Almizan :Duniya ba tare da Sahyoniyanci ba ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 17 Shawwal, 1426                 Bugu na 692                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Rubutun musamman

Duniya ba tare da Sahyoniyanci ba

Daga Muhammad Awwal Bauci IRIB Tehran –Iran (awwalubauchi@yahoo.com)

“Hmmm! Allah Mai girma! Kai Allah Ya ji kan Marigayi Imam Khumaini (RA),” in ji wani abokina (da babu bukatar ambato sunansa). Ni dai ba abin da na ce masa face; ‘amin summa amin.’ Ina mai karawa da cewa;, to amma abokina, me ya sa ka fadi hakan alhali kana mai jan dogon numfashi? Nan take sai ya ce min: “Bar ni kawai na tuna da wasu siffofi guda biyu ne da Imam din ya kira Amurka da haramtacciyar kasar Isra’ila da su da a halin yanzu ne nake fahimtar su sosai, sune kuwa: ‘Uwar Shaidanu’ ga na farkon, da kuma ‘Cutar Sankara’ ko kuma ‘Fatalwa mai shan jini’ ga na biyun.”

Shaikh Hasan Saffar

Ni dai na zuba ido kawai ina kallon sa, alhali kwakwalwata tana ta tuno irin ayyukan Allah wadai da wadannan ‘bakaken kuraye’ biyu suka aikata, kuma suke ci gaba da aikatawa. A gefe guda kuma ina mamakin kasashe da shugabannin da suke kare wannan haramtacciyar kasa. Daga karshe dai sai kawai na kawo karshen wannan mamaki nawa da karin maganar mutanenmu da ke cewa ‘Na gari na kowa, mugu sai mai shi.’

Ta yiwu wani ya ce wai wannan babatun me yake yi ne? To bari ka ji, idan ba ka sani ba. A ranar Larabar da ta wuce (26/10/2005) ne Shugaban kasar Iran, Dakta Mahmud Ahmadinejad, a wajen wani taron kara wa juna sani da aka ba shi sunan “Duniya Ba Tare Da Sahyoniyanci Ba” da aka gudanar a nan birnin Tehran, yayin da yake ishara da kalamin Marigayi Imam Khumaini (RA) na cewa dole ne a share (haramtacciyar kasar) Isra’ila daga bayan kasa yake cewa: “Duk wani mutum (wata kasa) da ya amince da haramtacciyar kasar Isra’ila tamkar ya sanya hannu wajen mika wuya da cutar da kasashen musulmi ne.” Har ila yau Shugaba Ahmadinejad ya kara da cewa: “Na yi amanna da cewa karuwar wayewa da farkawar da ake samu a kasashen musulmi, zai sa ba da jimawa ba za a tsarkake duniyar musulmi daga gwamnatin Sahyoniyawa.”

Wannan jawabi na Shugaban Iran, Dakta Ahmadinejad dai ya janyo ka-ce-na-ce, wato a daidai lokacin da mafi yawa daga cikin al’ummar musulmi da sauran ma’abota ’yanci suka yi maraba da kuma jinjina wa wannan kalami na jaruntaka (kamar yadda za mu gani nan gaba), wasu kuma ’yan amshin shatan Amurka da haramtacciyar kasar Sahyoniyawan, sai ihu suke yi bayan hari da ci gaba da nuna damuwa da wannan kalami.

Sabanin fadin Malam Bahaushe na cewa; “ana tsammanin wuta a makera, sai aka same ta a masaka,” a wannan karon kam, kamar yadda dama aka zata, a makerar aka samu wutar, don kuwa ba tare da wani bata lokaci ba, Amurka ta yi cara ta bakin mai magana da yawun fadar Amurka, Scott McClellan, yana mai Allah wadai da wannan kalami. Sai kuma sauran ’yan amshin shatan suka biyo baya, Birtaniyya, Faransa, Australiya, Jamus da dai sauransu, suna masu nuna goyon bayansu ga haramtacciyar kasar Isra’ila.

Babatun da wadannan kasashe dai suka yi kuma suke ci gaba da yi, ko da wasa bai taba zama abin mamaki ba ga duk wanda ya san inda dama aka sa gaba, face dai abin mamaki da bakin cikin shi ne yadda wasu da suke kiran kansu masana suka dauki wannan kalami na Shugaba Ahmadinejad a matsayin bakon abu. Babu shakka wannan shi ne abin mamaki da bakin ciki. Don kuwa duk wanda ya san Shugaba Ahmadinejad, a matsayinsa na wanda ya sha daga makarantar Marigayi Imam (RA), to ba zai yi mamakin jin wannan kalami daga bakinsa ba, abin mamakin ma shi ne idan ba a ji hakan daga bakinsa ba.

Wasu kuma cewa suke yi wai ya zo ne da wani sabon abu, to shi ma dai a hakikanin gaskiya abin mamaki din ne, don kuwa duk wanda ya san wannan juyi na Iran, ya san shi ne da wannan take da akida ta rashin yarda da halascin zaman Yahudawan Sahyoniya a kasar Palastinu da kuma wajibcin kawar da su daga wajen. Don kuwa tun ranar gini ranar zane, a lokuta daban-daban an sha jiyo Jagoran juyin-juya-halin Musulunci, kuma Mu’assasin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Marigayi Imam Khumaini (RA) yana kiran musulmi da su yi hobbasa wajen kawar da haramtacciyar kasar Isra’ila daga doron kasa. Don karin bayani ga wasu daga cikin irin wadannan kalamai na Imam:

“Al’ummar musulmin Iran da sauran al’ummomin musulmi da ma duk wani mai kaunar ’yanci, a hakikanin gaskiya ba zai yarda da kasancewar Isra’ila ba, a kodayaushe za mu goyi bayan ’yan uwanmu Larabawa da Palastinawa.

“Wajibi ne dukkanmu mu mike wurin ruguza Isra’ila, mu mayar da jarumar al’ummar Palastinu a gurbinta.

“A bisa asasin Musulunci ya hau kan dukkan musulmi su ’yanto Kudus su kawar da wannan Cibiya ta Shaidan a kasashen musulmi.

“Wajibi ne a kawar da Isra’ila daga shafin tarihi.

“Kada ku goyi bayan Isra’ila, wannan makiyar Musulunci da Larabawa domin wannan fatalwa mai shan jini ba za ta yi muku rahama ba, idan ta kai gare ku.

“Iran ta kasance kuma ma a yanzu ita ce makiyar Isra’ila, kuma ba za mu yi alaka da ita ba, domin mahandamiya ce, kuma makiyarmu ce.

“Ya wajaba a kan dukkan musulmi, musamman kasashen musulmi da su kawar da wannan Cibiyar fasadi iyakar kokarinsu.” Da dai sauran maganganu irin wadannan da za a iya samun su cikin maganganun Marigayi Imam din da aka tattara su cikin littafin nan mai suna Kalmomin Hikima da Wa’azi Na Imam Khumaini da Cibiyar Bincike da Wallafa Ayyukan Marigayi Imam ta buga da kuma yadawa.

Wadannan kalamai suna nuna mana akidar da juyin-juya-halin Musulunci na Iran ya ginu a kai, don haka kalamin Shugaba Ahmadinejad ba wani bakon abu ba ne, face dai jaddadawa ne da sake tunatar da wadanda suka mance. Hakan ne ma ya sanya kalamin ya samu goyon baya da jinjinawa daga jami’ai da al’ummar Iran. Bugu da kari kan sauran al’ummomin kasashen musulmi da sauran ma’abuta ’yanci ciki kuwa har da wasu daga cikin Yahuwadan kamar yadda za mu gani nan gaba.

A matsayin misali a ranar Juma’ar da ta wuce (kwanaki biyu bayan wannan jawabi, wato a ranar Kudus ta Duniya kenan), al’ummomin Iran a nan birnin Tehran da sauran garuruwan Iran sun fito kwansu da kwarkwatansu suna masu nuna goyon baya ga Shugabansu Ahmadinejad kan wannan kalami da ya yi. Daga cikin taken da suka dinga rerawa har da fadin cewa: “Ra’ise Jamhure Ma, Tashakkur, Tashakkur” (Shugaban kasarmu, mun gode- mun gode) da dai sauransu.

Baya ga al’ummar Iran din, Jagororinsu ma duk sun nuna amincewarsu da wannan kalami. Yayin da yake nuna goyon bayansa, Kwamandan dakarun juyin-juya-halin Musulunci na Iran, Janar Rahim Safawi, ya bayyana cewar: “Kalaman Shugaban kasa, a hakikanin gaskiya kalamun al’ummarmu ne da suka fito daga daga bakin Shugaba,….a hakikanin gaskiya kalaman Imam da al’ummarmu ya sake jaddadawa,….al’ummarmu suna tare da kalaman Shugabansu.”

Har ila yau shi ma yayin da yake nuna goyon baya ga wannan kalami, Kakakin Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran, Dakta Haddad Adil cewa yake yi: “Laifin haramtacciyar kasar Isra’ila na da yawan gaske.”

Shi ma tsohon Kakakin Majalisar, kuma mai ba wa Jagora Imam Khamene’i shawara, Shaikh Natiq Nuri cewa yake: “Abin da Shugaban kasa ya fadi akida ce ta Jamhuriyyar Musulunci ta Iran.”

Banda al’umma da jami’an kasar Iran, su ma sauran al’ummar musulmi na duniya ba a bar su a baya ba wajen jinjina wa Shugaban kasar Iran din kan sosa musu inda yake musu kaikayi da ya yi, don kuwa duk wani musulmi ya san cewa Isra’ila ba ta cancanci wanzuwa ba. A nasa bangaren, tsohon Limamin masallacin Al-Aqsa, Shaikh Muhammad Siyam ya bayyana cewa: “Ai tuni mai girma Shugaban kasar Iran ya bayyanar da abin da muke son fadi kan Baitul Maqdisi.

Har ila yau Limamin, wanda ke jawabi kan ranar Kudus ta Duniya a wani masallaci da ke kasar Kuwaiti, yayin da yake godiya da irin matsayar Iran ta dauka, ya kara da cewa: “A kodayaushe Jamhuriyyar Musulunci ta Iran ta kasance mai goyon bayan al’ummar Palastinu, kuma matsayarta kan masallacin Kudus abin alfaharin al’ummar musulmi ne.”

Shi ma Wakilin Yahudawa a Majalisar shawarar Musulunci ta Iran, yayin da yake nuna goyon bayansa ga kalaman Shugaban Iran din, ya bayyana cewa: “Dukkanin Yahudawa mabiya hakikanin koyarwar Annabi Musa (AS) sun san cewa Isra’ila mahandamiya ce.” Kai masu nuna goyon bayan dai suna da yawan gaske. Kai nagari na kowa, mugu kuwa sai mai shi!

To wasu dai suna ganin haramtacciyar kasar Isra’ila da sauran kawayenta suna da hakkin su nuna rashin jin dadi da amincewarsu da wannan kalami na Shugaban Iran. Mu dai ba wai mun ce kada su yi hakan bane, suna da ’yancin yin hakan, kamar yadda shi kansa Shugaban Iran din a yayin zanga-zangar Ranar Kudus ya bayyana cewa: “Suna da ’yancin su fadi duk abin da suke so, to amma kalamansu ba abin karba bane. Su azzalumai ne, da suke zaton cewa dole ne dukkan duniya su mika musu wuya.”

To sai dai tambayar da da dama suke yi ita ce; shin ina wadannan kasashe suke ne, ko kuma mu ce wane mataki suka dauka a lokacin da Isra’ilan take zubar da jinin dubun-dubatan Palastinawa da sauran al’ummar Larabawa? Shin sun yi ko da Allah wadai din kuwa kamar yadda suke yi a halin yanzu? Ina suke, kuma wane mataki suka dauka kan haramtacciyar kasar lokacin da take barazanar kai hari kan kasar Iran da Cibiyoyinta na makamashin nukiliyar zaman lafiya? Shin wane mataki suka dauka lokacin da wasu manya-manyan jami’an haramtacciyar kasar suka fito fili suna zancen kashe Larabawa da kawar da su a bayan kasa?

Duniya dai ta shaidi lokacin da aka jiyo Ariel Sharon, Firaministan haramtacciyar kasar na yanzu yana gaya wa Janar Ouze Merham a shekarar 1956 cewa: “Ni ban san da wani abin da ake kira Dokokin Kasa da Kasa ba. Na yi alkawarin kona duk wani jariri Bapalastine da za a haifa a wannan waje. Mata da kananan yaran Palastinawa sun fi mazajensu hatsari, saboda kasantuwan yaran Palastinawa na nuni da cewa za su ci gaba da wanzuwa kenan, shi kuwa babban mutum hatsarinsa kadan ne. Na rantse, da zan kasance farar hular Isra’ila guda da ya saura, idan na hadu da Bapalastine sai na kona shi in azabtar da shi kafin kashe shi. Bugu daya kawai na kashe Palastinawa 750 (a Rafah a 1956). Ina so in kwadaitar da sojojina da su dinga yin fyade ga ’yan matan Larabawa saboda matan Palastinawa bayin Yahudawa ne, za mu yi dukkan abin da muke son aikatawa da ita, kuma babu wanda zai gaya mana abin da za mu yi sai dai mu mu gaya wa wasu abin da za su yi.”

Ko kuma fadin David Ben-Gurion, tsohon Firaministan haramtacciyar kasar Isra’ila cewa: “Dole ne mu yi amfani da ta'addanci, kisan gilla, tsoratarwa, kwace filaye da katse duk wasu ababen bukatun yau da kullum don kawar da Larabawa.”

Ko kuma inda yake cewa: “Dole ne mu kori Larabawa da maye gurbinsu.” Da dai sauran irin wadannan maganganu na batanci da cin mutunci da bayyanar da ayyukan ta’addanci a fili da jami’an Yahudawan suka sha fadi. Shin wane mataki suka dauka? Ashe wadannan kalamai ba su kai a kori haramtacciyar kasar Isra’ilan daga Majalisar Dinkin Duniya ba? Ashe wadannan kalamai ba su kai a yi caa a kan haramtacciyar kasar ba? Ina! Nagari na kowa, mugu kuwa sai mai shi!!

To, amma tambayar da da dama suke yi ita ce; shin me ya sa ne Turawa suka yi caa a kan Iran da Shugabanta a daidai wannan lokacin, tattare da sun san cewa wannan kalami nasa ba bakon abu bane?

To masu kula da al’amurran yau da kullum dai suna ganin da gangan suka yi hakan. Na farko dai wani kokari ne na dushe kaifin Ranar Kudus ta Duniya da aka gudanar kwanakin biyu bayan wannan kalami. Saboda a fili yake cewa wannan rana ta Kudus ba karamin tayar musu da hankali take yi ba. Don haka duk wani kokarin da za su yi wajen dushe kaifinta za su yi.

Wasu kuma suna ganin kokari ne suke yi na kawar da hankulan al’umma daga irin ayyukan ta’addancin da suke yi wa Palastinawa, musamman cikin ’yan kwanakin nan a Gazza da Yammacin Kogin Jordan. Da dai sauran ra’ayoyi daban-daban da masana suke ta bayyanawa.

To ko ma dai menene al’ummar musulmi dai sun riga sun farka sun fahimci makircin Yahudawa da magoya bayansu. Don haka irin wadannan farfaganda da wuya ta yi wani tasiri a gare su, abin da ke tabbatar da hakan kuwa shi ne irin fitowar da al’umma suka yi wajen goyon bayan Shugaban Iran din kan wannan kalami nasa da kuma yin Allah wadai da Sahyoniyanci da masu daure musu gindi. Na gari na kowa, mugu kuwa sai mai shi!

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


 Shafin Gamji | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International