Almizan :Yahudawa ne ke haddasa rikici tsakanin musulmi ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 17 Shawwal, 1426                 Bugu na 692                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Tunatarwa:Tare da Shaikh Ibrahim Zakzaky

Yahudawa ne ke haddasa rikici tsakanin musulmi

SHAIKH ZAKZAKY
Malam Ibraheem Yaqoub Zakzaky H.

Masu karatu yau muna dauke ne da ci gaban jawabin da Malam Ibraheem Zakzaky ya gabatar a wajen taron Yaumu Shuhada na bana, wanda ya gabata a filin Kofar Shahada (Doka) Zariya a kwanakin baya. In dai ana biye da mu, yau muna mako na hudu kenan da soma kawo maku wannan jawabin. Za mu dan koma baya kadan don mu dauko maganar daga tushe. Kamar yadda aka saba, Musa Muhammad Awwal ne ya rubuto mana daga kaset. A sha karatu lafiya.

Su kuma ’yan ta’addan nan ba a san ma ko su waye ba. Suka ce ’yan Alka’ida ne. An kashe mutum shida amma ba a ga gawar ko mutum guda ba. Ba wani ka-ce-na-ce, ’yan sandansu ne, ma’aikatan KGB ne, su suka yi wannan shigar, suka yi wannan aika-aika da suka yi.

Sannan kuma suka ce ’yan Checeniya, Basayeb ne ya yi, sai ga shi an yi hira da Basayeb, ya ce lallai KGB suka yi. Har suka shiga babatu, don me talabijin din Amerika zai yi ‘Interview’ da Basayeb, alhali Mujrimi ne ya yi wannan barna.

Sune kuma suka sa Bom a London. Inda muka san su suka sa shi ne, sawan ke da wuya, duk sun yi ca a kan Musulmi. Ya zuwa yanzu ana da ‘Record’ na kai wa musulmi hari a gidajensu da masallatansu sama da 100, da kalmomi na kyamar al’ummar musulmi, da kuma daukar matakai na kuntata wa musulmi. Har da cewa, duk wani wanda yake goyon bayan ta’addanci ko yake yaba wa ’yan ta’adda, to za a hana shi shiga Birtaniya. In kuma yana ciki, za a fitar da shi.

Kuma in mutum yana kallo a Talabijin, in suna bayar da labarin meye ta’addancin nan, sai ka ga a daidai wannan lokacin sai su rinka sa hotuna, su rinka nuna ’yan Palasdinu masu gwagwarmaya suna wurga duwatsu. Sai a nuna cewa ’yan ta’adda, ’yan ta’adda, ’yan ta’adda. Sai a nuna Ka’aba da musulmi na salla, sai a rinka cewa ’yan ta’adda, ga ’yan ta’adda. Sai a nuna masallacin Annabi ana salla, ’yan ta’adda, ’yan ta’adda. Sai a nuna mata suna wucewa da hijabi, ’yan ta’adda, ’yan tadda, ’yan ta’adda. Wato a lokacin da ake ce maka ’yan ta’adda, to abin da ake nuna maka, ka gane su wanene. In ka ga mace da hijabi, to ’yar ta’adda ce. In ka ga mutum da dogon riga, ko ma cikin wadanda aka ce sun kai harin London, sai aka ce ai da can an san shi dabi’arsa irin ta Turawa ce, amma gab da zai yi harin nan sai aka ga ya fara wasu dabi’u masu ban mamaki. Sai aka ga yana yawan zuwa masallaci, kuma ya fara sa doguwar riga. Wato kun ga doguwar riga meye kenan? Ta’addanci kenan. Zuwa masallaci menene kenan? Ta’addanci kenan. Sai a ce ta’adda, ta’adda sai a nuna Liman yana huduba na Juma’a da rawani da abaya. Duk lokacin da suka ce ta’addan nan za ga sukan nuna musulmi ne.

Yanzu kafircin duniya da Yahudancin duniya yana ta kokarin ya nuna wa duk duniya gaba daya cewa in ka ji an ce dan ta’adda, to musulmi ake nufi. In kuma ka ji an ce ta’addanci, to addinin Musulunci ake nufi. Don kullum suka bude baki, sai su ce ai addininsu ne ya nuna haka nan. Yanzu ba kunya ba tsoro Tony Blair ya bude bukinsa ya yi magana da harshensa na Turanci ya ce ainihin ‘Terrorism is rooted in Islamic Religion.’ Ainihin ta’addanci ya samo asalinsa ne, tushensa daga addinin Musulunci.

Kuma har yana ta maganar cewa lallai yakin da za su yi na ta’addanci lallai za su yi yaki ne da ra’ayin ’yan ta’adda. Ya ’yan ta’addan ke tunani. Akidodinsu ne ke koya masu wannan. Wato ma’ana addininsu ne. Kuma har ya fadi wata magana ya ce, “abin da ya faru a London, da yawan musulmi ba su yarda da shi ba, domin da yawan musulmi suna tunani irin mu ne.” Wato ma’ana ba irin na addininsu ba. Wato su addininsu shi ne ke koyar da ta’addanci, yanzu ana kokari ne a raba musulmi da addinin nan da yake koya masu ta’addanci.

Kuma cikin abubuwan da sukan fadi na ta’addancin, tunda suna nuna ma har hijabi ma ta’addanci ne, har gemu ma ta’addanci ne,doguwar rigama ta’addanci ne, salla a masallaci ta’addanci ne, karanta Alkur’ani ma. Don an je ma Pakistan an ce daga nan ne ta’addanci ya samo asali. Sai a nuna ’yan makaranta suna kada kai suna karanta Alkur’ani, sai a ce to ka gani yadda ake koya masu ta’addanci tun suna yara, ka ga suna ta wani haka suna ta karatu, ta’addanci kenan. Nan da nan suka sa Musharraf ya ce a kori Dalibai da suka zo daga waje, sai ka ce ya yarda Daliban cikin gida su koyi ta’addanci kenan.

Da ganin wannan irin matakan da suka dauka, sun nuna su suka dasa bama-baman don su yi amfani da wannan sa bama-baman su yi wadannan miyagun ayyukan da suke yi na malkwaya abin da mayar da musulmi shi ne dan ta’adda, addininsa ne kuma ta’addanci.

YAHUDAWA NE KE HADDASA RIKICI TSAKANIN MUSULMI

Ba ni da lokacin da zan yi maku dogon bayani a kan wannan. Ina so in yi maku bayanin cewa don mutum ya sani, in ma ya ga ana rikici tsakanin musulmi da musulmi, to ya tabbatar da cewa wannan rikicin, in ya bi diddiginsa ya bincika sai ya samo asalinsa daga Amerika da Isra’iala aka yiwo.

Kuma shi Bayahude burinsa ya ga ya kashe mutum, kuma yana jin dadin ya ga gawa. Ya zo a Hadisi cewa in kuka kadaita da Bayahude daga kai sai shi, to abin da zai zo a tunaninsa shi ne ya zai yi ya kashe ka? Wato da za ku shiga tarago daya da Bayahude, in ka ga yana kallon ka, a zuciyarsa abin da yake tunani shi ne ya zai yi ya kashe ka? Wannan hadisin Manzon Allah ya zo da wannan.

Shi yana jin dadin ya ga gawa ta musulmi. Kuma bilhasali ma har a littafinsu sun rubuta suka ce wai ayar Allah ce a cikin Attaura, “ku kashe su duk cikansu, mazan ku kashe, matan ku kashe, har yaran ku kashe, duk dabbobinsu ku kashe, shanunsu ku kashe, awakinsu ku kashe, kajin ku kashe, har kwayayensu ku kashe.” Wai aya ce a cikin Attaura.

Kuma yanzu ma suna koya wa yaransu ’yan Firamare wakoki. In sun tashi daga makaranta za su koma gida, suna waka ne ana tafi. “za mu kashe su, za mu kashe su, duk cikansu za mu kashe su, Larabawa za mu kashe su, za mu kashe su, za mu kashe su.” Waka ake koya wa yaro dan karami in ya taso daga Firamare, “za mu kashe su, za mu kashe su, duk cikansu za mu kashe su, Larabawa za mu kashe su, kowannensu za mu kashe su, jariransu za mu kashes u, matansu ma za mu kashe su, manyansu za mu kashe su, za mu kashe su, za mu akashesu.” Wannan waka ake koya wa yaro.

Don ka sani in za ka zama karen Bayahude, jakin Bayahude, wanda zai yi amfani da shi ya kashe musulmi, to ka ba da kokari. Ka sani cewa ba mamaki wannan aya za ta yi aiki a kanka domin makomarka za ta kasance tare da shi ne. Shi kuwa in ya shiga wuta ba zai fita ba. Ba a yi wuta domin musulmi ba, amma Allah (T) yana cewa, “ku ji tsoron wuta wanda makamashinta mutane ne da duwatsu, wanda aka yi tanadinta domin Kafirai.” Domin ba a yi tanadin wuta domin Mumini ba, amma idan mumini ya fandare, shi ma sai ya bi kafirai a wajen shiga. An yi tanadinta domin su ne, su dawwama za su yi, in sun shiga ba su fita.

To kai ka ji tsoron wannan wutar wadda aka yi domin su, ka yi aiki dominsu ka koma makomarsu. Ka ci wuya biyu, nan kai sunanka mumini, gobe kiyama sunanka kafiri. Kuma ka fi su ma muni don sunanka munafiki, “Innal munafikina fid darkil asfali minannari walan tajida lahum nasira.” Munafukai sune a kuryan karshe na wuta, ba kuma za ka sami mai taimakonsu ba. Ba wanda zai ce ai wannan ya yi salla, ya yi hajji, ya ba da sadaka, ya taimaka wa jama’a, a ji tausayin sa. Ba wanda zai ce haka nan. Tunda ya yi aikin Yahudawa, ya taimaka masu, ya tafi makomarsu!

A irin wannan da so samu ne, da mun zauna musamman saboda jajanta abin da ya faru ranar Laraba da ta wuce a Kazimiyya (a lokacin da Malam yake wannan bayani). Wanda Yahudancin duniya, wanda Amerika ke wa jagoranci suka dira a kan musulmi ta hanyoyi daban-daban. Na farko, hanyar harba bama-bamai daga bayan gari, wanda muka san ba wanda zai iya harba wannan in banda Amerikawa, don su suke mamaye da kasar kuma su suke yawo da motoci da igogi a cikin garin.

Suka harba a cikin masallaci da dandazon mutane. Mutane suka fito, ana fitowa a firgice, don bama-bamai na dira a kan mutane, ana gudu, sai kuma aka bi ta gada, gadar kuma saboda turmutsutsu har ta karye kuma aka shiga harbi. Ana cikin wannan ma sai aka harba Katusha, wato bom din Katusha. Wanda yake za mu tabbatar sun yi amfani da wannan ne da gangan, don Katusha Rasha ke kerawa, kuma ’yan Hizbullah sun sha amfani da shi a kan Yahudawa. Saboda haka Katusha yakan ba su tsoro, kamar yana alamta cewa abin da musulmi ke harbin su da shi kenan. Amma su makamansu na MOSSAD da na Amerika wani abu ne daban, amma ran nan sai suka harba Katusha a kan musulmi, wato kamar mun rama, mun harbe ku da Katusha. Amma su Katushan Hizbullah ana harba ma mayakan Isra’ila ne wanda suke yakar al’ummar musulmi, su kuwa Katusha din sun harba a cikin masallaci ne a dandazon mutane masu AZA (ta’aziyya) na shahadar Imam Musa (AS).

Ana cikin wannan kuma, bayan wasu sun dira sun fada ruwa, gada ta karye ta zubar da wasu, sai kuma aka je asibiti aka lura wasu na mutuwa, kuma sai aka lura cewa an ba su abinci ne mai guba, ko ruwa na sha ko wani abinci suka ci da guba, wanda yake nufin Yahudawa sun zo kenan.

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


 Shafin Gamji | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International