Jarida don Karuwar Musulmi
Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki ISSN 1595-4471
Juma'a 10 Shawwal, 1426
Bugu na 691
Tunatarwa | | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari Tattaunawa | Labarai |
Gwamna Mu'azu, Lawal Kaita sun tsallake rijiya da baya a hatsarin jirgin sama
Mutanen da ba su gaza dari bane, ciki har da Gwamnan jihar Bauchi, Alhaji Adamu Mu'azu, tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Alhaji Lawal Kaita, tsohon karamin Ministan cikin gida, Mista Dubem Onyia da Edita-in-cif na mujallar NEWSWATCH, Mista Dan Agbese, suka tsallake rijiya da baya a ranar Litinin da ta gabata a wani hatsarin jirgin sama a Abuja.
Al'amarin, wanda ya wakana makwanni biyu kacal bayan aukuwar mummunan hadarin jirgin saman kamfanin Bellview wanda ya kashe mutanen da ke cikinsa su 117 a kauyen Lisa, Ifo jihar Ogun, ya faru ne da jirgin Aero Contractors. Sannan kuma mako daya baya, wani jirgin Associated Airlines dauke da mutane 20 ya rasa tayoyinsa na gaba yayin da yake sheka gudun tashi a titin tashin jiragen sama na filin jirgin saman Murtala Muhammad da ke Lagos. Wakilinmu ya shaida mana cewa al'amarin da ya auku ranar Litinin din da ta gabata ya faru ne a sanadiyyar matsalar tsuntsayen da ke filin. An ce wasu tsuntsaye ne suka shiga cikin daya daga cikin injinan jirgin yayin da yake shirin tashi da misalin karfe 2:30nr. Farfela bakwai ne na injin din suka lalace, abin da ya tilasta wa matukin jirgin ya fasa tashi. Wasu majiyoyi ma sun ce jirgin sai da ya yi asarar tayoyinsa biyu. Jirgin, kamar yadda wata majiya ta ce, matukinsa ya tura shi zuwa wani sashen filin jirgin sama, yayin da ya yi ta shaida wa fasinjojinsa cewa matsalar ta zo da sauki. Dukkanin fasinjojin, wadanda Jami'an jirgin, Hukumar filayen jiragen sama na tarayya, Hukumar kula da sararin samaniyar Nijeriya da na ma'aikatan sufurin jiragen sama na kasa suka taimakawa, duk sun sauka cikin murnar Allah ya kiyaye su. Daga baya wasu daga cikin fasinjojin sun sake hawa wani jirgin zuwa Lagos, a yayin da wasu kuma suka fasa tafiyar bayan sun karbi kudinsu daga kamfanin Aero Contractors. Edita-in-Cif na mujallar Newswatch ya shaida wa wata jarida cewa, "fasinjojin jirgin ba su rude ba, wasu ma mai da abin suka yi ba'a, suna cewa sun ma yi sa'a tsuntsuwa ce ta aukar da matsalar ba saniya ba!" |
| Tafsirin Alkur'ani | Hadisai | Crescent International |