Almizan :Yadda aka aukawa 'Yan uwa na Maradi a muzaharar Kudus ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 17 Shawwal, 1426                 Bugu na 692                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Babban Labarinmu

Yadda aka aukawa 'Yan uwa na Maradi a muzaharar Kudus

a

Yayin da aka kammala kusan duk muzaharar da ’yan uwa musulmi karkashin jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) suka shirya a kusan duk fadin Nijeriya a Juma’ar karshe ta watan Ramadan lami lafiya, sai ga shi jami’an tsaro sun yi amfani da karfi wajen tarwatsa masu muzaharar ta lumana a garin Maradi na Jamhuriyyar Nijar.

Kodayake bayanan da muke da su game da abin da ya faru a garin na Maradi sun karanta, amma mun samu rahoton cewa an ji wa da dama daga cikin ’yan uwan da suka fito domin nuna goyon baya ga Palastinawa, da kuma yin Allah wadai da ta’addacin da Yahudawa suke yi wa musulmi, rauni, an kuma kame wasu daga cikinsu.

’Yan uwan da suke muzaharar, wadanda suka hada da maza da mata yara da manya, sun ci karo da jami’an tsaro ne dauke da makamai suna cikin tafiya, ba tare da kuma wata-wata ba, sai suka far masu, inda suka yi awon gaba da su bayan sun ji wa da dama rauni a nan take.

A lokacin da suke muzaharar ta Kudus, wacce ba ita ce ta farko da suka yi a garin na Maradi ba, ’yan uwan sun rika rera taken nuna goyon bayansu ga Palastinawa, tare da yin kira ga kasashen duniya su yi wa Palastinawan da haramtacciyar kasar Isra’ila take zalunta adalci ta hanyar lura da lamarinsu bayan sun yi tir da Yahudawa da Yahudancin duniya.

Masu muzaharar sun fito karara sun goyi bayan kalaman da Shugaban Iran, Dakta Ahmadinajadi ya yi na cewa ya wajaba a share haramtacciyar kasar Isra’ila daga doron kasa.

Da dama dai a baya an sha auka wa ’yan uwa a wannan yankin idan suna yin wasu tarurrukansu wanda suka saba farawa da gamawa lafiya, bare da wani tashin hankali ba.

Wasu mutane sun yi zargin cewa wasu da suke kiran kansu “manyan gari” ne ba su son abin da ’yan uwa suke yi, ga zatonsu abin da ’yan uwan suke yi kamar cikas ne ga hanyar neman abincinsu.

A kowace shekara dai ’yan uwa na Harkar Musulunci a Nijeriya da Nijar suna gudanar da irin wannan taro na ‘Ranar Kudus’ don amsa kiran Marigayi Imam Khumaini (RA) wanda ya ba da umurnin mayar da ranar Jumu’ar karshe ta watan Ramadan mai alfarma ta zama ranar nuna goyon baya ga al’ummar Palastinu.

A kasashen musulmi daban-daban ma dai a wannan Jumu’ar an gudanar da taron ‘Ranar Kudus,’ ciki kuwa har da Lebanon, Siriya, Pakistan da dai sauran su.

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


  | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International