Jarida don Karuwar Musulmi
Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki ISSN 1595-4471
Juma'a 10 Shawwal, 1426
Bugu na 691
Tunatarwa | | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari Tattaunawa | Labarai |
|
|
Wannan mari da dan Majalisa Idris Zago ya sha ya faru ne lokacin da Gwamna Shekarau ya kira taron jiga-jigan 'yan jam'iyyar daga Kananan Hukumomin wadanda suka hada Shugaban majalisar dokoki Alhaji Sa'idu Balarabe Gani da Shugaban riko na jam'iyyar ANPP na jihar Kano domin tattaunawa da su kan yadda za a fitar da mutum daya da zai shugabanci jam'iyyar tsakanin Alhaji Haruna Danzago da Alhaji Ali Datti Yako.
Ana cikin tattauna yadda za a yi a fitar da mutum guda ne, sai dan majalisa Idris Zago ya mike ya shaida wa mahalarta taron cewa sun samu labarin cewa Alhaji Abdullahi Sani Rago, Kwamishinan Kananan hukumomi ya tara shugabanin Jam'iyya na Kananan Hukumomi 44 da ke cikin jihar ya kitsa masu cewa in lokacin zabe ya zo kar su zabi Danzago, su zabi Ali Datti Yako ne. Dan majalisar bai kammala bayaninsa ba, sai shi Kwamishina Rogo ya tashi ya yi kan Idris Zago Dambatta ya tattakura ya shara masa mari, ya kuma cakumi wuyan rigarsa yana cewa shi ya fada wa 'yan majalisa wannan maganar, yana tura masa ashariya (zagi).
Wata majiya ta shaida wa ALMIZAN cewa sai da Gwamna Shekarau ya yi magana sannan ya saki wuyan rigar. Majiyar tamu, wacce a kan idonta wannan al'amari ya faru, ta ci gaba da shaida mana cewa Gwamna Shekarau ya nuna fushinsa da bacin ransa har ya tashi ya fice daga zauren taron. Haka kuma taron ya tashi ba a cimma buri ba.
A ranar Litinin din da ta gabata ne kuma Gwamnatin Jihar Kano ta kira taron 'ya'yan jam'iyyar da iyayenta a jihar ta Kano gaba daya ta yi taro da su a dakin taro na Africa House da ke cikin gidan Gwamnati a karkashin jagorancin Gwamna Malam Ibrahim Shekarau.
Taron wanda aka hana manema labarai shiga, an yi shi cikin sirri, an kuma kammala babu sanarwar bayan taro, wanda daga dukkan alamu 'ya'yan jam'iyyar na ANPP, sun sanya wa bakunansu takunkumi a kan wannan abin kunya.
ALMIZAN ta nemi jin ta bakin bangarorin biyu, Kwamishina Rogo da Dan Majalisa Zago, amma sun ki su ce komai.
Sai dai kuma wani rahoton sirri da ALMIZAN ta ci karo da shi, cewa ya yi babu wani mataki da Gwamna Shekarau ko kuma bangaren Majalisa za su iya dauka kan Kwamishina domin yana cikin 'yan gaban goshin Gwamna wadanda ba sa tabuwa a cikin Gwamnatin ta Kano.
| Tafsirin Alkur'ani | Hadisai | Crescent International |