Almizan :Kasar Iraki: Fagen jihadi ko dandalin wasan kwaikwayon siyasa (5)? ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 17 Shawwal, 1426                 Bugu na 692                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Taska

Kasar Iraki: Fagen jihadi ko dandalin wasan kwaikwayon siyasa (5)?

Daga Mujtaba Adam (nigeria3000@yahoo.com)


Ci gaba daga makon jiya.

Abdul-Bary Adhwan Editan Jaridar AL-QUDSUL-ARABY sharhin da yake yi ya shako gaskiya da ya ce: “Amurka ta kware wajen yin amfani da Larabawa a matsayin makamin cimma manufarta. Ta yi amfani da kasar Saudiyya wajen samar mata da kudaden da ta yi yaki a kasar Afghanistan. Ta kuma yi amfani da ita saboda ta samar mata kawancen kasashen Larabawan yankin Tekun Fasha saboda ta yaki juyin-juya-halin Khumaini. Ta kuma yi amfani da ita saboda ta ba da kudaden da za ta yi yakin ’yantar da kasar Kuwaiti. Ta kuma yi amfani da ita wajen yakin da ta yi da Iraki. Haka nan lamarin ke ci gaba da gudana” Jaridar ALQUDSUL-ARABI ta ranar 9/9/2005.

Akidar kishin Larabci wacce a yanzu Sa’ud Faisal ke karewa ba ta tsinana wa Larabawan komai ba, domin kuwa ba ta ’yanto ko da taku daya na Palasdinu da ke karkashin mamayar Yahudawa ba. Hasali ma Larabawan sun sha kashi ne a hannun Yahudawa a daidai lokacin da wannan akidar take kan tashenta. Ilahirin kasashen Larabawa suka sha kashi a hannun Yahudawa a cikin kwanaki shida kacal daga fara yakin 1973. Saboda kare wannan akidar ne suka yaki Iran saboda su kawo karshen Khumaini da juyin-juya halinsa, ba a cikin kwanaki hudu, kamar yadda Saddam Hussain ya yi musu alkawari a ranar 22/09/1980 da ya fara yaki, amma ba su yi nasara ba. Littafin The Wars Against Saddam na John Simpson.

Wannan akidar ta kishin Larabci da bangarorinta biyu na Nasiriyya da Ba’asiyya ta riga ta yi wa kanta jana’iza tun a cikin shekaru na 60 da 70. Daruruwa, idan ba dubban ’yan kungiyar Ikhwanul Muslimin da Abdunnasir ya kashe a gidajen kurkukun Turra-laimuna, da watsa wa Kurdawa makamai masu guba da binne daruruwan ’yan Shi’a da Saddam ya yi, da kashe ’yan Ikhwanul Muslimin 40,000 da Hafizul Assad ya yi a garin Hama’a sun mai da ita daidai da akidun Nazi da bakin kishin kabilanci irin na Sabiyawa da Sahayoniya masu yin kisa bisa kabilanci da bangaranci.

Hatsarin wannan bakar siyasar ta Larabawa, musamman ma dai kasar Saudiyya shi ne yadda take samun masu yi mata fassarar addini. Matsaloli ne da suka shafi Larabawa su kadai, amma sai ta shafi wasu kasashe na musulmi da ke nesa da Gabas ta Tsakiya, saboda tsoma bakin Malaman addini a ciki. Malamai masu alakar akida da Saudiyya kuwa su fara tallata ta a tsakanin kasashen musulmi kai ka ce saukakken nassi ne da Mala’ika Jibrilu ya kawo wa Ma’aiki (S).

Abin da ke faruwa a kasa shi ne babban dalili. A shekarar 1991, lokacin yakin Tekun Fasha na biyu, irin wannan sabanin siyasar na Larabawa, wanda su kadai ya shafa ba wasu musulmin ba, ya shigo har cikin Nijeriya. Inda ’yan Izala suka raba masallatansu gida biyu tsakanin masu goyon bayan siyasar gwamnatin Saudiyya da ta yi daidai da ta Bush, da kuma masu goyon bayan Saddam Husaini. Har yanzu da akwai masallatan Izalar Bush, da masallatan Izalar Saddam a garuruwan Bauci da Gombe. Ba mamaki a nan gaba idan an sami wani masallacin da sunan Bush karami da kuma Zarkawy ko Usama Bin Ladan. Domin kuwa siyasar Saudiyya ce ta goyon bayan Amurka ta sa Izalar Gombe da Bauci ta rabu gida biyu.

Wannan siyasar ce kuwa ke ci gaba da wanzuwa har yanzu ba ta sauya ba. Wacce tun daga lokacin da aka kafa ta a matsayin masarauta ba ta shata wa kanta siyasar waje da ta yi karo da ta Birtaniya ko Amurka ba. Idan Shugaban Amurka Ronald Reagan yana kiran mayakan Afghanistan masu fadan neman ’yanci (Freedon Fighters), to gwamnati da Malaman Saudiyya na kiran su Mujahidun.

Gwamnati ko Malaman Saudiyya ba su ce uffan ba lokacin da Amurkan ta gaji da mulkin tatsinanci na ’yan Taliban, sannan ta rushe su. Da ma ita ce ta kafa su saboda su zamar wa Iran barazana, kamar yadda Ridhwan Sayyid ya fada a cikin littafinsa Assira’u Alal-Islam.

Yayin da Larabawa da suka yi yaki a kasar Afghanistan suka zama ’yan ta’adda a idon Amurka. To a wajen gwamnati da Malaman Saudiyya sunansu ‘batacciyar kungiya’ (Fi’atul-dhala). Malamin gwamnati kwara daya tilo da ya soki harin da Amurka ta kai wa Taliban da kuma fada da Alka’ida shi ne Shaikh Hamud Al-Shu’aiby. Saboda haka ne gwamnatin Saudiyya ta kore shi daga cikin kungiyar manyan Malamai Hai’atu Kibarul-ulama’a.

Sannan kuma ta hana shi ba da fatawa. Matukar Sarakunan Saudiyya masu kawance da shugabannin Amurka na nan kan mulki, sannan kuma Malaman fada na ci gaba da bayar da fatawowi domin kare siyasar Ali Sa’ud, to zaman lafiya a tsakanin al’ummar Musulumci ba zai samu ba. A fadar Al-Mashary Al-Za'yidy (Tubaben dan kungiyar Alka’ida kuma marubuci a jaridar SHARQUL-AUSAT.

’Yan kasar Saudiyya na son tsoma baki wajen haddasa rikici tsakanin musulmi da kiristoci a kasashe kamar Nijeriya. Shirin Al-Idha’at na tashar talbijin din AL’ARABIYYA (mallakin Saudiyya), Laraba, 23/7/2005.

Ba mu taba ganin wani dalibin da ya dawo daga Jami’ar Azhar ko wata kasa da akidar Wahabiyanci, ya ce ita ce akidar al’umma da kasa ba, ya zama matsala a kasarsa ta haihuwa, amma daliban da suka yi karatu a Jami’ar Madina ko Ummul-Qura da ke Birnin Makka sun zama hatsari ga sauran kasashen musulmi. Duk wanda ya tsallaka tekun maliya a cikinsu ya je kasar Saudiyya ya yi karatu, to zai dawo gida saboda ya kafirta iyayensa musulmi, ya kuma jefi makwabtansa da bidi’a, ya kuma kira mutanen unguwarsu mushrikai. Ya gina masallaci da kudin man fetur, saboda ya rika wa’azin ta da tarzomar yaki tsakanin musulmi da kiristoci. Gaskiya ce mai daci da fadar ta ya zama wajibi, saboda ba suka ga akidar Wahabiyanci ba, ko hana wani ’yancin yin abin da ya yi imani da shi ba, abin da ke faruwa ne da ba wanda zai kore shi.

Shafin www.ahlulbaiti.com da yake kunshe da bayanai na cusa kiyayya da gaba a tsakanin ’yan Nijeriya bisa akida ta Wahabiyanci, daya ne daga cikin dalilan da suke bayyana gaskiyar wannan magana. Ma’abota wannan shafin na yin yabo da jinjina ga ’yan daba da ’yan ta’addar da suka kashe ’yan uwa musulmi da suke kira ’yan Shi’a a birnin Sakkwato. Suna kuma yin kira ga musulmin Arewa (masu ra’ayi irin nasu na son ta da tarzoma da fitina) da su tanadi makamai da yi wa samarinsu horon soja saboda su yaki kiristoci da Shi’a da suka ce wai sune matsalar Nijeriya. Ashe zancen Al’zayidi na cewa da akwai hannun ’yan Saudiyya wajen ta da fitinar addini tsakanin musulmi da kiristoci a Nijeriya bai zama gaskiya ba?!

Kungiyar Alka’ida kuwa da dukkan sauran kungiyoyin da ke damfare da ita wacce tubalin da aka gina ta shi ne kafirta dukkan al’ummar musulmi. ‘Takfiriyya’ ta nisanta kanta daga ka’idojin jihadi saboda shelanta yaki a kan fararen hulan da ba su ji, ba su gani ba a biranen Baslan da Madrid da London da Bali da Sheramush-Sheikh da Bagadaza da sauran garuruwan Iraki. Maimakon su yi fada da abokan gaba na gaskiya da suka mamaye kasashen musulmi, sun buge da kashe fararen hula. Da sun kashe sojojin mamaya da sune abokan gaba kai tsaye, sai dukkan al’ummar musulmi su yi musu tafin nuna goyon baya, amma ba kashe fararen hula da ba su ji ba su gani ba.

Babu wani sanannen addini a doron kasa ko wata akida da tunanin mutum ya kirkire ta wacce ta halatta zubar da jinin karamin yaro, balle kuma addinin Musulunci da aka gina bisa jinkai da tausayi. Uwargijiya, Kali, da Indiyawa ke bauta, yanzu ta daina shan jinin kananan yara tun bayan da gwamnatin Indiya ta yi dokar hana yi mata layya da mutum. Kabilar Aztec ta tsohuwar Mexico ta tuba da cin naman abokin gaba, saboda sun rungumi kiristanci da ke cewa: “Kada ka yi kisa.” Masu bautar Shaidan (Devil Worshippers), sun halatta wa kansu yin komai, amma banda cutar da karamin yaro, kamar yadda ya zo a cikin doka ta tara a littafinsu mai suna ‘Stanic Bible’ wanda Anthony Levey ya rubuta.

Kisan da kungiyar Alka’ida ta yi wa kananan yara musulmi 35 ta hanyar harin kunar bakin wake saboda suna karbar alewa daga sojan Amurka a birnin Bagadaza shi ne babban dalilin da ke tabbatar da cewa sun la’anci kansu da kansu kafin la’antar Ubangiji da ta Mala’iku da ta salihan bayi, da ta dukkan wani mutum mai rayayyar zuciyar da take bugawa a cikin kirjinsa. Wannan kungiya ta Alka’ida ta tabbatar da cewa an kafa ta ne bisa tsarin kabilancin Larabawan Jahiliyya mazauna sahara da ke dogara da takobi wajen bai wa kawunansu gaskiya maimakon hujja. “Fi haddihil hadda bainal jaddi wal la’ibi!”

Kafirta dukkan al’ummar musulmi ba wai ’yan Shi’a ba kawai (kamar yadda ya zo a cikin jawaban kashe Jakadun Masar da Aljeriya) da kungiyar Alka’ida ta yi, ya mai da ita layi daya da kungiyar Lords’ Resistance Army ta Joseph Kony na kasar Uganda, wadanda suka halicci Ubangiji da kamanni irin nasu, suke kuma yi masa layya da jinin mutane saboda suna zaton yana bukatuwa da shi.

Muhammad Al-maqdasy, daya daga cikin shugabannin Salafiyya Jihadiyya a duniya, kuma wanda a hannunsa ne Abu Mus’ab Zarkawy ya tuba daga shan giya da yi wa mata fyade, sannan kuma ya mai da shi “mumini mai jihadi,” ya fadi cewa: “Kashe ’yan Shi’a yana da alaka ne da yakin Iran da Iraki, wanda Malamai (ko kuma ya fi dacewa in kira su Shehunnai) suka rika ba da fatawowi da suka yi daidai da manufar shugabanni na kafirta ’yan Shi’a. Wannan shi ne babban kuskuren da samarin Sunni da Shi’a suka fada a cikinsa. Na yi gargadi a kan fadawa cikin tarkon fadan mazhaba da ba wanda zai amfana da shi idan ba ’yan mamaya ba.” Kamar yadda jaridar ALHAYAT ta ranar 5/7/2005 ta ruwaito.

Gaskiya daya wacce fadar ta ya zama dole, in ji Mshari Al-Zaydi ita ce, “Tsattauran ra’ayin Musulunci, wanda yake da alaka da kungiyar Alka’ida da dukkan kungiyoyin da ke damfare da ita, sune ke da alhakin mace-mace da barnar da muke gani tana faruwa da idanunmu.” AL-SHARQ AL-AWSAT. 26/7/2005.

Tir da kabilancin Larabcin da ake bai wa kamannin addini a kuma halatta zubar da jini da sunan jihadi. Tir da fatawar zubar da jini da Malaman fada ke badawa saboda su kare bakar manufar mugayen shugabanni. Tir da addinin da Ubangijinsa ke jin dadin a zubar masa da jinin talakawa, leburori a filin “Sahatul-Uruba” a birnin Bagadaza. Tir da akidar da ke halatta wa mai bin ta zubar da jinin karamin yaro. Tir da akidar da aikin Malamanta shi ne gina wa kawunansu mutunci da matsayi ta hanyar cusa gaba a tsakanin al’ummar musulmi, ba hada kawunansu ba. Tir da Malaman da ba su da fasahar zaman lafiya sai dai ta da tarzoma. Tir da wankin kwakwalwar da ke sa samarin musulmi su kai harin kunar bakin wake a kan mutanen da ba su ji, ba su gani ba, musulmi ne, ko ba musulmi ba. Tir da Khawarijawan karni na ashirin da daya. Tir da wannan wasan kwaikwayon siyasa da ake yin sa a kasar Iraki bisa dandamalin da aka yi dabensa da jinin mutum.

”Idan har babu Ubangiji, to babu kyawawan halaye,” in ji Destoevsky a cikin littafinsa na BROTHERS KOROMOZOV. “Idan kuwa babu kyawawan halaye, to komai ya halatta.” Ka’idar mulkin nan na Machiavelli wacce a cikin litafinsa THE PRINCE, ya halatta yin amfani da komai domin kai wa ga manufar kasar Amurka bisa jagora a siyasarta ta waje. Ba ta da halaliya ko haramun wajen cimma manufarta kowace iri ce.

Wannan ka’idar ce ta yi mata jagora yayin da ta yi amfani da muminai Larabawa suka yi mata jihadi a kan tarayyar Soviet da ta mamaye a kasar Afghanistan. Kawancen da ke tsakanin kungiyar leken asirin Amurka CIA da kungiyar leken asirin Saudiyya-Mukhabarat da ta Pakistan ISI ne ya ba ta dammar cimma yin haka.

Ahmed Rashid dan rahoton mujallar FAR EASTERN ECONOMIC REVIEW ya rubuta wani rahoto a 1986, wanda a ciki yake cewa; “Shugaban kungiyar leken asirin CIA, William Casey ya amince da bukatar kungiyar leken asirin Pakistan na dauko mayaka (musulmi) daga ko’ina a cikin duniya domin su yi jihadi a kasar Afghanistan. Akalla musulmi masu tsattauran ra’ayi da adadinsu ya kai 100,000 ne suka shiga Pakistan daga 1982 zuwa 1992. Daga cikinsu mutane 60,000 sun shiga makarantun addini na masu tsattauran ra’ayi a Pakistan.”

John Cooley, marubucin littafin UNHOLY WARS, ya yi tsokaci da cewa: “Musulmin da aka dauke su a cikin Amurka saboda a tura su su yi yaki a kasar Afghanistan an aike da su zuwa sansanin ba da horo na ‘Camp Peary,’ wanda nan ne wurin da CIA ke bai wa ’yan leken asirinta horo a Virginia. A nan ne aka horar da Afghanawa da Larabawa daga Masar da Jordan da bakaken fata Amurkawa musulmi a kan ayyukan ta’adi da barna (Sabotage Skills).” Littafin UNHOLY WARS, Afghanistan, America and international terrorism.

Jaridar INDEPENDENT ta Birtaniya, wacce aka buga a ranar 1 ga watan Nuwamba na 1998 ta yi tsokaci kamar haka: “A cikin sansanin ba da horo na Alkifah da ke Brooklyn a birnin New York aka horar da mayaka a kan ayyukan ta’adi da barna, sannan aka tura su zuwa kasar Afghanistan domin su yi yaki a karkashin rundunar Hizbul-Islami ta Gulbuddin Hikmatayr.”

Dogon rahoton jaridar INDEPENDENT ya ci gaba da cewa: “Daga cikin wadanda suka sami horo a wannan sansanin da akwai Ali Muhammad, wanda sojan Amurka ne. Shi kuwa Ali Muhammad shi ne ya zama mai bai wa mayakan Usama Bin Ladan horo. Shi ne ya horar da wadanda suka kai hari a kan ofisoshin jakadancin Amurka da ke Tanzaniya da Kenya. Shi ne ya yi wa Al-Nasri horo. Shi kuwa Al-Nasir shi ne ya kashe Malamin addinin Yahudawa, Rabi Meir Kahane. Da kuma wadanda suka fara kai wa Cibiyar kasuwanci ta duniya hari a shekarar 1993.”

Wani bangaren na rahoton ya ci gaba da cewa: “A lokacin yakin Afghanistan, CIA, da ISI ta Pakistan da MUKHABARAT na Saudiyya sun kafa wani ofishi a kasar Pakistan da ake kira Maktab Khidmat, ko kuma MAK a takaice. Aikin wannan ofishin shi ne raba mukamai da sauran kayan yaki ga kungiyoyin da ke fada da Tarayyar Soviet a kasar Afghanistan. Usama Bin Laden ya rike shugabancin wannan ofishin a 1989.”

A shekarar 1986 Usama Bin Laden, tare da taimakon CIA da ISI da kuma MUKHABARAT sun gina wuraren ba da horo na karkashin kasa a cikin Afghanistan.

Tom Crew, tsohon jami’in sojan Birtaniya ne, SAS, wanda ya kasance tare da Mujahidun a Afghanistan. Ya fada wa jaridar OBSERVER ta ranar 13 ga watan Augusta 2000 cewa: “Amurkawa sun koya wa mayakan Afghanistan dabarun ta’adi da barna da suka hada da sanya bama-bamai a cikin motoci saboda su rika kai wa Rashawa hari a cikin birane. Da dama daga cikinsu sun wayi gari suna amfani da wannan fasahar ta ta’adi da barna a kan duk wani abu da suka ki jininsa.”

Norm Dixon a cikin mukalarsa mai taken “HOW CIA CREATED OSAMA BIN LADEN?” ya yi wata ishara kamar haka: “A wannan lokacin Usama Bin Laden yana aikata dukkan abin da kuniyar leken asirin ISI ta umurce shi ne kai tsaye, a bayan fage kuma abin da kungiyar leken asirin CIA ta umurce shi.”

Orjin Hatch memba ne na kwamitin da ke kula da tattara bayanan asiri a cikin Majalisar Dattijan Amurka. Kwamitin da ya yi dokar amincewa da a kulla hulda tsakanin gwamnatin Amurka da Mujahidun. Ya fadi cewa: “Idan a nan gaba ta , za mu sake yin irin wannan huldar.” Rahoton MSNBC 28/8/1998.

Maguz, jarumin kagaggen labarin "KARSHEN ALEWA KASA" na Marigayi Bature Gagare bai yi kuskure ba da ya so kwatar wa al’ummarsa ta Maguzawa hakkinsu da ya yi imani ana dannewa. Kukskuren Maguz shi ne yin amfani da haramtacciyar hanya da ta saba wa doka da kyawawan halaye wajen kai wa ga manufarsa. Ya kafa makarantar barayi da koya wa yaran da ya tara dabarun yin sane da fashi da makami da kashe mutum, sannan uwa-uba da hada-hadar wiwi da kuma shan ta. Sannan kuma ya shelanta tawaye ga kasa.

Wadda ta koya wa kungiyar Alka’ada ayyukan barna da ta’addanci, ita ce kasar Amurka a lokacin yakin Soviet. Ita ce kuma za ta yi amfani da su a lokacin 11 ga Satumba domin cimma wata babbar manufar tata a Gabas ta Tsakiya da ma duniya baki daya.

Malam Mujtaba Adam ma’aikaci ne a gidan rediyon Iran da ke Tehran Jamhuriyyar Musuluci ta Iran. Ya aiko mana wannan sakon ne ta hanyar I-mel dinsa (nigeria3000@yahoo.com).

Mun kammala.

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


 Shafin Gamji | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International