Almizan :Dangin Al-Zarkawi sun sake nisanta kansu da shi ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 8 Zulkidah, 1426                 Bugu na 695                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Duniya Labari

Dangin Al-Zarkawi sun sake nisanta kansu da shi

Daga Aliyu Saleh

Sama da mutane 370 ne a cikin dangi da ’yan uwan Shugaban Kungiyar Alka’ida reshen Iraki, Bajodane, Abu Mus’ab Al-Zarkawi suka sanya hannu a kan wata takarda da take Allah wadai da irin aikace-aikacen da yake yi.

Iyalin na Abu Mus’ab al-Zarkawi, wadanda suka sa hannu a kan wata takarda mai shafi guda da aka buga a jaridun Jordan sun yi da na sanin haihuwarsa.

Wasikar, wace ta biyu ce da dangin na Abu Mus’ab al-Zarkawi suka rubuta a kasa da kwanaki 20 ta roki Jodanawa da su yi watsi da duk wani mayakin da ya dauki alhaki ko ya danganta kansa da harin kunar bakin wake uku da aka kai lokaci guda a ranar 9 ga Nuwamba a otalolin da ke Amman, wadanda suka yi sanadiyyar kashe mutane 60 da kuma jikkata da dama.

Wannan wasikar ta zo kwana daya bayan Abu Musab al-Zarqawi, wanda shi ne Jagoran Kungiyar Alka’ida a Iraki, shi ma ya yi watsi da wannan dangin nasa, tare da sukar wannan sanarwar da suka bayar inda suka yi Allah wadai da shi.

“Makiyin Allah da ke jagorancin kasarmu (Sarki Abdallah) ne ya ingiza ku har kuka dauki wannan matakin a kaina. Wannan haka yake, ko kun yarda, ko ba ku yarda ba,” a ta bakin mai magana da yawun Al-Zarkawi, Abu Maysara al-Iraki.

Ya kara da cewa; “tunda wannan shi ne karo na farko kuna da uziri, amma a karo na gaba ba ku da ta cewa a gaban Allah Madaukaki.”

Abu Mus’ab al-Zarkawi, wanda sunansa na gaskiya shi ne Ahmad Fadheel Nazzal al-Khalayleh, ya samo wannan sunan nasa na Zarkawi ne daga Zarka, sunan birnin da aka haife shi da ke da nisan kolomita 17 arewa maso gabashin Amman.

Kungiyarsa ta Alka’ida dai ita ke daukar alhakin yawancin hare-haren bom da ake kai wa a masallatai, wuraren taruwan jama’a da kasuwanni, da kuma sace mutane a yi garkuwa da su a Iraki. Sojan mamaya na Amurka sun sa ladan Dalar Amurka miliyan 25 ga duk wanda ya kawo masu kansa, ko kuma ya ba su labarin da ya yi jagoranci ga damke shi.

“Mu ’ya’yan gidan Bani Husaini da suke dangantaka da masarautar Hashemite da ke Jordan, muna da goyon baya daga wajen jama’ar Jordan, amma muna Allah wadai da wannan aikin da kake yi,” in ji al-Khalayleh, daya daga cikin dangin Ahmad Fadheel Nazzal al-Khalayleh da ke kiran kansa Abu Mus’ab al-Zarkawi.

Wasikar, ta ci gaba da cewa, “muna Allah wadai da duk wani nau’i na ta’addanci wanda yake shafar mutanen da ba su san hawa ba su san sauka ba, ciki kuwa har da ’yan kabilar da muka fito.”

Bani Husaini, daya ne daga cikin mutanen dauri da suka yi suna, musamman a aikin soja, kuma ake girmama su a Jordan. Iyalan wannan gidan sun rike manyan matsayi da mukamai masu daraja a Ma’aikatun gwamnatin kasar.

A wasikar farko dai da dangin na Abu Mus’ab al-Zarkawi suka rubuta a ran 20 ga Nuwambar da ya gabata dai, mutane sama da 60 suka rattaba mata hannu, inda dukkansu suka yi Allah wadai da shi, suka ce ba su yi sa’ar haihuwa ba.

Tuni dai wata kotu a Jordan ta yanke masa hukuncin kisa a bayan idonsa, bayan shirya kai wani hari ga dakarun Amurka da ya yi sanadiyyar mutuwar Laurence Foley a 2002.

Tuntuben Kungiyar Alka’ida a kasar Jordan

Daga Uba Ahmad Ibrahim Jos (ubaahmad@yahoo.co.uk)

A kwanakin baya ne aka kai wani mummunan harin kunar bakin wake a Amman babban birnin kasar Jordan. Kungiyar Alka’ida bangaren Abu Mus’ab Alzarkawi a Iraki ta ce ita ce da alhakin kai harin.

Tun daga nan ne fa masharhanta da masana harkokin yau da kullum a yankin suka hau fadin albarkacin bakinsu, suna kuma ta aikin zakulo miyagun ayyukan da Kungiyar Alka’idan ke yi a yankin.

A wannan karon ra’ayi ya kara zamowa daya wajen cewa hauragiyar da Kungiyar Alka’idan ke yi sai kara kazanta yake yi. Allah wadai kuwa ba a taba ganin kamar sa a yankin cikin tsukin nan ba, domin su kansu masu goyon bayan Kungiyar Alka’idar ta Usama Bin Laden ba su ji dadin abin ba ko miskala zarratin.

Kuskuren Kungiyar Alka’idan a nan shi ne yadda suka bar fagen faman da suka yi imani da shi, inda suke yakar dubban daruruwan sojojin Amurka da kawayenta a kasar Irakin, suka taho Jordan suka tayar da bama-bamai a gurin da ke cike da mutane fararen hula, wasu ma biki suka zo na aure.

A cewa jami’an Kungiyar ta Alka’ida bangaren Iraki sun yi hakan ne domin goyon bayan da kasar ta Jordan ke bai wa Amurka a fagage da dama da suka shafi zamansu a Irakin, ba su san kuma kasar ta Jordan ba za ta iya toshe iyakarta da Iraki ba saboda yadda dubban ’yan Irakin da a kullum suke shigowa kasar domin biyan bukatunsu, kamar yadda ba Jordan kadai ba, makwabtanta ma irin su Saudi Arabiyya da Kuwait da Katar da Bahrain dukkansu ba za su iya kawar da kai a wannan lokaci daga bai wa sojojin kawance hadin kai komai kankantarsa a game da batun Iraki ba.

Ko ba komai za a iya daukar kasar Jordan a zaman mashiga ko mafita ta akasarin ’yan Iraki, ba talakawansu kadai ba, har ma da jami’an gwamnati da ’yan siyasa da ’yan Shi’a da kuma Malaman Sunnah.

Da wuya kuwa a ce wadannan al’ummomi na Iraki su iya wani motsi na ziyartar kasashen waje in ba su sami damar zirga-zirga ta hanyar Jordan ba. Wadannan abubuwa sun sa jama’a da dama daukar hare-haren a zaman ayyukan ta’addanci masu munin gaske wadanda shari’ar Musulunci ke kyama a kowane lokaci.

Wani abin takaicin kuma shi ne, yadda biyu daga cikin masu kunar bakin waken, -namiji da matarsa- suka shiga zauren da ake bikin aure sun ganewa idanuwansu abubuwan da ke gudana ga yara da mata cikin hijabi da makamantan hakan, amma kuma ba su fasa aikata wannan aika-aikar ba.

Sanin kowa ne cewa Usama Bin Laden bai taba yarda da a kai hari kan guraren da ke cike da Musulmi ba, haka kuma Mataimakinsa Aiman Al-zawahiri shi ma bai yarda da haka ba, ko da a kan ’yan Shi’a ne kuwa da dukkan sauran kungiyoyi da ake zaton ba jituwa suke yi da su ba, don haka ake ci gaba da shakku da mamakin ko dai kungiyar ta Alka’ida ta fara canza manufofinta ne, ta inda hatta fararen hula Musulmi maza da mata yara da manya ma ba za su tsira ba in har suka tashi kai hare-harensu?

Abin da zai sa a zaci ba haka lamarin yake ba shi ne; Allah wadai din da aka dinga yi ko ta ina hatta daga magoya bayan Alka’idan kanta, inda wani ma ta shafin sakar sama (Intrenet) ya yi kira ga Zarkawi da ya fito fili ya yanke wuyan wanda ya bayar da umurnin aikata wannan aika-aikar, saboda saba ka’ida da ya yi.

Batun bata wa Kungiyar suna kam da harin ya yi ba a magana, kuma tasirin hakan da wuya ya takaita a kan Kungiyar ita kadai, don kuwa ba mamaki ya kai ga sauran masu gwagwarmaya a Irakin da Afghanistan da kuma yankin Palasdinawa baki daya.

Idan kuwa hakan ya tabbata, to, Kungiyar ce babbar wadda ta tafka asara, domin sai da goyon baya daga ire-iren mutanen da suka amince da abin da suke yi ne za su iya ci gaba da gwagwarmayar tasu, idan kuwa suka fara rasa hakan, to hatta ma karin mutanen da za su dinga samu –musamman matasa- wadanda a kullum a cikinsu ake samun wadanda suke a shirye su ci gaba da aiwatar da ayyukan da ake sa su, ba karamin karanci zai yi a nan gaba ba.

Ba abin da ba ya bukatar siyasa wajen aiwatar da shi, musamman idan ya zamo zai kai ga sanya jama’a cikin mawuyacin hali, duk da cewa ana samun masu goyon bayan Kungiyar Alka’ida a wurare masu yawa a kasashen Musulmi, to, amma kuma fa akasarin masu yin hakan suna yin hakan ne saboda yaki da take yi da Amurka, amma daga ranar da ta fara kai hari har a kan Musulmi fararen hula, to, lalle ba karamar koma baya za ta samu ba.

Uba Ahmad Ibrahim ma’aikaci ne a sashin Hausa na rediyon Jamus, yana zaune ne a Masar. Ya aiko mana da wannan rubutun ne ta I-mel dinsa (ubaahmad@yahoo.co.uk).

Bi-ta-da-kulli bayan mutuwar Hariri

Daga Hasan Muhammad

Karin matsin lamba ta kasa da kasa da ake yi wa Siriya tun bayan da aka fitar da takardar bayani ta mai gabatar da kara dan Jamus, Detlev Mehlis, kan kisan da aka yi wa tsohon Firaministan Lebanon, Rafiq Hariri, al’amarin sai sauya kama yake yi.

Yayin da bayanai suke ta kara fitowa kan yadda ake zargin Amurka na da hannu a a cikin kisan yana ta kara sa alamar tambaya kan cewa me Amurka ke son ta cimmawa da wannana kisan?

Kuma ko ba koma ita kanta Lebanon ba ta nemi taimakon Amurka ba kan wa ke da hannu cikin kisan, amma Amurka ta yi kane-kane, ta yi uwa ta yi makarbiya cikin lamarin.

Tun bayan mutuwar Hariri ne dai cikin wani mummunan hari da aka kai masa a watan Fabrairu, hankalin kasashen duniya ya karkata ga kasar Siriya, inda masu sharhi ke ta faman maimaita abin da Amurka ke furtawa na cewa Siriya na da hannu cikin kisan na Hariri, duk da cewa ba su da wata kwakkwarar hujja kan hakan.

Haka kuma duniya ta amince ba tare da wani kokwanto ba cewa Siriya ce, yayin da kafafen yada labarai na kasashen Yammacin duniya suke nuna cewa wancan rahoto na Alkalin Jamus shi ne hujja ingantacciya da ke nuna cewa Siriya na da hannu a cikin kisan. Ba haka ba, suna nuna cewa duk wasu har-hare ma da aka kai a baya ita Siriya na da hannu a ciki, kuma yunkuri ne da Siriya din take yi na ganin cewa ta wargaza kasar Lebanon.

Haka kuma batun da Washington ke yi na cewa ta dauki tsattauran mataki ne a kan Siriya saboda yaki da ta’addanci ko kuma wani yunkuri ne da gwamnatin ta Amurka take yi bayan aukuwar lamarin 11 ga Satumba da nufin hana aukuwar makamancinsa a Amurkar, shi ma dai abu ne da aka kasa ganewa.

Abin da ya fito fili kuma aka gane shi ne cewa tsoma bakin da kasashen Yamma suka yi cikin harkokin kasashen Larabawa ba wani batu ne na yaki da ta’addanci ba, illa kawai wani mummunan shiri ne da a yanzu ba kowa zai iya fahimtar hakikanin yadda yake ba. Sai dai wani abu kuma da aka iya ganewa shi ne; tun bayan rushewar Tarayyar Sobiyet, wadancan kasashen na Yamma ke ta hakon arzikin man da ke dankare a kasashen Musulmi, musamman ma dai ita Amurka.

Sai dai har yanzu Amurka ta gaza cimma burinta na shawo kan kasashen tsakiyar Asiya don cimma burinta. Pakistan, Iraki, Turkiyya da Afghanistan, wadanda dukkansu suke kan hanyar da za ta kai ga inda dimbin arzikin man yake, tuni ta gama da su, suna cikin aljihunta. Wannan ne ma ya sa batun 11 ga Satumba ya amfani Amurkar matuka da gaske, domin ko ba komai wadannan kasashen sun ba ta dukkan hadin kan da take bukata wajen cimma burinta. Kuma babba burinta shi ne yadda za ta mallake wadannan kasashen mataki-mataki.

Yanzu da Amurka ta tsoma kazamar kafarta a Iraki, kuma ga dukkan alamu ba tana nufin ta tafi bane haka nan, inda take hari kuma nan gaba ita ce Siriya, kamar dai yadda masu nazarin harkokin yau da kullum suka nuna. Domin ko ita kanta Faransa ta bi sahun Amurka wajen bayyana Siriya da cewa ’yar ta'adda ce.

Wani sharhi da jaridar ARAB NEWS ta buga, ya nuna cewa ba wani abu ne ya sa Siriya ta zamo a saman jerin sunayen da Amurka ke son ganin bayansu ba, illa saboda cewa ta ki ta mika kai bori ya hau kamar yadda sauran kasashen suka yi.

Wasu na iya tambaya me ya sa aka sa Siriya a gaba ba Iran ba? Ba shakka kai wa Iran hari ba shi da sauki. Da ma kuma ga shi tuni ita Amurka ta lizimci wani yakin a Iraki, kuma ana jin tsoron cewa ba mamaki a ce ma tuni Iran din ta mallaki makamin nukiliya. Amma kasantuwar cewa da ma tuni tana da dakarunta a kasa, zai fi wa Amurka sauki ta auka wa Siriya maimakaon ta farmaki Iran.

A ranar Juma’ar makon shekaranjiya ne dai tsohon Shugaban Iran, kuma Shugaban Hukumar Fayyace Maslahar Musulunci ta Iran, Ayatullahi Hashemi Rafsanjani, ya zargi kasashen Yamma da laifin matsin lamba ga Siriya. Da yake jawabi ga masallata a ranar Juma’ar Rafsanjani ya yi kira ga kasashen duniya da su tsawaita kada a jefa yankin Gabas ta Tsakiya cikin rikici.

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


 Shafin Gamji | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International