Jarida don Karuwar Musulmi
Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki ISSN 1595-4471
Juma'a 17 Shawwal, 1426
Bugu na 692
Tunatarwa | | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari Tattaunawa | Labarai |
|
|
Shaikh Ibraheem Yaqoub Zakzaky ya gabatar da wani jawabi a karshen taron karawa juna ilmi na tsawon kwanaki biyu da Dandalin Ma’aikata (Resourse Forum) ta gabatar daga ranakun 4-6 ga watan Nuwamba na wannan shekara FIC Zariya.
A lokacin da yake gabatar da jawabinsa, Shaikh Ibraheem Zakzaky ya bayyana yadda ya kamata a yi amfani da kudaden da ake tarawa na Harkar Musulunci, inda ya nuna cewa kungiyoyi a halin yanzu suna gudanar da ayyukansu ne ta hanyar tattara gudummuwa daga ’ya’yan kungiyoyin nasu, wadanda a mafi yawan lokuta ma'aikatan gwamnati ne.
Sannan sai Shaikh Zakzaky ya nuna cewa a halin da wannan kasa ke ciki a yanzu, mafi yawan ma’aikata ba wani abin kirki suke samu ba a kowane wata a matsayin albashinsu, wadansu lokutan ma sukan share watanni ba a yi albashi ba, sannan su kansu ba sa iya rike lalurarsu zuwa wata daya kamili da albashin nasu.
Haka nan Shaikh Zakzaky ya bayyana cewa wadanda suke rike da kudi a kasar sune ’yan siyasa wadanda ba zai yiwu a iya samun wani abu daga gare su ba. Saboda haka, sai ya ce, ya wajaba mu da kanmu mu samar da yanayi na shigar kudade don aiwatar da ayyukanmu na yau da kullum.
A wani bangare na jawabin nasa, Shaikh Zakzaky ya bayyana shirin Harkar na fito da wata tashar talbijin da rediyo wadanda za a rika watsa su ta hanyar tauraron dan Adam.
Haka kuma ya nuna muhimmanci samar da wata jarida ta harshen Turanci wadda za ta rika kai wa sassan da ba sa jin harshen Hausa a kasar nan. Sannan kuma ya nuna cewa yanzu haka dai za a fara nazarin farko na aiwatar da shirin ta hanyar tuntubar kwararru kan abubuwan bukata don cimma wannan buri.
Shaikh Ibraheem Zakzaky, ya bayyana takaicinsa kan yadda wasu tashoshi ke watsa abin da suka ga dama da sunan mahanga ta addini, sannan ya nuna lalurar Harkar Musulunci ta sami kafa tata tashar wadda za ta rika fadin nata mahangar.
Daga karshe Shaikh Ibrheem Zakzaky shi ne ya rufe taron da addu’a.
| Tafsirin Alkur'ani | Hadisai | Crescent International |