Almizan :Muna binciken wasu kananan hukumomin Katsina ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 17 Shawwal, 1426                 Bugu na 692                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Babban Labarinmu

Muna binciken wasu kananan hukumomin Katsina

In Alhaji Abu Danmalam Karofi


o.
i

   

A wata tattaunawa ta musamman da babban Sakatare a Hukumar da ke kula da Kananan Hukumomi da masarautu ta jihar Katsina, Alhaji Abu Danmalam Karofi, ya bayyana wa ALMIZAN cewa; Hukumarsa a yanzu haka tana binciken wasu Kananan Hukumomi guda shida.

Kodayake Alhaji Abu Danmalam ya ki ya bayyana sunayen Kananan Hukumomin, amma ya ce lalle suna da hujjoji kwara-kwara cewa wadannan Kananan Hukumomin shida sun yi abin da ba daidai ba da kudin da ke wajensu. Ya kara da cewa suna ta musayar sako, suna cewa ba su ci ba, Hukumarsa na cewa sun ci.

Alhaji Abu Danmalam ya ce, lalle an yi tabargaza a wadannan Kananan Hukumomin, kuma idan har aka gama bincike za a bayyana su ga jama’a domin ya zama darasi ga sauran.

Ya kara da cewa; bincike ya yi nisa, kuma da zarar an kammala, aka gama duk abin da ya dace, za a bayyana sakamakon kowa ya sani.

Binciken ALMIZAN ya gano sunayen wadannan Kananan Hukumomi har ma duk zarge-zargen da ake masu, har ma mun fara bincike a kansu daya-daya. Binciken musamman kuma mai zaman kansa ne.

Abubuwan da jaridar ta ci karo da su suna da ta da hankali a wannan yanayi da ake ciki na kukan talauci da rashi tsakanin wadanda ake mulki, amma wadanda suka daukar wa kansu amana kuwa kowa kokarin azurta kansa har jikan jikoki da dukiyar da aka ba shi amana yake.

A rahoton da wata kungiya mai zaman kanta ta fitar, ta nuna mafi yawan shugabannin sun fi mai da hankali ga gina kansu fiye da taimakon al’ummar da suke mulki.

Wasu kuma sun nuna cewa wadanda ke kan mulkin ba su cancanta ba, yayin da wasu zazzafar siyasar da ake yi a yankin, ita ke hana ci gaba. Wata kuma kudaden da ake kashewa wajen daukar dawainiyar “manyan” yankin ke hana ci gaba.

Rahoton kungiyar, wanda ALMIZAN ta sami kwafi ta jeranta Kananan Hukumomin da aka fi samun zazzafar siyasa kamar haka: (A) Karamar Hukumar Mashi, Funtuwa, Danmusa, Jibiya da Charanchi.

Kananan Hukumomin kuma da “manya” ke juyawa sune, Katsina, Ingawa, Kaita, Kankara, Malumfashi, Kafur, Matazu, Musawa da Batagarawa.

Rahoton ya zayyana irin ficen da kowace Karamar Hukuma ta yi a fanninta da kuma inda ta gaza. Ta jinjina wa Karamar Hukumar Mashi da mai da karkara birane, duk da Karamar Hukumar ta yi fice da lunguna masu wahalar shiga sai a jakuna ko dawakai, amma yanzu motoci ke iya ratsa su, da kuma kai masu wutar lantarki da ruwan sha ta amfani da na’ura mai aiki da hasken rana.

Kungiyar sun misalta cewa; ana jin duk ’yan jihar Katsina babu inda mutanen karkara ke da wayewar siyasa irin Mashi. A rahoton sun zargi Shugaban Karamar hukumar, Alhaji Salisu Yusuf Majigiri da cewa su ’yan cikin garin Mashi suna jin cewa bai yi masu komai ba. Wannan zargin ya kara zafafar siyasar da ake yi a Karamar Hukumar.

Sai dai rahoton ya jinjina wa Karamar Hukumar Batsari a kan cewa tunda aka kafa ta ba a ta taba ayyukan da suka tabo kowane yanki kamar a wannan lokacin ba. Sun misalta Shugaban da wanda yake tare da “manyan” gari, kuma ya rike talakawansa.

Rahoton ya ce Karamar Hukumar Katsina ita ce ta yi zarra a wajen bayar da taimako da gudummuwa ga wanda ya bukata. Aka ce Karamar Hukumar ta yi zarra a bayar da agaji fiye da a aiki.

Rahoton ya zargi Karamar Hukumar Charanci da cewa surutunta a kafofin watsa labarai ya fi aikinta a kasa yawa.

Rahoton ya zargi karamar Hukumar Kaita da cewa nan ne aka fi ba da kwangiloli da tsadar gaske. Takardun da suka samu da suka kwatanta su da na wasu Kananan Hukumomin sun nuna cewa a Kaita ana ayyuka da tsada. Wasu ayyukan kuma ba su da inganci.

Rahoton ya jinjina wa Karamar Hukumar Daura a matsayin wadda ta kula da matasa da kafa masu Cibiyar koyon sana’o’i wadda babu kamar ta a duk jihohin Arewa ta tsakiya.

Rahoton ya jinjina wa Hukumar Kula da Kananan Hukumomi a kan yadda take sa ido ga Kananan Hukumomin da kuma bullo da shirin noman rani da ta yi, wanda har aka sa kofi ga wanda ya yi zarra.

A gasar ta noman rani ta bara, Kananan Hukumomin Jibiya, Kafur, Rimi da Mashi suna daga cikin wadanda suka yi zarra.

Shi kuwa Shugaban Karamar Hukumar Safana, korafi ya yi na cewa sun kasa cin gasar ne don babu ruwan dam a yankinsu, abin da ya hana su cin wani abu.

Komawa babban shafinmu        Komawa saman wannan shafin


  | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International