Almizan :Obasanjo ya kama hanyar Abacha ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 8 Zulkidah, 1426                 Bugu na 695                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Babban Labarinmu

Obasanjo ya kama hanyar Abacha

* Wai mataimakinsa na shirya masa juyin-mulki

* An kame dogarin Atiku

An dakatar da wani kamfanin mai na Atiku

Ina jin tsoron tsaron lafiyata

Rahotanni na nuni da cewa wani na hannun daman Mataimakin Shugaban kasar Nijeriya, Alhaji Atiku Abubakar, ya bayyana cewa akwai wani yunkuri da ake yi na kame shi, sannan a gabatar da shi a gaban kotu kan tuhumar cin amanar kasa.


.

Shi dai wannan na hannun daman Mataimakin Shugaban kasar ta Nijeriya, wanda ya nemi manema labarai da su sakaya sunansa, ya kara da nuna cewa masu neman Shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya zarce a wa’adi na uku ne ke cikin wannan shirin.

Haka nan ya tabbatar da cewa daga cikin cajin da ake son a yafa masa; akwai cewa yana yunkurin juyin mulki ta yadda zai ba da dama a yanke masa hukuncin kisa don kada ya kawo wa Obasanjo cikas a lokacin zabe na shekara ta 2007.

Amma kamar yadda rahoton jaridar DAILY TRUST da ake bugawa da harshen Turanci ya nuna, bayan an tuntubi Mista Femi Fani-Kayode, wani mai bai wa Obasanjo shawara kan lamarin kafofin watsa labarai, sai ya kore zancen, sannan ya nuna cewa wannan duk soki burutsu ne kawai.

Ana cikin haka ne kuma a ranar Litinin da ta gabata sai ga sanarwa da sa hannun shi Atiku tana cewa “Hankalina ya kai ga wasu takardu da ke yawo a kasar nan kan wani shiri da aka yi na jefa ni da wasu na kusa da ni cikin wasu munanan ayyukan girgiza kasa, wadanda sakamakonsu ba karami bane ga zaman lafiyar kasarmu da tsaron lafiyar ni kaina.”

Sannan Alh. Atiku ya jaddada imaninsa ga tsarin dimokradiyyar kasar nan, yana mai goranta cewa shi ne ma ya bankado wani shirin juyin mulki da wasu suka yi, har kuma ake tuhumar su yanzu haka a gaban kotu. Don haka ya bukaci da a yi watsi da duk wani da ke son shafa masa kashin kaji kan irin wannan aiki.

Daga nan ya ce, “zan yi amani da wannan dama don in mai da martani kan hasashen da ake yi kan ci gaba da taka rawar da nake takawa a wannan gwamnatin. A shirye nake na kammala wa’adin ofishina kamar yadda jama’ar Nijeirya suka ba ni lokacin da suka sake zaben Shugaba Olusegun Obasanjo da ni kaina a 2003, duk da hasashen da ake yi na murabus dina.”

A wani labarin kuma, jami’an tsaron kasa na SSS suna tsare da dogarin Mataimakin Shugaban kasa, wato ADC, CSP Abdul Yari, bisa zargin yana da hannu kan ayyukan kungiyoyin da ke goyon bayan Alh. Atiku Abubakar irin su Turaki Vanguard.

Amma kuma wata majiya ta ce an kama shi ne saboda irin rawar da ake zargin ya taka wajen kubutar Gwamnan Bayelsa daga hannun ’yan sandan London zuwa gida.

Wannan dakatawar ita ce ta takwas da aka yi wa masu taimaka wa Alh. Atiku Abubakar. Sauran bakwan sune: Dk. Adeolu Akande (Agustan 2003), Farfesa Sam Oyovbaire da Malam Garba Shehu (Disamban 2003), Onukaba Adinoyi Ojo (Afrilun 2005), Janar Ja’afaru Isa, Chris Mammah da Shima Ayati (Yulin 2003).

Har ila yau a wani mataki da ake ganin na ci gaba da rage fuka-fukan daukakar Atiku a siyasance, gwamnatin Tarayya ta dakatar da wani kamfanin jigilar jiragen ruwa mai suna Intel Shipping Company da aka ce mallakin Mataimakin Shugaban kasar ne.

Kodayake ba wata sanarwar gwamnati kan wannan mataki, amma mai magana da yawun Hukumar tashoshin jiragen ruwan kasar nan, Mista Christopher Borha ya ce gwamnati ba ta sanar da su a rubuce ba kan wannan mataki, don haka ba zai iya cewa komai a kai ba.

Kamar dai yadda aka sani ne a halin da ake ciki yanzu a Nijeriya, akwai musayar yawu mai yawa tsakanin jami’an kasar kan amincewa ko rashinsa kan aiwatar da wata kwaskwarima kan tsarin mulkin kasar, wanda zai ba da dama ga Shugaban kasar mai ci yanzu ya zarce a karo na uku.

Sai dai ta bangaren talakawan kasar wadanda sune suka fi yawa, tuni sun dawo daga rakiyar mahukunta, domin kuwa sun dade suna jin gafara sa, amma ba su ga kaho ba.

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


  | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International  | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International