Almizan :Muna bin sawun duk ayyukan da muka bayar ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 8 Zulkidah, 1426                 Bugu na 693                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Tattaunawa

Muna bin sawun duk ayyukan da muka bayar

In ji Gwamna Ibrahim Shekarau


Daga Aliyu Saleh

Mai karatu ga ci gaban hirar da tawagar editocin Leadership, Weekly Trust da Almizan suka yi da Gwamna Shekarau na jihar Kano. Dakta Mahdi Shehu ne ya shirya shirin, ya kuma gabatar aka watsa ta gidajen rediyo da talabijin mallakin jihar.

EDITOCI: Akwai masu zargin Shugaba Obasanjo da yawan tafiye-tafiye zuwa kasashen waje alhali ba wani riba da za a ce ga shi a kasa, to kai ma ka yi wasu tafiye-tafiye, ko menene mutanen jihar Kano suka amfana daga wadannan tafiye-tafiye naka?

GWAMNA SHEKARAU: Ina ga kafin in fadi me aka samo za mu kalli tafiye-tafiyen nan, ina aka je, guda nawa ne, me aka je yi? Sannan sai a lalubi wace riba ce ta biyo baya? Domin sai an san dalilin zuwa sannan ne za a san ko kwalliya ta biya kudin sabulu? Akalla zuwa yanzu na fita daga kasar nan sau shida tun hawana mulki. Kuma a gurguje, fita ta farko na je Netherlands, muka je Belgrade, muka karasa Amerika.

Zuwa Netherlands an gayyace ni ne. Wata cibiya ta shirya wani taro na tattaunawa a kan ’yancin dan Adam. Sai suka ga akwai bukatar su ji ra’ayin Musulunci ko musulmi, me Musulunci ya ce a kan ’yancin dan Adam? Na gabatar da jawabi kuma aka yi tambayoyi. Alhamdulillahi ko da muka fito daga taron akwai wadanda suka ce su sai a ran nan suka fahimci cewa ashe Musulunci ya fi kowane irin addini, kowace irin kungiya, kowane irin ci gaban kasa tanadin meye ’yancin dan Adam. Ka ga wannan a iya cewa nasara ce. Na je na yi tallar Musulunci.

Abin da ya kai ni Belgrade kuwa, muna da wani kamfani a nan Kano na gine-ginen kwangiloli. Kamfanin nan tun wajen shekaru 20 na hadin gwiwa ne tsakanin gwamnatin jiha da wani kamfani da cibiyarsa tana Belgrade din ne. Tun kan na zo wannan kamfani yake digirgire, kamfanin ya durkusa alhali kashi 60 na kudin kamfanin na gwamnatin jiha ne. Su wadancan da ke Belgrade sune suke ba da kwararrun tafi da kamfanin. To shi ne na je in ji me ya sa suke wasa da harkar kamfanin nan? In abin ba zai yiwu ba a ba kowa kudinsa mu nade tabarmar, mu mayar wa al’ummar Kano kudin ko mu zuba a wani kamfanin. Kuma alhamdulillahi muka samu tattaunawa da su. Yanzu an sake wa kamfanin sabon tsari. A nan Kano mun ba kamfanin wasu hanyoyi guda biyu ya gina. Ka ga nan ma muna iya cewa kwalliya ta biya kudin sabulu.

Zuwana Amerika kuwa mun ziyarci wurare guda biyu ko uku. Mun tattauna da ‘American Development Foundaition’ wacce take taimaka wa duk wani ci gaba na rayuwar al’umma, inda suka gamsu cewa akwai gaskiya da amana. Suka fahimci irin alkiblar gwamnatinmu, muka yarda za mu kaddamar da tsari na gina gidaje masu saukin kudi a dukkan manyan biranenmu na jihar Kano. Za mu gina gidaje akalla 15 a kowace Karamar Hukuma, wanda wannan zai ba mu gidaje kusan 600. Wannan Cibiyar ta yarda za ta ba mu kusan kashi sittin na kudin, mu kuma mu kawo kashi 40. Yanzu ma har sun ba mu somin tabi.

Akwai kuma wani kamfani da muka tattauna da shi na yin bulo da kasa. Injunan ma sun zo, muna so a gama tabbatar da yadda ake aiki da shi, mu sake shi ga al’umma don a samu yin bulo mai sauki.

Na kuma je Ajentina. Wannan ba tafiyar kaina bace, gwamnatin Tarayya ita ta neme ni in jagoranci tafiya ta Kwamishinonin kudi na jihohi goma da aka zabo. Ajentina ta shiga cikin bashi fiye da namu, amma sun farfado, to mu je mu gano yaya ake fita daga cikin mishkila ta bashi? Mu dawo mu ba da labari.

Tafiya ta uku kuwa mun yi ne da Shugaban kasa. Shi kuma tsari ne ba na yanzu ba, cewa duk sad da Shugaban kasa zai yi tafiya yana da damar ya gayyaci ko ma waye, ko wani Basarake ko Gwamna. To haka ya gayyace ni, na raka shi. Kamar yadda ni ma a nan jihar Kano, in zan yi tafiya ina daukar Shugaban Karamar Hukuma ko na ANPP ko na PDP. Ina gayyatar su su raka ni.

Na kuma je kasar Ghana. Shi ma tafiya ce ta addini. Akwai wata cibiya da ake kira Alfurqan Foundation. Wasu ’yan uwa musulmi na kasar Ghana a karkashin jagorancin shi Mataimakin Shugaban kasa na Ghana, wanda musulmi ne, suka gayyace ni cewa suna so don Allah in aza harsashin gina wannan Cibiya, sannan in gabatar da jawabi a kan muhimmancin ilimi ga al’ummar musulmi.

A karshe mun je China don mu tattauna da ’yan kasuwa kan yadda za a bunkasa harkar kasuwanci a tsakaninmu. Daya daga cikin babbar tattaunawar da muka yi ita ce wacce muka yi da wata Cibiya wacce take da kudin da za ta zo ta sa jari a gina katafaren kasuwa. Mun tattauna da su kan muna so a yi kasuwa ta zamani a Kano. Za su gina kasuwa su bayar haya, ’yan kasuwanmu suna biya da kadan da kadan har su mallaka. Duk wanda ya san kasuwanci ya san muna bukatar kasuwar da ta dara ta Sabon gari. Alhamdulillahi kasuwar Sabon gari ta yi suna ta yi fice, kuma har gobe muna alfahari da ita.

Tafiyata ta karshe hutu na tafi, na je umura. Wannan ko ban fada ba, babbar riba na je na yi ibada, da fatan Allah ya karba.

EDITOCI: Akwai zargin da ake wa tsohon Shugaban kasa Shehu Shagari da kai ma ake ma irinsa, na cewa kana da kyakkyawan niyya, amma wasu da ke karkashinka kamar Kwamishinoni suna yin wasu abubuwa ba daidai ba; ka taba jin haka, kuma me ake ciki?

GWAMNA SHEKARAU: Shi zancen wai-wai ko jita-jita, kunnuwanmu a bude suke. Don haka muna jin su. Amma ji daban yarda daban. Ya rage duk wanda ya ji jita-jita ya dauke ta ya sa ta a faife. Ni na kwan da sanin cewa wannan aiki ba aiki ne na mutum daya ba, tilas ne za a daura wa wasu. Tarbiyyar Musulunci ya wajabta min don na bai wa mutum aiki, ba kuma zan zuba masa ido cewa ai ranar lahira ba za a tambaye ni ba. Ni za a fara tambaya, ni da na ba shi aikin. Don haka babu zancen a yi wasaraire ko a zuba ido. Zargi na wadanda aka ba aiki ko aka daura masu wani nauyi ba zai taba karewa ba, ni ma da na ba da aikin ai ban tsira ba. Zargi iri-iri, wani lokaci ma mara tushe.

Wani takaitaccen misali da zan bayar shi ne na yarinyata ’yar shekara uku da haihuwa tana da rami a zuciyarta, wanda an duba ta a nan Asibitin koyarwa, an kai ta Abuja, an je Lagos, duk suka ba da shawarar cewa akwai wani asibiti na jarirai kwararru a kasar waje a kai ta can da gaggawa, amma wani ya shiga rediyo ya ce matata mura kawai take yi, amma ta kwashi ’yan rakiya mutum bakwai ta tafi asibiti kasar waje. Wanda ya fada a rediyo har rantsuwa ya yi. Amma ka ga sad da ta haihu a nan asibitin Nasarawa aka yi mata tiyata aka ciro jaririn, ai ba wanda ya ji.

In maganar ayyuka ne muna da Cibiyar zuba ido kan ayyuka. Don ma mu samu nagartar zuba idon ba ma’aikatan gwamnati muka dauka ba, wadanda suka yi ritaya ne gogaggu, amintattu, muka daura musu nauyin wannan Cibiya. Kuma aikin da suke yi ba kadan bane. Muna gano kurakurai ana gyara su. Har zuwa yau wallahi ba mu samu labarin wani aiki da muka bayar, labari ya ishe mu an yi wata almundahana ko son zuciya ba. In an ba da aiki ana bin sawu, duk inda aka ga wani gibi, nan da nan za a dawo kan layi.

EDITOCI: Me za ka ce dangane da korafin da wasu suke yi cewa hukumar A daidata sahu tana yin wasu ayyuka ne da ya kamata a ce wasu Hukumomin gwamnati irin su Ma’aikatar watsa labarai, Shari’a Commission da Hizba suna yi?

GWAMNA SHEKARAU: To a dukkan ayyukan wadannan cibiyoyi babu zancen cin karo da juna, illa kowanne ana ware masa wani hadafi, alkibla da zai mai da hankali a kai ya tabbatar ya dabbaka shi. Kamar ilimi ne, kana da Ma’aikatar ilimi, akwai na makarantun sakandare, na gaba da sakandare, su Hukumar firamare, muna da Mai ba da shawara kan makarantun Allo da na karatun manya. In ka tara su su biyar ko shida din nan, za ka iya cewa duk suna magana ne kan ilimi, ilmantar da mutane shi ne alkiblarsu. Amma kowannensu bangaren da ya sa a gaba daban-daban ne. To haka yake a duk Cibiyoyin nan. Duk abin da ake nema shi ne a ba da gudummawa a sanar da mutane a fadakar da su, a ilmantar da su. Amma kowanne da inda zai bullo wa al’amarin.

In ka dauki shari’a Commission, ai cibiya ce da duk abin da ya shafi Musulunci, amma ka ga wannan bai hana aka yi Hizba board ba. Shi aikinsa umurni da kyakkyawan aiki da hani da mummuna, wanda in dunkule shi za ka yi, ya dawo aikin Shari’a Commission. Haka in ka dauki zakka, shi ma dabbaka wani bangare ne. Hukumar A daidaita sahu, abin da take yi shi ne kullum ta dinga zakulo al’amura na lalacewa ko na tabarbarewar tarbiyya, a yi ta lugude a kan wannan, a jawo hankalin mutane. Kamar maganar tallace-tallace na yara kanana, wani abu ne da ya dami kowa, amma a fito da shi a yi ta fadar sa, a yi ta jawo hankali (wannan sai A daidaita sahu).

Yau in hukuma ta zartar cewa ga wani tsari da ta fito da shi, hakkin Ma’aikatar watsa labarai ne ta tallata wa mutane ga hukuncin gwamnati, ka ga ya saba wa abin da ita A Daidaita Sahu take yi. Ita ba tsayawa take yi tana gaya wa mutane meye manufar ayyukan gwamnati ba.

Abin da ya sa ake ganin kamar aikin na cin karo da juna, Hukumar A daidaita sahu za ta ce gyara kayanka, da ma mun yi gini ne a kan tarbiyyar Musulunci, za a goya da me Allah ya ce, me Annabi ya ce, sai a ji kamar an shiga aikin Shari’a Commission. Mu da ma nufinmu duk Ma’aikatunmu su zama ‘Ministries of Islamic Affairs’, shi ya sa ma muka ce ba za mu yi ‘Ministry of Religious Affairs’ ba, don muna son Musulunci a gan shi a ko’ina.

Za mu ci gaba insha Allah.

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


  | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International