Almizan :Zubairu Hamza ne gwarzon musabaka ta bana ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 8 Zulkidah, 1426                 Bugu na 695                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Babban Labarinmu

Zubairu Hamza ne gwarzon musabaka ta bana


Daga Ali Kakaki

Gasar musabakar Alkur’ani ta kasa karo na 20, wanda gwamnatin jihar Kano ta dauki nauyin gudanar da shi aka kuma kammala shi a ranar Asabar din makon shekaranjiya, Malam Zubairu Hamza Tahir Hotoro daga Karamar Hukumar Nassarawa a cikin jihar Kano ne ya amshe kambun gasar, inda ya zamo gwarzon shekara a gasar musabakar ta bana, ya kuma doke abokan takararsa daga jihohi 28 da suka halarci bikin, shi ne kuma zai wakilci Nijeriya a gasar musabakar ta duniya da za a yi a kasa mai tsarki, Saudiyya.

Malam Zubairu Hamza, ya zamo gwarzon shekarar ne a gasar hizifi 60 da tafsir, ya kuma samu kyaututtuka da suka hada da mota kirar KIA daga gwamnatin jihar Kano, sai wata motar kuma daga Gwamnan jihar Bauci, inda shi ma Gwamnan Zamfara ya ba shi mota. Ya kuma samu kyautar kujerin hajji har guda hudu, inda Mataimakin Shugaban kasa, Alhaji Atuku Abubakar ya dauki nauyin karatunsa a Jami’ar Madina.

Ita ma Malama Nafisa Muhammad Zannah daga jihar Nassarawa, ita ce ta zama gwarzuwar shekara a musabakar ta bana a karatun hizifi 60 da tafsir, ita ma ta samu kyautar motoci da kujerin hajji da wasu kyaututtuka daban-daban.

A gasar hizifi 60 babu tafsir kuma, Malam Hadi Muhammad Dole daga jihar Sakkwato shi ya zama na daya, Abdulsalam Isah Musa Yunus daga jihar Borno ya zama na biyu, sai kuma Abdullahi Ali Alhaji Abdullahi daga jihar Kano ya zama na uku.

A bangaren hizifi 40, Abdullahi Abubakar daga jihar Sakkwato ne ya yi na daya, sai Ibrahim Garba Hasan Jibrin daga jihar Jigawa ya rufa masa baya, inda shi kuma Nura Abubakar Salihu Gusau daga jihar Zamfara ya yi masa na uku.

A bangaren hizifi 20, Malami Abdullahi Sakkwato ya yi na daya, Abdul-Gaffar Abubakar Khalid daga jihar Nassarawa ya rufa masa baya, sai wanda ya yi musu na uku Idris Goni Dudu daga jihar Borno.

A karatun hizifi 10 kuwa, Umar Bishara Muhammad Musa daga jihar Borno shi ya yi na daya, Abdullahi Yusuf Salisu Nassarawa daga jihar kano ya rufa masa baya, sai wanda ya yi musu na uku Muzammil Abubakar Kariyoma daga jihar Nassarawa.

A musabaka ta hizifi biyu, Yusuf Muhammad Baffa Dukko daga jihar Gombe ya lashe gasar, Badamasi Yahya Lafiya daga jihar Nassarawa ya rufa masa baya, Umar Sani Muhammad daga jihar Kebbi ya yi musu na uku.

A kuma bangaren mata hizifi 40, Khadija Yunusa Iliyasu daga jihar Kano ta zama gwarzuwa a wannan bangaren, Amina Muhammad Ibrahim Abdullahi daga jihar Filato ta mara mata baya, sai kuma Habiba Muhammad Abdullahi daga jihar Sakkwato ta yi musu na uku.

Haka zalika kuma, a bangaren hizifi 20, Malama Fatima Umar Harun Yunus daga jihar Borno ce ta zamo ta daya, Khadija Tanimu Abdullahi daga jihar Filato ta mara mata baya, Halima Hasan daga Jihar Yobe ta yi musu ta uku.

Wadanda suka samu nasara a gasar hizif 10 sune: Zainab Muhammad Ibrahim Abdullahi daga jihar Filato, idan ta zamo kan gaba, Fauziyya Hashim Ali Adamu daga jihar Taraba ta mara mata baya, Mariya Abubakar Aliyu Umar daga jihar Gombe ta yi musu ta uku.

A musabakar hizifi biyu kuwa, Zulaikha Ayodele daga jihar Lagos ita ta yi ta daya, Habiba Afodun daga jihar Kwara ta mara mata baya, sai kuma Bilkisu Abdullahi Muhammad daga jihar Benue ta yi musu ta uku.

Da yake jawabi a wajen bikin rufe gasar, Mataimakin Shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya jaddada muhimmancin neman ilimi ne a tsakanin al’ummar Musulmi, inda ya yi fatan gasar karatun Alkur’anin za ta zama wata hanya ce ta cusa ilimin Alkur’ani a kirazan Musulmi da kuma zamowa wata hanya ta hada kan Musulmi.

Ya ce babban abin da ke gaban Musulmin duniya baki daya shi ne hada kai da kuma taimakon juna, wanda ya ce rashin wadannan abubuwa ne musabbabin halin ni-’yasun da Musulmin suka sami kansu a ciki.

A nasa jawabin, Gwamnan Jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya gode wa masu shirya gasar ne saboda damar da suka bai wa Jihar Kano na ta dauki nauyin gudanar da gasar na kasa, inda ya bayyana cewa, gwamnatinsa ta dukufa wajen ganin ta kyautata rayuwar almajirci da Alarammomin da ke jihar.

Shugaban Jami’ar Usman Danfodiyo da ke Sakkwato, Farfesa Tijjani Bande, wanda Jami’arsa ce ke shirya gasar ya ce, wannan gasar ita ce ta fi kowacce samun ’yan takara da yawa, inda dukkan jihohin kasar har da Abuja suka shiga takarar.

Farfesa Tijjani ya ce, gasar ta badi, in Allah Ya kai mu za ta gudana ne a jihar Bauci.

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


  | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International