Almizan :Ana ci gaba da kashe al’ummar Iraki ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 17 Shawwal, 1426                 Bugu na 692                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Duniya Labari

Ana ci gaba da kashe al’ummar Iraki

Daga Aliyu Saleh

Wani maharin kunar bakin wake ya kashe kansa da wasu mutane 37 a wani hari da ya kai ranar Talatar makon jiya, tare da ji wa wasu da dama rauni. Wasu 31 kuma sun rasu bayan wani harin na daban da wani ya kai gidan cin abincin da ake kira ‘Qaduri Restaurant’ da ke kan titin Abu Nawas a Bagadaza.

Sojan Amurka da na Iraki dai sun kaddamar da wani hari a kan masu kai hare-hare a garin Qaim da ke kan iyaka da Siriya. Ministan tsaron Iraki, Saadun Dulaimi ya ce sun kashe mayaka sama da 200 a harin.

Wasu Irakawa shida sun rasu, yayin da 13 suka samu munanan raunuka a ranar Talata bayan harin da wani Direban mota ya kai a wajen barikin sojoji da ke garin Tikrit mahaifar Saddam Husaini da ke arewacin kasar ta Iraki. Wasu fararen hula biyu sun rasu ’yan awanni bayan wannan harin da aka kai.

A wani tashin hankalin na daban, an ga wasu gawawwakin mutane 27 yashe bayan an harbe su a ka a kusa da kauyen Jassan daura da garin Kut.

Wani soja, Kanar Badr Basri, wanda ya ga gawawwaki ya bayyana cewa gawawwakin suna sanye ne da kayan fararen hula, kuma duk an daure masu hannunsu ta baya kafin a harbe su. “Mafi yawan wadanda aka kashe matasa ne da shekarunsu suka kama daga 20 zuwa 35,” in ji shi.

Jami’an jam’iyyar ‘Sunni Islamic Party’ sun ce an sace kuma an kashe, Ahmad Rashid Rawi a ranar Laraba a garin Ramadi da ke kudancin Bagadaza. Ita dai wannan jam’iyya tana goyon bayan shirin yin zabe da ake yi a Iraki.

Akalla mutane 10 ne aka ba da labarin sun rasu, biyar daga cikinsu fararen hula, yayin da wasu sama da 20 suka jikkata, bayan jerin fashewar bama-baman da ake binnewa a gefen hanya a garin Ramadi da ke kudacin Bagadaza a tsakiyar wannan makon.

Tashin bama-baman a jere ya jijjiga yankin tsaro na ‘Green Zone,’ inda ofisoshi da ma’aikatun gwamnatin Iraki da sojan mamaya na Amurka suke. Bayan wannan fashewar an ji kuma karar harbe-harbe da kananan bindigogi, yayin da hayaki ya turnuke yankin.

Ofishin jakadancin Amurka a Iraki ya sanar da mutuwar wasu ma’aikatan kwangila ta tsaro ’yan kasar Afrika ta Kudu biyu bayan harin da aka kai masu a motarsu, yayin da wasu uku da suka hada da Ba’amerike da kuma wani dan Iraki, gami da dan Afrika ta Kudun suka samu raunuka

Wani bom da aka boye shi a cikin wata tankar mai a wani gari da ’yan Shi’a suke da rinjaye a arewa maso gabashin Bagadaza ya yi sanadiyyar rasuwar mutane 26 da ji wa sama da 34 mummunan rauni a makon shekaranjiya.

Bayanan da muka samu daga shafin sakar sama na JORDAN TIMES, ya tabbatar da cewa harin ya kuma yi sanadiyyar tunkurar burji ga sojan mamaya na Amurka uku, tare da ji wa wasu takwas raunuka.

Wani bayanin kuma ya bayyana cewa wasu sojan mamaya na Amurka 10 sun shura bayan wani harin da aka kai masu ranar Asabar a wani kauye da ke daura da kan iyakar Siriya da Iraki, wajen da sojan mamaya na Amurka suka kai wa harin “a gama da su” a makon shekaranjiya.

Hare-hare sun ci gaba da tsananta a cikin kasar da rikice-rikice suka yi wa dabaibayi, yayin da zaben ’Yan Majalisa Wakilai da za a yi a kasar ran 15 ga Disamba mai zuwa yake kara karatowa.

Shi ma wani bom da aka kai hari da shi a garin Huweder da ke arewacin Bagadaza, inda Shi’awa suke da rinjaye, ya kashe mutane 45. Bom din, wanda aka boye shi a cikin masallaci ya fashe ne yayin da mutane suka shagaltu da ayyukan ibada a wannan lokacin.

“Abubuwan da suka fashe sun jijjiga kasa,” in ji Husani Mouwaffaq, dan uwan Qahtan, wanda ya rasu a yayin fashewar. “Titunan da ke daura da masallacin sun cike da naman mutanen da suka rasu. Mutane da yawa sun rasu wasu da dama kuma sun jikkata.”

Wani jami’in ’yan sanda, Laftar-Kanar Ahmad Abdul Wahab, wanda shi ne ya ba da kididdigar wadanda suka rasu a hari na kunar baki wake na garin Huweder, ya ce, adadin na iya karuwa, musamman idan aka yi la’akari da yawan wadanda suka jikkata a harin.

Shi dai wannan kauye na Huweder ya jima yana ganin hare-haren kunar bakin wake, dashe-dashen bama-bamai da kuma harbe-harbe, musamman a wajen duba ababen hawa na ’yan sanda da ke kauyen.

Wani asibiti da ke kusa da garin Baqouba yana makare da wasu da suka jikkata bayan wani harin na daban da aka kai, yayin da Likitoci da sauran ma’aikatan lafiya ke ta aiki wurjanjan don ganin sun ceto ran wadanda suke da sauran shan ruwa a gaba.

Wani dan jarida da ya ziyarci asibitin, ya bayyana cewa ya ga wani yaro a daya daga cikin gadajen da ke asibitin an daure masa wuya da bandeji, sakamakon mummunan raunin da ya samu bayan harin da aka kai masu. Wani mutum kuma da ke kusa da shi jini yana ta tsartuwa daga cikinsa.

Kofur Ahmad Jassim, ya fada cikin kuka cewa; “Muna tambayar ’yan ta’adda da ke kashe-kashe a Iraki da sunan jihadi, mutanen da suke kashewa da suka hada da mata da kananan yara me suka yi kuma?”

Sojan mamaya na Amurka biyu kuma sun mutu ranar Lahadi bayan motarsu ta ci karo da wani bom da aka binne a gefen hanya a kudancin Bagadaza. Wani sojan na uku kuma ya cika shi ma bayan sun ci karo da wani bom din da aka binne a gefen hanya a kusa da Beiji, da ke da nisan kilomita 155 a arewacin Bagadaza. Amurkawa sun ce sojansu hudu sun jikkata a harin na Beiji.

Wannan harin da aka kai dai shi ya cicciba yawan adadin sojan mamaya na Amurka da aka kashe a Iraki tun daga watan Maris na 2003 da suka mamaye kasar zuwa 2,060, wasu sama da 1500 suka jikkata, kamar yadda kamfanin dillacin labarai na Associated Press ya tabbatar. Yanzu haka dai sama da sojan mamaya na Amurka 135,000 ne ke Iraki.

Kodayake a bayanin da ya yi ta gidajen rediyon kasar a makon shekaranjiya, Shugaban Amurka Geioge Bush ya ce, suna samun nasara a Iraki, amma sai dai wani binciken jin ra’ayin jama’a da kamfanin dillacin labarai na Associated Press ya bayar na nuni da cewa Amurkawa na kara janye goyon bayan da suke bayarwa game da yakin na Iraki.

Cibiyar bayar da umurni ta sojan mamaya na Amurka a Iraki ta bayyana cewa dakarunsu sun yi arangama da masu fafutika a ranar Asabar a kusa da ‘Euphrates River’ da ke daura da kan iyakar Siriya da Iraki. Sun ce a harin sun kashe goma daga cikin masu fafutikar.

A kwanakin baya sojan mamaya na Amurka a Iraki sun ce jirgen samansu sun yi ruwan wuta a kan wani gida da masu leken asirinsu suka tsegunta masu cewa dan Saudiyya kuma memba a kungiyar Alka’ida, Abu Muhammad yana ciki yana ganawa da mutanensa. A harin sun ce sun kashe Abu Muhammad da kuma mutanen da suke tare da shi.

Sai dai su mazauna wannan unguwa sun tabbatar da cewa wadanda aka kashe din fararen hula ne ba mayaka ba. Wasu hotuna ma da kamfanin dillacin labarai na Associated Press da Television News Video suka nuna, sun nuna gawawwakin wasu mutane hudu da suka hada da mace. Masu gidaje a unguwar sun yi amfani da motar rusau wajen kau da sauran ginin da ya yi sura bayan harin da sojan mamaya na Amurka suka kai.

Wasu mutane da ba a san ko su waye ba, sun harbe Mataimakin Babban Daraktan kamfanin mai da ke garin Kirkuk, Mikhail Eros har lahira. Wasu ’yan sanda biyu kuma sun rasu bayan sun taka bom a yayin da suke sintiri duk dai a garin na Kirkuk.

A garin Bagadaza kuwa, wani maharin ne ya bude wuta a kan sojan Iraki a kusa da wani wajen duba ababen hawa da ke arewacin Bagadaza, inda ya kashe uku daga cikinsu, ya ji wa bakwai rauni. Sai dai ’yan sanda sun ce sun kashe uku daga cikin maharan.

Shi kuwa wani maharin kunar bakin wake mutane 20 ya kashe ya jikkata sama da 60, a kudancin Bagadaza, cikinsu kuwa har da sojan mamaya na Amurka hudu.

Harin, wanda aka kai kashe da misalin karfe 5:00 na yamma a gogon can, an kai shi ne a wata kasuwa da ke tsarkiyar ci a garin Musayyib da ke da sinsan kilomita 60 a kudancin Bagadaza.

A ranar 16 ga watan Yulin da ya gabata dai sama da mutane 100 aka kashe a wannan garin a wani harin kunar bakin wake da aka kai a wani masallacin Shi’a da ke garin.

An kuma yi wata kazamar arangama tsakanin sojan mamaya na Amurka da masu fafutika a garin Ramadi da ke da nisan kilomita 151 a yammacin Bagadaza. A wannan garin ne a ranar Talatar makon shekaranjiya sojan mamaya na Amurka da kuma wani ma’aikacin jirgin ruwansu suka rasu bayan sun taka wani bom da aka binne a gefen hanya.

Jama’a a garin Ramadi sun fito kan titi suna kwasar abin da ya yi saura na jirgi mai saukar ungulun samfurin M-16 da aka harbo har ya kashe sojan mamaya na Amurka biyu da suke ciki bayan mayaka a wannan garin da Amurka take kira ‘Cibiyar masu fafutika’ sun harbo shi da makaminsu bayan wasu bama-bamai sama da 500 da suka harba a garin. Ma’aikatar tsaron Amurka ta ce tana nan tana binciken hatsarin jirgin.

Laftanar-Kanar Steve Boylan, mai magana da yawun sojan mamaya na Amurka a Iraki, ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba Amurka za ta bude wata makarantar horar da sojoji a kusa da garin Taji da ke da nisan kilomita 19 arewacin Bagadaza don horar da sojan Iraki matakan yaki da masu kai masu hare-hare.

Sojan mamaya na Amurka Iraki sun ce sun kashe sama da mayaka 1,000 a hare-haren da suke kai masu a garuruwan kan iyaka. Sun ce sama da soja 2,500 ne za suka shiga wani shirin binciken gida-gida a garin Husaybah domin kakkabe abin da suka kira burbushin ’yan ta’adda da ke garin a wani hari da suka yi masa suna lakabi da ‘Operation Steel Curtain.’

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya jiwo Ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon tana kiyasta cewa ta kashe mayakan Iraki sama da 26,000, ko ta jikkata daga watan Janairu na 2004 kawo yanzu.

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


 Shafin Gamji | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International