Jarida don Karuwar Musulmi
Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki ISSN 1595-4471
Juma'a 17 Shawwal, 1426
Bugu na 692
Tunatarwa | | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari Tattaunawa | Labarai |
Zabubbukan PDP:Zabe ko nadi?
A makwannin baya ne aka gudanar da zabubbukan jam段yyar PDP a matakan mazabu, Kananan Hukumomi, Jihohi da shiyyoyi. Sai dai wasu mambobin Jam段yyar sun yi zargin cewa ba zabe aka yi ba, nadi kawai aka yi, domin su, a cewarsu, ba a yi masu adalci ba. A zaben da aka gudanar na jihar Kaduna, Alhaji Sulaiman Hunkuyi, wanda shi ne ya jagoranci zaben da aka gudanar na mazabu da Kananan Hukumomin jihar, wanda kuma duk wadanda suke kan mukamansu ne suka koma, ya tabbatar da cewa an yi abin da ya dace ne. A zaben da aka gabatar na shugabannin jam段yyar jihar ta Kaduna, Sanata Isiah Balat ne ya gabatar da shawarar cewa shi yana ganin cewa ya kamata duk wadanda suke kan mukamansu na jihar su koma kan matsayinsu saboda yadda aka gamsu da yadda suka gabatar da mulkinsu. Kuma Mista Garba Madaki Ali ya mara masa baya. Nan take kuma aka nemi jin ra誕yin jama誕, kowa kuma ya amince da shawarar. Haka dai zaben ya gudana, inda Alhaji Audi Yaro Makama Rigachikun da tawagarsa suka sake komawa kan karagarsa na Shugaban PDP jihar Kaduna. A taron jam段yyar na shiyyar Arewa maso yamma sake zaben dukkanin Shugabannin jam段yyar da suka fito daga shiyyar a karkashin Dokta Bello Halliru Muhammad ba tare da hamayya ba. Sauran wadanda aka zaba sune Alhaji Baba Lawal Aliyu a matsayin Sakatare. Sai Alhaji Aminu Korau Machika a matsayin Ma誕ji, da Alhaji Balarabe a matsayin Sakataren shirye-shirye, da Alhaji Sa段du Usman Bukuyum a matsayin mai bayar da shawara a fannin shari誕. Haka kuma akwai Husaini Dembo a matsayin jami段n hulda da jama誕, (PRO) wanda ya canji Dokta Damina, wanda shi kuma aka nada shi sabon Sarkin Kurama. Sai Nasiru Muhammad Gumel, mai binciken kudi. Sai Hajiya Hadiza Ado Yusuf a matsayin Shugabar mata da Sanusi Tukur, Shugaban matasa. Shugaban gudanar da zaben, Sanata Walid Jibrin, wanda har ila yau shi ne Sakataren babban taro da tarurrukan jam段yyar na kasa, ya ce, jami誕n jam段yyar da aka sake zaba sun cancanci karramawa, in aka lura da yadda suke tafiyar da jam段yyar a shiyyar. Ya kuma nuna gamsuwa kan yadda aka gudanar da zaben lami lafiya. Da yake tofa albarkacin bakinsa wajen taron, Gwamnan jihar Katsina, Alhaji Umaru Musa 炭ar誕duwa ya yaba da azamar Gwamnonin PDP da ke shiyyar ce na sake farfado da ita ta yadda za ta kafa gwamnatoci a jihohin da ba ta mulki a halin yanzu. Ya roki Allah ya taimake su wajen cimma wannan manufa, sannan ya nemi shugabannin jam段yyar su tabbatar suna aiki da tsarin mulkin jam段yyar. Da yake jawabin godiya, Shugaban jam段yyar, Dakta Bello Halliru, ya ce, sababbin shugabannin jam段yyar za su yi aiki bil hakki don bunkasa jam段yyar a shiyyar. Ya ce, 的na tabbatar muku da cewa kun zabi nagari, kuma za mu sadaukar da kanmu wajen yin duk abin da zai bunkasa wannan jam段yya a shiryyar Arewa maso yamma. Gwamnonin jihohin Kaduna da Katsina da Ministan tsaro, Dakta Rabi置 Musa Kwankwaso da tsohon Ministan harkokin kasashen waje, Alhaji Sule Lamido na daga cikin wadanda suka halarci taron.
|