Almizan :Amurka ta yi amfani da makamin kare dangi a Fallujah ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 17 Shawwal, 1426                 Bugu na 692                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Babban Labarinmu

Amurka ta yi amfani da makamin kare dangi a Fallujah

In ji wani shiri na tashar talabijin na Italiya

Daga Aliyu Saleh da Musa Muhammad Awwal

Wani shiri na musamman da tashar talabijin na 'RAI' mallakin kasar Italiya ya watsa, ya tabbatar da cewa sojojin gwamnatin kasar Amurka, sun yi amfani da bom mai gubar 'White Phosphorus' a lokacin da suke kai hare-hare a garin Fallujah na Iraki.


Tashar talabijin din ta RAI ta kara da cewa wannan amfani da sojojin suka yi ya shiga cikin karya ka’ida ta duniya na amfani da makaman kare dangi.

Rahoton tashar talabijin na BBC ta nuna cewa wata majiya ta sojojin Amurka ta karyata wannan labari, amma sun yarda da cewa sun yi amfani da gubar 'White Phosphorus' din a lokacin da suke yunkurin tarwatsa wadanda suke kira ’yan ta’adda.

Tashar talabijin din ta RAI ta watsa wannan shirin ne kwana daya bayan ziyarar da Shugaban kasar ta Iraki ya kawo zuwa kasar ta Italiya.

A farkon shirin, tashar talabijin din ta kawo wani takaitaccen bayani kan irin yadda sojojin na Amurka suka yi amfani da wasu nau’in makaman masu guba a lokacin yakin Vietnam.

Haka nan kuma a shirin an nuna gawawwakin wasu mutane a Fallujah sun kone kurmus, amma rigunan jikinsu na nan yadda suke, wanda ya kara tabbatar da cewa an yi amfani da guba ne wajen kashe su.

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


  | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International