Almizan:An sake kai wa 'yan uwa na Sakkwato hari ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 10 Shawwal, 1426                 Bugu na 691                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai

An sake kai wa 'yan uwa na Sakkwato hari

…Sun yi muzaharar Kudus

Daga Aliyu Saleh


Wani gungu na jami'an tsaro da gamin gambizar 'yan tauri da zauna-gari-banza, sun sake kai wa 'yan uwa na Sakkwato hari a Markaz da ke Unguwar Rimin Tawaye da talatainin daren ranar Alhamis din makon shekaranjiya, inda suka jikkata biyu, suka kuma yi awon gaba da 18.

Bayanan da muka samu daga birnin na Shehu, sun tabbatar mana da cewa; maharan sun humi 'yan uwan ne da misalin karfe 1:00 na dare, inda suka je masu da duk wani karfi da kwarewar da suke da ita da nufin kama Malam Kasimi Umar da kuma wani sashi na 'yan uwa a wani mataki na dakile shirin da 'yan uwan suke da shi na gudanar da muzaharar Kudus da aka saba yi duk shekara a washegarin wannan ranar.

Sai dai wani da aka kai harin a gabansa, ya tabbatar mana da cewa; duk da wannan matakin da maharan suka dauka, wannan bai hana 'yan kalilan din 'yan uwa da ke wajen sun fafare su kamar yadda suka yi masu a baya ba. Ya ce matakin tirjiya da cijewa da kuma dakewar da 'yan uwan, wadanda yake adadinsu ya karanta a lokacin, suka dauka shi ne ya hana maharan isa ga Markaz din.

Bayanan da muka samu, sun tabbatar da cewa, duk da sun samu mutanen Unguwar Rimin Tawaye suna barci a lokacin, amma an kwashe awowi ana gumurzu da dauki-ba-dadi, abin da ya tilasta wa gayyar maharan suka juya ba tare da sun cimma burinsu ba.

Wani bincike da muka yi mun gano cewa; maharan sun kawo harin ne da nufin dakile shirin gudanar da muzaharar Kudus da 'yan uwa suka shirya gudanarwa a garin ranar Juma'a. Sai dai duk da wannan harin da suka kai bai hana 'yan uwan gabatar da muzaharar ta Kudus a birnin na Shehu ba.

Ya zuwa lokacin da muke rubuta wannan rahoton dai, jami'an tsaro cikin motocin yaki da kuma na fararen kaya, sun yi wa Unguwar Rimin Tawaye zobe, suna ta sintiri da nufin damke wasu 'yan uwa da suke zargin suna da hannu a shiryawa da kuma aiwatar da jerin gwanon da suka ce zai iya kawo tashin hankali a garin.

Wata majiya mai tushe ta tabbatar mana da cewa; maharan sun kai harin ne a cikin wasu motoci 17, karkashin jagorancin wani mai ba Bafarawa shawara, Alhaji Tukur Alkali da nufin hana 'yan uwan gudanar da muzaharar Kudus, sai dai duk da wannan matakin da suka dauka bai hana 'yan uwa aiwatar da muzaharar kamar yadda aka shirya ba.

Da misalin karfe 7:20 na safiyar ranar Juma'a ne, 'yan uwa suka hau titi cikin sahu dauke da tutoci, kwalaye da kyallayen da ke rubuce da kalaman tausaya wa Palastinawa, gami da kuma yin Allah wadai da ayyukan ta'addancin da Yahudawa da sauran kafiran duniya suke yi a kan Musulmin duniya.

Wani da aka yi muzaharar da shi, ya labarta mana cewa; dubban 'yan uwa ne da suka fito daga duk yankin na Sakkwato da suka hada da Kebbe, Yawuri, Mafara, Gusau da sauran manya da kananan garuruwan yankin ne suka samu shiga muzaharar wacce ta ratsa kusan duk manyan tituna cikin burnin na Sakkwato.

Jama'a da dama ne suka yi dango a gefen titi cike da mamakin ganin 'yan uwa Musulmin da ake bi kwaro-kwaro ana gaya masu cewa an gama da su suna gudanar da muzaharar Kudus mazansu da matansu.

Al'ummar Annabi sun yi dafifi a gefen titunan Emir Yahya, Sultan Abubakar, Rijiyar Dorawa da kuma jikin masallacin Hurimi, inda aka kitse hancin muzaharar, suna ta yi wa 'yan uwa jinjina, tare da yin rige-rigen amsar takardar da 'yan uwan suke rarrabawa mai dauke da bayanin dalilin yin muzaharar da kuma fadakar da musulmi game da halin da Masallacin Kudus da Palastinawa ke ciki.

Mun samu labarin cewa; jami'an tsaro sun kama wasu 'yan uwa 50 da suka fito daga garin Illela suna shirin zuwa garin na Sakkwato domin aiwatar da muzaharar. Kodayake sun saki wasu, amma tuni har sun kai wasu daga cikinsu wata kotun-je-ka-na-ka da ke Karamar Hukumar Kware suna tuhumar su da niyyar ta da hankali, da kuma shiga cikin haramtacciyar kungiya.

Duk da yake an yi an gama muzaharar cikin kwanciyar hankali, amma har yanzu jami'an tsaro cikin shirin yaki ne suka sintiri a Unguwar su Malam Kasim Umar suna neman sa da niyyar su kama shi.

Da muke zantawa da shi ta wayar tarho ranar Asabar din nan a Sakkwato, Malam Kasimu Umar, wanda kuma shi ne Wakilin 'yan uwa na Sakkwato, ya yi Allah wadai da matakin da jami'an tsaron suke dauka na neman kassara dan zaman lafiyar da aka samu a garin da ya yi fama da rikice-rikice bayan auka wa 'yan uwa da wasu zauna-gari-bazan suka yi a watannin da suka gabata.

Ya ce, "idan ma har sun ce sun dauki matakin kai mana hari da tsakar dare ne don kar mu yi muzahara a samu tashin hankali, to, ai ga shi mun yi ba a samu a wani tashin hankali ba. Kuma ai ba a Sakkwato ne kawai aka shirya yin wannan muzharar ba. Kana kuma ba a yau ne muka fara yin muzahara muna tashi lafiya a garin nan ba."

Ya ce, "ba a taba samun tashin hankali ba idan muna muzahara ko wasu taruka, sai idan 'yan tashin hankali sun auka mana. Idan gaskiya ne, ba mu ya kamata a kai wa hari ba, masu ta da hankali ya kamata a kai wa hari don a tabbatar ba su ta da hankalin kowa. Da yake masu da ta hankali ba su fito ba, sai muka yi muka gama muzahararmu cikin kwanciyar hankali da lumana," in ji shi.

…Ta Kuduna ta ba da mamaki


Daga Aliyu Saleh

Muzaharar Kudus da aka yi a garin Kaduna ranar Juma'ar karshe ta watan Ramadan da ya gabata, ta ba da mamaki, musamman ganin ta wuraren da muzaharar ta bi, da kuma yawan jama'ar da suka shige ta.

Kamar yadda aka saba dai, a wannan karon ma an faro muzaharar ne bayan an kare sallar Juma'a a masallacin Juma'a na Maiduguri Road. Bayan kammala sallar Juma'a, sai wani dan uwa mai murya ya tsala kabbara, wanda ya nuna wa sauran dubban masallata akwai abin da ke faruwa.

Nan da nan 'yan uwa da suka hada maza da mata yara da manya suka dau harami, tutoci da sauran kwalayen da kyallayen da ke rubuce da kalmomin 'Masallacin Kudus na musulmi ne.' 'Amurka da Isra'ila ne 'yan ta'adda,' da dai sauran zafafan kalamai suka fara filfilawa a wajen.

Take 'yan uwa Hurras da suke dauke da katuwar tutar Palastinawa da kuma wasu jerin 'yan uwan da suka yi shigar baraden Al'aksa da kuma wasu da suka yi shigar fararen kaya dauke da badujaloli da wasu sanduna masu ban sha'awa suka hau sahu, sai sauran 'yan uwa da kuma wakilan da'irorin da ke yankin Kaduna su ma suka biyo baya.

Adadi mai yawan na 'yan uwa mata da kuma daliban Fudiyya, gami da wasu matasa sun ci gaba da kawata tsakiya da bayan muzaharar, a yayin da aka hau tsakiyar titin Maiduguri ana rera taken kwato masallacin Kudus da kuma shelanta tawaye ga Yahudawa da ma kafircin duniya kwata.

Mazaharar ta mazaya ta hau kan kokon zuciyar titin Ahmadu Bello, bayan an karado ta kan titin Katsina aka tsaya na dan lokaci a kusa da shataletalen Katsina Road ana fadin; "Masallacin Kudus na muuslmi ne, kwato shi ya zama wajibi."

Daga nan sai aka ratsa ta kan tinin Kano Road, aka bi ta jikin sabon masallacin Juma'ar da ake ginawa a layin. Aka tike hancin muzaharar a kan mahadar 69 da ke daura da babbar kasuwar Shaikh Abubakar Mahmoud Gumi.

Da yake jawabi kafin a yi addu'ar rufewa, sanye da alkyabba da hula, Malam Mukhtar Sahabi Kaduna, ya jadadda wajibcin kwato masallacin Kudus daga hannun Yahudawa. Ya ce, muddun al'ummar musulmi suna son su 'yantar da masallatansu da suka hada da na Makka da Madina, wajibi ne su tashi tsaye su hadu waje daya ba tare da bambancin fahimta ba, domin kwato masallacin Kudus mai alfaram. Ya ce, "duk wanda yake rike da masallacin Kudus, shi ke rike da masallatai biyu masu alfarma na Makka da Madina a zahiri ko a fakaice."

Malam Sahabi, wanda ya yi dogon jawabi a kan hatsarin da al'ummar musulmi suke fuskanta, ya yi Allah wadai ga masu cewa burin 'yan uwa shi ne kwatar masallatai. Ya ce tunda 'yan uwa suke ba su taba kwatar masallaci daga hannun wani musulmi ba, "mu duk masallacin da muka samu muna salla a cikinsa, domin a wajenmu duk masallaci na Allah ne."

Sai dai ya ce duk da haka 'yan uwa ba su yi kasa a gwiwa ba wajen ci gaba da hankoron kwato masallacin Kudus ko da kuwa sauran al'ummar musulmi sun kau da kai ga barin haka. "Amma za mu fara ne da kakkabe Yahudawan da suka yi kaka-gida a namu masallatan da muke da su a nan."

A lokacin da 'yan uwa suke gudanar da muzaharar, jama'a sun yi dafifi a gefen titi suna ta rububin karbar takardar da suke rabawa mai dauke da bayanin dalilin yin muzaharar. Da daman jama'a suna ta bayyana jin dadinsu da wannan kokarin da 'yan uwa suke yi na fadakar da al'ummar musulmin wajibin da ya hau kansu a daidai lokacin da wasu musulmin suka shagaltu da kafirta junansu a wajen tafsiran da suke gabatarwa a cikin watan na Ramadan.

A yayin da mutane ke hanzarin zuwa wajen da 'yan uwa suke gudanar da muzaharar ta juyayin Kudus domin jin sakon sake bayarwa ko kuma don kashe kwarkwatar idonsu, ko don kallon kwakwaf, wasu jama'ar da ALMIZAN ta ci karo da su kuwa zurawa a guje suke yi, wasu kuma suna ta rufe shagunansu ne don abin da suka bayyana da tsoron kada jami'an tsaro su kawo wa masu muzaharar hari kamar yadda suka saba.

"Idan su (masu muzaharar) ba za su gudu ba saboda sun shirya tarar su, mu dole ne mu san inda dare ya yi mana don kada su zo su lalata mana dukiya, ko su ji mana rauni," in ji wani Inyamuri yana fadi yayin da yake rufe shagonsa a kusa da inda 'yan uwa suka rufe muzaharar tasu.

Da yawa daga cikin mutanen da muka zanta da su, wadanda kuma suka ga yadda muzaharar ta faru har ta kare lami lafiya sun dora alhakin duk wani tashin hankali da ake samu a yayin da 'yan uwa suke gudanar da tarukansu a wuyan jam'an tsaro, "da yake ba su kawo masu hari ba, ga shi sun yi sun gama abinsu lami lafiya," in ji wani da ya bi muzaharar daga masallacin Kano Road.

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


  | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International