> Almizan:Matsafa sun kashe Ibrahim Shekarau ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 8 Zulkidah, 1426                 Bugu na 695                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Babban Labarinmu

Rashin tausayi!!

Matsafa sun kashe Ibrahim Shekarau

Sun kwakule masa idonsa
Daga Aliyu Saleh

A ranar Lahadin makon jiya ne aka tsinci gawar wani yaro dan shekara biyu da haihuwa an kwakule masa ido an yar da shi a gefen titi a kusa da gidan gwamnati na Hasan Usman Katsina da ke Kaduna.


Malam Ali Mai Fulawa, shi ne ya fara isa wajen gawar, ya bayyana mana cewa lokacin da aka kawo masu labarin abin da ya faru sai ya garzaya ya sanar da ’yan sanda da ke New Barak, “don kada su kulla mana sharri, su ce muna da masaniya, duk da kuwa taimako muka je yi.”

Binciken da muka yi ya gano cewa bayan ’yan sanda sun isa wajen da aka ga gawar yaron ne, sai aka dauke ta bayan an yi mata hoto, aka kai ta dakin ajiye gawawwaki na asibitin ‘Nursing Home’ da ke Kaduna.

Bayan kamar awa biyu ne da tsintar yaron, Mahaifinsa, wanda dama tun ranar Juma’a (ranar da yaron ya bata) ya kai rahoto wajen ’yan sanda ya samu labarin an ga gawar wani yaro karami ya je domin ya tabbatar ko ta dansa ce.

Bayan ya isa asibitin ne, ya gane gawar dansa Ibrahim Shekarau ce da ya bata a gida dab da sallar Magariba ta ranar Juma’ar makon da ya gabata. Daga nan sai suka amso gawar suka yi mata jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

ALMIZAN ta isa gidan su Ibrahim Shekarau da ke a No 15 Layin Kusfa Kawo Kaduna, inda Mahaifin yaron, Malam Iliyasu Adamu da aka fi sani da Shekarau, 30, ya bayyana mana yadda ya kadu lokacin da ya ga gawar Ibrahim dansa a kwance ta kumbura an kwakule mata ido, bayan an shake masa wuya da kebul.

Malam Shekarau, wanda yake direba ne, ya bayyana mana cewa ya yi wa Ibrahim ganin karshe ne, lokacin da suka tafi unguwa da Mahaifiyarsa da safe, shi kuma ya kama hanyar zuwa wajen aiki. “Ni zan fita aiki da safe, shi kuma ya zo yana ce mani ‘Baba sai ka dawo.’ Sai kawai da Magariba aka yin min waya aka sanar da ni cewa ba a ga Khalifa ba.”

Ya ce daga nan suka bazama nema cikin gari da kuma wuraren ’yan sanda. “Ba mu yi barci ba a ranar har 12 na dare, amma duk ba labari. Haka muka ci gaba da zama cikin tashin hankali, muna ta addu’i’o da kuma cigitawa. Sai a ranar Lahadi muka samu labarin ganin wani yaro da aka tsinta. Bayan na isa wajen da yake, sai na ga Khalifa ne, muka dauko shi muka yi masa jana’iza.”

Malam Shekarau, wanda ya bayyana cewa su ba su san yadda aka yi aka sace yaron ba, ya ce ba sa zargin kowa game da wannan al’amari, sun danganta komai ga Allah. “Har yanzu ba wani labari game da wannan. Mu ba wanda muke zargi. Duk wanda ya yi mana wannan ya yi wa kansa, mun bar shi da Allah. Matakin da muka dauka kawai shi ne addu’a da kuma kara kula da sauran.”

Ita kuwa Mahafiyar Ibahim Shekarau, Malam Maryam Ibrahim, 23, cikin kuka ta ce ba ta taba ganin tashin hankali irin wannan ba. “Muna jin labarin satar mutane a nesa, amma yau ga shi ya iso gare mu. Duk wanda ya sace mun Khalifa ya cutar da ni, amma ba komai Allah na nan.”

Malama Maryam, wacce take rike da Aliyu kanin Khalifa a lokacin da muke hirar, ta ce ita ta yi imani da Allah cewa ko da makasan ba su sace Ibrahim sun je sun kashe shi ba, da ma Allah ya tsara ba zai kwana ba. Amma abin da yake yin min bakin ciki a rayuwata, idan na tuna hankalina yake tashi shi ne, irin yanayin da aka kashe shi. Kisan wulakanci da wahalar da yaron ya fuskanta. Ni dai na dogara ga Allah, Ibrahim ba shi da hakkin kowa a kansa sai nawa, ni kuma na yafe masa.”

Kodayake ta ce ita ba ta zargin kowa game da wannan al’amari, “amma Allah da ya yi ni, ya yi su, ya fi mu sanin ko su waye suka yi mana haka. Mu dai mun bar wa Allah.”

Muhammad Sani Jagwa, mazaunin Hayin Bankin Kaduna, yana daga cikin mutanen farko da suka fara isa wajen da aka tsinci gawar Ibrahim Shekarau, ya bayyana mana cewa ya ga yaron an kwakwle masa ido kuma gawarsa har ta fara kumbura.

Ya dora alhakin wannan mummunan aikin a wuyan masu neman abin duniya ko ta halin-kaka. “Muna rokon Allah ya daidaita masu aikita wannan ta’asar.”

Malam Jagwa ya zargi gwamnti da yin sakaci da kuma jan kafa wajen taka wa masu satar mutane suna kashe su burki. “Gwamnati ba da gaske take yi ba wajen yaki da masu satar mutane. Mu dai yanzu mun zura wa gwamnatin ido ne kawai, domin mun san ba abin da za su iya yi don kare mana rayukanmu. Yanzu da manya da yara a Nijeriya duk suna cikin hatsari saboda ko a gida kake mutanen nan za su iya bin ka su kama ka su kashe su kwakwale maka ido su tafi.”

Ya yi kira ga iyayen yara da su ci gaba da yin kaffa-kaffa da ’ya’yansu, “a bar sakin ’ya’ya barkatai haka nan. Da babba yaro kowa ya rika kafa-kaffa da kansa. Su kuma wadanda suka yi wannan Ubangiji Allah ya tona masu asiri.”

Shi kuwa Malam Adamu Yunusa da ALMIZAN ta same shi a wajen da aka tsinci gawar Ibrahim Shekarau, ya bayyana mana kaduwarsa da wannan labarin da ya ji. Ya ce kasanceewar ana yawaita samun irin haka a garin Kaduna suna cikin hatsari. “Irin wannan abin yana matukar ta da hankalinmu babu ma kamar magidanta. Ina kira ga iyaye mata da su kula da yara.”

Shi ma ya dora alhakin wannan aika-aikar a wuyan wasu mutane da suke neman duniya, “masu neman duniya ko ta halin kaka su ke aikata wannan mummunan aikin.” Ya koka matuka a kan yadda ake sakin wadanda ake kamawa da ake zargi da aikata wannan mugun aikin. Ya kamata a rika hukunta su kamar yadda shari’a ta tanada.

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


  | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International