Almizan :Malam Turi ya jagoranci kaddamar da kaset din Bashir Dandago a Kano ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 8 Zulkidah, 1426                 Bugu na 695                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Rahotanni

Malam Turi ya jagoranci kaddamar da kaset din Bashir Dandago a Kano

Daga Muhammad Sakafa da Musa Aljegawy

H

A ranar Asabar 26/Shawwal 1426AH (25/11/2005) ne, shahararren mawakin Manzon Allah (S) da ke Kano, Malam Bashir Dandago ya kaddamar da sabon kaset dinsa, wanda ya yi wa Jikokin Manzon Allah (S) Imam Hasan da Husain (AS) wake, inda Malam Muhammad Turi ya jagoranci bikin kaddamarwa.

Shi dai wannan mawakin, Allah ya yi masa baiwa ta waka, shi ya sa masu adawa da wannan baiwar suke ta sukar sa a jaridu da sauran wurare. “Ba komai ya sa suke yin wannan ba, sai don fifiko da daukakar da Allah ya yi masa a kan waken Nana Fatima (AS) da yi,” in ji wasu mutane da muka zanta da su a wajen taron.

An dai yi wannan taron ne a Unguwar Gwammaja a Layin ’Yan Azara da ke Kano. Taron, na kaddamar da kaset din ya samu halartar ’yan uwa Musulmi maza da mata da yawan gaske.

A jawabinsa a wajen taron, Malam Turi ya yi bayani a kan halin da Musulmi da Musulunci suke ciki a duniya da kuma kaddamar da wannan sabon kaset. Ya ce makiya Musulmi da Musulunci sun fito a sarari suna yakar Musulmi da sunan yaki da ta’addanci.

Malam Turi ya yi kira ga al’ummar Musulmi da su hada kansu waje daya domin abin da ya shafi bambancin fahimta na wasu abubuwa ba zai sa Musulmi su kasa fahimtar junansu ba.

Malam Turi ya ce, duk wata fitina da ke faruwa a duniya a tsakanin Musulmi, Amurka da Isra’ila ke haddasa su.

Da ya juya kan kaddamar da wannan kaset din kuwa, Malam Muhammad Turi, ya kawo ayoyi da hadisai ne a kan darajojin da falalolin da Allah ya yi wa wadannan da aka yi wa waken. Ya ce duk wani abu da yake da nasaba da Iyalan Annabi son sa wajibi ne.

A lokacin fara kaddamar da kaset din, an sanya sunayen Imam Hasan (AS) da Imam Husain a matsayin ‘Chief Launcher’ kamar yadda Malam Mustapha Limaci ya ce; ya bukaci ’yan uwa da su tara wa masu wannan sunan Naira dubu 20 a matsayin ‘Chief Launcher.’

A nan fa ’yan uwa suka yi tururuwa suna ruwan Nairori a taron. An kuma bukaci wanda zai saya wa Jagoran Harkar Musulunci, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) kaset biyu a kan kudi dubu 20. Nan take wani dan uwa mai suna Malam Aminu mai takalma ya saya wa Malam a kan dubu 20.

Halkar Gwammaja ta sai kaset biyu kan dubu biyar, sai wani dan uwa Malam Aminu Ingawa ya sai kaset daya a kan 1000, sai kuma Alhaji Dalha Musa ya sai kaset daya a kan 1000.

Shi kuwa mawakin Malam Bashir Dandagi, ya yi wakoki masu yawa a wurin taron. Ya bayyana farin cikinsa da abubuwan da ’yan uwa suka yi masa.

Ina Shehunnan Malaman Maiduguri suka dosa ne?

Daga Muhammad Bello Gashuwa

Babban aiki da aka sani ga Malamai shi ne shiryar da al’umma zuwa ga hanya mikakkiya ta Musulunci, da kuma tsare su daga fadawa ga halaka da duk abin da ya sabawa Musuluncin.

Bisa ga dukkan alamu manyan Shehunnai da Ustazai na dukkan bangarori -Darika ne, ko Izala ko kuma Salafiyya- ne da ke cikin garin Maiduguri birnin Shehu da kawaye su ba abin da suka sa a gaba kenan ba. A kullum sai yawo da hankulan almajiransu suke ta yi ta hanyar jayayya a tsakaninsu a abubuwan da ko dai ba su da muhimmanci, ko kuma bai kamata a yi jayayya a kansu ba, ko kuma ma ya haramta. Sannan kuma a lokaci guda suna yi wa almajiran nasu muguntar kada su gane gaskiya ta hanyar kushe ta. A lokacin da kuma ga barna da fasikanci sun cika gari, kuma sun kau da kansu daga yin magana.

Duk wanda ya kwana ya tashi a cikin garin Maiduguri, ya san cewa idan ka je wuraren wa’azozin Shehunnai da Ustazai a gidajensu, ko a unguwanninsu, ko kuma ka saurare su ta gidajen rediyo, to ba abin da za ka ji illa sukar daya bangaren, wato in dan Darika ne yana sukar Izala, in kum dan Izala ne, ko Basallafe yana sukar Darika.

Mafi muni kuma shi ne akwai wani fili na awa biyu a kullum ranar Juma’a da gidajen rediyo da talabijin mallakar gwamnatin jihar, wato BRTV suke watsawa kai tsaye mai suna: “Ulama’ur-Rashidun” wanda a kowane mako suke gayyato Malami daya daga Malaman garin, ko kuma daga waje inda za a rika yi masa tambayoyi kai tsaye ta hanyar tarho yana amsawa. To a yayin shirin a kowane mako, manyan abubuwan da ake ta jayayya a kansu abu biyu ne. Na daya shi ne tambayoyi a kan Allah Ta’ala “a ina Allah yake? Yana saukowa a kullum da asuba? Yana da hannu?” da makamantan wadannan, har da tambayoyin da suka fi wadannan muni a kan Allah Ta’ala.

Na biyu kuma tambayoyin kule ne a kan akidar Malamin da aka gayyato. Kuma masu tambayar ba sa taba gamsuwa da amsoshin da ake ba su. Alhali a daidai wannan lokacin da suke ta wannan barkata, alamajiransu suna nan suna jiran a ba su ‘irshadi’ amma sai jayayya ake koya masu.

Duk da wannan mayen jayayya da wadannan “Malamai” suka jefa al’umma a ciki, amma sai ya zama akwai wani sauti karkashin jagoranci Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) yana ta kiran al’ummar Musulmi da a zo a hada kai, amma abin mamaki sai wadancan Malamai suka yi caa a kan wannan kira na hadin kai da cewa ai wadancan ’yan Shi’a ne, ita kuma Shi’a ba Musulunci bace. To su da ba ’yan Shi’a ba, su hade kansu mana, ko al’umma ta huta da wannan bakar jayayya da suke ta yi a kullum.

A irin wannan yanayin sai ka ga rayuwar Malaman tana cikin hadari. Na daya, sun shiga jayayya a tsakaninsu, wanda ba shi da amfani ga Musulunci. Na biyu, sun rudar da mabiyansu. Na uku, sun kange su daga fahimtar gaskiya. Na hudu, ga nau’o’in barna da tsoron Allah sun yi kaca-kaca a cikin al’ummar da suke raye a ciki, amma ba sa cewa komai.

Hurras sun yi fareti a Ringim

Daga Muhammad Sakafa da Mukhtar Kazimiyya Kano (muhammadsakafa@yahoo.com)

A kwanakin baya ne ’yan uwa musulmi Hurras na garin Ringim ta jihar Jigawa suka gudanar da wani fareti na musamman don tunawa da ranar da aka haifi daya daga cikin Jikokin Manzon Allah (S), wato Abul Fadlul Abbas (AS).

Shi dai wannan Jika na Manzon Allah (S) Abul Fadlul Abbas (AS) shi ne dan Imam Ali (AS), dan uwa ga Imam Husain (AS), wanda ake yi masa lakabi da “Kamru Banu Hashim” (wata mai haskakawa daga Banu Hashim). Kuma shi ya zama garkuwar Imam Husain (AS) ranar Ashura a filin Karbala, wanda a sakamakon shahadarsa Imam Husain (AS) ya tabbatar da karyewar al’amura a lokacin.

Faretin, wanda aka gabatar da shi cikin nutsuwa da tsari ya kayatar ainun, wanda aka faro shi daga masallacin Alkali aka kammala shi a bakin kasuwa.

Bayan kammala shi ne sai aka saurari takaitaccen bayani daga Kwamandan Harisawa na garin, Malam Rabi’u Husain Ringim, inda ya ba da tarihin wannan babban Jika na Manzon Allah (S), tare da muhimman darussa da za a dauka daga wannan gwarzon gidan annabta, Abul Fadlul Abbas (AS).

Kamar yadda Wakilanmu suka habarto mana, wannan faretin na Harisawa shi ne ya zama na farko da ya sami karbuwa a wajen jama’ar garin, tare da sa su farin ciki da murna ganin wannan abu mai tarin albarka da aka yi masu a garinsu su ma, abin da ya sa jama’a suka yi wa masu faretin rakiya.

Ba za a iya bice hasken da’awar Malam Zakzaky ba

In ji Malam Aliyu Takakume

Daga Musa Jega

A ranar Asabar 18/11/2005 ’yan uwa Musulmi na Da’irar Jega da kewaye da ke jihar Kebbi suka gabatar da taron wa’zi a babban masallacin Juma’a na Jega.

Da ma kamar yadda aka tsara, wa’azin na yankin Sakkwato da Kebbe da Zamfara, Malam Kasim zai gabatar da wa’zin a Zamfara, Malam Abubakar Nuhu Talatar Mafara ya gabatar a garin Sakkwato a yayin da Malam Aliyu Tatakure zai gabatar da nasa wa’azin a jihar Kebbi.

Shi dai wannan wa’azin yana da nasaba da neman infaki na samar da kafafen yada labarai a Cibiyoyin ’yan uwa Musulmi.

Shi dai wannan wa’azin ya samu halartar ’yan uwa da daman gaske, ciki har da shahararren mawakin gwagwarmayar nan, Malam Mustapha Gadon Kaya da Malam Janaidu Hubbare Sakkwato.

Da yake jawabi a wajen wa’azin, Malam Aliyu Takakume ya ce, shakaru 13 Manzon Allah (S) ya yi yana da’awa a kan Tauhidi, don mutane su yarda da cewa Allah daya ne, Manzon Allah (S) da Sahabbansa sun sha jarrabawa da wahalhalu har ta kai ga sai da aka yi masa rotsi har ta kai ga wasu suka yi hijira suka bar matayensu da ’ya’yensu da dukiyoyi da gonakinsu duk a kan wannan addinin Musulunci, “amma wannan bai sa sun ja da baya ba, sai da suka cinye jarabawar.”

Ya ce lokaci ya yi da ya kamata jama’ar kasar nan su fahimci kiran da Malam Zakzaky yake yi wani abu ne da ba za iya bice haskensa ba, “musamman da yake idan muka dubi tarihin Shehu Usmanu Danfodiyo da gwagwarmayarsa da kuma almajiransa ba a iya murkushe su ba, da tarihin Shaikh Abdulkadir Jilani da almajiransa da tarihin Imam Khumaini da almajiransa, to tunda ba a iya danne ta wadannan Shaihunai ba, to haka ba wanda zai iya bice hasken da’awar Malam Zakzaky (H) da almajiransa a wannan kasa,” in ji shi.

Za a sa zare tsakanin Hukuma da ’yan kasuwar Wuse Abuja

Yanzu haka dai babbar kasuwar birnin Abuja (Wuse) ta fara daukar zafi, wanda hakan ka iya haifar da mummunan fushi daga ’yan kasuwar sakamakon wani sabon matakin takurawa da Hukumar kasuwar ta dauka a kan ’yan kasuwar.

’Yan kasuwar dai sun fara hassala ne sabili da matakan da Hukumar kasuwar ke dauka a kasuwar, wanda Hukumar ta kira da yunkurin kakkabe ’Yan Atachment, wanda Hukumar ta ce suna neman dawo wa kasuwar karfi da ya ji.

Sai dai su ’yan kasuwar suna zargin Hukumar da wuce makadi da rawa wajen daukar matakin, inda ta kai ga hana sai da nau’in kaya biyu a shago daya, musamman a bakin kofar shago.

A da dai Hukumar tana ta kokawa ne da ’yan talla a kasuwar, inda a kullum ake allan-ba-ku tsakanin ’yan tallar da Hukumar kasuwar,

Da dama daga ’yan tallar suna ganin zalunci ne hana su sana’arsu da karfi da yaji a kasuwar, suna masu fadin cewa mafi yawan ’yan tallar samari ne, kuma hana su na iya kara haifar da zauna-gari-banza, wanda hakan zai iya kai wa ga samarwa da birnin barayi, wanda hakan ba zai haifar da da mai ido ba.

Wakilinmu ya yi kicibis da yadda ’yan sandan kwantar da tarzoma suka biyo wani saurayi da ke dauke da kayan takalma, suka kama shi, amma suka sake shi bayan sun karbi na goro a hannunsa.

Da Wakilinmu ya tambaye shi ko me ya sa ba sa karbar katin shaidar talla da zai hana yi musu wannan cin kashin? Sai ya ce, “ai ko da mun karba, bayan wani lokaci sai a ce sai mun sake wani.”

Su kuwa ’yan sandan sun shaida wa Wakilinmu cewa, su fa ba da son ransu bane suke wannan aikin. Yanayin aikinsu ne, ba yadda suka iya.

Wani abu da ’yan kasuwar ke kuka da shi shi ne, yadda Hukumar ta yiwo hayar ’yan sandan kwantar da tarzoma masu dimbin yawa don tabbatar da an bin dokokin da suka shimfida sau da kafa.

’Yan kasuwar da dama na ganin irin haka ne yake haifar da tashin tashina, musamman idan aka yi la'akari da sanadin tashin hankalin da ya auku a kasuwar a watannin baya.

Wasu daga cikin ’yan kasuwar suna ganin wannan matakin na haifar da fargaba a zukataan abokanan huldarsu masu zuwa sayan kaya.

Wasu ’yan kasuwar da Wakilinmu ya ji ta bakinsu sun ce, duk da wannan abu Hukumar na matsa musu wajen karbar kudin gudanar da kasuwar (Service Charge).

A wata daban kuma, Hukumar kasuwar ta Wuse ta kudiri aniyar sabunta takardun mallakar shaguna a kasuwar daga watan Janairun shekara mai zuwa kamar yadda wata sanarwa daga Hukumar ta bayyana.

Sanarwar ta ci gaba da bayyana cewa; masu shagunan za su biya harajin shagunan na tsawon shekaru 50, wanda shi ne zai tabbatar wa mai shago mallakar shagon na zawon shekaru 50 din.

Hukumar kasuwar ta nuna za ta yi amfani da kudaden ne wajen samar da wasu kasuwannin don amfanin wasu ’yan kasuwan.

Sai dai masu lura da yadda al’amura ke tafiya a kasuwar ta Wuse na ganin cewa ya zama dole ga Hukumar da ta canza salon da take tafi da al’amura a kasuwar domin daukar irin wannan mataki da Hukumar kasuwar ke yi yana iya janyo bakin jini ga kasuwar ta yadda masu saye da sayarwa za su kaurace wa kasuwar, wanda kuma hakan na iya janyo rushewar tattalin arzikin Hukumar, musamman idan aka yi la’akari da dimbin biliyoyin Nairorin da Hukumar kasuwar ke samu.

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


 Shafin Gamji | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International