Almizan :Zargin fashi da ake yi wa DPO na Ganjuwa: ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 10 Shawwal, 1426                 Bugu na 691                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Babban Labarinmu

Zargin fashi da ake yi wa DPO na Ganjuwa:

Ali Kwara ya fayyace komai

Daga Lawal K/Madaki da Idris Ibrahim Azare

a

Sakamakon gardandamin da ake yi tsakanin jama'ar garin Ganjuwa da jami'an tsaro, a daya bangaren da Alhaji Ali Kwara Azare, wanda ke aikin kama barayin nan, bayan kama DPO na garin Ganjuwa da kuma Shugaban kungiyar nan ta 'Babban Gwani Vigelante Group,' Malam Shehu Na Kurma ne bangarorin biyu suka kira wani taron manema labarai na hadin gwiwa a Bauci don a fayyace yadda gaskiyar maganar take.

Da yake ganawa da 'yan jarida, Alhaji Ali Kwara ya bayyana cewa da ma ya jima yana neman wadannan 'yan fashin, kuma ya jima yana kiwon su, jira kawai yake yi Hukuma ta nemi taimakonsa wurin kama su.

Dangane da zargin da ake yi wa DPO na Ganjuwa, Alhaji Adamu Shehu kuwa, Ali Kwara sai ya ce, "wadannan tsofaffin barayi ne. Sun sami kungiya wacce ke tubar da barayi ta hanyar wanke su a kan sun daina fashi," sakamakon matsin lambar da shi Ali Kwara din ya yi musu, yana neman su ruwa a jallo.

Ya ce kuma sukan biya kudin tuba Naira dubu 30, ganin haka ne sai ya sanar da Kwamishinan 'yan sanda kan ya kira DPO na Ganjuwa ya kai masa wadannan barayin da suka tuba, amma sai shi DPO ya ki mika su, kamar yadda Ali Kwara ya bayyana.

Da aka tambayi Ali Kwara dangane da tubar 'yan fashin, sai ya ce, "ni ban yarda da wani tuban dan fashi ba. Yaya za a yi a ce mutum bayan aika-aikar da ya aikata, ya kashe mutane babu iyaka, sannan a ce wai ya tuba, har ma wai a ba shi Alkur'ani ya rantse, har ma a yi sha'awar kudin hannunsa bayan ya kashe mutane," ya jaddada.

Shi kuwa Malam Shehu Na Kurma, Shugaban kungiyar da ke tubar da barayin, ya shaida wa 'yan jarida cewa; lalle kungiyarsa tana tubar da barayi ne a karkashin DPO na Ganjuwa, Adamu Shehu, "shi ne sai wani mai suna Kacalla Dutsi ya zo ya tuba, kuma ya kawo bindigogi guda biyu ga DPO, wato wanda yake fashi da su, tare da kudi 20,000 da sunan ya tuba, shi kuma DPO bai bincike shi ba, to ashe ba duk bindigoginsa ya ba da ba, to dalilin da ya sa aka kama mu kenan," in ji shi.

Dangane da batun shanun da suke zargin sa da tarawa kuwa don ba manya, sai ya ce wadannan shanu gidauniya suke yi a duk inda suka kafa kungiya domin su sami kudin da za su tafiyar da kungiyar tasu.

Da aka tambaye shi dangane da tubarsa kuwa sai ya ce, "lalle Ali Kwara ne ya matsa da kashe mana mutane. Amma mu lalle ba fashi muke yi ba."

Shi kuwa Kacalla Dutsi, wanda shi ne musabbabin janyo musu wannan kamu cewa ya yi, lalle tun farko ya shiga kungiyar bayan ya tuba, amma duk da haka sai ya ji Ali Kwara ya matsa da nemansa, kuma ya ga tabbas wannan kungiya ba za ta kare shi ba daga Ali Kwara ba, don haka sai ya watsar da kungiyar ya koma fashinsa.

Ko da aka tambaye shi, ina suke samun bindigogi? Sai ya ce a wurin fashi suke samu. "In mun kashe dan sanda ko mobayil sai mu dauke bindigoginsu," ya ce.

Shi kuwa Musa Yalo shaida wa 'yan jarida ya yi cewa, suna sayen harsasansu ne a hannun 'yan sanda a kan kudi N3,000 kowane faket. Sai dai daga baya sakamakon wani artabu da suka yi da Ali Kwara a Lafiya, sai farashin harsasan ya karu zuwa 6,000 har 7,000. Da aka tambaye shi inda suke saye, sai ya ce a jihar Binuwai ne da Filato.

Sai dai wani dan kungiyar ta 'Babban Gwani Vigelante Group,' da yanzu haka yake tsare a hannun Alhaji Ali Kwara a gidansa da ke Azare, Ali Modake ya shaida wa Wakilinmu cewa, asalin kungiyar Kacalla Dutse ne ya kafa ta, daga bisani ne jagorancin kungiyar ya koma hannun Shehu Na Kurna.

Ali Modake, wanda yake shi me rikakken dan fashi ne, ya tabbatar da cewa shi ma Shehu Na Kurma din tsohon dan fashi ne. Ya ce, "ya daina fashin ne bayan da ya ga an samu masu yi wa 'yan fashi kamun kaji, shi ne sai ya kafa wannan kungiyar da sunan yaki da fashi da makami, ya dawo Ganjuwa ya ce wai ya tuba," in ji shi.

Ali Modake, wanda ya nuna mana katin shaidarsa na zama dan kungiyar 'Babban Gwani,' ya ce daga cikin ayyukan kungiyar tasu sun hada har da tubar da 'yan fashi. Sai dai kafin a tubar da su din sai sun ba su kudin tuba Naira dubu 30, da kuma kudin bude Alkur'ani da za a bai wa Malaman da za su tubar da dan fashin, kafin a yarda ya tuba. Ya ce idan ya tubar kuma sai ya shiga cikin kungiyar tasu.

Wani dattijo da muka samu a gidan Ali Kwara Azare ya biyo sawun dansa da ke tsare a gidan, ya tabbatar mana da cewa kafin a yarda dan nasa ya tuba a can Ganjuwa sai da ya bai wa DPO da Shehu Na Kurma kudin tubarsa Naira dubu 30.

Wani bincike da muka yi a tsakanin wadanda suke tsaren, mun gano cewa kungiyar ta 'Babban Gwani' ta yi dabara da kokarin ganin an daina fashi a Ganjuwa da kewayenta.

"Ba a fashi a yankin Ganjuwa sam. Wannan kuma shi ya sa mutanen Ganjuwa suke ganin DPO da Shehu Na Kurma suna aiki. A maimakon haka sai suka koma yankin Jos da Nassarawa suna fashi da makaminsu. Idan suna dawowa sai su kamo barayin awaki su kawo wa DPO, shi kuma sai ya harbe su," in ji wani dan kungiyar Babban Gwani da ke tsare a Azare.

Shi ma wani da ake tsare da shi a "kurkukun" na Ali Kwara Azare, wanda ake tsare da shi sakamakon zargin sayar wa da 'yan fashin makami, ya tabbatar mana da cewa; suna da alaka ta kut-da-kut da DPO na Ganjuwa, Alhaji Adamu Shehu, da kuma Alhaji Shehu Na Kurma. Ya ce, "mafiya yawan wadanda ake kamawa ake kashewa a wannan yankin namu ba 'yan fashi bane."

Ya ce, "babu wani zargi, duk wani fashi da ake yi musamman a yankin Jos da Nassarawa da akwai hannun DPO na Ganjuwa da kuma Shehu Na Kurma a ciki."

Katin shaidar zama dan kungiyar 'Babban Gwani Vigilante Group Association,' Ali Modake kenan. Ga hotonsa nan a jiki.

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


  | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International