Almizan :Da a ce Manzon Allah ya rubuta mana wasiyya… ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 8 Zulkidah, 1426                 Bugu na 695                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Littafai

Da a ce Manzon Allah ya rubuta mana wasiyya…

Idan har Khalifa Umar zai kange Manzon Allah (SAWA) daga rubuta Hadisansa a gaban sauran sahabbai, ba tare da sun iya cewa komai ba, har kuma yana mai cewa ‘Manzon Allah (SAWA) ba ya cikin hayyacinsa,’ tare da sauran kalmomi wadanda ya fada, wadanda kuma tarihi ba zai taba mantawa da su ba, to kuwa babu mamaki da bayan wafatin Manzon Allah (SAWA), shi Khalifa Umar ya sami goyon bayan wasu masu ra’ayi irin nasa, suka yi dukkan yadda za su yi domin su hana a bayyana wa mutane hadisan Manzon Allah (SAWA).

Shaikh Hasan Saffar

Babu shakka, wasu da yawa sun goyi bayan Khalifa Umar ne (na hana bayyana Hadisan Manzon Allah (SAWA), ko dai saboda kwadayin abin duniya, ko saboda tsoron sa da suke ji, ko kuma saboda munafunci. Haka nan kuma ya sami goyon baya daga wasu manya daga Kuraishawa, wadanda suke fada-a-ji, sannan daga cikinsu ma, wasu manyan Sahabban Manzon Allah (SAWA) ne.

Ku duba fa ku gani, duk yawan Sahabban da ke zagaye da Manzon Allah (SAWA) a wannan lokacin, dukkaninsu sun goyi bayan Khalifa Umar na cewa ‘Manzon Allah (SAWA) ba ya cikin hayyacinsa. Haka nan kuma, sune suka goya wa Khalifa Umar baya a nan take wajen kange Manzon Allah (SAWA) daga rubuta abin da ya gaya musu cewa zai rubuta. Wannan ne kuma ya sa bai rubuta wannan bayani ba, domin kuwa Ubangijinsa ya sanar da shi irin gagarumar makarkashiyar da aka shirya, wadda za ta kawo rudu a cikin Musulunci, wanda da a ce ya rubuta wannan bayani da shi kenan an waraka.

Da a ce Khalifa Umar da sauran Sahabban da ke tare da Manzon Allah (SAWA) a wannan lokaci ba su hana ba, kuma da a ce sun bar shi ya rubuta wannan bayanin da ya ce, ba shakka da ya kange al’ummar wancan lokaci, da dukkan sauran al’ummarsa da za su zo bayansa, har zuwa tashin duniya, daga sakin hanya madaidaiciya, kuma da ba a rika samun matsalolin da suka dabaibaye Musulmi suke raba kawunansu, musamman a wannan zamanin da muke ciki ba. Amma kuma abin takaici shi ne, ’yan-a-fasa-kowa-ya-rasa, sun kammala shirinsu domin ganin sun juya wannan sako ya zama hanyar da za su bi su karkatar da jama’a, har su juya wa Musulunci baya.

Hakika, wannan al’amarin ya faru ne a lokacin da Manzon Allah (SAWA) ke kwance kan gadonsa na wafati, yana samun wahayi daga Ubangijinsa. A daidai lokacin da zuciyarsa ke cike da takaicin yadda al’ummarsa suka saki hanyar Allah. “IDAN YA MUTU, KO KUMA AKA KASHE SHI, SAI KU JUYA A KAN DUGADUGANKU?” Wannan ayar, Allah ya saukar da ita ne, saboda yadda ya san makarkashiya, da kuma yaudara da munafuncin da ke cikin zukatan wadansu mutane. A saboda haka, ya sanar da Annabinsa (SAWA), tare da kwantar masa da hankali, saboda ba zai kama shi da laifin da al’ummansa suka aikata na juya baya daga gaskiya ba a bayansa.

Da akwai inda Allah (SWT) ya yi bayani a cikin Alkur’ani dangane da ranar da wadanda suka ketare iyaka za su yi da na-sani, su ce: “Boni ya tabbata a gare su, da a ce sun bi hanyar da Annabinsu ya nuna musu. Sannan kuma za su yi da-na-sanin yin riko da wasu a matsayin abokai na gaskiya. Haka nan za su yi da-na-sanin yadda aka batar da su daga ambaton Ubangiji, bayan kuma gaskiya ta bayyana a gare su. Hakika Shaidan mai batar da mutane ne.”

Haka nan kuma Manzon Allah (SAWA) zai fadi ya ce: “Ya Ubangiji, al’ummata sun yi wa Alkur’anin nan rikon sakwa-sakwa.”

“Ba mu aiko kowane Annabi ba, sai ya sami makiya daga cikin masu sabo. Hakika Ubangijinka ya ishe ka da shiriya da kuma taimako (25:27).

A cikin wannan binciken da muke yi, za mu gano cewa, irin makarkashiyar da su Abu Sufyanu da Mu’awiya suka yi wa Manzon Allah (SAWA), ya samo asali ne tun daga yadda Khalifa Umar Bin Khattab ya kasance mai yin fito-na-fito da Manzon Allah (SAWA), musamman dangane da mu’amalarsa da shi, kuma shi ne ya share musu fage, ya gadar musu da wannan kaskantacciyar turbar.

Ku duba mana, kuma ku bincika ku gani, za ku ga yadda Khalifa Umar Bin Khattab a duk tsawon kasancewarsa a tare da Manzon Allah (SAWA), yadda ya rika yin fito-na-fito, da adawa, da kuma kalubalantar Manzon Allah a lokuta da yawan gaske. Wadannan abubuwan da su Khalifa Umar suka yi wa Manzon Allah (SAWA), hakika ba a bisa hatsari suka faru ba, domin kuwa duk yana da nasaba da irin kokarin da suka yi ta yi don ganin an rage darajar Manzon Allah (SAWA) a idanuwan al’ummarsa da za su zo daga baya, har su rika yi masa kallo a matsayin mutum kamar su. Har cewa suka yi, Manzon Allah (SAWA) ba ma’asumi bane, don haka zai iya aikata son zuciyarsa, ko kuma ya sabi Ubangiji (Wa’iyazu Billahi).

Don Allah dubi wata ruwaya mana da aka kirkiro; ku duba a cikin farko da karshen littafin Ibn Kathir, inda Muslim, Imam Ahmad, Abu Dawud, da Al-Tirmidhi suka ruwaito: Haka nan kuma da akwai wannan ruwaya a cikin littafan Al Sira-Al-Halabiya, da kuma Al-Sira-Al-Dahlaniya, juzu’i na 1, shafi na 512, inda aka ruwaito cewa; sau da yawa Allah kan saukar da ayoyin Alkur’ani, wadanda wai suke gaskata maganganun Umar Bin Khattab, kuma su yi jayayya da hukuncin Manzon Allah (SAWA). Har Manzon Allah (SAWA) kan fashe da kuka ya ce “Da a ce Allah zai saukar mana da wata masifa, babu wanda zai tsira a cikinmu sai Ibn Khattab.”

Haka nan kuma, ku dubi wata ruwayar da ke cikin littafin Sahih Bukhari, juzu’i na 1, shafi na 46, (babin da ke yin bayani dangane da mata a kan abin da ya shafi shiga makewayi), inda aka cewa, Umar Bin Khattab ya yi ta shawartar Manzon Allah (SAWA) da ya sanya iyalinsa su rika sanya hijabi (lullubi). Manzon Allah bai yi hakan ba, sai a lokacin da Allah ya saukar da ayar da ta umurce shi da sanya iyalin nasa su sanya hijabi.

Haka kuma, wata ruwayar a cikin Bukhari, juzu’i na 4, shafi na 96, da juzu’i na 8, shafi na 161, inda aka ruwaito cewa, Shaidan ba ya firgita idan ya ga Manzon Allah (SAWA), amma da zarar ya ga Umar Bin Khattab, sai ya ranta a na kare. Kai, da akwai hadisai na karya da karairayi wadanda aka kirkiro, ba domin komai ba, sai domin a rage darajar Manzon Allah (SAWA), sannan a fifita Sahabbai.

Haka nan kuma, da akwai wani hadisin da aka kirkiro duk domin a kambama Umar Bin Khattab, kuma a rage darajar Manzon Allah, inda ake cewa wani lokaci Manzon Allah (SAWA) yakan yi kokwanton Annabtansa. Manzon Allah (SAWA) wani lokaci yakan ce: “Idan na ga Jibrilu (AS) ya dade bai zo min da wahayi ba, sai in yi tsammanin wajen Umar Bin Khattab zai je.”

Dukkan irin wadannan hadisan an kirkire su ne a lokacin Mu’awiya Bin Abu Sufyan, a lokacin da suke ganiyar shirya makarkashiya domin rage darajar Manzon Allah (SAWA), da kuma kokarinsu na yin babakere a kan matsayin da Allah da Manzonsa suka bai wa Ali Bin Abi Talib. A saboda haka ne, Mu’awiya ya bi dukkanin hanyoyi, ya sa aka kirkiri hadisan da aka kambama Abubakar, Umar da Uthman, kuma aka daukaka matsayinsu a idanuwan al’ummun da za su zo daga baya. Ya yi haka ne saboda dalilai biyu.

Za mu ci gaba insha Allah.

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


 Shafin Gamji | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International