Almizan :GINA SHAKSIYYAR 'YAR UWA MUSULMA (1) ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 10 Shawwal, 1426                 Bugu na 691                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Dandalin Iyali

GINA SHAKSIYYAR 'YAR UWA MUSULMA (1)


GABATARWA

Daga Maimuna Abdullahi Kano


Da sunan Allah Mai rahama, Mai jinkai. Tsira da aminci su tabbata ga Manzo Muhammad da Iyalansa tsarkaka. Kasancewarta uwa, babu shakka mace na da muhimmiyar rawa a cikin al'umma, musamman da yake raino da mafi yawan nauyin tarbiyya na kanta ne. Saboda haka ginuwarta a kan ginshikin tarbiyyah da ilmi da sanin ya kamata babban tabbaci ne a kan nagartar wadanda za ta tarbiyyantar. Al'amarin da zai haifar da gyara a al'ummar baki daya. Sanannen abu ne ma cewa gyaruwa ko lalacewar kowace al'umma na da alaka da tarbiyyar mata. Domin haka ne Musulunci ya bai wa mace babbar martaba da kulawa a dukkan matakan rayuwarta na 'ya da mata da uwa.

Mu'assasatuz Zahra (A.S.), Kano Cibiya ce da aka kafa a 'yan shekaru, babbar manufarta shi ne kokarin ganin kyautatuwar al'amuran mata da ma al'ummar musulmi baki daya, ta hanyar ilmantarwa, fadakarwa da zaburarwa ga dukkan ayyukan alheri. A kan hakan ta shirya bitoci da tarurrukan wayar da kan jama'a tsawon samuwarta wadanda suka ba da kyakkyawan sakamako. A wannan karon Cibiyar ta tattara wasu jawaban da aka gabatar a bukukuwan Ranar Mata a littafi da ta sawa suna "GINA SHAKSIYYAR 'YAR UWA MUSULMA" domin yada sakonnin da ke ciki masu matukar fa'ida. A lokaci guda kuma domin samun gudummawa ta yadda za ta kyautata ayyuka ta bunkasa su. Ina bai wa 'yan uwa shawarar karanta wannan littafi a natse domin (kodayake karami ne a hannu), amma ma'anonin da ke tattare da shi masu yawa ne.

Godiya ta musamman ga Jagoranmu Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a kan karantarwa da irshadin da yake mana. Haka nan Malam Muhammad Turi bisa da ba lokacinsa da ya yi wajen yi mana nasihohi da ba mu shawarwari ga wannan Cibiya. Muna kuma gode wa marubutan wadannan mukaloli masu matukar muhimmanci da dimbin darrusa. Haka ma dukkan 'yan uwa maza da mata da ke ba da gudummawa domin ci gaban wannan Cibiya mai albarka. Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai.

MACE TA GARI TUSHEN GYARUWAR ALUMMA

Da sunan Allah Madaukakin Sarki, tsira da aminci su tabbata ga Fiyayyen halitta, Manzon Rahama Muhammad (S) da Iyalensa tsarkaka (AS).

Hakika mace na da babban matsayi a cikin al'umma kasancewarta uwa mai tarbiyya. Tana da hakkoki kamar yadda akwai hakkokin da suka hau kanta. Ita baiwa ce ga Allah Ubangijinta, 'ya ga iyayenta, mata ga mijinta, kuma uwa ga 'ya'yanta. Dadi a kan haka kuma ita bangare ce na faffadar al'umma da ke da hakkin kyautatawa a kanta kamar makwabta da sauran wadanda yanayi zai sa ta yi mu'amala da su.

Tarbiyyantuwar mace da tarbiyar Musulunci madaukakiya da dabi'u kyawawa da ayyuka, duk da tsayuwa da dukkan hakkokin da ke kanta domin kyautatuwar zamantakewarmu, manufarmu da gina shakhsiyarta ta yadda za ta kai ga babban matsayin tarbiyya a kan kanta, ta tarbiyyantar, ta kuma zama abar koyi ga saura.

Allah na cewa; "Lalle wadanda suka yi imani kuma suka aikata ayyukan kwarai, wadannan sune mafifita alherin halitta." Da saukar wannan aya Sahabbai suka tambayi Manzo (S) wannene mafi alherin halitta? Sai ya ce; "Ali da Shi'arsa," wato jama'arsa kenan. Don haka dole ne mace ta gari ta kasance a cikin Shi'ar Ali, a kan haka ne kuma za mu nazarci yadda alakar mace musulma ya kamata ta kasance da wadanda muka ambata a baya.

MACE MUSULMA DA MAHALICCINTA (SWT)

A matsayinta na baiwa akwai bukatar mace ta kasance mai tsoron Allah mai imani na kwarai, ta yi duk abin da za ta yi saboda Allah, ta sani cewa hasken zuciya da ruhi na tare da imani da tsoron Allah, kuma ta tsayar da ibadun da Allah ya dora mata, farilla da mustahabbai.

Manzon Allah ya taba tambayar Sahabbai da cewa; "in mutum na da kogi a gaban gidansa yana wanka sau biyar a rana, zai kasance yana da dauda? Sai suka ce, "a'a," sai ya ce, "shi ne kamar salla sau biyar a rana, in mutum ya yi alwala ya yi salla sau biyar babu zunubinsa da zai ragu, an gafarta masa kura-kurensa."

Kuma sallar farali wacce aka yi ta daidai ta fi Hajji dubu da Umrah dubu wadanda aka yi karbabbu. Domin salla duk wanda ya tsayar da ita ya tsayar da addini, duk wanda ya wulakanta ta, ya wulakanta addini. Imam Ja'afar (AS) na cewa; "Duk wanda ya yi salla raka'a 51 a wuni shi ne mumini." Wato farillai da nafilfilinsa kenan na dare da yini.

Manzo (S) na cewa; "Bawa ba zai gushe ba yana kusantar Ubangijinsa da sallolin nafilfili har sai Allah ya so shi, sai ya zama jin sa da yake ji da shi, da ganin sa da yake gani da shi, da hannunsa da yake riko da shi, da kafafunsa da yake tafiya da su, idan ya nemi tsarina sai in kare shi," Idan Allah Ya So bawa sai ya kira Mala'ika Jibril ya ce; "Ni ina son wane dan wane, ka so shi. Sai ya so shi, sai ya yi yekuwa ga ma'abota sama, ya ce 'Allah na son wane dan wane ku so shi! Sai su so shi. Sai a sa shi a zukatan bayin Allah a duniya. Sai su so shi. Haka ma in Allah ya ki wani."

An ruwaito cewa; Ummul Muminina Zainab tana rataya igiya a masallaci don in ta gaji da salla (nafila) sai ta kama igiyar ta rike. Sai Manzo ya ce, in mutum yana jin nishadi ya yi salla a tsaye, idan kuma ya gaji ya zauna. Daga cikin ibadun da za su kusantar da mutum da Allah ba kamar azumi. Manzo (S) ya ce; "Duk wanda ya yi azumi yana mai imani, ana sa ran Allah Ya gafarta masa duk abin da ya gabatar na kura-kurensa."

Duk ayyukan da dan Adam zai yi ana ba shi lada ninki goma, Allah ya ce, "ban da azumi, domin shi nawa ne. Ni ne zan ba da ladansa. Mutum ya bar ci da sha da sha'awa don Allah ne."

Azumin nafila yana da muhimanci sosai, kamar na ranaku wanda ya hada da shidan Shawwal, wanda in mutum ya yi shi ya sa da shi da Ramadan. To kamar ya yi azumin rayuwa ne gaba daya. Haka ma na 13, 14 da 15 na kowane wata. Da kuma azumin Ghadeer (wato ranar 18 ga watan Zulhijjah). Da na ranar Maulidin Fiyayyen halitta (17 ga Rabi'ul Awwal), na ranar aike (Yaumul Bi'ithah), wato ranar 27 ga watan Rajab. Na ranar Shimfida Kasa (25 ga Zil Kaadah), na ranar Arfa (9 ga Zil hijjah), na ranar Mubahala (24 ga Zil hijjah), azumin Alhamis da Juma'a, azumin ranar farko ga watan Zul hijjah zuwa ranar tara ga watan, da watan Rajab watan Allah, watan da Manzo ya ce duk wanda ya azuminci kwanaki uku a cikinsa Aljanna ta wajaba a gare shi, wanda kuma ya azuminci kwana daya za a shayar da shi ruwa daga koramar Aljanna.

Haka nan ma an so yin azumi a watan Sha'aban, watan Manzo ne, duk wanda ya azumci kwana daya a cikinsa Aljanna ta wajaba a gare shi. Da kuma azumin ranar Nairuz, sai kuma azumin farko na Muharram zuwa tara ga watan.

Sai kuma abin da ya shafi karatun Kur'ani mai girma. Alkur'ani littafin Allah ne, shi waraka ne da magani ga masu imani. Duk wanda ya karanta ko da harafi daya ne yana da lada goma, mutum ya karanta akalla izu biyu a rana, ya sauke bayan wata guda. Kowace sauka ana halittar Mala'iku dubu 70 suna masu roka masa gafara har zuwa ranar gobe kiyama.

Sai abin da ya shafi zikirori, su Tasbihi, Hailala, Tahmidi, Takbiri da Istigfari da Salatin Annabi (S). Manzon Allah na cewa; "duk wanda ya ce Subhanallah Walhamdulillahi, Wallahu Akbar za a shuka masa itaciya a cikin Aljanna. Sannan ya ce; "kada ku aikata zunubin da zai kona wannan itaciyar." Akwai lokacin da Manzo (S) ya yi mi'iraji yana tare da Mala'ika Jibrilu a Aljanna, sai ya ga wasu Mala'iku suna ta gini da lu'u-lu'u da zinare da azurfa. Amma idan sun yi ginin sai su tsaya, sai Manzo ya tambayi Mala'ika Jibrilu. Sai ya ce gidan wani bawan Allah ne. To sai ya ce me ya sa suke tsayawa? Sai Jibrilu ya ce, ba a kawo musu kayan aiki bane. Ya ce kayan aiki shi ne "Subhanallah, Walhamdulillahi, Wallahu Akbar."

Sai salati, shi ko duk wanda ya yi daya, Allah zai yi masa goma, ya gafarta masa kurakuransa goma, kuma ya daukaka darajarsa goma.

Sai abin da ya shafi addu'a. Akwai addu'o'in Ma'athurai, wasu a Mafitihu, wasu a Baladul Ameen. Wasu a Misbahul Mutahajjid da Minhajud da'awat. Akwai addu'o'in rana da kwanakin wata da addu'o'in kowace salla da sauransu. Allah Ya sa mu dace Amin.

Za mu ci gaba insha Allah.

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


 Shafin Gamji | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International