Almizan :Inda aka tsaya kan gyaran Masallacin Abuja ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 17 Shawwal, 1426                 Bugu na 692                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Daga I-Mail

Inda aka tsaya kan gyaran Masallacin Abuja

Daga Salisu Na’inna Dambatta (salisunainna@yahoo.com)
Sayyid Ali Khemene’i yana mika kyaututtuka ga wasu Amare da ya daura wa aure kwanakin baya a Tehran
Sayyid Ali Khemene’i yana mika kyaututtuka ga wasu Amare da ya daura wa aure kwanakin baya a Tehran

Mutane da yawa a kasar nan, musamman masu kishin addini da son ganin ya kara kankama, ciki har da masu karanta wannan jarida, sun san da batun nan na yi wa babban masallacin Abuja da ya lalace ’yan gyare-gyare.

Bukatar gyaran wannan katafaren masallaci, wanda ya kamata mu yi ta gode wa Allah da muke da kamar sa a Nijeriya, ta taso ne lokacin da kwamitin kula da al’amuran masallacin, a karkashin jagorancin Sultan na Sakkwato, Alhaji Muhammad Maciddo, dan Marigayi Sultan na Sakkwato Abubakar na III, ya sa aka kai maganar gyaran masallacin gaban Shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo, inda aka bayyana masa bukatar musulman kasar nan ta shi Shugaban kasar ya shiga maganar, wato ya tallafa wajen gyara wannan wurin ibada.

To, shi Shugaban kasa bai dauki wannan bukata da wasa ba. Saboda haka sai aka shirya ranar wata Juma’a da hantsi ya ziyarci harabar masallacin domin ya ga irin lalacewar da wannan babban gini mai kayatarwa ya yi.

Sultan na Sakkwato da babban mai shari’a na kasa, Alhaji Muhammad Lawal Uwaisu da Shugaban Majalisar Wakilai ta Tarayya, Alhaji Aminu Bello Masari da wasu Gwamnonin jihohi da shugabannin wasu daga cikin manyan kungiyoyin Musulmi da manyan Maluman addinin Musulunci, da wasu jiga-jigai da aka sani da kishin addini ne suka tarbi Shugaban kasa a lokacin da ya ziyarci masallacin, kuma suka yi masa bayani dangane da wuraren da suka lalace a masallacin. Shugaban kasa dai bai shiga cikin kwaryar masallacin ba a lokacin da ya kai wannan ziyara.

Bayan ’yan kwanaki da kai waccan ziyara, sai Cif Olusegun Obasanjo ya kafa wani kwamiti na kasa baki daya a kan batun masallacin nan. Shi Cif Obasanjo din ne Shugaban wannan kwamiti. Mataimakin Shugaban kasa, Atiku Abubakar kuma Mataimakin Shugaban wannan kwamiti.

Domin a yi aikin cikin sauri da nasara, sai aka kafa wani karamin kwamiti na masana harkar gine-gine domin su yi nazari mai zurfi a kan irin lalacewar da ginin ya yi, su kuma fasalta gyare-gyaren da suka wajaba, tare da kiyasta yawan kudin da kowane fanni na gyare-gyaren zai ci. Malam Ahmad Nasir El-Rufa’i, wato Ministan babban birnin Tarayya na Abuja ne ya shugabanci wannan kwamiti.

Aikin da wannan kwamiti ya yi, ya zarce na gano zurfin lalacewar da masallacin ya yi, da irin gyare-gyaren da yake bukata, domin kuwa ya ma bayar da shawarwari a kan wasu gine-ginen da tun farko aka tsara masallacin da su, to amma Allah bai ba da ikon yin su ba.

Gine-ginen da ba a yi ba sun hada da makarantun firamare da sakandare, inda za a karantar da dalibai addini da kimiyya. Haka kuma akwai gidajen kwanan Malaman makarantun, da masaukin baki na kudi da shagunan da za a bayar haya da kantin cin abinci da dan karamin asibiti da sayen motar daukar marasa lafiya, ga kuma biyan bashin da masallacin ya ci, tare da gyara gidajen hadiman masallacin.

Bugu da kari, wannan kwamiti ya gano cewa saboda fatara, kwamitin kula da masallacin ya kasa biyan kudin ruwan famfo da na wutar lantarki da na wayar tangaraho da kudin harajin da ya kamata a rika biyan gwamnati a duk shekara, ga shi kuma hatta biyan albashin masu shara da ’yan gadi da masu kula da furannin kawata harabar masallacin, da duk sauran hadiman masallacin, manyansu da kanana, ya faskara.

To, daga karshe dai, kwamitin da Malam Nasir El-Rufa’i ya shugabanta ya gano cewa baki daya dai idan za a samo Naira miliyan 2000, to za a gyara masallacin tsaf, a kammala duk gine-ginensa da ba a yi ba, a biya bashin da ake bin masallacin, biyan albashin ma’aikatansa ya daidaita, a ajiye kamar miliyan 500 a gefe saboda bacin rana, yadda daga karshe dai, masallacin zai sami cikakken gata.

To, amma tunda gwamnatin Tarayya ba za ta debi kudin baitulmali ta gyara masallacin ba saboda wasu ka’idojin zama irin na Tarayya, shi ne Shugaban kasa ya kafa wani kwamiti daban, a karkashin jagorancin Gwamnan jihar Nassarawa, kuma Sarkin Yakin Keffi, Alhaji Abdullahi Adamu. Alhaji Bashir Yusuf Ibrahim, wani babban jami’i mai taimaka wa Mataimakin Shugaban kasa a kan al’amuran siyasa ne Sakataren kwamitin. Aikin wannan kwamiti shi ne ya kaddamar da gidauniyar neman taimakon kudin da za a magance matsalolin masallacin da su.

Duk wani Gwamnan jiha Musulmi yana cikin wannan kwamiti, ga kuma wakilan manyan kungiyoyin Musulunci na kasar nan, tare da wasu hamshakan ’yan kasuwa Musulmi wadanda aka san ba sa wasa da harkar addininsu.

Shi ma Gwamnan jihar Nassarawa, Alhaji Abdullahi Adamu, wanda mutane da yawa suka san mutum ne mai kwazo da juriyar daukar nauyin hidima mai amfani kamar ta gyaran masallacin nan, bai yi wani wuni-wuni ba, sai kawai ya kama aikin gano hanyoyin da za a bi domin haka ya cimma ruwa a kan gyaran dakin Allah.

Shi da Gwamnoni da wakilin Sarakuna da sauran wakilan kwamitin da yake shugabanta, sai suka dukufa wajen yin taruka domin a cika wannan aiki. Suka je jihohi daban-daban, inda ya rika ganawa da Gwamnoni da Sarakuna domin yi musu bayani da jan hankulansu a kan wannan babban aiki. Shi ya rika daukar hayar jirgin sama da daukar motoci da sauran duk wani nauyi da ya shafi irin wadannan tafiye-tafiye.

Da tafiya ta yi nisa, sai Allah ya ba shi basirar shigar da dukkanin Shaihunan Malaman addinin Musulunci na kasar nan a cikin harkar. Kuma da yake sun ga aikin Allah ne, nan da nan suka hadu. Malaman sun hada da Shaikh Dahiru Usman Bauci da Shaikh Sani Yahya Jingir da Shaikh Mahmud Salga da Shaikh Khalifa Ibrahim Saleh da Shaikh Kariballah bin Nasiru Kabara da Shaikh Tijjani Bala Kalarawi da Shaikh Muhammad Yusuf Sambo Rigachikum da Malam Shattima A. Kaita da Shaikh Isa Idoko da sauran wasu da dama.

Wani babban alheri da ya biyo shigar da manyan Maluman nan cikin wannan aiki shi ne, sun yi aiki ba tare da la’akari da bambance-bambancen fahimta ba, sannan suka ce daga yanzu sun zama tsintsiya madaurinki daya. A takaice dai, sun hada kai, sun dunkule, ba sauran jayayya da juna, kuma duk lokacin da wani al’amari da ya shafi addinin Musulunci ya taso a kasar nan ko a duniya baki daya, to za a tunkare shi da murya daya. Shi kuma Gwamna Alhaji Abdullahi Adamu ya amince zai ci gaba da goyon bayan ganin hakan ta faru, kuma an dore a kan hakan.

Bayan kwamitin manyan Maluman nan kuma, sai ya nemi ’yan sa-kai, masu yi wa Allah aiki, masu yawa, daga ko’ ina a cikin kasar nan, su ma suka shiga aikin.

To, da yake kamar yadda na fara nusar da mai karanta wannan bayani, shi Gwamnan Nassarawa, Alhaji Abdullahi Adamu ya goge a tafiyar da harkokin jama’a, kuma ga hikima da jin shawara, sai ya kafa wasu kananan kwamitoci guda uku a kan tara kudi a karkashin jagorancin Gwamnan Jihar Neja, Injiniya A. A Kure, da na karbar baki da tsara wurin da aka yi taron neman taimakon kudin, wanda Shugaban Ma’aikatan gwamnatin Tarayya, Alhaji Mahmoud Yayale Ahmad ya shugabanta, da kuma na aikin fadakarwa ta kafofin sadarwa da yada labarai, a karkashin Gwamnan jihar Lagos, Alhaji Bola Ahmad Tinubu.

Kafin ka ce kwabo, sai kasa ta dumame da zancen neman taimakon kudin gyaran Masallacin Abuja.

Daga karshe dai, a ranar 10 ga watan Maris na shekarar 2005 aka kaddamar da gidauniyar nan. Babban mai kaddamarwa Alhaji Aminu Dantata ya rantse zai ba da sadakar Naira miliyan 250 domin wannan aiki.

Ya zuwa yau din nan ana jira ya kawo su, to amma gwamnatocin jihohi da jama’ar Shugaban kasa da ’yan kasuwa da sauran jama’a masoya ayyukan alheri, sun ba da kudi lakadan fiye da Naira miliyan dubu da dari uku domin a sa su a aikin gyaran masallacin nan. Misali, gwamnatocin jihohin Nassarawa da Kogi da Bayelsa da Katsina da Oyo da Kano da Bauci duk sun bayar da abin da suka ce za su bayar. Sai dai dan abin da ba a rasa ba, kamar Naira miliyan 44 da kananan Hukumomin Jihar Kano 44 ba su bayar ba tukuna.

Jihar Sakkwato da Yobe da Biniwai da Taraba da Lagos da Jigawa ba su ba da ko anini ba daga cikin kudin da suka yi alkawarin bayarwa har yanzu, amma jihohin Kwara da Borno da Zamfara da Adamawa da Filato da Kebbi da Gombe da Kaduna da Nejar sun ba da wani abu daga cikin kudin da suka yi alkawari, amma ba su kawo ciko ba, har yanzu ana jira. Wasu manyan ’yan kasuwa ma irin su Alhaji Aliko Dangote da Alhaji Abdussamad Isiyaku Rabi’u da Alhaji Aresekola Alao da sauransu da dama, ba su bayar ba har ya zuwa ranar da na kammala rubuta wannan sharhi.

Gwamnan jihar Nassarawa ya sa an bi sawun kudaden da wasu gwamnatocin jihohi suka bayyana da kansu a wurin taron nan za su bayar, kuma shi da kansa ya tuna wa Gwamnonin da ba su ba da ba, amma har yanzu suna cikin bashin alkawarin da suka yi a bainar dubun-dubatar mutane. Sai dai ana sa ran za su cika dukkanin alkawuran da suka dauka. Mu dai mu yi addu’a, Allah ya ba su damar yin hakan.

To, kila mai karatun wannan sharhi zai so jin inda kudin da suka shigo hannu suke, da kuma abin da ya sa har yau ba a fara aikin gyaran masallacin ba. Gaskiyar magana ita ce, kudi suna nan ba a taba ko anini daga ciki ba. Ba a fara aikin gyaran masallaci ba saboda har yanzu ba a nada kwamitin amintattun da za a danka wa alhakin aikin gyaran masallacin ba. To amma alamu na nuna cewa saura kadan a nada wakilan kwamitin, su zauna su kama aikin.

Wani babban sirri da jama’a da yawa ba su sani ba shi ne, tun sad da aka nada Gwamnan Nassarawa, Alhaji Abdullahi Adamu shugabancin kwamitin neman kudin da za a gyara masallacin nan; yau kusan shekara guda cur, shi ne ya dauki nauyin biyan albashin ma’aikatan masallacin nan duk wata. Kudin albashin kuwa sun haura Naira miliyan daya da rabi kowane wata. Bayan wannan, na sani cewa shi ne ya dinga ba da kudin shirye-shiryen kaddamar da asusun kudin gyaran masallacin, kodayake Gwamnonin wasu jihohi biyar sun ba da Naira miliyan dai-dai don tafiyar da harkar.

A takaice dai, Gwamnan Nassarawa, Alhaji Abdullahi Adamu, Sarkin Yakin Keffi, yana nan ya yi tsayin daka wajen hana taba kudin nan, kuma ba shakka ya dauki nauyi mai yawa a kan wannan harka. A ganina, ya dace, ko in ce ya cancanci mu yi ta yi masa addu’ar neman Allah ya yi masa sakayya da alheri a kan wannan aiki da ma wasu ayyukan kirki wadanda mutane da yawa suka shaida ya sa a gaba.

Salisu Na’inna Dambatta ma’aikaci ne A Kwamitin Neman Kudin Gyaran Masallacin Abuja. Ya aiko mana da wannan rubutun ne ta I-mel dinsa (salisunainna@yahoo.com).

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


 Shafin Gamji | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International