Almizan :Filin Tambaya da Amsa ya dawo ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 17 Shawwal, 1426                 Bugu na 692                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Babban Labarinmu


Wajibi ne mace in za ta fito tsakar gida a gidan haya sai ta sa hijabi?

SHAIKH ZAKZAKY
Malam Ibraheem Yaqoub Zakzaky H.
Ya na amsa tambayoyinku

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malam, menene bambanci tsakanin giba da gulma, kuma wannene ya fi girman laifi a tsakaninsu?

Daga Ahmad Sa’idu Hizbullah Potiskum 0803 619 4123

SHAIKH ZAKZAKY: Giba dai dama kalmar Larabci ce, gulma kuma kalmar Hausa. Kuma da yake da Hausa dai mukan yi amfani da wannan kalmar ta giba, shi ya sa ta zama, in an ce giba, ana iya fahimtar abin da ake nufi. Gulma tana iya zama wani nau’i ne na giba, tunda galiba abin da ake nufi da gulma shi ne mutane su zauna wani ya rinka kawo labarin wani. Wala’alla a cikin wannan labarin akwai bata sunansa, don abin da giba take nufi kenan, yi da wani. A fadi wani abu dangane da wani mutum wanda zai iya zama aibi ne gare shi, wannan abin kuwa ko da gaskiya ne. Domin an ce ma in ma ba gaskiya bane ya fi giba kenan tsanani. Saboda haka a takaice wadannan kalmomi ne wadanda suna iya ma’anar abu guda; yi da wani, illa iyaka.

TAMBAYA: Akwai masu cewa in mutum ya yi giban wani, to sai ya same shi ya roke shi gafara sannan Allah zai yafe masa. Menene gaskiyar wannan batu?

SHAIKH ZAKZAKY: Akalla ita dai giba haramun ce. Kuma idan ka yi wa mutum giba, bacin ga shi ka aikata haram kana da laifi, to shi kuma ka taba mutuncinsa. Saboda haka wajen neman mafita, shi ne ka roki Allah ya yafe maka, kuma Ya maye masa gurbi wannan mutumin wanda yake ya sani ko bai sani ba, ka tuna ko baka tuna ba, yana nan da rai ko ba shi da rai. Kamar yadda ya zo a cikin addu’a ma’athur, Imam Zainul Abidin, yana cewa wani mutum da yake da wani hakki nasa a kaina ta hanyar taban mutuncinsa ko dukiyarsa ko abin da ya yi kama da haka nan, ko giba da na yi masa, ko na karkata ya zuwa gare shi da son rai, ko wani abu mai kama da haka nan. Ina rokon ka ya Rabbi ka biya shi da abin da za ka yarje masa, ni kuma kar ya zama ka rage wani abu na laifin da za ka cire mani na laifuffukana gobe kiyama. Ka ga wannan daga cikin ma’athuri muna iya cewa ana iya neman gafara na yi wa wani giba daga wajen Allah, don a wajen Allah akwai isasshen abin da zai iya biyan wadanda hakkokinsu ne. Amma ba a ce mana tilashin mutum ne sai ya je ya nemi gafara wajen wanda ya yi masa ba.

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malam, ina hukuncin yin salla da riga wacce ke dauke da hoton wani azzalumi, ko kuma wani fasiki?

Daga Ali M. Abdullahi Al-Sistani Fatimiyya PMS Potiskum jihar Yobe

SHAIKH ZAKZAKY: To ba dai zai shafi salla din ba. Idan ita sutura din ta suturce al’aurarsa kuma mai tsarki ce. Illa iyaka dai a wani babin daban, sa wannan rigar bai dace ba, ganin cewa yana tallata wannan fasikin ne ko Azzalumin.

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Allah Ya gafarta Malam, ina hukuncin jinin da yake fitowa bayan an yi wa mace wankin ciki?

Daga Alhaji Muhammad Ali Kademi 0803 599 7310

SHAIKH ZAKZAKY: Wannan shi tamkar jini ne na ciwo kenan, ba shi da hukuncin jinin haila, tunda tabbas an riga an san cewa ba jinin haila bane, jini ne na ciwo. Saboda haka ba wani abin da ya hau kanta kamar abin da ya hau mai jinin haila. Illa iyaka za ta tare jinin daga fita, kuma za ta yi alwala da sallarta da komai da komai.

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malam, idan mace tana da ciki kuma ya tsufa ya rage mata saura kwanaki kadan ta haihu, sai take ganin wani ruwa fari yana fito mata daga farjinta, daga baya sai ta haihu, ya matsayin sallolinta kenan a wannan halin da ruwan yake fitowa?

Daga Salisu Salihu Sakkwato mazaunin Akure.

SHAIKH ZAKZAKY: Tun da yake jinin haila ne yake hana salla, wannan kuma abin da ya fito mata ba sunansa jini bane. Kuma ga shi nan an ce masa ma farin ruwa, ba zai hana salla ba.

TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam ina matsayin azumin kwana shida na watan Shawwal?

SHAIKH ZAKZAKY: Lallai ana iya yi. Akwai ruwayar haka nan. Wanda ya yi azumin Ramadana ya bi shi da kwana shida a cikin Shawwal, ya zama tamkar wanda ya azumci shekara. Kuma ba lallai bane sai a jere za a yi su ba, sai dai ya fi kyau haka nan. Amma dai duk kwana shidan da ka samu a cikin Shawwal ya wadatar.

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Allah Ya gafarta Malam, zan iya bin Limamin da yake yawan bata karatun salla?

Daga Abu Summaya Sakkwato

SHAIKH ZAKZAKY: Mutumin da ya bi Limamin da bai iya karatu ba, in shi ya iya, idan abin ya shafi abin da ya zama salla ba za ta inganta ba sai da wannan, kamar kira’a din Fatiha ko surah, to zai zama wajibinsa ya sake salla din, amma ba a ce kada ya bi shi ba.

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malam, ya halatta mutum ya bar matarsa ta yi karatu a manyan Kwalejoji da Jam’o’in wannan kasa, musamman idan aka yi la’akari da halin da kasar nan ke ciki. Akwai shawarar da Malam zai ba ni game da haka?

Daga Sunusi Sakkwato

SHAIKH ZAKZAKY: Ba abin da ya hana mace ta yi karatu a jami’o’in kasar nan. Illa iyaka dole ita ta lizimtu da abin da yake ka’idodi na addini, ta kame kanta, ta sa cikakken hijabi. Kuma kar ta yi wasanni da mutane, abokanin karatunta ne ko da Malamanta wadanda za su dauka kamar ita ma sauran dalibai ne wadanda suka saba da irin wadannan wasannin.

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malam, mutum ne ya saki matarsa da ciki, shin wajibi ne ya dauki nauyinta kamar ciyarwa da sauransu?

Daga Ibrahim Zubairu jihar Kano.

SHAIKH ZAKZAKY: In ta haihu ne aka ce. Na farko dai in ya sake ta da ciki, tana idda ne, saboda haka tana matsayin matarsa ne. In kuma ta haihu zai dauki dawainiyar yaron har ya zuwa shayar da shi. Saboda haka za mu dauka in ya sake ta dama tilashinsa ne ya dauki dawainiyarta saboda tana da ciki har sai ta haife a matsayinta da cewa a wurinmu ita matarsa ce. Allahumma sai dai idan ya zamana sakin ba’ini ne, haihuwarta ne ya hau kansa. In ta haihu ne alhakin dan ya hau kansa.

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malam, mune muna cikin yin salla ta jam’i, sai bayan mun kusa gama sallar, sai muka ankara da Limamin bai cancanci limanci ba saboda dalilai na shari’a. Ya za mu yi kenan? Za mu yanke sallar ne, ko kuwa za mu gama ne, sannan mu sake wata sabuwa?

Daga Tukur Rufa’i No 10 Zainab House Layin Tanki Gambaga Kasuwar Kantin Kwari jihar Kano

SHAIKH ZAKZAKY: Duk da yake shi bai yi bayanin wane dalili ne ya hana Limamin zama Limam ta fuskacin shari’a ba. Amma ina fata ya riga ya san abin da yake hana wa Liman zama Liman ta fuskacin shari’a din. Da mu kaddara misali, Limamin ba musulmi ne ba, ka ga dama ba salla tun asali. Kuma da za mu kaddara misali, ba baligi ne ba, misali. To da za mu kaddara shi kenan mutum sai kammala salla din sannan sai ya sake. Ina fata dai shi ya san me ke hana mutum zama Liman a shari’a din.

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Allah Ya gafarta Malam, idan mutum ya bar aiki sai kuma aka ba shi kudadensa na sallama, idan sun kai nisabin zakka zai iya fitar masu da zakka kenan?

Daga Ibrahim Teacher Funtuwa

SHAIKH ZAKZAKY: A’a ai ba a ce da zarar kudi sun zo hannunka in ya kai nisabi sai ka ba da zakka ba, an ce sai ya zama mallakinka har cikakken shekara. Saboda haka ba zai yiwu ya ba da zakka nan take ba, sai dai in ya ajiye kudin har sun shekara a hannunsa kammalallen mulki, cikakkiyar shekara.

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malam, idan muna zaune a gidan haya, wajibi ne matata in za ta fito tsakar gida, ko da za ta zauna da sauran mata ne, sai ta sa hijabi?

Daga Muhammad Mai Kananzir Kafin Hausa jihar Jigawa

SHAIKH ZAKZAKY: To in dai har zai yiwu wanda ba muharraminta ba ya gan ta, zai zama haka din.

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malam, ni matafiyi ne, a cikin jakata akwai Alkur’ani, sai fitsari ko bayan gari ya kama ni, sai na yi, amma ban samu ruwan da zan yi tsarki ba. Idan na dauki jakar tawa ban yi tsarki ba, ba komai? Ko kuma zan iya karanta wata aya a cikin Alkur’ani a irin wannan halin na rashin tsarkin da nake ciki?

Daga Yakubu Sulaiman Mai Hoto Tudun Wada Funtuwa jihar Katsina

SHAIKH ZAKZAKY: Daukar jaka dai da Alku’ani a ciki, babu alwala, babu laifi; saboda yanzu jaka kake dauke da ita ba Alkur’ani ba, haka zalika ma shi kansa daukar Alkur’anin. Abin da muka san ya haramta shi ne taban rubutun Alkur’anin. Saboda haka mutum zai iya karanta Alkur’ani da ka, kuma zai iya taban bango, kodayake ta fuskacin ‘Ihtiyadi’ ana cewa ya kiyayi taban bangon ma saboda girmama shi ko da da bai haramta. Kamar yadda na fadi, kaya sunansa kaya ko da akwai Alkur’ani a ciki. Sannan kuma karatu in da ka ne zai iya yi, amma in zai lizamta ma sa taban rubutu, to shi ne ba zai yi ba.

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malam, wasu suna cewa wai idan mutum ya zubar da ciki wanda yake bai kai wata hudu ba, wai ba shi da laifin komai, kuma wai bai yi kisan kai ba. Suna kafa hujja da hadisin Manzon Allah (SAWA) da yake cewa: “Lalle dayanku ana tara halittarsa ne a cikin mahaifiyarsa kwana 40….” Har ya zuwa karshen hadisin. Malam haka abin yake?

Daga Bala Hasan Gidan Galadima Wunti Dada Jihar Bauci Nijeriya

SHAIKH ZAKZAKY: Zubar da ciki ba zai halatta ba shar’an da mujarradin cewa dan tayi bai kai wata hudu ba, sai dai in da wani dalili da ya sabbaba zubar da ciki din, alal misali kamar ya tabbata daga binciken masana cewa ba zai yiwu ta rayu ba in har cikin ya girma ya kai mikidarin haihuwa, to sai ya zama zabi ne ake da shi tsakanin tayi din da ita. Amma idan har ta zubar, to zai zama hukuncin kisa ne kawai bayan ya kai wata hudu. Amma ba yana nufin ya halatta ne kafin wata hudun ba.

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malam, mutum ne ya auri Bazawara sai ta zo da ’ya, to dan wannan mutumin zai iya aurenta?

Daga Ahmad Tijjani Sa’idu Sakafa Gashuwa Sabon Garin ’Yan Sadin jihar Yobe

SHAIKH ZAKZAKY: Eh zai iya.

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malam, mutum ne zai yi tafiya neman kudi kuma zai kwashe akalla makonni uku, sai ya bar wa matarsa abincin da zai ishe ta ci na tsawon wannan lokacin, ya halatta ya yi tafiya shi kadai ko kuwa sai dole da matar tasa?

Malam Yusuf Ladan Sabuwar kasa jihar Katsina

SHAIKH ZAKZAKY: Lallai ba inda aka ce dole mutum ya yi tafiya da matarsa. Illa iyaka dai akwai abin da ake ce ma wa’adi na ila’i, wata hudu wanda ake ce wa akalla mutum ya kasance tare da matarsa akalla sau daya a tsawon wannan lokaci na wata hudu. Saboda idan ma tafiya ya yi ya je wani wuri, in dai yana iya makanuwa ya zo, akalla duk wata hudu sai ya zo wajenta.

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malam, mutum zai iya sa hotunan Imamai ko karatun Alkur’ani a cikin wayarsa, musamman da yake wata rana zai iya mantawa ya shiga makewayi da wayar?

Ba suna.

SHAIKH ZAKZAKY: In dai shiga makewayi ne, tunda ba rubutun ne aka fito da shi balo-balo ko hotuna aka fito da su balo-balo ba, suna rufe ne a cikin wani abu, bai zama an shiga da su ba. In haka nan ne da sai a ce har da shi ma ba zai shiga makewayi ba kenan tunda yake akwai Alkur’ani a kansa. Amma kamar sa shi a waya da irin abin da ya yi kama da haka nan, in akwai abin da za a iya dauka kamar rashin girmamawa, to abin da ya fi alheri shi ne a girmama Alkur’ani din. Alal misali kamar an sa shi a inda za ka saurara kafin a kira maka wani, wasu maimakon kida din mai yiwuwa mutum ya ce bari ya sa Alkur’ani. In ya san masu bugo masa waya mutanene da za su saurari Alkur’anin kuma ya amfane su, ba laifi da wannan. Amma in kowane irin mutum zai saurara har ma ko ya yi wata magana ko kuma abin da ya yi kama da haka nan, to sai ya sa wani abu, maimakon kida, sai ya wani abinda yake da amfani, in ya ga babu girmama Alkur’ani a ciki. A takaice abin da nake cewa shi ne dole inda za ka sa Alkur’ani, ya zama akwai girmamawa. Amma yana cikin kwakwalwar kwamfuta ta hannu ko ta aljihu ko wane iri ne, wannan bai zama daidai da rubutunsa ba.

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Mutum zai iya yin azumi ya ce ya sadaukar da ladan ga Fadimah (AS) ko wani Imami, musamman a lokacin Maulidinsu?

Daga Kabiru Abba Funtuwa mazaunin Wuse Abuja 08036116512

A biyo mu mako na gaba don jin amsar wannan tambaya da ma wasu insha Allahu

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


  | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International