Almizan:Taron sulhunta rikicin Izala ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 17 Shawwal, 1426                 Bugu na 692                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Babban Labarinmu

Taron sulhunta rikicin Izala

An tashi baram-baram

*Mun cimma matsaya
-Shaikh Dk. Ahmad Gumi
*Abdulkarim Dayyabu ya fasa kwai
Daga Musa M. Awwa da Aliyu Saleh

Ranar Juma’ar da ta gabata ne aka gudanar da gagarumin taron sulhunta rikicin da ya dabaibaiye kungiyar Jama’atu Izalatul Bidi’a wa ikamatus Sunnah, wanda Shaikh Dakta Ahmad Gumi ya kira, sai dai a wannan rana kam wannan kyakkyawar manufa ta Dakta din ba ta cimma manufa ba, domin an tashi taron ne baram-baram.


Kamar yadda Wakilanmu da suka kutsa cikin zauren taron da aka yi a asirce suka shaida mana, shugabannin Izala bangaren Jos dukkaninsu ba wanda ya halarci taron. Sannan kuma su ma na banagaren Kadunan ma wasunsu ba su halarci taron ba, da suka hada da Shaikh Yusuf Sambo Rigachikun da Imam Abubakar Ikara.

Wani abu da zai nuna cewa an tashi wannan taro baram-baram shi ne ganin yadda a wasu lokuta biyu a zaman taron aka nemi ba hammata iska a sakamakon wadansu kalamai da ba su yi wa wasu dadi ba, wanda hakan ya sa suka tashi domin nuna fushinsu.

Wakilan namu sun labarta mana cewa batu na farko da aka yi wanda bai yi wa wasu dadi ba shi ne; cewa a lokacin da Shugaban taro, tsohon Kwamishinan ’yan sanda, kuma tsohon Gwamnan tsohuwar jihar Sakkwato, Alhaji Usman Farouk yake jawabi, ya nuna takaicinsa ne, inda ya ce a lokacin da aka kafa Izala takan shiga kauyuka ne tana wa’azi don wayar wa da jama’a kai game da addinin Musulunci, amma sai ya ce da tafiya ta yi tafiya, sai Malaman suka bar kauyen suka dawo bariki suna wa’azin neman kudi.

Wannan kalami na Shugaban taron bai yi wa wasu da dama daga cikin mahalarta dadi ba, inda a nan take Shaikh Abubaker Gero Arugungu daga jihar Kebbi, ya mike cikin fushi yana nuna yatsa yana fadin “karya ne! Ba mu yarda ba!” Wasu kuma su ma suka mike suna mara masa baya, wanda hakan ya raba wurin biyu, ana ta hayaniya. Daga bisani shi kansa Shugaban taron ya ce, “to jama’a ku yi hakuri na tuba a kan wannan kalami nawa, na janye maganata, a yi hakuri.” Sannan da kyar aka lallashi Shaikh Gero Arugungun ya zauna.

Batu na biyu da ya yamutsa dakin taron shi ne, cikin jawaban da Dakta Gumi ya gabatar, shi ma akwai inda yake nuna cewa wajibi ne a rinka sanya shugabanni da dattijai a cikin wannan tafiya ta Izala don su rika tsawatawa, don gudun kada a sami wata matsala.

Ya nuna cewa masu nuna wai ba za a tafi da shugabannin ba, “ai misali idan Gwamnan jihar nan (Kaduna) ya ce daga yau kar wanda ya sake wa’azi, ai ba wanda ya isa ya yi.” Fadin wannan kalami nasa ke da wuya sai wasu suka mike suna furta, “wallahi karya ne! Ba wanda ya isa ya hana mu wa’azi! Ba mu yarda ba sam!” Wannan kalami da Dakta ya yi ya jawo hayaniya matuka. A nan ma dakin taron sai ya rabe biyu, wasu na goyon bayan kalaman Dakta, wasu kuma na inkarin su.

Akwai wani daga cikin masu goyon bayan Dakta Gumin da yake nunin yatsa ga wani yake ce masa, “kai ka ce ba wanda ya isa ya hana ka wa’azi, to a nan an taba hana mu ‘tahajjud’ da watan azumi. Ba na son cika baki, zauna kawai!”

Shi dai wannan taro an kira shi ne a babban masallacin Juma’a na Sultan Bello da ke Unguwar Sarki, Kaduna. Kuma sai aka raba abin zuwa gida biyu, wasu suna masallaci ana ta wa’azin muhimmancin hadin kai, wasu kuma, musamman shugabannin kungiyar ta Izala, an kebe su a dakin taro na Arewa House, inda nan ne aka tattauna batun hadin kan, ganin cewa ba zai yiwu a tattauna wannan abu a cikinta taron jama’a masu yawa ba.

Jama’ar wannan kungiya ta Izala da dama sun taru, domin Wakilanmu da suka halarci wannan taron sun shaida mana cewa masallacin ya cika makil ciki da waje har da kan titi. Kuma dakin taron ma duk da cewa zaben wadanda za su shiga aka yi, shi ma ya cika makil, sai ma da aka rufe kofa saboda babu masaka tsinke.

Don ganin cewa an yi wannan abu a gaban idanun, Wakilan namu, sun rabu biyu ne, wasu suka tsaya a masallaci, wasu kuma suka shiga tawagar manema labarai suka shiga dakin taron.

A dakin taron, Janar Muhammad Buhari yana daga cikin manyan bakin da suka amsa kiran. Sannan kuma akwai Tsohon Gwamnan jihar Sakkwato, Alhaji Usman Farouk, wanda yake ma shi ne shugaban taron. Akwai kuma Shugaban tafiyar, Dakta Gumi. Da wakilan Sarakunan, Kano, Zariya da na Sakkwato.

Da yake gabatar da jawabinsa, madugun tafiyar, Dakta Ahamd Gumi, ya bayyana cewa hadafin wannan taro shi ne a taru a hada wannan kungiya a dinke barakar da ke tsakaninta ta koma kamar yadda aka kafa ta tun asali. “Haduwar wannan kungiya da haduwar Musulmi gaba daya wajibi ne a kanmu,” in ji Daktan.

Dakta Gumi ya ci gaba da cewa kowane musulmi ya sani cewa za a tambaye shi a ranar lahira kan cewa wane yunkuri ya yi domin ganin an hada kan musulmi masu fada da juna?

Sannan kuma ya yi zargin cewa babbar matsalar Izala a iya fahimtarsa, matsala ce ta shugabanci, don haka ne yake ganin cewa kamata ya yi a rushe duk shugabannin bagarorin a kafa kwamitin Shura wanda zai sasanta tsakani, sannan ya fitar da shugannin wadanda kowa zai amince da su. Ya meni mabiya da su bijire wa duk wani Shugaban da ya ki yarda a hada kai da shi.

Ya kuma yi nuni da cewa wajibi ne kowane dan Izala ya gane cewa Izala ba ta wani mutum daya bace, Izala ta kowa da kowa ce, “ni ba na son in ji ana jingina Izala da wani mutum. Izala ta al’uumar musulmi ce,” Daktan ya jaddada.

Da yake bayani game da irin nasarar da taron da ya kira ya samu, Dakta Ahmad Gumi cewa ya yi; “an sami nasara, domin kuwa jama’ar da aka gayyato zuwa taron sun amsa kira. Duk wanda yake tare da mu a nan zauren da zagaye da cikin masallacin, suna tare da mu a wannan yunkuri na alheri, wato na hada kai wuri daya.”

Shi kuwa Shaikh Alhasan Sa’idu Jos, a cikin jawabansa matukar goyon bayansa ya nuna ga wannan yunkuri na hade kungiyar ta Izala, sai dai ya nuna cewa akwai gyara a tafiyar. Ya nuna cewa kamata ya yi a ce an kira wani zama ne na musamman. A kira shugabannin bangarorin biyu a fara zama da su, amma ba wai babban taro irin wannan ne za a ce za a sulhunta ba. Ya ce ba za a taba samun nasara ta hanyar kiran taron mutane irin wannan ba.

Shaikh Alhasan Jos ya ci gaba da cewa shi yana daya daga cikin wadanda aka kafa wannan kungiya da shi, “duk a dakin taron nan ba wanda ya girme ni a Izala. Da ni aka soma tunanin kafa Izala. Ban ce ilimi ko shekaru, kudi, ko wani abu ba, amma dadewa a Izala, duk dakin taron nan ba wanda ya girme ni,” Shehin Malamin ya tabbatar.

Shehin ya kuma yabi Izalar da cewa a duk fadin kasar na babu wata kungiyar Musulunci mai taimaka wa addini irin Izala. A nan ne ya bayyana cewa Jama’atu Nasril Islam sam ba ta, domin ba ta taimakon addini. Ya ce ba ta gina masallatai, ba ta gina makarantu da dai sauransu.

Sultan na Sakkwato ne, Alhaji Muhammad Maccido aka shirya zai halarci wannan taro, amma bai sami zuwa ba, sai ya wakilta Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris, wanda shi ma bai sami halarta ba, sai ya turo Salanken Zazzau, Alhaji Dakta Bello Abdulkadir, wanda shi ma a cikin jawabin nasa ya nuna goyon bayansa ga masu neman a dage wannan taron a nada kwamiti na musamman wanda zai shiga tsakani ya sasanta, inda ya nuna cewa ba za a taba samun nasarar sulhuntawa a taron jama’a mai yawa irin wannan ba.

Da yake zantawa da ALMIZAN bayan an tashi daga taron, Dakta Ahmad Gumi, ya tabbatar da cewa duk da wasu suna ganin kamar taron bai yi nasara ba, amma an samu gagarumar nasara, kuma ya cimma matsaya kamar yadda ya kamata.

Dakta Ahmad Gumi, wanda yake magana ta bakin mai magana da yawunsa, Shaikh Husaini Zakariyya, ya ce, ana kafa wani kakkarfan kwamiti karkashin jagorancin Sarkin Dutse, Alhaji Sunusi don ganin ya samar da hanyar da za a bi don ganin an hada kan ’ya’yan kungiyar waje daya da kuma warware matsalar da ake fuskanta.

“Wadannan fitattun Malaman, za su yi aiki na wata uku zuwa shida, inda za su zauna da shugabannin bangarorin biyu, kowa ya bayar da shawarar yadda za a gyara al’amura. Sannan daga baya sai a kafa kwamitin da zai shirya zaben sabbin shugabanin kungiyar,” in ji shi.

Ya ce shi a ganinsa duk bangarorin da suke rikici da juna sun samu halartar taron, kuma shi ba shi da wani bayanin akwai wani bagare ba bai je taron ba. Ya ce wadanda ma ba su halarta ba ya ba su uzurin cewa sun yi tafiya zuwa Umura ne ba su dawo a kan lokaci ba.

Tun da farko, Dakta Ahmad Gumi, ya bayyana irin fadi-tashin da ya kwashe sama da shekara daya yana yi don ganin ya hada hancin ’ya’yan kungiyar waje daya.

Shi kuwa da muke zantawa da shi bayan kammala taron, Alhaji Abdulkarim Dayyabu, bayyana irin manakisar da wasu suka shirya ne don raba kan kungiyar.

Ya ce akwai wani littafi da wani Baturen Amurka, Ousmane Kane ya rubuta bayana ya kwashe wata cur yana bincike a Nijeriya, a ciki ya bayyana filla-fillar yadda gwamnatin Babangida ta yi amfani da kudi da kuma wasu mutane da suka shigo Izalar suka raba kan kungiyar don dai ta cimma manufarta na wancan lokacin.

Alhaji Abdulkarin Dayabu, wanda shi ne Shugaban Rundunar Adalci, kuma Shugaban jam’iyyar AD, kana kuma tsohon Shugaban Izala na farko a jihar Kano, ya fayyace mana komai a kan abin da ya kawo darewar kungiyar gida biyu har ta kai suna kafirta juna.

Alhaji Abdulkarim Dayyabu, wanda ya fadi irin rawarar da gwamnatin Babangida ta taka wajen kawo rikici da rabuwar kungiyar Izala gidan biyu, ya fayyace komai a kan abin da yake jin shi ne zai iya hada kan ’ya’yan kungiyar waje daya. Za mu zo da cikakkiyar hira nan gaba kadan insha Allah.

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


  | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International