Almizan :Burin kowannenmu ne shahada a tafarkin Allah ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 8 Zulkidah, 1426                 Bugu na 693                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Tunatarwa:Tare da Shaikh Ibrahim Zakzaky

Burin kowannenmu ne shahada a tafarkin Allah

SHAIKH ZAKZAKY
Malam Ibraheem Yaqoub Zakzaky H.

Muna ba dubban masu karanta wannan filin mai farin jini da albarka hakuri, sakamakon wasu kurakurai da aka samu a makon jiya a wannan shafin. Wannan dalilin ne ma ya sa muka sake maimaita shafin.

Idan dai ana biye da mu mako shida muka yi muna kawo maku wannan jawabin da Malam Ibraheem Zakzaky ya gabatar a wajen taron tunawa da Ranar Shahidan wannan Harka - Yaumu Shuhada na bana, wanda ya gabata a filin kofar Shahidai (Doka), Zariya a kwanakin baya. In dai ana biye da mu mun tsaya ne a inda Malam yake bayani game da Shahadar Imam Musa Alkazim (AS). Yau ma kamar yadda aka saba, Musa Muhammad Awwal ne ya rubuto mana daga kaset. A sha karatu lafiya.

DUK TARIHIN A’IMMA SHAHADA NE BAYAN SHAHADA

Sai ya ce da shi: “Ya Imam, yaushe za mu gan ka?” Sai ya ce da shi, “ranar Juma’a mai zuwa.” “A ina?” Ya ce, “a masallacin Juma’a za ku gan ni.” Saboda haka sai ya je ya gaya ma duk almajiransa, mabiyansa; duk aka gaggaya masu a bobboye cewa ranar Juma’a za a ga Imam a masallaci. Sai suka shisshirya kowanne ya yi wanka ya sa sutura mai kyau. Duk aka cika masallaci ana tsammanin za a ga Imam. Zuwa can bayan salla sai aka ga an shigo da gawar wani mutum. Sai aka ce jama’a wani ya mutu za a yi masa salla, ba a san ko wanene ba. Sai suka duba suka ga shi ne. A wajen kai gawar har da shi Harun din, shi ma ya bi sahun jana’izar, har yana kuka. Wai yana cewa; “yanzu da wanne zan ji, da mutuwarka kai dan uwana, ko kuwa da tunanin da ake mani cewa wai ni na kashe ka?” Alhali sun san shi ya kashe shi.

Ya yi azumi ne, wannan mai tsaron nasa, La’in, ya kawo masa dabinon bude baki, alhali ya zuba guba a cikin dabinon. Kuma ya mika masa har ya tsaya ta wundo yana kallon ko in lokacin bude baki ya yi zai ci. Sai ya ga Imam ya dauka ya ci, ya sake dauka ya ci, ya sake daukar na uku ya ci. Sai ya ga kamar ya daina ci haka. Sai ya ce ci gaba mana da ci. Sai ya ce, “ai wannan bukatarka ta biya. Wannan ma da na ci bukatarka ta biya, abin nufinka ya yi.” Sannan Imam (AS) ya kwanta Allah ya dauki ransa Shahidi. Allah ya rahamshe shi.

BURIN KOWANNENMU NE SHAHADA A TAFARKIN ALLAH

Wannan shi ne tarihin A’imma, wadanda yau duk tarihinsu shahada ne bayan shahada. Wannan ita ce sunnar Babansu Ali Ibn Abi Dalib, ita ce sunnar Hasan da Husaini da Ali Ibnil Husain da sauran A’imma bayan A’imma, har ya zuwa Limaman nan guda biyu, Askariyyawa, Askariyyai.

To wannan ita ce sunnar a wajenmu, kyakkyawan karshe a nan duniya da shahada insha Allahu. Burin kowannenmu ne ya zama in Allah (T) ya kaddara masa mutuwa, ya kasance kashe shi za a yi a tafarkin Allah.

Wadanda suka yi shahada mu a wurinmu, ba bakin ciki muke yi da takaici ba, taya su murna muke yi. In ma da abin bakin ciki, to bakin cikin namu ne, mu da ba mu san ya za mu karasa ba. Don mutuwa ‘la mahalata,’ za a mutu. Ko ka yi rashin lafiya ka mutu, ko ka mutu a hadarin mota, ko kuma a yi rikicin siyasa ko na kabilanci ko wani abu. Ga su nan. To amma duk a hanyoyin mutuwa din nan, to shahada, a kashe ka saboda wani yana ganin kai addini kake yi kuma ba ya son addinin, ya kashe ka, wannan sunnar Annabawa ce.

An kashe Annabawa da yawa, an kashe bayin Allah da yawa. Saboda haka duk burin Bawan Allah shi ne Allah ya sa ya yi irin wannan kyakkyawan karshe na wani ya kashe shi saboda ba ya kaunar sa don yana addini. Kuma Shaidan ya sawwala masa abin da yake yi daidai ne.

BA ZA KU TABA CUTAR DA MU DA KISA BA

A yau na gargadi masu kisa da kalmomi masu taushi ko za su wa’aztu, kuma na tsokane su da cewa don ubansu ko za su harzuka; duk wanda suka ga dama su dauka. Ko su ji haushi su zo su ci gaba da kisa, ko su wa’aztu su fasa; duk ruwansu. Amma mu muna tabbatar maku da cewa ba za ku taba cutar da mu da kisa ba, kuma ba za mu taba maku saranda ba har abada. Bara’a mun riga mun yi, da ita za mu rayu, da ita za mu mutu. Kuma ba mu ba ku a nan duniya, ba mu ba ku lahira. In kuwa kisa ne, sai mu ce ku ba da kokari. Yau muna tuna shahidanmu ne wadanda aka karkashe a wannan tafarki, wanda kuma burin kowannenmu, in da gaske ne kana Harkar nan.

KAR KA SHIGO CIKINMU IN BA KA SHIRYA MUTUWA BA

Don sukan yi don su ba mutane tsoro cewa kada su shigo. To mu ma muna so mutane su dauki darasi. Kar ka shigo cikinmu in ba ka shirya mutuwa ba; ja da baya matsoraci! Ba mu bukatar ka a nan. Kamar yadda ba su so ka zo, mu ma ba mu so ka zo. Ka zo kawai in ka yarda a kashe ka ne.

Tarihi bai taba nuna an kashe addini da bindiga ba. Bil hasali ma da wannan kisan da kuke yi, da shi yake tabbata. Mu mun san cewa ba za mu yi nasara ba sai kun karkashe mu. Kamar yadda Imam Khomaini, Allah ya rahamshe shi yake cewa, “ku yi ta kashe mu, sai mutanenmu su yi ta farkawa.”

Su a tsammaninsu in sun yi kisa din, sai abin ya mutu, to sai masu barci su farka. Saboda haka masu kisa ku yi ta kisa, ku yi ta ta yi. Mu kuma insha Allahu kun dinga ta da mu kenan, mun kuma dinga bumbuntowa kenan. Ku yi ta yi har ya zuwa lokacin da Allah ya rubuta za mu murkushe ku. Kuma tutar ‘La’ilaha illallahu’ ta filfila!

Wannan kasa insha Allahul Azim makomarta addini ne. Kuma wannan da’awa ta riga ta gabata. Nakan ga wadansu, habawa, ka makara! Sai ka ga ma wadansu ko meye muka yi, wai su ma sai su yi. Da aka yi fareti a nan ya burge su, su ma “didiririr” wai su ma suna fareti. Har da kareti, a sa wani gare-gare a yi wani cillawa. Na ce ka ga sunnar ’yan Burazas ba. To yana da kyau haka nan.

Haka ma ka ga Maulidi, masu gaba da Mauludi sun yi, sun yi, sun kasa, sai dada gaba yake yi. Har wani na cewa, “kai wadannan mutane, da har mun gama da Mauludi an daina yi, amma ga shi kuma ’yan Shi’an nan duk sun dagula komai. Duk sun dawo da Mauludin, kuma ya zama danye.” To kila in suka ga abin ya ki ci ya ki cinyewa, sai su ce “kai za a yi ba mu, Mauludau!”

Tunda yake na san lokacin da aka yi fareti a nan, da suka shiga gari, akwai wani Limami yana kuwwa a sifikar masallaci. Yana cewa; “na ga mutane suna kallon wannan fareti din, sun ganin ya ba su sha’awa. To wannan ba abin sha’awa bane, abin ku yi kuka ne, ba ku yi murna ba. Wannan hadari ne.” Ya ce wadannan mutane da suka gwada suna da tirenin, abu daya suke bukata, bindiga don su kwace gwamanatin kasar nan.”

BA DA BINDIGA AKE KWACE GWAMNATI BA

Da yake shi wawa ne, ba da bindiga ake kwace gwamnati ba. Za mu kwace gwamnati, kuma ba da bindiga ba. Canza tunanin mutane ne. Bilhasali ma, su za su yi amfani da bindiga don su hana, sai abin ya tabbata. Amma sune za su yi amfani da bindiga, ba mu ba. Ya ce bindiga kawai suke bukata don su kwace gwamnatin kasar nan.

To da suka ga abin ba na yi bane shi ne wai su ma suna kwaikwayo. To yanzu kuma mun yi asusun taimaka wa ’yan Nijar, saboda fama da yunwa da suke yi. Wai su ma za su yi asusu. To duk dai a yi ta ta yi. Ba komai, duk kuna koyon bidi’o’i ne da muke ta kirkirowa. In mun kirkiro bidi’a, sai ta burge mutum sai ya koya. Gama da suna cewa bidi’a, bidi’a, suna ta ihu, sai kuma su kwaikwaya. To ku ba da kokari, kun dinga zama Jama’atu bidi’atu kenan.

Haka kuma duk wanda yake ganin shi zai bullo da addini, don ya gane cewa sauyi da’awa ce, kuma ta riga ta gabata. A nan wurin ’yan watannin baya muka yi bikin cika shekaru 25 da ayyana da’awa, to tun wannan lokacin aka yi juyin-juya-hali din, ya rage kammalawa. Saboda, da can ana nizami wanda ke iko wanda ba ruwansa da addini, aka sami kira ya ce a koma ga addinin Allah. Shi kenan an riga an sami sauyi, ana bukatar kawai tabbata ne. Kar ka dauka wai yanzu kuma za ka zo ka ce wai ka yi da’awa, sai dai ka bi sunna. Wallahi sai dai ka yi koyi kawai! Duk wani wanda zai bullo da wani salon addini, ko ya ce yana shari’a, ko ya ce ya yi wata kungiya, ko ya ce yana mene, ko yana mene, oho dai, koyi dai kake yi insha Allahu. Mu kuma mun gode wa Allah (T) da ya yi mana baiwa da cewa mun yi addini ne ba domin mun yi ritaya daga aiki ba. Ba kuma domin an kore mu daga aiki ba. Ba kuma domin muna neman abin duniya ba.

Nakan ji ma har wasu suna ta surutun wai ana da kaza, ana da kaza. Da can ba a da shi, kuma aka yi addinin, yanzu kuma shi ma wannan abin duniyan da yake tsole maku ido, ba zai hana mu addini ba. Ku kowannenku abin duniyar yake so, in mutuwa ya hango ya danna a guje. Mu kuwa ku daki kirji ku ce mana matsorata mana, in kuna iyawa! Kun sun san ba zai yiwu ba. Ko da wani zai ce; “matsorata kawai, suna jin tsoron mutuwa.” Wani zai ce masa; “karya kake yi.” Saboda mu son Shahada din shi ne addininmu, shi ne burinmu. Babu wani dayanmu wanda ba burinsa kenan ya yi kyakkyawar cikawa ba. Kyakkyawar cikawar da ta fi kowanne, ita ce ita kanta mutuwar ta kasance ‘fisabilillah.’

Daga cikin ‘Ma’athur’ akwai inda ake cewa “Allahummaj’al Khaira a’amali khawatimah, wa khaira ayyami yauma alkaka.” Mutum yana fatan lokacin da shekarunsa suka yi yawa a lokacin Allah ya yawaita arzikinsa, ya kyautata ayyukansa, kuma Allah ya cika masa da mafi kyau. To wane aiki ya fi kyau da a ce ita kanta mutuwa ita ma a tafarkin Allah aka yi ta?

Ka ga a ce mu kaddara ka yi aiki mai kyau kamar yadda Imam Musa ya yi azumi ya yi bude baki da dabino wanda aka sa wa guba. Kun ga aikinsa na karshe kana iya cewa mene? Azumi! To amma kuma wanne ne ya fi? Daga azumi sai mutuwa, to amma sai ta zama ita kanta mutuwar kuma ita ma aiki ce fisabilillah. Ka ga cikawa kenan da mafi kyau, shi ne burin kowannenmu. Ya zama mutuwar tasa ba bingirewa zai yi ya mutu ba, zai zama ya yi shahada ne a tafarkin Allah.

YA RABBI KA BIDI JINAINAN SHAHUDAN NAN A KAN WADANDA SUKA YI WANNAN TA’ASA

Zan kammala wannan magana tawa da cewa Allah (T) muna rokon ka duk da mun yi farin ciki da murna, murnar sa shahadar ’yan uwanmu, amma muna rokon ka duk da haka Ya Rabbi ka bidi hakkinsu, ka bidi jinainansu, ka bidi hakkin marayun da suka bari a kan mutanen da suka yi wannan ta’asa. Muna rokon ka Ya Rabbi, wadannan la’anannu, Yahudawan duniya da kafircin duniya, da Amerika da Yammacin duniya da suka dirar wa Musulmi, Allah Madaukakin Sarki ka yi daidai da su. Allah ka nuna mana mummunan karshensu. Allah Madaukakin Sarki kuma duk wanda ya bi su ya taimaka masu, Allah ka hada da shi a ko’ina yake. Allah Madaukakin Sarki ka sa jinainan wadannan Shuhada ya zama ruwan da zai shayar da itaciyar tabbatar addini a wannan nahiya namu, ruwa har ya zuwa ga ganin tabbatar wannan addini. Allah Madaukakin Sarki ya sa kowannenmu ka yi masa kyakkyawan karshe da samun shahada a yayin da ajalinsa ya zo. Kuma ka rayar da mu rayuwar bayinka na gargaru wadanda suka tsaya kyam har suka yi shahada. Ka karbi ranmu irin yadda ka karbi ransu. Ka riskar da mu da mu da su. Ka sa kuma karshenmu insha Allahu tare da su ne, makomarmu Aljannar Firdausi insha Allahul Azim. Wassalamu alaikum warahmatullahi ta’ala wabarakatuh.

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


  | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International