Almizan :Hausa da Hausanci a karni na 21: Kalubale da madosa (3) ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 8 Zulkidah, 1426                 Bugu na 693                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Rubutun musamman

Hausa da Hausanci a karni na 21: Kalubale da madosa (3)

Abdalla Uba Adamu (auadamu@gmail.com)
Ci gaba daga makon jiya

AL’ADA DA HAUSANCI

Saboda haka da yawa daga cikin karon da ake yi na ma’anar al’ada, ana nufin ko dabi’a, ko kuma tada. Da yawa daga masu nazarin rayuwar Bahaushe suna musayar ma’anar al’ada da kuma tada ko kuma dabi’a. Domin tunatarwa, na fassara al’ada a matsayin sindarin mu’amalar mutum, ko kuma mores and mindsets, da Turanci.

Wannan sindarin mu’amalar shi kan fitar da abin da za a kira mutumin kirki, wanda kuma halayya ce, ko kuma tarbiyya. A takaice, al’ada hali ne, ba sarrafi ba. Wannan ma’aunin ya fito daga hannun masana da suka nazarci rayuwar Bahaushe a zamanin da ake ganin babu yawan cudanya tsakanin Hausawa da wadansu hanyoyin sadarwa da za a ce sun zama rariyar daukar wadannan halayen. Kuma tun kafin zuwan Musulunci, Hausawa na da wadannan halayen – da Musulunci ya zo, ya inganta sune.

A binciken da manazarta suka yi, an gano cewa al’adar Bahaushe, a bisa wannan ma’aunin na ma’anar al’ada, na tattare a sinadaran mu’amala guda 21. Wadannan ba sune kadai ba. Dole za a iya samun wadansu sinadiran; amma dai a wadannan masana kamar su Kirk-Greene da kuma Zarruk suka gina sinadarin al’adar Bahaushe da kuma Bafillace, tunda yanzu an zama daya. Saboda da haka a wannan ma’auni nasu, al’adar Bahaushe ita ce al’adar mutumin kirki a cikin al’ummar Hausawa. Takan yiwu sauran kabilun su ma suna da ire-iren wadannan, amma abin da ya fi damunmu a nan shi ne, yadda rayuwar Hausawa take, domin da mutum ya yi abu za ka ji an kwabe shi ana cewa, “haba, sai ka ce ba Bahaushe ba?” Wannan ya nuna ashe akwai ma’aunin Hausanci, ba wai kawai a tada ko dabi’a ba.

In an lura duk wadannan sinadirayen sun dogara ne a zuciyar mutum, amma suna amfani da dabi’a domin a aiwatar da su – shi ya sa ake ganin dabi’a da al’ada kamar daya ne. Misali, mutunci ne mutum ya sa tufafi masu kyau. Amma a dabi’ance, zai iya sa tufafin da suka dace da yadda ya sami kansa. Amma kuma ko da a haka ne, saka tufafin zai dogara ne ga shekarunsa – wanda kuma an jawo dattaku ciki. Misali, idan mutum dan shekara 50 mai sha’awar kallon wasan kwallon kafa, ya saka wandon jins da T-shat ta wani dan bal, da kuma hula hana-salla, to gani za a yi ya karya dokokin al’adar Bahaushe ta hanyar zubar da mutuncinsa, da kuma rashin nuna dattaku, duk da cewa babu wata illa ga kayan da ya sa, domin sun kare tsiraicinsa, sun dace da sha’awarsa ta kallon bal, kuma duk da cewa a wata alkaryar ta Musulmi (misali, Masar), za a iya samun takwaransa ya saka wadannan kayan, kuma ya samu karbuwa.

Saboda haka al’adar Bahaushe ba wai gine-ginen da ko na zamani bane. Ba wai iya dafa wani abincin da ko na yanzu bane; ba kuma saka tufafin da ko na yanzu bane. Al’adar Bahaushe yanayin hali ne wanda ya fitar da shi daban da sauran jama’a, ya zama duk inda yake yana wakiltar duk wani mutum da za a kira Bahaushe, kuma ta wani fannin, ko da Bamaguje ne. Misali, Bahaushen da ke zaune a Ingila ba dole ne ya sa manyan kaya irin wadanda zai sa a kasar Hausa ba. Amma yana da halayyar Bahaushen da komai jimawa a kasar da ya yi, za a san lalle Bahaushe ne. Saboda haka don bai sa manyan kaya ba, wannan halin zaman wurin ne ya kama haka, amma sinadarin halayensa na Bahaushe suna tare da shi, sai dai ya bijire musu, ko kuma ya dakatar da su saboda wadansu dalilai.

Bari in ba da misalina na karshe wanda yake da dangantaka da dalilin taruwarmu a yau. Babu abin da aka fi yawan saka shi a cikin kwandon da ba nasa ba kamar rawa da waka. Kusan duk mai yin magana a kan rawa da waka za ka ji ya ce ai al’adar Bahaushe ce. Ina da ja a nan. Rawa da waka ba al’adar Bahaushe bace, domin ba ta zama tilas a kan kowanne Bahaushe ba, sabanin halayyar al’ada, wadanda suka wajaba a kan duk wanda ke ikirarin shi Bahaushe ne.

Idan aka bi ma’aunin gwajin al’ada, to tabbas rawa da waka ba al’dar Bahaushe bane. Hasali ma dai yin su na nuna kusan rashin duk jerin ayoyin tarbiyyar da aka gina al’adar Bahaushe da su ne. Rawa da waka sana’a ne, saboda haka tadodi ne. Kuma ko a sana’ance, suna da muhallinsu; ta wani fannin ma gadonsu ake yi, ba shigege ba. Bugu da kari a rayuwar Bahaushe, mawaka da makada an dauke su a matsayin maroka. Su kansu mawakan, kamar Sani Dan Indo, suna nuna cewa ba sa fatan ’ya’yansu su gaje su a wannan sana’ar tasu, duk da sun yi kudi, kuma sun yi tashe a cikinta. Ganin haka ne ya sa ake nisanta al’adar Bahaushe ta tarbiyya, da rawa da waka.

A wannan rayuwar, rawa da waka ba su da matsayin rayuwar yau da kullum, kamar al’ada, saboda ba su zama dole ba. Akwai rayuwar da za a iya yi babu rawa da waka, kuma a zauna lafiya, domin wani ma ba ya son su ko kadan. Amma babu yadda za a yi rayuwa babu, misali, ladabi, dattaku, karamci, amana, da sauransu. Ashe saboda haka rawa da waka tunda ba su zama tilas a rayuwar Bahaushe ba, ba za a kira su al’adar Bahaushe ba.

Saboda haka in ka nuna mutum ya shiga bala’i, sai ya bige da rawa da waka, to wannan ya keta al’adar Bahaushe, domin a al’adance, zai yi tawakkali ne. Haka kuma komai farin cikin da zai samu ga mutum, ba za ka ga ya je wajen mahaifiyarsa yana yi mata rawa da waka ba; zai durkusa ne ya sanar da ita abin da rayuwarsa ke ciki, in har ta kai sai ya fada mata. Kuma komai soyayyar da mutum yake yi wa matarsa, babu yadda za ka ce al’adar Bahaushe ce ya dinga rera mata waka, ko don wa’azi ko don nishadi. Ita kanta in ya fara ma za ta dauka ko ya haukace ne!

Amma a tadance, lokacin biki, suna ko wani taro, in mutum yana so, zai iya tara makada da mawaka a cashe har gari ya waye. Wannan shi ya so. Amma a sigar zaman yau da kullum, ko su kansu da sana’arsu ce rawa da waka ba haka suke yin ta ba, domin su ma ba al’adarsu bace.

Saboda haka daukaka al’adar Bahaushe, daukaka addinin Musulunci ne, domin al’adar Bahaushe gaba dayanta na cikin Musulunci.

WAKILCIN BAHAUSHE A HANYOYIN SADARWA NA ZAMANI

Bari in rufe wannan dan gajeren jawabin nawa da waigen jigon wannan taron – wakilincin al’adun Hausawa da addini a Finafinan Hausa, kodayake masana za su yi magana a kan wannan nan ba da dadewa ba.

Fim wata hanya ce ta haskaka al’umma a da ko kuma a yanzu. Babban makasudin yin fim shi ne jawo hankalin jama’a ga wadansu abubuwa da ke gudana a rayuwar zahiri, da yin kalubale ga dorewar wadannan abubuwan. A takaice, idan mutum ya ce zai yi fim, yana da niyya ya wayar da kan jama ta yadda zai isar da sakonsa ta hanyar jawo hankalinsu ga lura da muhimancin sakonninsa. Wannan shi ne manufar yin fim daga wadanda suka kirkiro sana’ar, ba wai manufar fim daga yadda ’yan sana’ar na kasar Hausa suka dauka ba – domin sau da yawa a cikin hira da ake yi da ’yan san’ar fimafiman Hausa, sun ce ba don fadakarwa suke yin fim ba, sai don neman kudi.

Wannan babu aibu, domin in dai za a bi inganttacciyar hanya a nemi kudi, yana da kyau. Amma babban sabani a nan shi ne makasudin neman kudin. Rini, misali, shi ma sana’a ce, kamar fim. Amma babu marinin da zai ce da kai yana rini ne domin ya wakilci Hausawa. Haka ma duk makeri, ko manomi, ko mai sayar da yaduka, da sauransu. Inda fim ya bambanta, kuma aka saka ido a kai shi ne, ikirarin wakilcin rayuwar wadansu mutane da ake yi ta hanyarsa. Idan da fim bai zamanto hanyar wakiltar Hausawa bane, to da babu wanda zai damu da sana’ar, kamar yadda a yanzu ba za ka taba jin an yi wata bita a kan sayar da tsire ba!

Tari da yawa in ana takaddama tsakanin jama’ar gari, manazarta da ’yan fim, kowa maganar wakilcin al’adar Hausawa yake yi. Abin da ya kawo wannan kuwa shi ne saboda kowa na fassara al’ada yadda ya fahimce ta. Ina fata daga yau an sami wani abin kalubale a kan rabe-raben da ke tsakanin dabi’a, tada, da kuma al’ada.

Babban abin da ya jawo dalilin damuwa da wakilcin Bahaushe a sigar fimafiman ba wani abu bane illa ganin cewa da harshen Hausa ake wadannan fimafiman. Yin amfani da harshen Hausa ya nuna wa mai kallo cewa rayuwar Hausawa ake haskakawa, kuma ake wakilta. Ganin haka ya sa dole masu harshen su nuna damuwarsu in su a ganinsu ba a wakilce su daidai a wani fim ba. Tari da yawa kalubalen ba yana ga dabi’a, ko canza sigar tada bane; yana ga al’ada, wanda ya shafi tarbiyya. Ba za a samu ci gaba ba dole sai an zauna an yarda da ma’anar al’ada ta yadda kowa zai gamsu. Abin mamakin shi ne sauran al’ummatan da ke haskaka rayuwarsu ta hanyar fim, kamar Yarbawa da Ibo, ba su da wannan takaddamar; hasali ma yaba musu ake yi a kan yadda kullum a fimafimansu suke daukaka tadodinsu da al’adunsu.

Kamar yadda na ce, kalubalen ba yana ga canjin dabi’a ko tada bane. Idan mutum ya zauna a tebur ya ci abinci, ba wai ya bar rayuwar Bahaushe bane, shi kansa a zauna a gini mai kusurwa hudu ba na Bahaushe bane, ara ya yi daga wajen Larabawa. Idan Bahaushe ya ci cek a fim ba wai ya nuna Turanci bane, ai yana da gireba, wacce ita ma cek ce, amma daga wajen Larabawa ya aro, sai dai kawai a ce yin amfani da girebar ya fi a yi amfani da cek din, domin a inganta ita girebar, tun ma ba ga wadanda ba su san ta ba.

Idan an ce babban mutum a fim bai sa babbar riga ba, ai wannan ba aibu bane, ita kanta babbar rigar ba ta Bauhaushe bace, aro ta aka yi daga wajen mutanen kasar da yanzu ake kira ‘Western Sahara’ (wani yanayi na Buzaye). Idan an ce Bahaushe na cin abinci da cokali, wannan ba wani abu bane; da da hannu yake cin abinci, da ya samu cokali daga wajen Azbinawa ya ga ya fi tsafta ya ci abinsa da wannan cokalin. Kazalika nuna mutane a manyan motoci ba wai nuna bijirewar Bahaushe bane – da jaki da mota duk daya ne a rayuwar Bahaushe domin duk abubuwar hawa ne da aka aro su, amfani da kowanne ya danganta ga tatttalin arzikin mutum.

Duk wadannan ba sune tushen kalubalen wakilcin al’adar Bahaushe ba. Bari mu ga wadansu misalan keta wakilcin al’adar Bahaushe bisa wannan ma’aunin. Misali, mutum ya mari surikinsa. A wannan babu ladabi, biyayya, kara, karamci, dattaku, ko da kuwa shi surikin shi ya jawo a mare shi. Keta al’ada ne ’ya ta ce da mahaifinta, “ka yi kukan jini ma,” saboda an nuna rashin ladabi. Keta al’ada ne a nuna mutum da iyayensa suna zaune duk a kujera, sabanin shi ya zauna a kasa, domin in ya yi sahu da su ba a lokacin salla ba, to ya nuna rashin ladabin Bahaushe. Idan aka nuna Basarake da rawaninsa yana rawa a cikin mata, wannan ya keta al’adar Bahaushe, domin ya nuna wannan Basaraken ya zubar da mutuncinsa, ko da yana haka a cikin gidansa tsakaninsa da matansa, wannan ba haka yake a cikin jama’ar da sarautarsa ke wakilta ba.

A wannan babu maganar wani zamani, ci gaba, rage duhun kai na Bahaushe da sauransu domin wai a canza al’adar Bahaushe a zamanantar da shi. Rashin nuna kyakkyawar tarbiyya ba su daga cikin al’adar Bahaushe. Za a iya nuna rashin al’ada a gidan kara (wanda shi ne orijina na Bahaushe), sannan kuma a nuna tsabagen al’ada a katafaren gidan zamani. Saboda haka keta al’ada ko kuma nuna al’ada bai tsaya ga gine-gine, abinci, tufafi, motoci, kayan zamani da sauransu ba. Inganta sinadarin mu’amala na tarbiyya shi ne al’ada. In a fim an inganta wadannan, to an wakilci Hausa da Musulunci. In kuwa ba a yi ta, to ba a wakilci Hausa da Musulunci ba. Wannan ne babban kalubalen ke gaban mu – yadda za a kiyaye al’adun da muke tinkaho da su a zamanance.

Mun kammala.

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


  | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International