Almizan :Kame Mai Rago: Makarfi ya tsame hannunsa ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 10 Shawwal, 1426                 Bugu na 691                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Babban Labarinmu

Kame Mai Rago: Makarfi ya tsame hannunsa


Daga Musa Muhammad Awwal

Akwai zargin da ake ta yadawa cewa Gwamnan jihar Kaduna, Alhaji Ahmad Muhammad Makarfi ke da hannu dumu-dumu a tsige Alhaji Yusuf Hamisu Abubakar, Mai Rago daga kan mukaminsa na Shugaban Hukumar PTDF kuma ya bayar da sunan Alhaji Husaini Jalo a madadin Mai Ragon. Haka kuma shi ne dai ke da alhakin mika Mai Ragon ga Hukumar EFCC wanda ta cafke shi ta tsare.

Sai dai Gwamna Ahmad Muhammad Makarfi ya karyata duk wadannan zarge-zarge, inda ya nuna cewa shi sam ba shi da hannu a kan wadancan abubuwa da aka zarge shi da su.

Gwamnan ya musanta wannan zargi ne ta hannun Darakta-Janar dinsa na yada labarai, Alhaji Mukhtar Zabairu Sirajo, wanda shi kuma ya rubuta ya rarraba ga manema labarai a Kaduna.

Ya ci gaba da cewa a irin wannan zargi, har da inda masu zargin ke nuna cewa wai Makarfi ya ci amanar Mai Rago, ya saba alkawarin da suka yi a 2003 lokacin da aka nemi Mai Ragon ya janye daga takarar da ya so yi na kujerar Gwamnan jihar a shekarar ta 2003. "Babu wata yarjejeniya da ta faru tsakanin Makarfi da Yusufu Hamisu Abubakar kafin zaben shekarar 2003, in ji sanarwar.

Sai dai sanarwar ta tabbatar da cewa akwai wani lokaci da shi Mai Ragon, a gaban Mataimakin Shugaban kasa, ya so Gwamna Makarfi ya yi wannan alkawarin, amma sai Makarfin ya ki yi da zuciya daya.

Sanarwar ta ci gaba da cewa; "akwai wani taro da aka taba gabatarwa na shugabannin jam'iyya a gidan gwamnati na Hasan Usman da ke Kawo, Kaduna, wanda kuma Mataimakin Shugaban kasa ne ya shugabanci taron. Makarfi ya bukaci Mataimakin Shugaban kasa, Atiku Abubakar da ya yi bayani in akwai wata yarjejeniya tsakaninsa da Mai Rago domin a fid da dukkan zargi. Amma Mataimakin Shugaban kasa, bai tababatar da wata yarjejeniya ba a tsakaninsu."

Sanarwar ta kara da cewa; "babu wani lokaci da Yusuf Abubakar ya taba sakar wa Gwamna Makarfi takarar Gwamna a 2003. Har lokacin da jam'iyyar PDP ta yi zaben fid da gwani kuma aka zabi Makarfi, to su Yusuf Hamisu da sauran 'yan takara suna kotu suna kalubalantar zaben."

Sanarwar ta kuma musanta zargin da aka yi ta yi cewa Makarfi ya karbi wata gudummawa daga Yusuf Hamisu, "Makarfi ne ma a lokuta da dama ya rinka taimaka wa da kudade a mazabar Mai Ragon ta Karamar Hukumar Kaduna ta Kudu don gabatar da zabe," in ji sanarwar.

Alhaji Mukhtar Zubairu Sirajo, ya kuma bayyana cewa ya san cewa Gwamna Makarfi ya sha bayar da mukamai ga wadanda suke mutanen Mai Rago ne a cikin gwamnatin jihar Kaduna. Saboda haka sai ya tabbatar da cewa ba shakka wadannan abubuwa da ya zayyana haka suke, kuma duk wani mai musun su yana iya yi ta kowace hanya.

A karshe ya kara jaddada cewa; Gwamna Makarfi ba shi da wata masaniya game da halin da Mai Rago ya shiga da Hukumar ta EFCC.

Jama'a dai suna wannan zargin ne bayan kayen da Makarfi ya sha a kotu bayan samun sa da laifi da wani Kwamitin bincike a kan badakalar kudi da aka samu a lokacin da Mai Ragon yake Kwamishinan kudi na jihar Kaduna da kuma cire shi da aka yi daga kan mukamansa aka maye gurbinsa da Alhaji Husaini Jalo.

Duk wani kokari da muka yi na ganawa da bangaren Alhaji Hamisu Abubakar, Mai Rago, abin ya ci tura. Sun ce za su yi magana, amma ba yanzu ba.

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


  | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International