Jarida don Karuwar Musulmi
Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki ISSN 1595-4471
Juma'a 17 Shawwal, 1426
Bugu na 692
Tunatarwa | | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari Tattaunawa | Labarai |
|
Wakilinmu da ya ziyarci wurin jim kadan da faruwar lamarin, ya shaida mana cewa wannan abin tausayi ya faru ne a sakamakon wani hayaki da taso daga wani wuri inda ake aikin kafinta, wanda kuma yana jikin wannan makaranta ce. Waikilin namu ya shaida mana cewa su dai wadannan yara suna zaune a azuzuwansu suna jiran a kawo masu takardu domin fara rubuta jarabawarsu ta wannan rana tunda dama suna daukar jarabawar NECO ne, wasu kuma suna azuzuwa suna daukar darasi, kawai sai suka ga hayaki ya fara turnukewa. Ganin haka sai wasu suka dauka kamar gobara ce ta kama makarantar, don haka sai aka fara ihu wuta! Ihu wuta!! Ai fa nan take sai sauran da suke a sauran azuzuwan kowa sai ya firgice, wuri ya rude aka fara guje-guje, aka rinka bi ana tattake juna, wasu kuma suna diddirowa daga benen. Ita dai wannan wuta ta samo asali ne daga wata bola (kashin kafinta) ta wani kafinta wanda yake yana jikin makarantar ne, kuma a lokacin shi kafintan ma ba ya nan wutar ta tashi. Saboda haka sai wuri ya rude wasu suka shiga diddirowa daga bene mai hawa uku, wasu kuma daga mai hawa biyu, da yake makarantar tana da hawa uku ne. Garin diddirowa ne fa wasu suka rinka gamuwa da ajalinsu, wasu kuma suka rinka karairayewa, wasu kuma suna samun munanan raunuka. Wani abu kuma da ya taimaka wajen yin wannan asara shi ne cewa ita wannan makaranta wata katafariya ce kuma tana da hawa uku da azuzuwa da dama, amma matakala, wato wurin hawa da sauka daya ce kawai, kuma aka yi rashin sa’a, daidai wannan matalakar ne wutar ta tashi, don haka ko wadanda suka biyo ta matakalar ma sai suka rinka faduwa wasu ana bi ta kansu, wanda a nan ma da dama sun rasa rayukansu. Wakilinmu ya lura da cewa baya ga cewa matakalar daya ce rak a makarantar, sai kuma a zagayen benayen, ba a yi irin kariyar nan wanda ke kange mutum fadowa daga gidan sama ba, wato irin karafuna ko gini da bulo da akan yi a gidajen sama domin maganin yara, don haka yaro na fitowa daga aji kawai sai ya sulmuyo, musamman ma da yake a rude kowa yake. Wani daga cikin wadanda sune suka rinka zuwa suna tara hannayensu Yaran na fadowa, ya shaida wa Wakilinmu cewa yawanci mata ne suka fi diddirowa. Haka ma a can wajen matakalar, mata ne suka fi mutuwa, “cikin gawarwaki 8 da muka kwantar a nan makarantar, mata 6 ne daga cikinsu, maza biyu ne kawai,” ya ce. Sannan kuma sauran hudun sun karasa ne a asibiti. Lallai wajibi ne a ce rudewa ce ta yi sanadiyyar duk wannan abu, domin ita wannan wuta sam ba ta ma shafi ginin makarantar ba, hayakin da ya rinka shigowa makarantar ne ya sanya wasu suka rinka ihu wuta, su kuma wadanda ba kusa suke da inda abin ya tashi ba, sai suka zaci ai ihu wutan da ake yi, a makarantar ce wutar take. A nan take aka rinka daukan marasa lafiya da gawarwakin zuwa wasu asibitocin da ke kusa da inda abin ya faru, wato kamar asibitin Biba, Aminci, Zaitun da kuma Salamat, wadanda duk kusa suke da makarantar, za a ma iya cewa unguwarsu daya. ALMIZAN ta zagaya asibitocin domin ganin wadanda abin ya shafa. Lokacin da muka ziyarci asibitin Zaitun wanda daura yake da makarantar, Nurse din ta shaida wa Wakilinmu cewa lallai an kawo masu yara biyu amma lokacin da aka shigo da su, shi ainihin likitan yana dakin tiyata, don haka sai suka ba su shawarar a wuce da su zuwa wani asibitin. Haka kuma lokacin da Wakilin namu ya je asibitin Biba da ke kan titin Matazu Road, an shaida masa cewa yawancin wadanda aka kawo masu duk gawarwaki ne kuma masu su sun riga sun karbi abinsu. Marasa lafiyan da aka kawo kuma an riga an ba su magani an sallame su. Kashe garin da abin ya faru ne Mataimakin Gwamnan Jihar Kaduna, Mista Patrick Ibrahim Yakowa ya kai ziyarar gani da ido a wannan makaranta, inda ya nuna takaicinsa matuka da wannan abu da ya faru a lokacin da yake zantawa da manema labarai a harabar makarantar. Ya ce gwamnati ba za ta zura ido ana wasa da rayukan jama’a ba. Mataimakin Gwamnan ya ce, don haka sun umurci Ma’aikatar ilimi ta jihar da ta gaggauta rufe wannan makaranta har sai hali ya yi, kuma za a kafa kwamitin bincike wanda zai tantance makarantun da ya zama wajibi ne a rufe su saboda rashin inganci. Don haka sai Mista Yakowa ya isar da sakon ta’aziyyar Gwamantinsa ga duk wanda wannan abu ya shafa, ya kuma yi alkawarin cewa gwamantin jihar za ta taimaka wa wadanda suke kwance a asibiti. Daga nan ya yi addu’ar Allah ya ji kan wadanda suka mutu. Kwamishinan ilimi na jihar Kaduna, Alhaji Bello Kagarko ya bayar da sanarwar rufe wannan makaranta nan take, tare da kafa wani kwamiti wanda zai dauki alhakin tantance duk makarantu masu zaman kansu domin a rufe wadanda ba su cika sharudda ba. Alhaji Kagarko ya kuma ce ya bayar da izinin a kamo shi kafintan da wutar ta tashi daga shagonsa domin ya fuskanci shari’a. Haka wani abu mai kama da wannan ya taba faruwa a wani kogi da ke kusa da Filin saukan jiragen sama na Kaduna, inda wasu yara ’yan sakandare su ma kimanin su 8 suka rasa rayukansu a sakamakon juyewar da kwalekwalen da suke ciki ya yi da su a lokacin da suka je domin yawon bude ido. Su dai wadannan yara dukkansu ’yan wata makaranta ce da ke Abuja, kuma sun ziyarci wannan wuri ne don abin nan da dalibai kan je wasu wurare don bude idanu, wato a turance ake cewa ESCURSION. Komawa babban shafinmu Komawa saman wannan shafin
| |
| Tafsirin Alkur'ani | Hadisai | Crescent International
| Tafsirin Alkur'ani | Hadisai | Crescent International
|