Jarida don Karuwar Musulmi
Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki ISSN 1595-4471
Juma'a 10 Shawwal, 1426
Bugu na 691
Tunatarwa | | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari Tattaunawa | Labarai |
Mahajjatan bana sun shiga uku
Obasanjo ya rufe ofishin Nijeriya a Makka
G a dukkan alamu mahajjatan bana za su dandana kudarsu a kasa mai tsarki sakamakon rufe ofishin Mahajjatan Nijeriya da ke Makka, 'Nigerian Hajj Mission,' wanda da shi ne ake yin amfani wajen sama wa mahajjatan kasar nan masauki, sufuri da sauran kayan more rayuwa a lokutan aikin hajjin. Jaridar DAILY TRUST ta ranar Alhamis 27 ga watan Oktoban da ya gabata ta ci karo da wata takarda wacce Jakadan Nijeriya a kasar ta Saudi Arebiya, Sanata Ibrahim Kazaure ya rubuta zuwa ga Shugaban ofishin Mahajjatan Nijerian da ke Jidda domin sanar da shi rufe wannan ofishin, wanda umurnin hakan ya zo ne daga Shugaban mulkin farar hular Nijeriya, Cif Olusegun Obasanjo. Takardar, ta nuna cewa rufe wannan ofishin zai fara aiki ne nan take, kuma duk ma'aikatan ofishin su tattara ya-nasu-ya-nasu su koma hedikwatar Ma'aikatar kasashen waje da ke Abuja zuwa karshen watan Nuwambar nan. Saboda haka nan take Ambasadan ya umurci Shugaban wannan ofishi na 'Nigerian Hajj Mission' ya shirya ya mika bayanai ga Shugaban wani karamin ofishin Nijeriya da ke Riyadh, Mista A.D. Manzo. Wani bincike na Jaridar ya kuma nuna wani sako da Ministan harkokin kasashen waje na kasar nan, Ambasada Olu Adeneji ya aika wa Ambasada Kazaure inda yake ba shi umurnin ya gaggauta aiwatar da shirye-shiryen rufe Ofisoshin Nijeriya da ke Riyadh da kuma na Jidda. Shi dai wannan ofishin Mahajjatan Nijeriya da ke kasa mai tsarki shi ne da alhakin kulawa da mahajjatan kasar nan a lokutan aikin Hajji, kuma ana kula da shi ne ta hanyar cire wani kaso daga kudaden da maniyyata suka biya, kuma an bude shi tun a Sittinoni, (1960's). Sannan kuma Ofishin Jakadanci shi aikinsa ya kula da sauran harkokin hulda na kasa da kasa. Saboda haka ake ganin cewa rufe wannan ofishi da gwamanatin ta Obasanjo ta yi lallai zai kuntata wa mahajjatan, musamman ganin cewa wannan ofishin ke da dawainiyar kusan duk wata zirga-zirga ta mahajjata a lokutan aikin hajjin. Akwai hujjoji da dama wadanda suke nuna cewa in ba wani gagarumin shiri aka yi ba, to lallai bakar wahalar da mahajjatan kasar nan suka saba sha a duk shekara, bana abin zai karu. Wani karamin takadiri shi ne irin wahalar da masu zuwa Umura suka sha filayen jiragen saman kasar nan, a karshe ma dai wasu ba su sami tafiya ba. Sai dai kuma Ambasadan ksar nan a kasar Saudi Arebiya, Ambasada Ibrahim Musa Kazaure ya musanta wannan batu na cewa rufe Ofishin zai kawo takura ga mahajjatan, ya ce an rufe wannan ofishi ne don amfanin mahajjatan. Don haka sai Ambasada Kazaure ya bukaci musulmi da su dauki rufe wannan ofishi a matsayin wani ci gaba da aka samu a harkar aikin hajjin. Ya kuma nuna cewa ai tuni ya kamata a ce an rufe wannan ofishin, amma ba a rufe ba sai a yanzu. Ya ci gaba da cewa shi wannan ofishin da aka rufe yana maimaita ayyukan Ofishin jakadancin Nijeriya a kasa mai tsarki ne. Don haka shi a ganinsa rufe wannan ofishi wani abu ne da ya dace kuma babu wata mishikila a ciki. Komawa babban shafinmu Komawa saman wannan shafin
| |
| Tafsirin Alkur'ani | Hadisai | Crescent International |