Almizan : A Takaice kai Tsaye: Na M.M Awwal, Ta GSM,0803 451 4692 ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 17 Shawwal, 1426                 Bugu na 692                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
A Takaice kai Tsaye: Na M.M Awwal, Ta GSM,0803 451 4692

ALMIZAN, ALLAH YA KARE MANA KU

Assalamu alaikum. Na bugo ne domin na yaba maku da irin kokarin da kuke yi. Gaskiya muna jin dadin irin yadda kuke kawo mana bayanai filla-filla ba tare da wani son rai ko azarbabi ba. Allah ya yi maku taimako, ya kuma kare mana ku da mu, amin.

Daga Alhaji Shu’aibu Mai Fata Kwanar Dangora jihar Kano 0803 964 1849

MUN RIGA MUN RUSA SHIRINKU

To Malamai, watanni uku kenan kuna neman ku hada fitina tsakanin Shi’a da Sunna, har na ji kun yi rabon Aljjana, amma ba ku ba ’yan Shi’a ba, to yanzu dai mun rusa sharrinku, cikin awa uku.

Daga 0806 242 1374

ALMIZAN MAKARANTA CE

Assalamu alaikum. Al’umma ya kamata mu gane cewa ALMIZAN tamkar wata makaranta ce, wacce in mutum yana karanta ta zai ilmantu, ko da kuwa shi ba musulmi bane. Kodayake sai mai ilimi da hankali da basira ne kadai zai iya gane haka.

Daga Muhammad Aruwa Kofar Goga Katsina 0803 692 0810

SIDI SHARIF AL’ALAWAYI HAKA NE?

Assalamu alaikum. Sidi Sharif Al’alawi ya haka ne? Mun ga irin taimakon da kake bai wa makarantun Islamiyoyi, Cibiyoyin addini, kungiyoyi da dai-daikun mutanen, amma ga Fudiyoyinmu nan masu yada koyarwar Kakanninka suna bukatar taimako, amma na ji shiru. Ko ba ka san da su bane?

Daga Ado NEPA Kofar Waimbai Kurna jihar Kano 0802 437 9973

IYAYEN MANZON ALLAH MUMINAI NE

Assalamu alaikum. Yan Salafiyya da Izala ku tuba zuwa ga Allah, iyayen Annabin Rahama (S) Muminai ne ba Mushirikai ba. Yan Aljanna ne, ba kamar yadda kuke riyawa ba. Allah ya kiyashe mu, amin.

Daga Abdulwahab Lafiyar Galambi jihar Jigawa 0806 206 8055

AHMADINAJADI MUN GOYI BAYANKA

Dakta Ahmadinajadi mun goyi bayan maganar da ka yi wacce kasashen duniya da kuma kafafen yada labaran Yammacin duniya da masu sharhi daban-daban suke ta yin batsaltsale a kai, suna cewa wai rashin gogewa ce ya sa ka fadi haka, amma mu mun san cewa imaninka ne. Muna yi maka jinjina ta musamman. Hakika ka nuna wa duniya kai mabiyin Imam Husaini ne, kuma ka samu tarbiyya daga wajen dodon Yahudawa, Imam Khumaini. Allah ya kare mana kai da Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Daga Haruna Abba Kazimiyya Computer Center Potiskum jihar Yobe 0803 839 9910

…SHAFE ISRA’ILA SHI NE ZAMAN LAFIYA

Assalamu alaikum. Shugaban kasar Iran, Dakta Ahmadnajadi, ni ma na goyi bayanka a kan a shafe haramtacciyar kasar Isra’ila daga taswirar duniya domin dama ba a kan halasci aka kafa ta ba, kasa ce ta ’yan ta’adda da ta’addanci. Don haka shafe ta daga doron duniya shi ne zaman lafiya ga baki dayan al’ummar duniya.

Daga Hamza M Djibo Jamhuriyya Nijar (djibohamza@yahoo.fr)

…DAKTA AHMADINAJADI YA DACE DA SHUGABANCIN IRAN

Assalamu alaikum. Lalle Dakta Ahmadnajad ne ya fi dacewa da shugabancin Jamhuriyyar Musulunci ta Iran a wannan zamanin, saboda a ’yan kwanakin da ya yi yana bisa karagar mulkin Iran sai da ya girgiza duk wata gaba ta kafircin duniya. Madalla da wannan shugabanci na Ahmadinajad. Insha Allah sai ka cimma hadafin da ka sa a gaba.

Daga Amiru Mu’azu Muhammad Funtuwa jihar Katsina (profnomagic@yahoo.com)

KIYAYYAR TA FI KOWACCE MUNI

Ku sani ya ku iyaye! Hakika kiyayyar da ta fi muni daga kiyayya ga Sahabbai, Tabi’ai, Tabi’an-tabi’un, kai dama ko wanene na daga ababen halitta, ita ce kiyayya ga Ahalin Gidan Annabi (SAAW). Domin kiyayya gare su, kiyayya ce ga Annabi, kiyayya ga Annabi kuma, kiyayya ce ga Allah, ita kuma halaka ne. Ga shi kuma Allah Ya yi umarni cikin Alkur’ani da a so su. Mu kuwa wannan wajibi ne a wurinmu! Muna son su, muna son duk abin da suke so, muna kuma kin duk abin da suke ki! Abin koyi kamar su kuwa, ba mu gani ba.

Daga Awwal Sulaiman, G. Dutse, Kano. (awwalusuleiman@yahoo.com)

HABA ’YAN IZALA!

Assalamu alaikum. Haba ’yan Izala! Idan ana neman hadin kai, ba sukar wani bangare ake yi ba.

Daga Adamu Hayin Rigasa Kaduna 0803 287 3662

INA MALAM YAHYA SHARFADI?

Assalamu alaikum. Malam Yahya Sharfadi, ka ji tsoron Allah, kuma ka nemi sanin sa a matsayi na hakika. Na tabbatar idan ka yi haka, za ka fahimci yadda al’amuran suke.

Daga 0806 567 0981

AMSA KIRAN MALAM ZAKZAKY NE MAFITA

Assalamu alaikum. Al’ummar Musulmi ku sani babu zaman lafiya, ko saukin al’amuran rayuwa sai mun yi da’a ga Allah (T). Ga Malami nan na Allah ya kira mu, shi ne Malam Ibraheem Zakzaky, don haka mu karba masa kawai shi ne mafita.

Daga 0803 692 0810

ME YA SA BA MA GANIN ALMIZAN A GOMBE?

Assalamu alaikum. Mu dai a nan Gombe mun daina ganin ALMIZAN, lafiya dai ko?

Daga Ibrahim Mai Soso Je Ka Da Fari Gombe 0802 839 7026

Malam Ibrahim muna kai jarida ALMIZAN Gombe a kowanne sati kamar yadda muka saba, don haka sai ka binciki Malam Dan Yarwa bin Laden don ka samu naka kwafin.

-Edaitan Shafi.

KIRAN MALAM ZAKZAKY SHI NE HANYAR HADIN KAI

Assalamu alaikum. Dakta Ahmad Gumi, kiran Malam Ibraheem Zakzaky shi ne hanyar hadin kai. Don haka ina fatan kai da masu tunani irin naka za ku amsa kiran Malam Zakzaky don sama wa musulmin Nijeriya mafita.

Daga 0802 450 8106

ALMIZAN KO KUN MANTA NE?

Assalamu alaikum. Don Allah ALMIZAN wai ina batun mai da wasika zuwa ga Malam Shekarau littafi ta kwana ne? Ko dai kun manta ne?

Daga Abdulwahab Yankari Experss Bauci 0806 206 8055

MALAM ABUDULJABBAR ALLAH YA SAKA MAKA

Assalamu alaikum. Malam Abduljabbar ka ci gaba da fadar gaskiya. A gaskiya Shaikh kana kokari wajen zakulo gaskiya don fadakar da al’ummar musulmi a game da kara sanin tarihin Musulunci. Hakika kwanaki mun ji irin abubuwan da ka fada game da Shi’a a kusa da Unguwar Adakawa. Allah ya saka da alheri.

Daga Nura Shitu Idris Kano 0802 861 9629

Assalamu alaikum. Ina sanar da Mustafa Usman Kaduna cewa kalmar la’ilaha illallahu ba a rubuce take ba a aikace take. ’Yan Izala da makamantansu kuwa suna aikata ta ne a aikace.

Daga 0802 871 4251

MUN YI MUZAHARAR KUDUS LAFIYA A KANO

To makiya Annabi (S), mun yi muzaharar Kudus kuma an tashi lafiya a Kano, duk da cewa ba haka wadansu suka so ba.

Daga Yakubu Nasir Bacirawa Kano (yakubnas@yahoo.com)

HADIN KAN MUSULMI, KO HADIN KAN IZALA?

Assalamu alaikum. Ina so ne na tambayi Dakta Ahmad Gumi game da hadin kan da yake cewa yana neman ya yi, na musulmi ne, ko kuwa na Izala? Gaskiya dai daya ce; daga kin ta kuma sai bata. Dakta da ka je Zariya ka karo ilimin yadda ake hada kan musulmi.

Daga Shu’abu J. Imam Kinkinau jihar Kaduna 0803 287 3959

ALMIZAN HADIN KAI YA DACE KI KOYAR

Assalamu ala’imu. ALMIZAN hadin kai ya dace ki koyar, domin wallahi yanzu tamkar rana kike, kowa dubarki yake yi. Don haka ki yi kokarin hada kan mutane ba raba su ba.

Daga Aliyu Bakir 0806 546 6454

MUNA GOYON BAYAN SHUGABAN IRAN

Ina taya al’ummar musulmin duniya murnar sakon da Shugaban Jamhuriyyar Musulunci ta Iran ya aika ga kafircin duniya, domin a madadin musulmi ya aika. Muna goyon bayansa 100 bisa 100. Domin ko da Hitla ne ya dawo da manufar share haramtacciyar kasar Isra’ila daga bayan kasa, sai mun goyi bayansa, balle Shugaban Iran. Allah ya taimake shi.

Daga Mahmud Shehu Tudun Fulani PO BOX 12940 Kano. (mahsheik@yahoo.com)

ABIN DA YA KAMATA MATASA SU SANI

Assalamu alaikum. matasa ku sani kune kashin bayan ci gaban al’umma, Amma yanzu kun zama kune kaskantattu, kuma koma baya, tamkar bayin mahukunta na wannan kasa, saboda kun ki amsa kiran Ubangiji.

Daga Muhammad Kofar Guga Katsina. 0803 692 0810

A GAISHE KU DA AIKI

Assalamu alaikum. ALMIZAN ina gai da ku da aiki da kuma fadin gaskiya. Allah ya taimake ku, amin.

Daga Arma Gindin Gada, Singa Kano. 0806 554 7469

ALHAJI ALI DATTI YAKO YANA AIKI

Gaskiya yadda Alhaji Ali Datti Yako yake aiki abin yabawa ne. Da haka Kantomomi suke aiki da sai mu ce Allah ya sa duk Nijeriya a nada Kantomomi.

Daga Ishaka (Babban Yaya) Kwanar Dangora, Karamar Hukumar Kiru, Jihar Kano 0803 628 8042

KASASHEN TURAI DA AMURKA KU YI HATTARA

Tsarin tattalin ariziki na Jari-Hujja ba abin da zai haifar sai abin da ake gani yanzu a Faransa. Saboda haka kasashen Turai da Amurka sai a ku yi hattara.

Daga Bilyaminu Kiru, Jihar Kano 08023097766

SAI MUN GAMA DA ’YAN SHI’A A KANO

Kai ja’iri na ga sakonka zuwa ga Shekarau, wanda aka buga a cikin shaidaniyar jaridarku ta wannan satin (18 Ramadan 1426). Mu kam mun san cewa a Sakkwato an sami nasara a kan ’yan Shi’a. Muna fata Allah ya ba mu irin wannan nasarar a kan dukkanku ’yan Shi’a da ke nan Kano da kewaye, mu halaka ku duk.

Daga 0802 870 0438

To Malam, kodayake ba ka sanya sunanka da adireshinka na gaskiya ba, ga dukkan alamu ba ka da gaskiya. Muna wata mai alfarma ne, amma ka furta irin wadannan munanan kalaman. To ko ma dai menene ga sakonka nan mun rubuta, sai dai mun cire wuraren da ka yi zage-zage, wannan kuma kai da Ubangijinka. Batun nasara a Sakkwato da ka ce, to ka sake bincike dai. Sannan kuma niyyar da kuke da ita a Kano, kar ku fasa, mafi munin abin da za ku yi mana shi ne mafi alheri a wajenmu.

- Editan Shafi

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


 Shafin Gamji | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International