Jarida don Karuwar Musulmi
Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki ISSN 1595-4471
Juma'a 10 Shawwal, 1426
Bugu na 691
Tunatarwa | | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari Tattaunawa | Labarai |
'Ranar Kudus' ta duniya a Iran a bana ta zarce na sauran shekaru
A ranar Juma'ar karshe ta Ramadan ne dai aka gabatar da bukin Ranar Kudus a Tehran babban birnin jamhuriyar Musulunci ta Iran da kuma dukkanin sauran biranen kasar tare da la'antar Yahudawa 'yan mamaya da kuma nuna goyon baya ga al'ummar Palasdinu. Tun da sanyin safe, wajen karfe tara da rabi agogon Iran, dimbin al'ummar musulmi a ko'ina cikin kasar suka fara taruwa daga hanyoyi daban-daban na kasar don gabatar da wannan ibada ta siyasa, ta nuna goyon baya ga gwagwarmayar al'ummar Palasdinu da kuma yin tir da Allah wadai ga Yahudawa 'yan mamaya. A Tehran, babban birnin kasar al'ummar birnin ne daga kowane bangare suka rika gunguntowa, yara da manya, maza da mata suna rike da tutoci dauke da taken nuna goyon bayansu ga al'ummar Palasdinu da kuma tir ga haramtacciyar kasar Isra'ila da 'yan kanzaginta Amurka da kasashen Turai. Rahoton manema labarai ya nuna cewa an soma jerin gwanon Ranar Kudus ne daga yankuna bakwai manya na birnin Tehran, kuma masu jerin gwanon sun kare ne zuwa babban masallacin Juma'a na birnin da ke cikin Jami'ar Tehran, inda aka gabatar da sallar Juma'a karkashin jagorancin Ayatullah Hashemi Rafsanjani. Cikin wadanda suka halarci jerin gwanon har akwai manyan jami'an kasar da suka hada da Shugaban kasar, Dk. Mahmood Ahmadinejad da kuma sauran malamai da mahukunta. Bayan jerin gwanon, an fitar da jawabin bayan taro, wanda ya kunshi wasu muhimman abubuwa da aka yanke shawara a kai. Ciki har da ci gaba da tafarkin marigayi Imam Khumaini (RA) na ci gaba da taimaka wa al'ummar Palasdinu da nuna masu goyon baya a kowane lokaci. A wani labari makamancin wannan, Shugaba Ahmadi Najad ya nuna cewa shirin yaudara da haramtacciyar kasar Isra'ila ta fito da shi na janyewa daga yankin Gazza don ta nema wa kanta halascin ci gaba da zama a inda ta mamaye bai ruda al'ummar musulmi ba, domin kuwa kowa ya san Yahudawa 'yan mamaya ne, kuma wajibi ne su fita daga Palasdinu gaba daya. Ahmadi Najad ya ci gaba da nuna cewa a yanzun Yahudawan sahayoniya suna son su ga cewa sun lalata wannan hadin kan da ke tsakanin 'yan Palasdinu ta hanyar shigo da yaudara. Saboda haka ya kirayi al'ummar kasar da su kasance masu taka tsan-tsan don kada su fada tarkon makiya. Haka nan kuma a lokacin jawabin nasa, Shugaban kasar Iran ya tabo hakkin 'yan Palasdinu na cewa wajibi a kai lokacin da za su gudanar da zabe 'yantacce a kasarsu, inda za su zabi tsarin da suke so da kuma Shugaban da zai jagorance su da kansu. Wannan taro dai ya sami halartar wakilai daga kungiyoyin gwagwarmaya na Palasdinu daban-daban da kuma wasu daga cikin manyan jami'an gwamnatin kasar Iran da sauran jama'a. |
| Tafsirin Alkur'ani | Hadisai | Crescent International |