Almizan :RANAR KUDUS TA DUNIYA ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 17 Shawwal, 1426                 Bugu na 692                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Rahotanni

RANAR KUDUS TA DUNIYA

Daga Aliyu Saleh

H

A duk ranar Juma’ar karshe ta watan Ramadan ne musulmi a duk inda suke a fadin duniya suke gudanar da jerin gwanon lumana domin nuna goyon bayansu ga Palastinawa raunana, gami da tabbatar da hankoronsu na kwato Masallacin Kudus mai alfarma daga mamayar Yahudawan Sahayoniya, gami da yin Allah wadai da kisan kiyashi da kuma wuce gona irin da haramtacciyar kasa Isra’ila ke yi a duk lokacin da suka bushi iska.

Ita dai wanann rana ta Kudus da ake yin ta a kowace Jum’ar karshe ta watan Ramadan, Marigayi Imam Khumaini (KS), kuma mu’asassin Jamhuriyar Musulunci ta Iran ne ya assasa ta a shekarar 1979 domin nuna juyayi game da halin da Palastinawa da kuma masallacin Kudus mai alfarma suke ciki.

Wannan juyayin da ake yi kamar wani goyon baya ne ga Palastinawa da kuma nuna wa Yahudawa da Yahudanci baka, tare da kuma sanar da su cewa Musulmin duniya fa suna sane da irin hawan kawara ko kuma cin kacar da suke yi wa Musulunci.

Kazalika ana amfani da wannan rana ta Kudus ta duniya, domin tunatar da al’ummar Musulmi sabuwar makidar da Yahudawa suke shirya wa al’ummar musulmi a wannan karnin.

A karni na 20 ne, bayan wata yarjejeniyar ruwan sanyin da ake yi wa lakabi da ‘Sykes-Picot’ da aka cimma tsakanin Birtaniya da Faransa ne akidar Yahudanci ta samu gindin zama a yankin Gabas ta Tsakiya. A lokacin ne kuma aka zabi Palasdinu a matsayin masaukin wannan akidar. Wannan ya faru ne da goyon baya da kuma hadin kan manyan kasashen duniya.

Kamar yadda bayanai suka tabbatar, a 1916 ne gwamnatin mulkin-mallaka ta Birtaniya a Palastinu, tare da hadin bakin Faransa, a sannu a hankali suka goyi bayan kore Palastinawa da kuma gusar da su daga kasarsu ta gado, tare da maye gurbinsu da Yahudawa ’yan mamaya. Suka kuma goyi bayan ta’addancin da kungiyoyin ta’addanci na Yahudawa kamar su; ‘Hagana,’ ‘Stern Gang,’ ‘Irgun,’ da ‘Etsel’ suke yi wa Palastinawa.

A wancan lokacin bai buya ga kowa ba cewa Faransa da Birtaniya bisa rufa bayan Amurka ne suka samar da wadannan kungiyoyin ta’addancin na Yahudawa, tare da samar masu da manya da kananan makaman da suka rika amfani da su wajen kwakkwashe Palastinawa, tare da kwakkwace masu gidaje da shaguna da kuma lalata masu gonaki. Kuma sun rinka daukar nauyin biyan jiragen ruwan da suka rika jigilar Palastinawa daga kasarsu ta haihuwa zuwa wasu kasashen daban na duniya.

A takaice ma dai, in ba don da tallafi da taimakon Faransa, Birtani da Amurka ba, da ’yan ta’addan Yahudawa ba su samu karfin gwiwar yi wa Palastinawa da kuma sauran musulmin duniya ta’addanci, da kuma mamaye masu kasashe ba.

Bayan yakin duniya na biyu, Faransa da Birtaniya sun samu wani karfi da iko gami da karfin halin da ya ba su damar harhada hancin duk Yahudawan da suke warwatse a duniya su sama da miliyan shida domin su kai su yankin Palastinu. Wannan ya faru ne tare da goyon baya da taimakon Amurka, wacce a lokacin take taka rawar mai neman kawo karshen yakin duniya na biyu. A haka dai aka sanar da kafa haramtacciyar kasar Isra’ila a 1948.

Da ma kamar yadda kowa ya sani ne, yana daga cikin manufar masu mulkin mallaka a kasashen musulmi baya ga karya masu tattalin arziki, da kuma yada masu kiristanci da fasadi, akwai burin kada su bari a sake samun wata daular Musulunci shigen ta ‘Ottoman’ wacce ta ruguje a shekarar 1916.

A wancan lokacin, Birtaniya, Faransa da kuma Amurka sun yi yunkurin rushe Masallacin Beit-ul-Moqaddas, wanda shi ne alkiblar farko ta musulmi, Cibiyar da zukatan musulmin duniya sama da biliyan daya da digo hudu suke fuskanta.

Da haka, da haka dai, daga 1948 zuwa 1967, gwamnatin Yahudawan Sahayoniya ta haramtacciyar kasar Isra’ila ta ci gaba da dabarar kammala mamaye Beit-ul-Moqaddas da kuma sauran yankunan Palastinawa. Wannan shiri bai ci nasara ba sai da taimakon Amurka, Birtaniya, Faransa da kuma sauran kasashen Yammacin duniya.

Sai dai kuma abin takaici, duk da wannan kutungwilar da kafircin duniya ya shirya wa musulmi da Musulunci, su sauran al’ummar musulmin duniya ko a jikinsu. Ba su yi wani yunkuri na a-zo-a-gani ba game da dawo da wannan Masallaci na Beit-ul-Moqaddas mai alfarma da wajen da ke kewaye da shi hannunsu ba. Ko yakin da aka yi na kwanaki shida tsakanin Larabawa da haramtacciyar kasar Isra’ila a 1973, ba komai ya jaza ba, sai ma sake bai wa Yahudawa damar sake mamaye karin wuraren da ba su kai ga mamaye su ba tunda farko. Ba a samu wani canji mai kama da kule ga Yahudawan Sahayoniya ba, sai da Marigayi Imam Khumaini ya asassa wannan rana ta Kudus ta duniya a shekarar 1979.

Wani karin abin haushi ma shi ne; yanzu haka gwamnatin haramcciyar kasar Isra’ila, wacce take a tsakiyar kasashen Musulmi ta mallaki kundun harbawa na makamin kare dangi sama da 400, ba kuma wata kasa ko kungiya daga cikin kungiyoyin kasa da kasa da ke fafutikar kayyade makamai da suka isa su daga mata kara. Wannan yana faruwa ne saboda goyon bayan da take da samu daga Amurka, Birtaniya, Faransa da kuma sauran kasashen Yammacin Turai. Amma ita Iran kokarin mallakar makamashin take yi domin samarwa da jama’arta wutar lantarki, amma ana ta kai gwauro da mari don ganin ba ta samu zarafin yin hakan ba.

Wannan rana ta Kudus da Imam Khumaini ya sanar ta zo wa al’ummar Palastinu a kan gaba. Palastinawa tuni suka dawo daga rakiyar sauran kungiyoyin kasashen duniya da ke babatun samar masu da ’yanci da kuma zaman lafiya a yankin nasu ba tare da dawo masu da yankunansu da masu mamaya suka kwace ba, ba tare da kuma tattauna yadda za a daina kai masu hare-hare ba kakkautawa. Tuni Palastinawa suka sakankance a kan cewa ta hanyar gwagwarmaya (Intifada), nuna kin amincewa da mamaya da kuma yin fito-na-fito ne kadai kasarsu da aka kwace masu za ta dawo.

Daga karshe dai dole ne gwamnatin Yahudawa masu ta’addanci ta rube, ta kuma durkushe, tunda ko mulkin Musulunci ba ya dorewa matsawar da zalunci, amma sai na kafirci ya kai labari matsawar da akwai adalci.

MU KAURACE WA KAYAYYAKIN YAHUDAWA

Shawarata a nan ita ce don Allah in har da hali ku rinka buga mana sunayen kayayyakin da ya kamata a ce ba ma amfani da su kamar yadda kuka buga a can baya, kamar su coca-cola da sauransu. Wato kayan da Yahudawa suke yi ko suke da hannu a ciki.

In da son samu ne, da sai in ce duk sati, to ko da a bayan sati biyar ne sai a rika buga mana. Kuma don Allah ’yan uwa mu ba zuciyarmu magana, mu kaurace wa kayan Yahudawa. Domin dukkan Musulmi dan uwan juna ne. Wannan ko mutum ya gane ko bai gane ba. Sannan kuma duk inda kafiri yake yana taimakon dan uwansa ne. To mu ma menene zai sa ba za mu taimaki ’yan uwanmu ba? Don haka nake kira ga dukkan Musulmai da su ji tsoron Allah su rika kauce wa irin wadannan kaya.

Ina rokon Allah (S.W.T.) ya saka wa Malam Zakzaky da alheri ya cika masa gurinsa, ya bar mu a tare da shi har abada, albarkacin Iyalan Gidan Manzon Allah (S).

Daga ’Yar uwarku a Musulunci Amina M. Ahmad Dankwaro, Karamar Hukumar Kafur jihar Kastina

Ina ’yan uwa mata ne?

Assalamu alaikum. Bayan dubun gaisuwa irin ta addinin Musulunci, tare da fatan alheri. Edita, ina rokon samun fili a cikin wannan jarida tamu (ALMIZAN), mai farin jini, mai tsage gaskiya komai dacinta, domin na dan yi tsokaci ko kuma kira ga ’yan uwa mata masu gwagwarmayar tabbatar da addinin Musulunci a Nijeriya karkashin jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H).

Sai dai kafin in yi nisa da bayani, ina son in yi amfani da wannan dama domin mika gaisuwar salla zuwa ga Jagorana, Kwamandan tumbuke kafirci da fitsara, Maulana, Sharafuddeen, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), da fatan Malam (H) da daukacin al’ummar musulmi sun sha ruwa, kuma sun yi salla lafiya. Allah ya maimaita mana, amin.

Bayan haka, zan so yin dan tsokaci ne, musamman ga ’yan uwa mata (Sistas) da suka yi shakulatin bangaro da kulen da ake ta yi masu, na su dinga rubutu da ba da gudummawa a cikin ALMIZAN. Shin ba mu da mata masu hazakar rubutu ne? Ko kuwa suna jin tsoro ne?

Domin nakan ga da zarar wani namiji ya yi rubutun da bai gamsar da su ba, suna ta kokarin mayar da martani ta kasa ta sama, babu kakkautawa. To amma yaya aka yi ba sa kokarin ba da tasu gudummawar, sai dai kokarin mayar da martani? Misali: Ina filin girke-girke? Ina filin tarbiyyar iyali? Ina filin gudummawar mata a al’umma? Ina filin gwarazan mata? Ina? Ina? Ina..?

To, ’yan uwa mata, ba za mu daina korafi, caccaka da zungura ba, har sai mun ga kun amsa wannan kulen da ake muka yi maku. Idan har kuna da rayayyen yunkuri, kaifin basira, wasassar hikima, to muna so mu gani a kasa, wai an ce da kare ana biki a gidansu.

A nan nake cewa sai na ji daga gare ku. Ku huta lafiya.

Daga Muhammad Sani Aliyu Kofar Kaura Katsina GSM;- 0803 594 5001

i-mel: msaliyukatsina@yahoo.com.

Dubun ’yan fashi ta cika a Zamfara

Daga S. Samaru

A cikin makon sherakanjiya ne wasu matasan Fulani kimanin su tara da dattawa guda uku dubunsu ta cika bayan sun fita aikin dare, a yayin da suka aikata fashi da makami, tare kuma fyade a wani kauye da ake kira Marbe cikin Karamar Hukumar Tsafe a jihar Zamfara.

Kama wadannan matasa ya biyo bayan mutum daya da aka kama ne mai suna Abubakar; shi kuma ya tona asirin sauran.

Su dai wadannan matasa ana zargin su da fashin makudan kudade daga wasu maza ne tare kuma da yi wa wasu mata fyade su uku, ciki har da mai juna biyu, wadda a sanadiyyar wannan fyade cikinta ya zube.

Su dai wadannan matasa sun karyata wannan zargi da ’yan sanda suka yi masu. Wasu daga cikin su sun ce Abubakar ne kawai ya ambaci sunansu.

Shi dai Abubakar shi ne aka ce shugabansu, shi kuma ya ce bai san hawa ba balle sauka da asuba zai yi sahur aka kama shi wai sun yi fashi.

Wani daga cikinsu mai suna Sani ya gaya wa manema labarai cewa ita bindigar toka da aka same shi da ita ta Ardo ce da ya ba shi don yana masa kiwon shanu yana ba shi lada.

Shi kuwa Ardo mai kimanin shekaru 60, shi ma ya karyata wannan zargi da ake yi masu. Ya kara da cewa ita bindigar da ake magana ta fi shekara goma a hannunsa yana bai wa yara suna masa kiwon shanu; cikin yaran kuma har da shi Sanin.

Shi kuwa Mataimakin Kwamishinan ’yan sanda na jihar Zamfara, Mark A. Idakwo, a zantawarsa da manema labarai a ofishinsa da ke Gusau, cewa ya yi; suna nan suna bincike, kuma bincikensu ne zai tantance wadanda ba ’yan fashi bane daga cikinsu. Kuma suna nan suna kai gwauro suna kai mari sai sun gano wadanda suka ari takalmin kare suka bai wa hanya kashi daga cikinsu.

Mataimakin Kwamishina, Mark, da aka tambaye shi cewa ba ya ganin wadannan za su iya guduwa kamar yadda ya faru a baya da wasu, sai ya ce, ko alama, “in Allah ya yarda ba zai faru ba. Kuma mun dauki duk matakin da ya dace don kaucewa aukuwar hakan,” in ji shi.

Daga karshe ya mika godiyarsa ga Gwamnatin jihar ta Zamfara da kungiyar ’yan sintiri da al’ummar jihar Zamfara da suke ba su goyon baya.

‘Babu al’ummar da aka zalunta a wannan karni kamar Palasdinawa’

Na’ibin Limamin Juma'a a birnin Tehran, kuma Shugaban Hukumar fayyace maslahar tsarin Musulunci a Iran, Ayatullah Hashemi Rafsanjani ne ya jagoranci al’ummar musulmi sallar Juma’ar da aka gabatar a masallacin Juma'a na Tehran.

A lokacin da yake gabatar da hudubobin sallar Juma’a, Ayatullah Rafsanjani ya fara ne kamar kowanne mako da kiran al’ummar musulmi zuwa ga tsoron Allah, sannan ya shiga bayani kan tarihin shigar Yahudawa ’yan mamaya Palasdinu da kuma irin gurace-guracensu na farko, da yadda a yanzun suka fara samun gangarowa kasa saboda irin dagewar al’ummar Palasdinu wajen fafatawa da su.

Ayatullah Rafsanjani ya nuna cewa haramtacciyar kasar Isra’ila ta kafu ne tare da goyon bayan da kasar Birtaniya ta ba ta a wancan lokacin da kuma rawar da Majalisar Dinkin Duniya ta taka ta wancan lokacin.

Na’ibin Limamin masallacin Juma’ar har ila yau, ya nuna irin yadda Firaministan haramtacciyar kasar Isra’ila, Ariel Sharon ya dauki alwashin ganin bayan gwagwarmayar Palasdinawa ta ‘Intifadha’ cikin watanni uku bayan hawansa kan karagar mulki, amma cikin ikon Allah tare da dagewar da al’ummar Palasdinu suka nuna ga shi wannan gwagwarmaya ta kwashe shekaru ana yi.

Na’ibin Limamin, har ila yau ya nuna irin yadda a yanzun gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke ta gangarowa kasa, sannan kuma gwagwarmayar al’ummar musulmi a ciki da wajen Palasdinu sai kara ci gaba take yi. Sannan ya bayyana cewa wannan yana kara karfin gwiwa ne ga musulmi cewa lalle nasara tana kusa.

A wani bangare na hudubar tasa, Ayatullahi Rafsanjani ya yi magana ne a kan hakkin Iran na mallakar makamashin nukiliya da kuma taya murna ga al’ummar kasar Iraki kan ci gaba da samun tabbatar da zaman lafiya da samar da gwamnati ta al’umma a kasar. An tuna da cikar shekaru 41 da korar Imam Khumaini (RA) zuwa gudun hijira

Kimanin shekaru 41 da suka gabata, a ranar 4 ga watan Nuwamban shekara ta 1964 jami’an tsaron Sarki Shah na Iran da aka hambarar suka tafi birnin Kum, inda Marigayi Imam Khumaini (RA) ke zaune suka kama shi sannan suka fitar da shi daga kasar zuwa gudun hijirar farko kasar Turkiyya.

Tun cikin daren ranar 4 ga watan na Nuwamba ne dai jami’an tsaron na hambararren Sarkin kasar, Shah, suka tafi gidan Marigayi Imam da ke can birnin Kum, inda suka kama shi sannan suka nufi filin jirgin saman Mehrabad da ke Tehran da shi sannan suka saka shi a jirgi suka kore shi daga kasar.

Sarki Shah hambararren Sarkin na Iran ya tsorata ne kwarai da gaske kan yadda kiran Marigayi Imam Khumaini (RA) ya rika samun karbuwa a wancan lokacin tsakanin dukkanin bangarori na al’ummar kasar, saboda haka nan sai ya fara ganin babbar barazana ne kiran Imam zai kasance gare shi.

Babban abin da ya fi tayar wa Shah hankali a wancan lokacin shi ne irin yadda Marigayi Imam Khumaini ya yi wa shirinsa na kwaskwarimar mallakar filaye (Land Reforms) kule, don haka ya firgita ya ga cewa in dai yana son shirin ya tabbata, to dole ne sai Imam Khumaini ba ya kasar, kamar yadda yake zato.

Imam Khumaini a wannan shekara ya mai da babban ranar idi ta kasa da ake kira da 'noruz' a matsayin ranar juyayi, saboda juyayin irin yadda Shah ya mayar da kasar zuwa ga dogaro da kasashen waje.

An gudanar da manya-manyan gangamomi a dukkanin manyan biranen kasar saboda tunawa da wannan muhimmiyar rana ta tarihi a kasar Iran.

Sayyid Khamna’i ya mai da martani

Kan hayaniyar jawabin Ahmadinajad

Jagoran juyin-juya-halin Musulunci a Iran, Ayatullahil Uzma Sayyid Ali Khamna’i ya mai da martani kan irin yadda kasashen Yamma da haramtacciyar kasar Isra’ila suka rika yawaita hayaniya kan jawabin Shugaban kasar Iran Dakta Ahmadinajad.

Ayatullah Khamena’i ya bayyana cewa kimanin shekaru 10 da suka gabata ma Shugaban kasar wancan lokaci na Iran, ya yi magana kan kashe Ishaq Rabin, tsohon Firaministan haramtacciyar kasar Isra’ila, inda shi ma ya janyo mummunar hayaniya daga bangaren Yahudawa da kuma dukkanin kasashen da ke tare da su na wancan lokacin.

Sayyid Ali Khamna’i ya bayyana takaicinsa da rashin jin dadinsa kan yadda wasu kasashe suke tsananin tasirantuwa da zaluncin Yahudawan Sahayoniya a duniya.

A wani bangare na jawabin nasa, Ayatullah Khamena’i ya bayyana irin yadda Amurka da wasu daga cikin kafafen yada labarai suke kokarin alakantar da wannan jawabi na Ahmadinajad da lamarin mallakar makashin nukiliya na Iran. Sannan ya nuna cewa ai ba karfin nukiliya ne yake kifar da wata gwamnati ba, abin da yake kawar da mabarnata shi ne yunkuri na al’umma.

Haka nan kuma Jagoran ya jaddada cewa lalle yadda Palasdinawa suke fafatawa da Yahudawan Sahayoniya, karshen lamarin zai kai su ga nasara.

Jagoran ya yi wannan jawabi nasa ne a lokacin da yake ganawa da wasu jami’ai da ma’aikatan gwamnati wadanda suka ziyarce shi a gidansa.

An sake samun rikici da jami’an tsaro a Rasha

A safiyar ranar Talatar makon shekaranjiya ne wani sabon rikici ya sake barkewa tsakanin bangarorin wasu mutane da jami’an tsaro a garin Nalchik da ke kudancin kasar Rasha,

Shi dai wannan rikicin ya zo ne mako guda bayan wata gwabzawar da aka yi a wani rikicin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da 100.

Gwamnatin Rasha ta bayyana cewa ta tabbatar da cewa wadanda suka ta da wannan fitina suna da alaka da kungiyar ’yan a-ware na Chechenya.

Jami’an tsaro sun ba da sanarwar cewa jama’a su ci gaba da zama a gidajensu, sannan kuma an umurci iyaye da su kwaso ’ya’yansu ’yan makaranta daga makaranta zuwa gida.

Sai dai mutanen kasar na gani cewa harin da jami’an tsaro ke kai wa ya fi daukar rayukan ’yan kasa wadanda ba su ji ba ba su gani ba fiye abin da suke cewa ’yan tawayen na yi.

Haka nan kuma a halin da ake ciki yanzu fadan ya fara watsuwa zuwa wasu sassa na baki dayan kasar Rashan.

Ranar 13 ga watan 'Aban' ne aka tona asirin Amurka a Iran

A daidai ranar 13 ga watan ‘Aban’ shekara ta 1358 hijira shamsiyya daidai da 4 ga watan Nuwamba shekara ta 1979 wato watanni bakwai bayan cin nasarar juyin Musulunci a kasar aka mamaye ofishin jakadancin Amurka da ke kasar Iran.

’Yan watanni bayan cin nasarar juyin Musulunci a Iran, bayan kafa gwamnatin rikon kwarya ta Mahdi Bazargan, Amurka a lokacin shugabancin Jimmy Carter, ta yi amfani da wasu munafukai a cikin Iran wajen yunkurin kifar da sabuwar gwamnatin ta Musulunci, saboda haka ya zama ofishin jakadancin Amurka a Tehran tamkar wani sansani na shiryawa da kuma aiwatar da makirce-makircen ta da fitinu a Iran.

Ana cikin haka ne wasu dalibai na Jami’a wadanda suka kira kansu dalibai masu goyon bayan tafarkin Imam Khumaini (RA) suka shirya, kuma suka aiwatar da mamayar ofishin jakadancin, tare da kame jami’an ofishin har na tsawon fiye da shekara daya.

A wannan lokacin ne aka ci karo da dimbin takardu na asiri na irin yadda Amurka take aiwatar da ta da fitinu a kasar da kuma wasu kayyakin aiki masu karfi wajen sadarwa ta yadda suna iya daukowa da kuma aika dukkanin maganganun jami’an Iran.

Wannan ya kara gaskata irin abin da dadewa ake hasashe na cewa ofishin wata sheka ce kawai ta leken asirin kasar Amurka a Iran.

Marigayi Imam Khumaini (RA) ya yabi wannan yunkuri na daliban, har ma ya kira shi “juyin-juya-hali na biyu wanda ya fi na farko.”

Ta’addancin Yahudawa ya kai ga shahadar mutane biyu a Gazza

A ci gaba da ta’addancin Yahudawa a yankin Gazza, a ranar Talatar makon shekaranjiya ne, sojojin Yahudawan haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai wani hari a arewacin Gazza, wanda ya yi sanadiyyar shahadar wasu manyan jami’an masu fafatawa da Yahudawa guda biyu.

A wani hari na makamai masu linzami da sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai ne a kan motar ‘Jeep’ da ke dauke da jami’an a sansanin ’yan gudun hijira a Jabaliya ya kai ga shahadar mutane biyun.

Rahoton tashar talabijin na BBC, ya bayyana cewa; wasu mutane biyar ma sun jikkata a lokacin da aka kai harin.

Wannan dai shi ne karo na biyu da sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai hari kan yankin na Gazza a cikin wannan makon.

Hasan Madhun, wani jami’i na kungiyar Aqsa Brigade, wanda dama jami’an haramtacciyar kasar Isra'ila ke nema suna tuhumar sa da shirya kai masu hari yana cikin wadanda suka yi shahada a harin.

Fiye da shekaru 50 da suka gabata dai Yahudawan Sahayoniya suka mamayi Palasdinu, tare da taimakon gwamnatin Britaniya ta wancan lokacin.

Ayatullah Khamena’i ya gana da shahidai masu rai

Jagoran juyin-juya-hali na Musulunci a Iran, Ayatullahi Sayyid Ali Khamena’i ya yi wata ganawa ta musamman da Shahidai masu rai, tare da iyalansu wadanda suka sami raunuka a lokacin yakin kare kasa, yayin da suka kawo masa ziyara a gidansa.

Su dai wadannan Shahidan masu rai da suka gana da Sayyid Khamena’i suna cikin wadanda rauninsu ya kai kashi 70 cikin 100 na kimar da ake yi wa wadanda suka ji rauni a lokacin yakin.

Da ma dai a kasar Iran shahidai masu rai suna da darajoji daban-daban ne, akwai wadanda ake cewa kashi 10 cikin 100, akwai kuma wadanda suka fi haka, kowanne gwargwadon yadda raunin da ya ji ya lalata jikinsa ake ajiye shi.

A lokacin da yake gabatar da jawabi a lokacin ziyarar, Sayyid Ali Khamena’i ya bayyana cewa yana daga cikin manufofin tsarin mulkin Iran kariya da kuma taimaka wa Shahidai masu rai, kuma zai ci gaba da zama a haka har abada.

Ayatullah Khamena’i ya kara da cewa; Shahidai masu rai suna da wata falala wadda Shahidan da aka kashe ba su da shi, wannan kuwa shi ne su suna raye a wannan duniya, saboda haka in har suka ci gaba da hakuri da dauriya a kan bautar Allah, a kowane lokaci ana ci gaba da kara masu lada da daukakan daraja ne.

Da yake magana game da yadda iyalai, musamman ma matan Shahidai masu rai suke tarayya da masoyansu cikin dukkanin wahalhalun da suke ciki, Ayatullah Khamena’i, ya nuna cewa tabbas su iyalan za su yi tarayya da su cikin lada.

Saboda rabon kudi: Hayaniya ta kaure a masallaci

Daga Al-Husain Dakace

Kamar yadda aka sani, idan aka ce an samu kudi don rabawa ake samun hayaniya, musamman idan ba a yi a hankali ba. Irin wannan hayaniya da ta kaure ta baya-bayan nan saboda rabon kudi ita ce na wanda Hajiya Mariya Sunusi Dantata, Mahaifiyar Aliko Dangote, ta kawo kudi masu yawan gaske don rabawa a lokacin da aka idar da sallar kiyamullaili da aka saba gudanarwa a masallacin Juma’ar da ke Kofar gidanta a unguwar Koki cikin birnin Kano.

Wakilimu, wanda ya gudanar da i’itikafi a masallacin, ya ga yadda da farko an bi sahu ana bai wa kowa N2000 ba tare da hayaniya ba, ya zuwa wani lokaci sai hayaniya ta kaure a ciki da wajen masallacin. Ala tilas aka dakatar da rabon kudin duk da cewa Limamin masallacin, Malam Ali ya sanar wa jama’a cewa kowa ya tsaya cikin sahu, don kuwa kowa zai samu. Amma duk da haka rabon kudin ya gagara.

Ganin haka masu rabon kudin sun tunkari sashen matan da suka zo masallacin don tahajjud. Ai nan ma abin gagara ya yi. Karshe dai ana ji ana gani rabon kudin ya faskara daga wajen matan har mazan. Haka aka mayar da kudin kowa na gani.

Har ila yau ALMIZAN ta ga yadda mafi yawan jama’ar da suka halarci tahajjudin na karshe, maza da mata dauke da goyo da tsofaffin mata da maza da matasa, sun ki tafiya gidajensu, bisa zaton ko watakila masu rabon kudin su sake shawara su sake dawowa bayan sallar subahi.

ALMIZAN ta ga matan da su aka yi sallar ta asuba, sun ki tafiya gida, amma daga karshe haka suka koma hannu-rabbana. Amma a wani bincike da ALMIZAN ta gudanar kan rashin komawar matan gidajensu, duk da kasancewar ba su sami kudin tun farko ba, ta gano cewa don tsoron bata gari kar su far musu ne, amma wani abin ban mamaki shi ne wasu matan har wajen karfe 7:00 na safe suna nan suna jiran tsammani.

ALMIZAN ta zanta da wani bawan Allah da shi ma ya gudanar da I’itikafi a masallacin, inda shi ma ya sami nasa kason na N2,000 mai suna Alhaji Sani. Ya ce, hakika Hajiya Mariya ta cancanci yabo, “domin,” a cewarsa, “tunda aka fara I’itikafi a masallacin ta rinka auno dafaffen abinci kyauta domin ’yan i’itikafin.” Sai ya shawarce ta cewa, nan gaba idan za ta yi irin wannan bayar da sadaka na kudi, “to ya kamata a yi shi cikin tsari, ta yadda al’umma za su amfana.”

ALMIZAN ta ga yadda masu gudanar da i’itikafin na bana a cikin masallacin suka gudanar da nau’in ibadojinsu kala-kala ba tare da wata tsangwama ba tun daga kan jami’an masallacin har ya zuwa ’yan uwansu masu i’itikafi. An kuma gudanar da shi lafiya, an tashi lafiya.

GINA SHAKSIYYAR ’YAR UWA MUSULMA (2)

Ci gaba daga makon jiya.

Mace musulma ta kasance tana sa hijabi yadda Allah Ya siffata shi daga wadanda bai kamata su gan ta ba. Dokar Allah ce a kan dukkan mata sai dai ga mazajensu ko iyayen mazajensu, ko ’yan uwansu maza, ko ’ya’ya maza na ’yan uwansu, ko ’yan uwansu mata ko wadanda hannayensu suka mallaka, ko kuma yara kanana wadanda ba su san al’aurar mata ba.

To sai ku lura a nan irin su yayyin miji, ko kannensa ba ya halatta, kuma haramun ne su gan ta ba hijabi, kamar yadda mata suke bayyana adonsu ga wasu mazaje, lalle bai halatta ba. Don wannan zai sa su gamu da fushin Allah, kuma ya kai su zuwa ga halaka.

Kuma shi hijabi dole ya cika wasu siffofi irin kamar su tsayi da yalwa, ya kasance ba shara-shara ko kuma mai ado ba. Kamar yadda wasu suka dauka cewa lullubi hijabi ne, to ba haka bane, lullubi ba hijabi bane, kuma a kula da wadanda ake ce musu yara, wasu samari ne, wasu kuma yara ne, amma sun san komai. Ire-iren wadannan ba za a yi sakaci da hijabi a gabansu ba. Idan mace tana tunanin zafi ko takurar hijabi, to wutar jahannama ta fi zafi.

Mace musulma a kan kanta ya zama wajibi ta kula da kanta ta san irin abincin da za ta ci ta sha. Ta kula da motsa jiki sannan ta zama mai tsafta. Dole ta yi wanka akalla sau daya a rana, kuma ta kula da gashinta, ta yi kitso akalla sau daya a sati biyu, ta wanke gashin kanta sau biyu a wata. Ta yi ado ta yi kwalliya tunda za ta rufe da hijabi ta sa turare mara kamshi irin su ‘sure’ a hammata. Ta kula da wanke hakoranta akalla sau biyu a rana, safe da yamma, ta sa kaya masu kyau da saukin kudi.

MACE MUSULMA DA IYAYENTA

Wajibi ne ta yi wa iyayenta biyayya (ta karshe), ta san cewa Allah ne ya dora mata yi musu da’a matukar ba su saba ba. Biyayya ga iyaye, musamman uwa, kamar yadda Manzo ya nanata har sau uku, sannan uba. Don ita ta sha wahala ta dauki ciki wata tara, ta yi nakuda ta haihu, ta shayar, ta yi reno har aka girma. To har ma bayan an rabu da su iyaye lafiya an je gidan miji dole ne a ci gaba da tunawa da su da kyautata musu kamar kai musu kyauta da hidima ta jiki idan an yi ziyara, da kuma yi musu addu’a, da yi musu sadaka, a roki Allah ya raba su da duniya lafiya, ya shigar da su Aljannar Firdausi kusa da Manzon Allah (S).

MACE MUSULMA TARE DA MIJINTA

Allah na cewa; “kuma akwai daga ayoyinSa ya halitta muku matan aure daga kanku domin ku natsu gare ta, kuma Ya sanya soyayya da rahama a tsakaninku. Lalle a cikin wancan akwai ayoyi ga mutane masu yin tunani.” Rum: 21.

Saboda haka idan muka duba za mu ga cewa aure mukaddari ne daga Allah, kuma babu ginin da ya fi soyuwa ga Allah kamar sa. Shi ya sa babu halal din da idan aka aikata shi Allah ba ya so kamar saki. Manzon Allah ya ce ana auren mace saboda dalilai hudu: Kyanta, addininta, dukiyarta da matsayin iyayenta. Sai ya ce na hore ku da aure saboda addini. Duk wanda ya yi aure don kyau, to matar za ta tsufa, kyan ya tafi, idan kuma don kudinta ne, zai kare, idan kuma don matsayin iyayenta ne, za a rasa matsayin. Amma shi addini ba zai gushe ba sai dai karuwa da imani. Kuma idan niyyar mutum don addini ne to zai samu duk wadannan tare da ita. Amma Manzo (S) ya ce wanda ya yi ba saboda addini ba, hannayensa su shafi kasa. Wato ba zai samu abin da yake so ba.

Manzon Allah ya ce; “duk wanda yake son ya riski Allah da tsarki abin tsarkakewa, to ya mutu da aure.” Manzo ya ce; “aure sunnata ce, duk wanda ya ki sunnata, to ba ya tare da ni.”

Duk namijin da ya yi aure, Shaidan zai dinga kururuwa yana cewa; ya kaiconsa! Wannan mutum ya kare kansa daga daya bisa uku daga gare shi. To Manzon (S) ya ce ya ji tsoron Allah a sauran kashin.

Manzon Allah (S) ya ce, mutum ya yi aure ya cika rabin addininsa, to ya ji tsoron Allah a sauran rabin. Mai aure yana barci ya fi mara aure mai salla.

Imam Sadik (AS) ya ce, raka’a biyu da mai aure ya yi ta fi raka’a 70 ta mara aure. Kuma ya ce mutane uku ranar kiyama za su shiga cikin inuwar Allah, ranar da ba wata inuwa sai ita. Wanda ya hada da mutumin da ya auri musulma ya yi mata hidima, kuma ya boye sirrinta.

Wanda ya fi kowa hakki a kan mace kuwa shi ne mijinta. Namiji kuma Mahaifiyarsa. Bone ya tabbata ga duk macen da take fusata mijinta, kuma madalla da macen da take yardadjiya a wurin mijinta. Manzon Allah (S) ya jaddada bukatar kiyaye hakkokin juna sosai a tsakanin ma’aura.

Hakkin mace a kan mijinta shi ne ya tufatar da ita, ya ciyar da ita, ya ba ta wurin zama, kuma kada ya sake ta sai dai idan alfasha ta bayyana. Magana da miji zai ce wa matarsa ina son ki ba za ta bar zuciyarta ba har abada.

Game da hidimar mace ga mijinta kuwa, Manzon Allah (S) ya ce, duk matar da ta yi wa mijinta hidima tsawon kwanaki bakwai, Allah Zai rufe mata kofofin wuta ya bude mata na Aljanna guda takwas ta shiga ta duk wadda ta so.

Manzon Allah (S) ya ce mafificinku shi ne wanda ya fi kyautata wa iyalensa. Ya ce “nine mafificinku.” A gidansa yakan yi shara, ya yi wanki, ya yi wanke-wanke, ya yi dinki, kuma wannan ya daukaka darajarsa ne. Duk mijin da ya yi hakuri a kan cutarwar matarsa, Allah zai ba shi ga kowane yini da daren da ya yi hakuri, lada kamar irin ladan da ya bai wa Annabi Ayuba (AS).

Duk macen da ta yi hakuri a kan cutarwar mijinta, Allah zai ba ta lada na Hasiya matar Fir’auna. Babu kyautar da mumini zai samu a duniya da ta wuce mace saliha.

Za mu ci gaba insha Allah.

Lalacewar al’ummar nan ya yi tsanani
In ji Malam AbdulRahman Abubakar Yola

Daga Isa Al-Musawi Gombi (musawiy@yahoo.com)

“Lalacewar wannan al’umma ya dace da lokacin Jahiliyya, kafin bayyanar Manzo (S).” Wanda ya bayyana hakan kuwa shi ne Malam AbdulRahman Abubakar Yola a yayin da yake gabatar da jawabi a masallacin GMMC (Ramat) Yola wurin taron (IVC) karo na uku da kungiyar Dalibai Musulmi ta Kasa (MSSN) shiyyar jihar Adamawa ta shirya a kwanakin baya.

Malam AbdulRahm Yola, ya haska wa mahalarta wannan taro yadda rayuwar al’umma ta kasance kafin aiko da Manzo (S), yadda al’umma take rayuwa, inda har ta kai ga yin yaki na kimanin shekara 40 a kan rakumi guda, duk da cewa a tsakanin wadannan gidajen biyu da suke rikici da juna akwai auratayya a tsakaninsu. “Kuma Larabawa a lokacin har binne ’ya’ya mata suke yi da rai saboda rashin tsari da kuma rashin dabi’u na gari.”

Ya ce, amma saboda rahama ta Allah (S) sai ya turo wa wannan al’umma Manzo, saboda ya tsamar da ita daga halakar (wuta) da take shirin fadawa.

Malam AbdulRahman Yola, ya bayyana irin kyawawan halayen da Manzon Allah (S) ya nuna wa daukacin mutanen garin Makka da kewaye. “Shi ne wanda saboda kyawun dabi’unsa, Allah yake cewa al’umma; ‘hakika kuna da abin koyi daga rayuwar Manzo (s).”

Ya ce, Manzo Muhammad (S) bai bar duniya ba sai da ya sauya rayuwar al’umma, ya nuna mata hanyar da za ta kyautata halayyarta. “Amma yanzu in muka dubi yadda wannan al’umma ta lalace har ta kai in za a yi tallar abin sayarwa sai a nuna wata mace tana tallar abin. Misalin tana tallar taya, ko fenti, kuma wannan matar takan kasance ne tsirara.”

Malam AbdulRahman Yola, ya kara da cewa; wannan al’umma ta kasance da yawa daga cikinta suna karatun boko, wanda wadannan makarantun boko, Bature da ya zo ya kafa su yana nufin ya yaye horarrun matasan kiristoci ne, wadanda kuma wannan dalilin ne ya sa wasu daga cikin ’yan boko suke kasancewa masu girman kai da kuma son kai. Har ila yau kuma wadannan munanan dabi’un sune ummul haba’isin bijire wa dokokin Allah.”

Malamin, ya yi mamakin yadda kiri da muzu hukumomin makarantu suke hana wa mata dalibai masu karatun aikin likita sanya hijabi, amma a daya bangaren kuma a lokacin aikin fida a asibiti sai an sanya tufafin da zai rufe dukkan jiki kafin tiyata. “Abin da wannan yake nunawa shi ne za a kafirce wa Allah wurin bin son rai,” ya ce.

“Mafita ga wannan al’ummar shi ne na farko ta bi umurni da kyakkyawan aiki da kuma hani da mummunan aiki, da kuma samar da ilimin tafiyar da al’amuran soja da siyasa da tattalin arziki da kuma kyakkyawar mu’amala irin ta Musulunci.”

Malam AbdulRahman ya ce yin hakan ne zai taimaka wurin samar da Hukuma Musulma, “shi ne kuma mafita gare mu. Watakila wani ya yi tunanin cewa hakan ba zai yiwu ba. To sai mu ce akwai abin da ya fi karfin Allah? Amsa ita ce; babu.”

ALMIZAN ta tuntubi Malam AbdulRahman Yola din don jin ko me zai ce game da shekaru 50 da kafa MSS? Sai ya bayyana cewa: “MSS ta yi rawar gani a shekaru 50 da kafawa.”

Malam AbdulRahman Yola, ya ci gaba da bayyana cewa; “ai Harka Islamiyya da ke karkashin jagorancin Malam Ibraheem Zakzaky ta fito ne daga MSS, ka ga wannan ma ai ci gaba ne ga ita MSS din. Kuma yana daga cikin kokarin da MSS ta yi a farkon shekarun kafa ta shi ne na ganin an kwato wa dalibai musulmi ’yancinsu.”

An koka da kisan da jami’an tsaro ke yi a yankin Neja-Delta

Kungiyar kare hakkin bil Adama ta ‘Amnesty International’ ta ce a kokarinsu na kare cibiyoyin mai, dakarun tsaron Nijeriya suna yawaita kashe fararen hula wadanda ba su dauke da makamai.

Kungiyar ta ‘Amnesty’ ta fadi haka ne a cikin wani rahoton da ta bayar a ranar Alhamis din makon jiya cewa; an kyale dakarun tsaro a yankin suna kashe mutane, tare da lalata kauyuka da tsangayoyi ba tare da tunani ba.

Kungiyar ta yi kira ga gwamnatin Nijeriya da ta kafa wata Hukuma mai zaman kanta domin ta binciki wannan cin zarafi. Har ila yau ta ce su ma kamfanonin mai na kasashen waje da ke aiki a yankin suna da nasu alhakin na keta hakkin jama'a da ake yi, “kuma ya kamata su dauki matakan inganta wannan lamari,” in ji ta.

Rahoton ya yi magana, musamman a kan wani lamarin da ya faru, inda jami’an tsaro suka kashe mutane 17 lokacin da suka kai farmaki kan wani kauye mai suna Odioma a watan Fabrairun da ya gabata. Ta ce dakarun tsaron suna farautar wasu ’yan daba ne da ke dauke da makamai, amma kuma babu ko dayansu da aka kama a lokacin.

Martabar Amurka za ta zube kasa warwas
Idan ta azabtar da fursunonin da ta kama

In Ji Sanata John McCain

Wani sanannen dan jam’iyyar REPUBLICAN a Majalisar Dattijan Amurka, ya ce martabar Amurka za ta zube kasa warwas a idanun duniya idan har ta fara azabtar da mutanen da ta kama take tsare da su.

A lokacin da yake magana cikin wata hira da gidan talabijin na CBS, Sanata John McCain, ya ce mutuncin Amurka ya zube a duniya bayan da aka fallasa irin cin zarafin da ake yi wa fursunoni a gidan kurkukun Abu Ghraib. Ya kara da cewa tilas ne Amurka ta tabbatar da cewa ba ta azabtar da mutane ba.

Sanata McCain shi ne marubucin kudurin dokar da za ta haramta wa Amurka azabtar da fursunonin da ta kama, kudurin da Majalisar Dattijai ta amince da shi da gagarumin rinjaye a watan da ya shige.

Fadar ‘White House’ ta yi barazanar hawa kan kujerar na-ki a game da wannan kudurin doka, amma kuma mai bayar da shawara a kan harkokin tsaron kasa, Stephen Hadley, ya fada a ranar Lahadi cewa gwamnatin Bush tana aiki tare da Sanatoci domin gyara kalmomin dokar ta yadda za ta biya bukatun Sanatocin, tare da kare Amurka daga hare-haren ta’addanci.

A mako guda da ya shige ne a kasar Panama, Shugaban Amurka, Bush ya yi ikirarin cewa Amurka ba ta azabtar da mutane.

Sama da mutane 57 aka kashe a harin da aka kai Jordan

’Yan harin kunar bakin wake sun kashe mutane akalla 57 a kasar Jordan, suka raunata wasu fiye da 100 lokacin da suka kai hare-hare kan wasu otal-otal uku a birnin Amman. Wadannan hare-hare sun auku ne kusan lokaci guda da misalin karfe 9:00 na daren Laraba agogon birnin Amman.

An kai wadannan hare-haren ne a otal din ‘Hyatt’ da ‘Radisson’ da kuma ‘Days Inn.’ Masu magana da yawun ’yan sanda sun ce hare-haren bom din na kunar bakin wake ne. Majiyoyin tsaro sun ce hare-haren sun yi kama da irin na Kungiyar Alka’ida.

Mukaddashin Firaministan Jordan, ya fada wa gidan talabijin na CNN cewa; da alamun biyu daga cikin ’yan harin bam din suna sanye da rigunan kunar bakin wake da aka cika da bama-bamai, yayin da na ukunsu kuma ya tuka mota shake da bama-bamai.

Rahotanni daga birnin Amman sun ce, akasarin barnar da aka gani a cikin otal-otal din ne ba wai a wajensu ko kofofinsu ba. ’Yan kasashen Yammacin duniya suna yawaita zuwa ko zama a wadannan otal-otal, amma hukumomin Jordan sun ce akasarin wadanda suka mutu Jordaniyawa ne.

Bam din da aka dasa a otal din Radisson ya tashi ne a tsakiyar wani dakin taro a daidai lokacin da ake gudanar da wani bukin aure a ciki.

Sarki Abdullahi na Jordan ya ce, wadannan ayyukan ta’addanci ne da aka kai kan fararen hular da ba su san fari ba, balle baki. Sarkin ya katse ziyarar da yake yi a kasar Kazakhstan ya doshi gida a bayan hare-haren.

A bayan fashe-fashen, ’yan sanda da sojojin Jordan sun killace unguwannin da ke kewaye da wadannan otal-otal din. Otal din Grand Hyatt da na Radisson suna wata unguwa ne da ake kira Jabal Amman, inda akwai manya-manyan otal-otal da kuma ofisoshin jakadancin kasashe da dama. Otal din Days Inn yana unguwar Rabiyah a kusa da ofishin jakadancin Isra’ila.

Wani rahoton da aka samu daga kamfanin dillancin labarai na Faransa ya ce Jordan ta rufe bakin iyakokinta na kasa har sai illa masha Allahu.

Wannan shi ne hari mafi muni da aka kai a kasar Jordan cikin ’yan shekarun nan. A cikin shekaru biyar da suka shige, hukumomin Jordan sun ce sun tono kungiyoyin ta’addanci da yawa da kuma makarkashiyar kai hare-hare na ta’addanci. A cikin watan Oktoba, wani harin roka da aka kai a tashar jiragen ruwan Aqaba da ke bakin Bahar Maliya ya yi kusan samun wasu jiragen ruwan yaki guda biyu na Amurka da ke tsaye a can. Daya daga cikin rokokin da aka harba ya fada kan wani dakin ajiye kayayyaki na soja da ke kusa da nan, inda ya kashe sojan kasar Jordan daya.

Jordan tana daya daga cikin manyan kawayen Amurka a Gabas ta Tsakiya. Ta zamo babbar hanyar da ma’aikatan kasashen waje ke bi domin shiga Iraki.

Iyalan Saddam Husain da dama da jami’an gwamnatinsa sun koma kasar Jordan da zama tun bayan da Amurka ta tumbuke gwamnatinsa a 2003. Wasu attajiran na Iraki ma sun gudu sun koma can domin tserewa tashin hankalin da ake yi a kasarsu.

Tuni dai Kungiyar Alka’ida a Iraki karkashin jagorancin Bajordane, Abu Musa’ab Al-Zarkawi ta ba da sanarwar daukar alhakin wannan harin da aka kai, ta ce wannan wani sharar fage ne kan wani gagarumin harin da ke tafe.

’Yan sintirin Kaduna sun yi kira ga gwamnati

Daga Wakilinmu

Kungiyar ’yan sintiri ta kasa reshen jihar Kaduna ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta taimaka mata domin ta sami damar gabatar da ayyukanta yadda suka kamata.

Shugaban Kungiyar na jihar Kaduna, Alhaji Ibrahim Muhammad Bakin Dogo ne ya yi wannan rako bayan kammala wani taro da suka gabatar a ofishinsu a Kaduna.

Shi kuwa Sakataren Kungiyar na kasa, Elder John Ibakwe kira ya yi ga mambobin kungiyar kan su hada kansu kuma su kasance masu da’a domin samun ci gaban aikinsu.

Elder John ya ce, ya kamata ’yan sintiri su kasance masu hakuri da juna tare da yin tunani a duk ayyukan da suke gabatarwa.

Tun farko a nasa jawabin, babban Sakataren kungiyar na jihar Kaduna, Malam Muhammad Bala, kokon baransu ya mika ga gwamnatin jihar Kaduna da ta taimaka masu da kayan aiki irin su na’urorin sadarwa, motocin faturo, sannan kuma a sanya ’yan sintiri cikin kwamitocin tsoro na jiihar.

An dai sanya watan Disambar badi a matsayin watan da za a yi taro na gaba a Makarfi.

Binciken jiragen sama ba ma shakka
- Alhaji Ahmadu Chanchangi

Daga Musa Muhammad Awwal

Tun bayan da aka yi hadari jirgin nan na ‘Bellview’ ne Majalisar Dattijai ta Tarayya ta kafa wani kwamiti wanda zai yi bincike mai zurfi a kan jiragen da ke yawo a sararin samaniyar kasar nan, musamman mallakin ’yan kasa.

Shugaban kamfanin jiragen sama na Chanchangi Airlines, Alhaji Ahmadu Chanchangi ya bayyana cewa suna maraba da wannan mataki, kuma kamfaninsa a shirye yake, ba ya shakka, domin shi ya san lafiyar jiragensa.

Alhaji Ahmadu Chanchangi ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan rufe tafsirin watan Ramadan na masallacin da ke gidansa.

Ba ka daukar kudi kawai ka je ka sayi jirgin sama, sai Hukuma su sa masu ilimi, Injiniyoyi, su je su duba yana da lafiya, ko ba shi da lafiya? Shekararsa nawa? Ina aka yi aiki da shi? Duk yin wannan wani abu ne mai tarihi,” in ji Alhaji Ahmadu Chanchangi.

Shugaban ya kara da cewa; haka kuma in mutum ya sayi jirgi, to dole ne ya rinka kulawa da gyara don tsare lafiyarsa. Ya ce in ba a kulawa da gyara dole ne irin wannan abu ya faru.”

Alhaji Chanchangi ya kuma bayyana cewa ba jiragen kadai ba, hatta su kansu masu aikan jiragen sai ana kulawa da lafiyarsu. “A kowane wata shida za a duba kwakwalwarsa. Ka ga kenan a kowace shekara ana buda shi sau biyu,” in ji shi.

Ya ce, “haka kuma baya ga duba lafiyarsa, dole ne matukin jiragin saman ya lizimci zuwa karo ilimi a kai-a kai don kara kwarewa a aikinsa.” Ya ce a shekara direbobin jiragen sama suna zuwa karo ilimi sau hudu ne. In jirgi zai fadi, ya za ka yi? Ina za ka taba? Amma in ka daina zuwa kwas din, shi kenan ba za ka tuka jirgin ba kenan,” in ji shi.

Don haka sai Alhaji Ahmadu Chanchangi ya ce, shi in dai binciken jirage ne ba ya shakka, “ba ma tsoron komai. Ba ma tsoron sa, muna tsoron Allah don azabarsa, muna tsoron Allah, kuma muna kaunar rahamarsa,” ya jadadda.

Daga nan sai ya mika ta’aziyyarsa ga wadanda suka rasu a wannan hadarin na Bellview.’

Tun da farko a jawabinsa wajen rufe tafsirin masallacin nasa, Alhaji Ahmadu Chanchangi ya fara ne da yi wa Allah godiya da ya yi mu a cikin addinin Musulunci, ya ce, wannan ba karamar falala da baiwa bace ta Allah (T); “duk wanda ya sami kansa cikin Musulunci, to ya gode wa Allah,” in ji shi.

Daga nan kuma sai ya bayanin cewa falalar Alkur’ani tana da amfani matuka ga rayuwar musulmi, don haka sai ya yi jinjina ta musamman ga Malamai masu tafsirin.

A karshe, Attajirin ya yi kira da babbar murya ga musulmi da su hada kansu su zama al’umma daya. A cewarsa, “hadin kai wani abu ne wanda yake wajibi ga musulmi.”

Jama’atu ta yi taron salla a Kaduna

Daga Wakilinmu

Kungiyar Jama’atu Nasril Islam ta reshen jihar Kaduna ta gabatar da wani kwarya-kwaryan taron cin abinci don murna da yin karamar salla bayan kammala azumin watan Ramadan.

Taron, wanda ya kunshi musulmi da kiristoci an gabatar da shi ne a dakin taro na ‘Women Multipurpose Centre,’ Kaduna.

Da yake gabatar da jawabinsa a wajen wannan biki, Shugaban kungiyar Jama’atu Nasril Islam reshen jihar Kaduna, Alhaji Ja’afaru Makarfi, ya bayyana cewa makasudin wannan biki shi ne domin su gayyato kiritoci su zo su taya su murna da yin salla lafiya.

Ya ce, “su zo mu zauna mu gaggaisa da juna domin kara samun fahimtar juna, tare da neman hanyoyin samar da zaman lafiya a tsakaninmu.”

Shugaban ya ci gaba da cewa wannan abu da suka yi shi ne na farko a duk fadin kasar nan, inda musulmi suka gayyaci kiristoci domin su taya su murna.

Alhaji Ja’afaru Makarfi ya ce ya kamata gwamnatin Tarayya da sauran jihohin su yi koyi da gwamnatin jihar Kaduna wajen kirkori da Ma’aikatun addinai masu kula da harkar Musulunci da na kiristocin.

Ya ce ta hanyar kafa wadannan Ma’aikatu ne za a sami wayar wa da mabiya kai don kowa ya san hakkin da ya rataya a kansa.

Da yake tofa albarkacin bakinsa a wajen taron, Mataimakin Gwamnan jihar Kaduna, Msita Patrick Yakowa ya yaba kwarai da irin wannan biki da Jama’atun ta shirya, wanda ya ce zai taimaka matuka wajen samar da fahimtar juna.

Daga nan sai ya yi wa daukacin musulmi murnar kammala azumin watan Ramadan, tare da fatan an yi salla lafiya.

A karshe ya yi fatan cewa wannan taro zai kara taimakawa wajen samar da zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin musulmi da kirista.

Da yake amsa tambayoyin manema labarai a wajen, dan Majalisa mai wakiltar mazabar Zariya, Hon. Bala Alwa’u cewa ya yi shi a ganinsa wannan taro zai bayar da muhimmiyar gudummawa wajen samar da zaman lafiya.

Domin a cewarsa, rashin haduwa da juna ne ke haddasa rashin fahimtar juna. Ya ce, ya kamata a rinka zama ana tattaunawa da juna.

Mu ’yan siyasa rudaddu ne
In ji Sanata Isah Kacako

Daga Danjuma Katsina

Wani dan siyasa, kuma tsohon Kantoman jihar Katsina na wasu kwanaki, Alhaji Isah Kacako ya ce, ’yan siyasa rudaddu ne. Ya kara da cewa mafi yawan hayaniyar siyasa ba ta da wata madafa, ko kuma dalilin yin ta. “Mafi yawan hayaniyar da ake yi, ana yi ne ba bisa ka’ida ko tsari ba.”

Sanata Isa Kacako, wanda yake fadin wadannan kalaman a wata ganawa da ya yi da manema labarai a Katsina, ya bayyana adawar da su Rimi ke yi a matsayan rikici ne maras madafa ko iko. Ya ce ba wata hujja ta abin da suke yi, kuma ba su bi tsarin da ya dace ba a kokarin yin abin da suke yi.

Ya kara jaddadawa cewa jami’an ta da husuma ne kan yi amfani da wasu da suke kawo rudu da hayaniya a jam’iyyun siyasa bayan ana zaune lafiya. Ya ce irin wadannan ’yan a-fasa-kowa-ya-rasa, su suna samun abin da ake biyan su ne daga kungiyar asiri ta CIA. “CIA ke daukar dawainiyarsu, ta biya su da tsara masu, sannan ta zugo su domin su ta da zaune tsaye.”

Sanata Isa Kacako ya kara da cewa, ’yan PDP a Kano daya suke, ba su da wata rigima ko fitina a cikinsu, illa kawai wasu ’yan gunagunin da wasu ke yi daga gefe.

Ya jinjina wa mulkin PDP da kuma gwamnatin Obasanjo, ya ce hakika Shugaban ya yi kokari, kuma yana bukatar a taimaka masa ya ci gaba.

Ya tabbatar da cewa kasar nan na cikin hatsarin rudu da rashin sanin ina aka sa gaba. Ya ce amma aikin wannan ba na wane da wane bane, “a’a aikin na kowa da kowa ne.”

Sanata Kacako, wanda ya ce su tasu ta yi gama, sun manyanta, yanzu sai gangara suke yi. Ya ce ya rike duk wani mukami da yake da girma banda Shugaban kasa a kasar nan. “Ni yi Kantoman jiha, na yi Ambasada, na kai babban matsayi a soja. Me nake jira?” Ya kara da cewa ya kamata mutane su sa hankali ga wannan hali da ake ciki domin a fita baki daya.

Ya ce, ya dade bai yi hira da manema labarai ba, sai a Katsina da ya zo salla, “don Katsina garina ne na biyu, kuma ina takama da shi. Na yi aiki a nan, na yi aure har na hayayyafa da jikoki, kuma a zamana har yanzu da ba na zaune a garin ana nuna min mutunci sosai. Wannan ya sa na ga lokaci ya yi na magana da manema labarai.”

Daliban GGC Dala 145 suka sauke Kur’ani

Daga Al-Husaini Dakace

Kwanakin baya daruruwan ’yan uwa da abokan arziki gami da iyaye ne suka halarci makarantar ’yan mata ta Dala watan GGC Dala don ganin yadda daliban makarantar kimanin 145 suka sauke karatun Alkur’ani mai girma da kuma daya daga cikin ’yan matan da ta haddace Kur’ani.

Kafin babban bako mai jawabi a wurin ya yi jawabi, watau Sarkin Kano, sai da Shugabar makarantar, Malama Bilkisu Waziri ta tabo kadan daga cikin tarihin makarantar, inda ta ce an bude makarantar ne a 1960, wanda kuma marigayi Sardaunan Sakkwato, Ahmadu Bello ya bude, inda aka tare da dalibai 36 da azuzuwa hudu.

Malama Bilkisu Waziri ta ce makarantar tana da dalibai kamanin 1,990 da kuma dakunan gwaje-gwajen kimiya tare da karatu da kuma kwamfuta.

Shugabar ta bayyana wasu daga cikin matsalolin da suka addabi makarantar kamar rashin ruwa da kujerin zaman dalibai, da kuma yadda makarantar take fama da karancin malamai da kuma rashin magudanan ruwa.

Bayan ta gama jawabinta ne, sai aka gabatarwa da Sarkin Kano Dakta Ado Bayero daliban da suka sauke karatun na Alkur’ani, inda ya yi godiya ga Allah kan namijin kokarin da daliban suka yi na sauke Kur’ani.

Daga nan sai Sarkin na Kano ya yi kira ga iyaye da su ci gaba da koya wa yara darussan addinin Musulunci.

Har ila yau Sarkin ya yi kira ga iyaye da cewa ya kamata su sa ido sosai a kan abokanin da yaransu suke hulda da su. Ya kuma yi amfani da wannan dama da yin kira ga masu hannu da shuni da cewa su ci gaba da taimaka wa addinin Musulunci a nan duniya ko sa samu sakamako mai kyau gobe kiyama.

Bayan nan sai Shugaban Darikar Tijjaniya na Afrika, sannan Khadimu Kur’an, Khalifa Isiyaka Rabi’u ya taimaka wa wadda ta haddace Kur’ani da kyautar tsabar kudi har N100,000 da kuma yin alkawarin cewa idan Allah ya sa ta samu mijin aure, Khalifan zai taimaka mata da kayan daki. Sannan daya daga cikin matan Khalifa ta agaza mata da turmin atamfa da leshi kyauta.

Sai dai wani abu da ya faru a wurin bikin saukar karatun shi ne yadda gaba daya aka kasa fadar sunan dalibar da ta haddace Kur’ani mai girma, hatta ’yan jarida da suka tambayi Shugabar makarantar sunan dalibar sai ta ce a gaskiya ta manta sunanta. Haka dai jama’ar da suka taru a wurin suka watse ba tare da an bayyana sunan dalibar da ta haddace Kur’anin ba.

Harkar addini ba ta yiwuwa sai da sadaukarwa
In ji Malam Abdulhamid Bello

Daga Isah Adamu

An bayana cewa harkar addini bata yiwu wa sai da sadaukarwa ta bangaren dukiya da rai. Wannan baani Malam Aabdulhamid Bello ne ya yi ga daurruwan ‘’yan uwa a garin Potiskum ranar litinin 6/10/1426 lokacin da ya funatarwa a taron goron Salla da mu’assatul Shuhada ta shirya a garin.

Malamin ya kuma yaba da kokarin ‘’yan uwa na Potiskum wajen muna sadaukarwa a dukkanin al’amaran wannan harkar ta addini. Inda ya ce “Sirrin da ya sa ‘’yan uwa na Potiskum ke kan gaba wajen taimakawa harkar addin ta kowanne janibi ba wani abu ne ba illa cikakkar wiliyar su ga Malam Zakzaky.” Daga nan ya hori ‘’yan uwa da su ci gaba da faimallawa musamman ga iyalan shahidai.

Da yake tsokaci kan irin mutanen nan da ke da’awar cewa wannan harka ta addini wanda Malam Zakzaky ke jagorana akwai ta da hatsari Malamin ya bayyana cewa wannan ba abun la’akari ba saboda a tsawon tarihin harkan nan cikin shekaru Ashirin da biyar yawan shahidan da ake da 117 ne. Sannan ya yi tambaya cewa mutum nawa suka rasu a hatsarin mota cikin wannan shekara akan hanya daga Potiskum zuwa Kano.

Tunda fako Malam Yusuf Poly daga kadama ya bude taro da addu’a da kuma karatun alkur’ani daga Alhaji Kyari. Yayin ‘’yan uwa kuma suka rika saye kayayyakin mu’assasatus Shuhada gami da yanka hakin mu’assa daga shekaru biyar zuwa goma.

Kafinmai jawabi sai da Malam Mustapha Lawan Nasidi wakilin ‘’yan uwa na garin Potiskum ya bayyana makasadin taro da kuma jaddadawa ‘’yan uwa muhimmancin bada infaki saboda Aliyu Yabo ya refe taro da addu’a sai dai ‘’yan uwa sha’irai irinsu Saidu Potiskum, Abdullahi Lushi da Nura Shahidi suka raira baitukan falalar shahada da bada infaki. An tashi taro da misalin karfe 11:45nd.

Shirye muke don kwato kudu
In ji Malam Mustapha Lawan Nasidi

Daga Isah Adamu

“Mu kam a shirye mu ke, albarkacin Imam Khomeini (RA) da Malam Zakzaky (H) don kwato masallacin Kudus daga mamayar da da’anannun yahudawan Isra’ila ke ci gaba da yi wa masallacin na Kudus.” Wadannan kalamai wakilin ‘’yan uwa na shiyyar Potiskum Malam Mustapha Lawan Nasidi ne ya yi lokacin da yake jawabin kamala muzaharar Kudus ga dandazon al’ummar musulmi almajiran Malam Zakzaky jim kadan bayan kamala muzahara kamar sauran al’ummar musulmin duniya a ranar juma’a 27/9/1426.

Malamin ya ci gaba da cewa sakamakon hangen nesa na bayin Allah salihai musamman Imam Khomeini (RA) wand aya assasa wannan al’amari ya snya al’ummar musulmi duniya da ma wadanda ba musulmi ba suka san halin da masallacin Kudus ke ciki da kuma gallazawar da yahudawan Isra’ila ke yiwa al’ummar Palasdinawa.

Da yake tsokaci kan tarihin masallacin na Kudus malamin ya bayyana cewa wjaibi ne ga al’ummar musulmin duniya su yunkura don daura damarar kwato shi (Kudus) daga la’ananun yahudu kasantuwar sa (Kudus) markhazin Annabawa Allah (T) kuma cibiyar da manzon Allah (SAW) ya bi don zuwa mi’iraji. Saboda haka in ji Malam Mustapha lokaci ya yi da al’ummar musulmin dunya zasu yi duk abin da suka iya yi don kwato wannan masallacin kamar yadda magabata suka yi tun kafin bayyanar mai daukar fansa da iyalan gidan manzon (SAW), wannan kuwa ba kowa ba illa Imamul Hujjah (AS).

Malamin ya kuma bayyana karara cewa manyan kasashe azzalumai irin su Amurka da Birtaniyya ke agazawa la’anannun iyayen gidan su na Isra’ila. “Saboda haka ku kwana da sanin cew aba gudu ba ja da baya ga wannan yunkuri na kwato Kudus.

Tun da farko sai da masu gudunar da muzaharar suka rika raira taken kwato Kudus da la’anannun

Harkar addini ba ta yiwuwa sai da sadaukarwa
In ji Malam Abdulhamid Bello

Daga Isah Adamu

An bayana cewa harkar addini bata yiwu wa sai da sadaukarwa ta bangaren dukiya da rai. Wannan baani Malam Aabdulhamid Bello ne ya yi ga daurruwan ‘’yan uwa a garin Potiskum ranar litinin 6/10/1426 lokacin da ya funatarwa a taron goron Salla da mu’assatul Shuhada ta shirya a garin.

Malamin ya kuma yaba da kokarin ‘’yan uwa na Potiskum wajen muna sadaukarwa a dukkanin al’amaran wannan harkar ta addini. Inda ya ce “Sirrin da ya sa ‘’yan uwa na Potiskum ke kan gaba wajen taimakawa harkar addin ta kowanne janibi ba wani abu ne ba illa cikakkar wiliyar su ga Malam Zakzaky.” Daga nan ya hori ‘’yan uwa da su ci gaba da faimallawa musamman ga iyalan shahidai.

Da yake tsokaci kan irin mutanen nan da ke da’awar cewa wannan harka ta addini wanda Malam Zakzaky ke jagorana akwai ta da hatsari Malamin ya bayyana cewa wannan ba abun la’akari ba saboda a tsawon tarihin harkan nan cikin shekaru Ashirin da biyar yawan shahidan da ake da 117 ne. Sannan ya yi tambaya cewa mutum nawa suka rasu a hatsarin mota cikin wannan shekara akan hanya daga Potiskum zuwa Kano.

Tunda fako Malam Yusuf Poly daga kadama ya bude taro da addu’a da kuma karatun alkur’ani daga Alhaji Kyari. Yayin ‘’yan uwa kuma suka rika saye kayayyakin mu’assasatus Shuhada gami da yanka hakin mu’assa daga shekaru biyar zuwa goma.

Kafinmai jawabi sai da Malam Mustapha Lawan Nasidi wakilin ‘’yan uwa na garin Potiskum ya bayyana makasadin taro da kuma jaddadawa ‘’yan uwa muhimmancin bada infaki saboda Aliyu Yabo ya refe taro da addu’a sai dai ‘’yan uwa sha’irai irinsu Saidu Potiskum, Abdullahi Lushi da Nura Shahidi suka raira baitukan falalar shahada da bada infaki. An tashi taro da misalin karfe 11:45nd.

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


 Shafin Gamji | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International