Almizan :Ina hukuncin aske gemu a addinin Musulunci? ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 8 Zulkidah, 1426                 Bugu na 693                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Tambaya da amsa:Tare da Shaikh Ibrahim Zakzaky

Ina hukuncin aske gemu a addinin Musulunci?

SHAIKH ZAKZAKY
Malam Ibraheem Yaqoub Zakzaky H.
Ya na amsa tambayoyinku

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malam, ko ya halatta mutum ya yanke farcensa ya bar wani sashi, misali yatsa daya, ko biyu bai yanke ba?

Daga Ahmad Sa’id Ahmad Hizbullah 0803 619 4411

SHAIKH ZAKZAKY: Lalle wannan ya saba wa koyarwar sunna, sai dai in bisa wani dalili ne kamar na rashin lafiya. Amma a matsayin ado, ya saba wa sunna. Sunna ita ce a yanke farcen yatsu gaba daya.

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malam, idan mutum yana bin Liman salla, zai iya yin salawat a cikin zuciyarsa?

Daga Muhammad Erana

SHAIKH ZAKZAKY: Kila abin da yake nufi shi ne zai iya yi a asirce ba tare da ya bayyanar ba? Don haka sai mu ce in a asirce yake nufi, ya yi. Azkar ana furta su da baki ne. Idan ka bayyana murya, a bayyane kenan. In ka boye murya, a asirce kenan.

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malam, ni makanike ne, sai wani mutum da muke aiki kusa da masallacinsa ya ce mu daina shiga masa masallaci domin muna bata masa shimfida. To ya za mu yi kenan, sai mu daina shiga ko kuwa tunda masallaci na Allah ne mu ci gaba da yin sallarmu?

Daga Muhammad Yusuf Kawo Kano

SHAIKH ZAKZAKY: Masallaci na Allah ne, amma ba ka je ka kazanta shi da kayanka ba. Saboda haka a matsayinka na makanike, idan lokacin salla ya yi sai ka cire kayan kanikanci, ka wanke jikinka ka sa kaya masu kyau, har ka bulbula turare ka je masallaci, don shi masallaci akwai hakkokin sauran masallata, ba za ka kazanta masu wuri ba, ba kuma za a shiga da wari ba. Ka ga akwai cewa Manzon Allah (S) yana cewa; “wanda ya ci wannan abin, kada ya kusanci masallacinmu,” yana nufin tafarnuwa. Wannan yana nufin idan akwai wari a jikinka ba za ka je masallaci ba, don za ka cutar da wasu. Saboda haka shi wannan bai kamata ya ce kawai masallaci na Allah ne sai ya je ya cuci mutane ba.

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malam, tambayata dangane da Sharifai ne. Wadanda muke da su a nan, su ma suna daga Ahlul Baiti, ko kuma sai Larabawa?

Daga Sani Benin Nijeriya 0802 304 3450

SHAIKH ZAKZAKY: A shari’a an san cewa duk wanda yake zuriyar Abdulmudallib ne yana cikin Sayyadodi, wadanda aka haramta masu Zakka, kuma aka wajabta masu Khumusi. Su wadannan Jikokin Abdulmudallib sun watsu a duniya, akwai su a kabiloli daban-daban na mutane a duniya. Na’am asalinsu Larabawa ne, amma sun bazu sun koma wasu kabilu. Wannan ba yana nufin duk wani mutum da aka ce masa Sharifi lalle ya zama haka nan ne ba. Don haka a shari’a idan mutum ya ce shi jinin Abdulmudallib ne, za a hana masa abin da yake gare su, amma ba za a ba shi abin da yake nasu ba. Ma’ana za a haramta masa Zakka, amma ba za a ba shi Khumusi ba. Sai an tabbatar.

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malam, ina da mata tana cutar da ni, sai na kai ta wajen iyayenta suka goyi bayanta, sai suka matsa min sai na sake ta, sai kuma na yi hakan. Na yi laifi game da hakan?

Daga 0802 745 9235

SHAIKH ZAKZAKY: Matsinsu dai ba zai sa ya sake ta ba, sai in dai haka ya so, saboda saki yana hannunsa ne. Ko ba komai su ba hukuma bane ballantana ya ce sun yi masa tilas. Saki yana hannunsa ne, in ya so ya sake ta, in ya so ya rike ta. Ni dai abin da na fahimta a nan dai, shi ne ya ga daman ya sake ta, ba wai matsinsu ne ya jawo (ya yi sakin), saboda ba su da wani hakki a kan su matsa masa, tunda ba iko suke da shi ba.

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malam, menene ingancin cewa lokacin da Manzon Allah (SAWA) ya je mi‘raji ya ga Allah, don na ji wasu suna cewa ya gan shi, wasu kuma suna cewa bai gan shi ba?

Daga 0802 745 9235

SHAIKH ZAKZAKY: Ganin Allah ‘mustahili’ ne, saboda ba ka ganin abu sai idan yana da jiki, ko kuma yana da iyaka, kuma wadannan sun saba wa siffofin Allah (T), domin shi bai kebanta da muhalli ba, bai da kuma iyaka. Gani ba ya riskar sa, shi kuwa yana riskar gani, kamar yadda ya siffanta kansa a Alkur’ani. Saboda haka wannan zance na ganin Allah ba dai a ruwaya ingantaciyya ba.

TAMBAYA:

TAMABAYA: Assalamu alaikum. Malam, yaya ruwan alwala idan kasa mai tsarki ta zuba ciki, yana halatta a yi alwala da shi kuwa?

Daga Sani Karami Badawa Kano

SHAIKH ZAKZAKY: To ai kasa ba ta jirkita yanayin ruwa. Kasa ba ta jirkita ruwa. Abin da kan jirkita ruwa adatan ya maishe shi ana iya amfani da shi waje sha ko ci ko dafa abinci, amma ba za a yi amfani da shi wajen alwala ba, shi ne in ya jirkita da wani abu kamar wanda ake ci, misali, kamar gari, ko dussa, ko wani abu mai kama da haka nan. Amma ita kasa da ma tana daga cikin abin da yake asali a wajen ruwa saboda ana debo ruwa daga kasa, daga rijiya masalan ko daga kogi. Saboda haka idan ya jirkita da abin da yake galiba a tare suke, ba a cewa ya jirkita.

TAMABAYA: Assalamu alaikum. Malam, ina iya bin fasiki wanda yake yin zina salla kuwa?

Daga Muhammad Salisu Karofi jihar Bauci

SHAIKH ZAKZAKY: A wajenmu dole ka san mutum a matsayin adili kafin ka bi shi salla. Wato a wajenmu limanci ba ya inganta sai daga wajen adili. Adilin kuma ka ga wato kenan fasiki shi ba adili bane. Saboda haka idan ka san mutum fasiki ne, ba za ka bi shi salla ba. Ko kuma in ka bi shi ba ka da salla, in ka sani. (Bin mazinaci salla), ba zai halatta masa ba, in kuma ya bi shi ba shi da salla din, in har ya sani. Saboda daga cikin sharuddan limanci akwai adalci, adalci kuma shi ne misaltuwa da umurnin Allah da barin abin da Allah ya hana. Saboda haka fasiki ba adili bane.

TAMABAYA: Assalamu alaikum. Malam, mutum ne ya yi wa matarsa saki, ba ta gama idda ba sai Allah Ya yi masa rasuwa, shin za ta yi masa takaba ne ko kuma idan ta gama iddar shi kenan? Kuma za ta gaje shi, duk da cewa ba ta haihu da shi ba?

Daga 0803 689 5892

SHAIKH ZAKZAKY: Lalle tana cikin lissafin matansa ne ai, tana matsayin matarsa ce. Idan mace tana idda, ana lissafta ta a matsayin matar mutum ne. Saboda haka idan ya rasu, ya rasu tana matarsa ce, ita ma in ta rasu, ta rasu tana matarsa ne. Saboda haka ita dai ya mutu ya bar ta a matsayin matarsa. Saboda haka za ta yi masa takaba kuma za ta sami gado.

TAMABAYA: To kuma iddanta ta kare kenan daga lokacin da ya rasu?

SHAIKH ZAKZAKY: Na farko, zan yi masa gyara dangane da idda da takaba, don ga alama shi ya dauka ma’anarsu daban-daban ne. Ga alama ya dauka idan an ce takaba, ana nufin iddar wadda mijinta ya rasu. Idan kuwa an ce idda ana nufin iddar wanda aka saka. To duk sunansu idda ne. Ana cewa wannan iddar saki, wannan iddar mutuwa. To abin da ya kamata ya tamabaya shi ne, to iddar saki za ta yi ko iddar mutuwa? Sai mu ce to, tun da yake a yayin da take iddar saki ana lissafta ta a matsayin matarsa ce, saboda haka yanzu iddar mutuwa za ta yi. Sannan kuma abin da mu muke ce wa takaba, shi kuma ana yin sa ne a lokacin idda, ba shi ne iddar kansa ba. Shi takaba shi ne yanayi na jaje. Ya zama wato kenan ba za ta yi ado ba, ba za ta sa turare ba, za ta zauna a cikin wani hali, yanayi na jaje har zuwa wata hudu da kwana goma. To wannan kuma shi ne abin da ya hau kanta yanzu, kuma tana da gado. Da ma shi gado ba shi da dangantaka da haihuwa, kamar yadda ya ce duk da cewa ba su haihu ba. Shi gado bai da wani dangantaka da haihuwa. Saboda haka matar mutum, ta haihu da shi ko ba ta haihu da shi ba, sunanta dai matarsa. Kuma abin da ya hau kanta shi ne shigen abin da ya hau kan sauran matansa in yana ma da sauran matan da bai saka ba. Kuma in ita ce kadai matarsa tana da gado daidai yadda ya kama, ko daya bisa hudu, ko daya bisa takwas, ko kuma in da wasu, ta hadu tare da su a wannan kason.

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malam, wasu suna cewa duk abin da ya samu mutum na kuncin rayuwa Allah ne ya fi son ya ga mutum a haka. Haka abin yake kuwa?

Daga Ahmad Sa’id Potiskum

SHAIKH ZAKZAKY: To, da arziki da kunci mu a wurinmu Allah ne ke rabawa. Saboda haka in aka yi masa kyakkyawan fassara na cewa Allah (T) ke raba arziki, na’am ya yi daidai. Amma kar ya zama cewa, misali, idan shi ne bai nemi arziki ba, sai kuma ya zo ya ce da ma haka Allah ya kaddara masa. To sai mu ce wannan ya yi wa abin mummunar fassara kenan.

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malam, ina hukuncin mutumin da ya kulle dakinsa ya hana matarsa shiga?

Daga Babayo Musa Jos NNPC Makurdi 0803 667 3532

SHAIKH ZAKZAKY: A nan za mu dauka shi yana da dakinsa, ita ma tana da dakinta, shi sai ya kulle nasa ya hana ta shiga. Abin dai da muka sani shi ne cewa tana da hakki. In dai yana ba ta hakkinta, shi yana zuwa ya kwana a dakinta, to amma kuma shi dakinsa sai ya ce kar ta shiga, ya kulle, to wannan sai mu ce ba wani damuwa. In dai yana ba ta hakkinta.

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malam, ina hukuncin kiran salla da ake yi yanzu da lasifika maimaikon a wajen masallacin kamar yadda aka sani?

Daga M. D. Dutsinma.

SHAIKH ZAKZAKY: Shi dai kiran salla kamar yadda aka sani ana kiran na waje ne su zo masallaci, kuma duk yadda ya kama. In da can ana yin ‘manar’ a hau a kira don ya isa can, in yanzu ma ba a hau ‘manar’ din ba za a ji, shi kenan ya wadatar. Ba a ce hawan ‘manar’ din shi ne kiran salla din ba. Ko ba a lura ba? Shi kiran ya je ga na wajen masallaci shi ne makasudi, tunda kuma makasudi ya samu, ba wani damuwa ko da ma ina mai kiran sallar ya kasance. Makasudin shi ne kiran.

Yana da kyau ya zama mutum ne akili, baligi yake yake kiran a daidai wannan lokacin, ba wai ya sa kaset bane, misali. Domin shi kiran salla tamkar isar da shaida ne ga al’umma cewa lokacin salla ya yi. Ka ga kuwa ya kamata ya zama akili ne yake yi a daidai wannan lokacin.

TAMBAYA: Malam mu a wajenmu, mata idan mijinsu ya rasu sukan yi wani zama ba sa sa wasu kaya masu kyau, ko takalmi. Idan har ya zama wajibi su sa, sai dai su sa ba iri daya ba. Ba sa sutura sai dai bakake. Ko yin hakan ya halatta? Idan kuma ba haka ya kamata a yi ba, to yaya ya kamata a yi?

Daga Muhammad Abu Muhammad Itasgadau jihar Bauci

SHAIKH ZAKZAKY: Shi wannan shi ne tamkar tambayar da na amsa a baya, inda na nuna cewa akwai wani abu da ake ce masa takaba, shi ne ‘ihdad.’ Shi ne yanayin zama na makoki. Da ma shi wannan zaman makokin, al’ada takan nuna daga wuri zuwa wuri, sai dai al’adar in ta saba wa shari’a ba za a yi ta ba. Duk wata hanya da ake ganin jaje ne, misali, in dai bai saba wa shari’a ba babu laifi da shi. Alal misal, ba a ce su zauna da kazanta ba, suna zaunawa ne da kaya masu tsafta, sai dai ba masu ado ba, a sutirar jikinsu kenan. Haka kuma in ana ganin wasu abubuwa kamar su kitso da kunshi, alamar mai farin ciki ke yi, ita ba za ta yi ba kenan. Ta yiwu kuma a wata al’adar ba su damu da wannan ba. Haka kuma sanya bakin kaya a wata al’adar zai zama yana da ma’ana, a wani wurin ya zama ba zai yi ma’ana ba. Sa takalmi ya zama ba iri daya, shi wannan zai iya zama ya saba wa shari’a. Abin da muka sani dai shi ne cewa ba za ta shagaltu da ado ba, -wanda shari’a ta sani kenan- amma kuma kamar yadda na ce al’ada na iya kawo abin da aka san shi sunansa jaje ne. Kuma in bai saba wa shari’a ba ba laifi da yin sa, wanda ya saba wa shari’a ne, kamar kazanta, da a ce kamar ba za ta yi magana da mutane ba, ko ba za a yi ganin ta ba sam-sam, ko ba za ta fita daga cikin gida ba sam-sam, ko kuma za ta daura wani abu marar tsarki, ko wani mai kama da haka nan. To wanda dai ya saba wa shari’a ne ba za a yi ba.

TAMBAYA: Malam ina halascin ci abincin nan da ake ce wa karafish (crayfish) ne?

Daga Sani Karamu Badawa Kano

A biyo mu bashin amsar wannan tambayar da ma wasu a mako na gaba insha Allah.

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


  | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International