Almizan :Allah ya yi wa Dakta Hadi Shaikh Dahiru Bauci rasuwa. ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 8 Zulkidah, 1426                 Bugu na 695                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Babban Labarinmu


Allah ya yi wa Dakta Hadi Shaikh Dahiru Bauci rasuwa.

Daga Adamun Adamawa


A ranar Talatan nan ne Allah ya yi wa Dakta Hadi Dahiru, babban dan Shaikh Dahiru Usman Bauci rasuwa, daya daga cikin manyan Malaman Nijeriya, sakamakon wani hatsarin mota da suka yi a kan hanyarsu ta dawowa daga garin Jama’are zuwa Bauci.

Shi dai Dakta Hadi Dahiru Usman Bauci yana aikin ne na wani kwamitin kusanta juna tsakanin musulmi da kirista, wanda gwamnatin Tarayya ta kafa karkashin jagorancin Sarkin Ningi da ake kira INTER-RELEGION COMMITTEE. Suna zazzaga Kananan Hukumomin jahar Bauci, kafin su kai ga zaga jihohin Nijeriya.

Wannan hatsarin dai ya faru ne da misalin karfe 9:00 na dare a hanyarsu ta dawowa daga Jama’are, sakamakon yunkurin wuce (over taking) wata babbar mota da direban nasu ya yi, sai kuma ga wata roka, nan take aka yi taho-mu-gama, motane hudu suka rasu nan take, bayan kuma motocin sun yi kaca-kaca, yayin da wasu suka samu raunuka.

Baya ga Dakta Hadi da ya rasu a hatsarin, akwai kuma wani dan jarida Abubakar Zubairu, sai wani Arch Bishop na cocin Anglican da ke garin Bauci.

Sauran mutanen cikin motar mafi yawa sun samu raunuka. Malam Yakubu Isa Sulaiman daya ne daga cikin ’yan tawagar, wanda kuma shi ne mai daukar hoton da ke wakiltar Karamar Hukumar Bauci, ya shaida mana cewa; “tun lokacin da muka taso daga Jama’are, Dakta Hadi da ke zaune a gaba, ba abin da yake yi sai karatun Alkur’ani, har lokacin da muka shiga hadarin, kowa na salati, amma shi karatun Alkur’ani ya ci gaba da yi. Wallahi har ya rasu abin da yake yi kenan,” in ji shi.

An dai yi jana’azar Dakta Hadi ne da misalin karfe 4:00 da ’yan mintuna a kofar fadar Sarkin Bauci. Daga cikin dimbin jama’ar da suka halarci salar har da Gwamnonin Bauchi da Gombe da kuma wasu ’yan Majalisa da manyan kusoshin gwamnatin jihohin.

Jama’a sun yi ta rusa kuka a lokacin da ake yin jana’azir. Wasu somewa suka yi lokacin da suka samu labarin rasuwar Dakta Hadi.

Dakta Hadi shi ne babban dan Shaikh Dahiru Usman Bauci, kuma shi yake turawa ya wakilce shi a kusan duk wasu al’amuran da suka taso masa. Wannan rasuwar ta jijjiga Shaikh Dahiru Bauci sosai, sai dai duk da haka wadanda suka gan shi sun ce ya nuna juriya sosai.

Har ya zuwa lokacin da muke rubuta wannan rahoton dai jama’a daga kusan duk kusuwar kasar nan sai bumbuntowa suke yi garin Bauci don yi wa Shaikh Dahiru Bauci da sauran dangi ta’aziyyar wannan babban rashin da aka yi. Allah ya ji kan sa da gafara, ya sa Aljanna ce makoma, amin.

ALMIZAN na mika sakon ta’aziyyarta ga Shaikh Dahiru Usman Bauci dangane da wannan rashin da muka yi, Allah ya yi masa rahama, ya sa ya huta, amin.

ALLAH YA JI KAN DAKTA HADI DAHIRU BAUCI

Harka Islamiyya, karkashin jagorancin, Shaikh Ibraheem Yaqoub Zakzaky, na mika sakon ta’aziyyarta da jaje ga Shaikh Dahiru Usman Bauci da suran iyalai dangane da rasuwar babban dansa, Dakta Hadi Shaikh Dahiru Usman Bauci, wanda ya Allah ya yi wa cikawa ranar Talatar nan da ta gabata sakamakon hatsarin mota da ya rutsa da shi a kan hanyarsa ta dawowa Bauci daga Jama’are. Hakika wannan babban rashi ne ba kawai ga iyalan Dakta Hadi ba, amma har da Musulmin duniya da Musulunci baki daya. Muna rokon Allah ya ji kan sa da gafara, ya sa ya huta, ya sa Aljanna ce makoma, mu kuma da muka rage a duniya, Allah ya sa mu yi kyakkyawan karshe, amin.

Sanarwa daga Harka Islamiyya, karkashin jagorancin, Shaikh Ibraheem Yaqoub Zakzaky.

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


  | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International