamnati ba, abin da yake kawar da mabarnata shi ne yunkuri na al'umma.

Haka nan kuma Jagoran ya jaddada cewa lallai yadda Palasdinawa suke fafatawa da Yahudawan sahayoniya, karshen lamarin zai kai su ga nasara.

Jagoran ya yi wannan jawabi nasa ne a lokacin da yake ganawa da wasu jami'ai da ma'aikatan gwamnati wadanda suka ziyarce shi a gidansa.

Dole ne mu kwato masallacin Kudus!!

In ji dubun-dubatar Musulmi a Bauchi
Daga Lawal K\Madaki

Kamar kowace shekara, bana ma da'irar Bauchi ta bi sahun jerin Da'irorin kasar nan wurin gudanar da jerin gwano (Muzahara domin juyayin Kudus, wadda ake wa lakabi da RANAR KUDUS TA DUNIYA.

Muzaharar, wacce aka soma ta bayan idar da Sallar Juma'a ranar 25 ga Ramadan 1426 (28 ga Oktoba 2005) 'yan uwa musulmi almajiran Malam Zakzaky (H) maza da mata, yara da manya daga ko'ina cikin fadin yankin na Bauci ne suka shiga jerin gwanon, wanda aka faro daga Masallacin Juma'a na Ajiyan Bauchi.

Duk da kasancewar ana cikin yanayi na Azumi, hakan bai hana nuna juriya daga masu muzaharar ba. Mafi yawan masu muzaharar sun rika shelantawa cikin izza da karfin murya "Mutuwa ga Isra'ila da Amurka! Allah ya tsine wa Yahudawa! Allah ya tsine wa Bush da Sharon!"

Ga kuma wani sashe na masu muzaharar da ke shelanta wa jama'r gari da suka yi dafifi a bakin titi suna kallon muzaharar dalilin fitowa da yin wannan jerin gwano, suna masu bayyana halin da Masallacin Kudus da kuma al'ummar musulmin wurin ke ciki, duk da cewa Masallacin shi ne mai daraja ta uku a duniyar Musulmi.

Harisawa kuwa abin ba a magana, domin ga sautin Badujala na tashi, ga kuma Digin da murza kwalta da suke yi, kai ka ce a ranar sallah ne ake muzaharar ba cikin azumi ba.

Muzaharar ta bana ta samu tsari sosai, domin goshin muzaharar jerin Babura ne da sauran ababen hawa, sai Harisawa a biye da su, sanye da fararen riguna da bakaken wanduna, ga tutocin Palasdinu, sannan ga wasu dauke da hotunan jagororin gwagwarmayar addini na duniya irin su Shaikh Ahmad Yaseen, Shahid Bakirul Hakim, Dk. Ahmad Rantisi, Sayyid Muktada Sadr da sauransu.

Wakilan 'yan uwa na garuruwan da ke jihar ta Bauchi su ma ba a bar su a baya ba, domin sune kewaye da Wakilin 'yan uwa na Bauchi, wato Malam Ahmad Yusuf Yashi. Can bayansu kuma dandazon 'yan uwa ne dauke da kwalaye masu nau'in rubuce-rubuce da ke dauke da sakonnin muzaharar kala daban-daban. Wasu a nuna goyon baya ga Palasdinawa, wasu na gargadi ga Amerika da Isra'ila, wasu kuwa kira ne ga musulmi da su fito mu yi sa'ayi wajen ganin mun 'yanto wannan masallaci mai daraja daga hannun Yahudawa.

Wani abin karin burgewa da ban sha'awa shi ne yadda 'yan uwa mata suka fito kwansu da kwarkwata cikin kuzari da karfin gwiwa, suna masu shelanta cewa dole ne Isra'ila ta bace daga doron kasa. "Dole ne mu share Isra'ila daga samuwa! Masallacin Kudus na Musulmi ne! Kwato shi ya zama wajibi!" in ji su.

A bangaren al'ummar gari kuwa, duk ta inda aka wuce sai jinjina suke yi wa 'yan uwa, hatta wadanda ba musulmi ba sun tsaya a bakin kofofin shagunansu suna kallon muzaharar. Tambayar da na yi wa wani Inyamuri mai sayar da takalma a yayin da ya tsaya yana kallon muzaharar ita ce "Shin ko ya san su waye wadannan masu wucewa? Sai kawai ya ce " Mutanen Shi'ah ne! Sune masu tafiya da Sojoji!" Daga nan kuma sai ya shaida min cewa ko su ma ba sa goyon bayan zaman Amurka a Iraki tunda sun kama Saddam.

A yayin da aka kitse wannan muzahara, Malam Ahmad Yashi ya bayyana godiyarsa ga 'yan uwa bisa amsa wannan kira na Imam Khumaini da suka yi, duk da halin azumi da ake fama da shi. Ya yi kira ga al'ummar musulmi da su hada kai wuri guda a duk inda suke domin tunkarar kafircin duniya. "A kan haka ne Maulana Shaikh Ibraheem Zakzaky yake kiran al'umma," in ji shi.

Malam Ahmad Yashi ya kara da cewa Marigayi Imam Khumaini shi ya assasa wannan rana ta Kudus, kuma ana gabatar da ita ne duk Juma'ar karshe ta Ramadan. Kuma kada wasu su dauka Kudus a Iran take, ganin cewa Imam Khumaini dan Iran ne. Daga karshe ya ja hankalin musulmi da su kwan da sanin cewa in ma mutum ya ki yin gwagwarmaya saboda tsoron mutuwa, to ya sani mutuwa tana ko'ina, inda ya ba da misali da irin mace-macen da aka yi ta yi a wannan wata na Ramadan a cikin garin Bauchi.

Ita dai wannan muzahara, kamar yadda aka fara ta cikin lumana da kwanciyar hankali haka aka kare ta.

Hayaniya ta kaure a masallaci

Wajen rabon kudi
Daga Alhusain Dakace

Kamar yadda aka sani idan aka ce an samu kudi don rabawa ake samun hayaniya, musamman idan ba a yi a hankali ba. Irin wannan hayaniya da ta kaure ta baya-bayan nan saboda rabon kudi ita ce na wanda Hajiya Mariya Sunusi Dantata, mahaifiyar Aliko Dangote, ta kawo kudi masu yawan gaske don rabawa a lokacin da aka kammala sallar kiyamul laili da aka saba gudanarwa a masallacin Juma'ar da ke Kofar gidanta a unguwar Koki cikin birnin Kano.

Wakilimu da ya gudanar da i'itikafi a masallacin ya ga yadda da farko an bi sahu ana bai wa kowa N2000 ba tare da hayaniya ba, ya zuwa wani lokaci sai hayaniya ta kaure a ciki da wajen masallacin. Ala tilas aka dakatar da rabon kudin duk da cewa Limamin masallacin, Malam Ali ya sanar wa jama'a cewa kowa ya tsaya cikin sahu, don kuwa kowa zai samu. Amma duk da haka rabon kudin bai yiwu ba.

Ganin haka masu rabon kudin sun tunkari sashen matan da suka zo masallacin don tahajjud. Ai nan ma abin gagara ya yi. Karshe dai ana ji ana gani rabon kudin ya gagara daga wajen matan har mazan. Haka aka mayar da kudin kowa na gani.

Har ila yau ALMIZAN ta ga yadda mafi yawan jama'ar da suka halarci tahajjudin na karshe, maza da mata dauke da goyo da tsofaffin mata da maza da matasa, sun ki tafiya gidajensu, bisa zaton ko watakila masu rabon kudn su sake dawowa bayan sallar subahi.

ALMIZAN ta ga matan da su aka yi sallar ta asuba, sun ki tafiya gida, amma daga karshe haka suka koma hannu-rabbana. Amma a wani bincike da ALMIZAN ta gudanar kan rashin komawar matan gidajensu, duk da kasancewar ba su sami kudin tun farko ba, ta gano cewa don tsoron bata gari kar su far musu ne, amma wani abin ban mamaki shi ne wasu matan har wajen karfe bakwai na safe suna nan suna jiran tsammani.

ALMIZAN ta zanta da wani bawan Allah da shi ma ya gudanar da i'itikafi a masallacin, inda shi ma ya sami nasa kason na N2,000 mai suna Alhaji Sani. Ya ce, hakika Hajiya Mariya ta cancanci yabo, "domin," a cewarsa, "tunda aka fara i'itikafi a masallacin ta rinka auno dafaffen abinci kyauta domin 'yan i'itikafin." Sai ya shawarce ta cewa, nan gaba idan za ta yi irin wannan bayar da sadaka na kudi, "to ya kamata a yi shi cikin tsari, ta yadda al'umma za su amfana."

ALMIZAN ta ga yadda masu gudanar da i'itikafin na bana a cikin masallacin suka gudanar da nau'in ibadojinsu kala-kala ba tare da wata tsangwama ba tun daga kan jami'an masallacin har ya zuwa 'yan uwansu masu i'itikafi. An kuma gudanar da shi lafiya, an tashi lafiya.

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


 Shafin Gamji | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International