Almizan :Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 8 Zulkidah, 1426                 Bugu na 695                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Babban Labarinmu

Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kaduna
Yadda aka yi waje-Rod da shi

Daga Musa Muhammad Awwal

A halin da ake ciki dai mulkin da Alhaji Bashir Zubairu ke yi wa jama’a a matsayinsa na Shugaban Majalisar Dokokin jihar Kaduna ya zo karshe, domin a ranar Talatar da ta gabata ne aka tsige shi daga kan mukamin nasa bayan wata fafatawa da aka yi a zaman majalisar na ranar.


Wakilinmu da ya shaidi wannan badakalar, ya kuma shaida mana cewa shugabancin Alhaji Bashir Zabairu ya zo karshe ne a sakamakon wata hayaniya da ta tashi a zauren majalisar bayan an karanto wata takarda da Gwamnan jihar Kaduna, Alhaji Ahmad Muhammad Makarfi ya aiko wa majalisar yana rokon su da su sassauta hukuncin da suka yi wa Shugaban Karamar Hukumar Lere a kwanakin baya.

Da ma ga dukkan alamu shi Bashir ya san da wannan aniya ta wasu ’yan majalisar cewa suna niyyar tsige shi, don haka ko da aka kammala karanta waccan wasika ta Gwamna, sai kawai aka nemi a dage zaman majalisar zuwa wani lokaci, wanda hakan bai yiwu ba, wasu suka ce sam ba su yarda ba.

Wakilin namu ya ci gaba da shaida mana cewa, bayan da kalamai suka fara yin zafi ne, sai shi Dogarin majalisa ya dauki sandar majalisar don ya jagoranci ficewa daga majalisar, amma ina hakan ba ta yiwu ba, domin kuwa ko da wasu suka kyallara ido suka ga ya sungumi sanda, sai kawai suka dumfare shi suka kawace sandar.

Honorabul Maria Samuel Dogo daga Karamar Hukumar Chikun da Honorabul Muhammad Sani Iliyasu (Baba) daga mazabar Kawo ne suka jagoranci kwace wannan sanda, kuma nan da nan ba tare da bata lokaci ba suka yi waje da sandar, wanda kuma a ka’ida ficewa da sandar nan daga zauren majalisar ya kawo karshen Shugabancin Bashir Zubairu, wanda kusan kowa yana madalla da wannan abu.

Daga bisani su membobin majalisar sun shiga wani taron sirri, wanda kuma bayan sun kammala taron, sai suka nemi manema labarai wadanda dama suna nan suna jira a waje, aka kira su domin a shaida masu sakamakon taron.

Wakilinmu da yake cikin manema labaran da suka sami shiga dakin taron, ya shaida mana cewa Shugaban masu rinjaye na majalisar, Alhaji Abdullahi Adamu Ikara ne ya bayyana wa manema labaran sakamakon taron nasu.

Alhaji Abdullahi Adamu ya bayyana cewa sakamakon abin da ya faru a majalisar, sun zauna sun tattauna kuma sun zartar da cewa sun tsige Alhaji Bashir Zabairu Birnin Gwari daga matsayin Shigaban majalisar dokokin jihar Kaduna saboda wadansu dalilai, kuma nan take sun nada Mataimakin Shugaban Majalisar, Hon. Emmanuel Maisango a matsayin Shigaban riko kafin su sake zabe.

Shugaban masu rinjayen ya shaida wa manema labaran dalilansu na tsige Bashir, wadanda suka hada da rashin mutunta majalisar, mulkin kama-karya, rashin mutunta jama’a da dai sauran wasu hujjoji.

Don haka sai Alhaji Abdullahi Adamu Ikara ya ce sun dogara da tsarin mulki na 29-2c na shekarar 1999 sun tsige Bashir daga shugabancin majalisar dokokin jihar Kaduna, wanda ya ce mambobi 25 ne suka rattaba hannun nuna goyon baya, 9 ne kawai ba su sanya hannu ba.

Manema labaran sun tambayi Alhaji Ikara, ko wadanne halaye suka gani suka ce Bashir ba ya ganin mutuncin membobin? Sai ya ka da baki ya ce “bari in ba ka wani misali guda daya, idan muka sanya zaman majalisa karfe10:00, to Bashir ba ya zuwa sai 11 ko ma fiye.”

An kuma tambaye shi cewa anya kuwa wannan mataki nasu ba daga fadar Gwamnatin jihar ne aka kullo shi ba? Nan take ya ce shi dai ya sani a iya saninsa, sune suka gaji da halayen Bashir kuma suka tsige shi. Don haka sun san cewa za a sami zargi da dama, amma su bai dame su ba, ko mai mutum zai ce ya ce, su dai sun aiwatar da abin da suke ganin shi ya fi masu. Kuma sun yi haka ne don suna neman gyara.

In dai ba a manta ba, wannan abu da ya faru, kaikayi ne ya koma kan Mashekiya, domin shi ma Bashir din yataba kwace sandar, ya kuma karyata ya fito a guje ya haura ta Katanga ya tafi da ita a karon farko na wa’aadinsu. Kuma ya aikata wannan abu har kimanin sau biyu.

Don haka ne wasu ke ganin cewa abin da ya yi wa wasu ne shi ma yau ta koma kansa.

A wata sabuwa kuma, tsigaggen Shugaban majalisar, Zubairu ya shaida wa wasu manema labarai a ranar da aka tsige shi a gidansa cewa shi dai a iya saninsa shi ne Shugaban majalisar, kuma da zarar gari ya waye zai nufi ofishinsa ya ci gaba da aiki.

To, amma Wakilinmu ya shaida mana cewa ko da garin ya waye, Bashir ko leka ofis din bai yi ba. Don haka ne wasu ke ganin cewa da ma dai kurari ne kawai.

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


  | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International