Jarida don Karuwar Musulmi
Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki ISSN 1595-4471
Juma'a 17 Shawwal, 1426
Bugu na 692
Tunatarwa | | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari Tattaunawa | Labarai |
AMODARI (Pedicolosis–lice)
Amodari wata cuta ce mai matukar yaduwa a tsakanin mutane wanda wasu kwayoyin halitta dangin ‘parasite’ masu cutarwa ke haddasawa. RABE-RABEN AMODARI: Amodari ya kasu kashi uku gwargwadon wuraren da ya kama a jiki: Amodarin kai (P.h Capitis) Amodarin jiki (P.h Corporis) Amodarin mara (P. pubis) YADUWARSU: Amodari kowane iri yana yaduwa ne daga wani mutum wanda ya kamu zuwa ga wani wanda bai kamu ba, wato mai lafiya, ta hanyar hada jiki kai tsaye, ko kuma a kaikaice ta hanyar yin amfani da wasu kayan amfani ga jikin, wanda ya kamu zuwa ga wanda bai kamu ba. Misali a nan kamar hada amfani da masharcin gashi ko sanya tufafin mutane barkatai da amfani da zanin shimfidar wani ko bargo da sauransu. ALAMOMIN AMODARI: Kusan alamar amodari babba ita ce a ga gari-garin kwayayen wannan cuta like da fatar wurin da kwayoyin cutar suka makale. Akwai matsanancin kaikayi a inda suke, musamman gefen kunnuwa da sauran wurare a jiki. Wannan a jumlacen alamomin cutar kenan, wato dukkan rabe-rabensa, ina nufin amodarin kai, da jiki da mara. Amma kowanne za a iya ganin wasu alamomi na musamman wadanda suka kebanci irin wannan nau’in amodarin, a inda ya kama a sashen jiki. Insha Allah za a ga karin bayanin alamomin kowanne idan aka fara bayaninsa kamar haka: AMODARIN KAI: Alama mafi muhimmanci ga amodarin kai, musamman ga yara kanana ita ce; za a ga wani gari-gari busasshe yana fita a jikin kai, wato karkashin gashi, musamman a gefen kunnuwa. Wani lokacin har da kananan kuraje masu kaikayi, wani lokacin su girma su rika yin ruwa. KULAWA DA AMODARIN KAI: Akwai matakin kara inganta tsaftar kai ta hanyar wanke kai da sabulun kuraje kamar sabulun salo ko sabulun toka da sauran sabulan kuraje. Akwai abubuwan shafawa masu iya kashe wadannan kwayoyin cuta kamar man “1% permethrin lotion” ko “0.5% malation lotion” wadanda ake amfani da su, kodayake suna da ka’idoji sosai wadanda lalle kafin a shafa su ya kamata a tuntubi masana magani ko Likita a kan yadda ake amfani da ruwan wannan magani. A rika amfani da hannu ko buroshin shartar kai a rika cire wadannan kwayaye a jikin fatar kai. Duk burushin da aka yi amfani da shi domin taje gashin a tsoma shi cikin maganin kisan kwayoyin cutar, ko a tsoma shi cikin tafasasshen ruwa na wani lokaci. Haka kuma a lura da kum na taje gashin da kayan shimfida kamar zanen shimfida da rigar matashin kai da matashin kan da sauransu. Banda duk wadannan akwai yiwuwar yin amfani da magunguna wadanda Likita zai iya tsarawa maras lafiya. A bar barin gashin kai yana taruwa. AMODARIN JIKI: An fi samun irin wannan nau’in amodari a cunkoson jama’a yayin wasu bala’o’i kamar zama cikin cunkoso a gidan yari, sansanin ’yan gudun hijira, kwana bisa titi ko jeji da sauransu wadanda za su tilasta mutane zama cikin mawuyacin halin rashin tsafta da sauran matsaloli. ALAMOMIN AMODARIN JIKI: Akwai matsanancin kaikayi, da wasu ’yan kuraje kanana masu ’yan ruwa idan suka fashe, kuma za a lura da alamomin soshe-soshe a fatar jiki. Wadannan ’yan kananan kuraje sun fi yawa bisa kugu gewayen zariyar wando da tsakiyar baya da cikin hammatar hannu da bisa duwawu da sauran wurare. Sannan za a iya ganin gari-garin kwayayen wadannan kwayoyin cuta bisa tufafin mutum har suna zuba kasa. KULAWA DA AMODARIN JIKI: A inganta tsaftar jiki ta hanyar yawaita wanka da wanke tufafi da sabulu, musamman sabulan kuraje kamar sabulun salo ko sabulun toka da sauran sabulan zamani kamar tetmosol, carat, asepso, terry, movate, septol da sauransu. A rika tsoma tufafin da aka wanke da omo cikin ruwan zafi tafasasshe su yi kamar minti 15–30, sannan a tsame a matse a shanya a rana, sannan a goge da dutsin guga mai zafi kwarai. Haka kuma sauran kayan sawa kamar huluna, belt, sarka, agogo, safa, takalma; akwai garin hodar kisan kwayoyin cuta, wato ‘0.5% permethrin’ ko wata makamancinta kamar ‘0.3% lindane powder’ wadda za a nemi shawarar masana maganin a kan irin wadannan hodar a rika zubawa kaya lokaci zuwa lokaci. Ana son akalla a yi kamar kwana goma ana amfani da wannan hoda ko wasu makamantan wannan. AMODARIN MARA: An fi samun amodarin mara ga manyan mutane, wanda kuma yana saurin yaduwa ne ta hanyar haduwar jima’i ko hada kayan sanyawa. ALAMOMI: Za a samu irin wannan amodari a jiki kusan duk inda gashi ke fitowa a cikin jiki kamar a gaban marar mutum, ko hammata, bisa cinyoyi, fuska, da sauransu. A wasu lokutan irin wannan amodarin dan rakiyar wasu cututtukan jima’i ne, wato (Sexually Transmitted Diseases, (STDs). Don haka tun farko ana iya fara la’akari da wannan wajen nemawa maras lafiya lafiyar jikinsa. KULAWA DA AMODARIN MARA: Matakin farko shi ne aski. Wato a bi a hankali, a aske duk wani gashin tsakiyar jiki, sannan a ci gaba da wanka da sabulan kuraje da shafa man kuraje kamar yadda misalai suka gabata. Kada a takaita kulawa ga wanda ya kamu kwarai, ana iya hadawa da abokan zama, kamar mata da miji da sauransu. A bincika dalili, musamman idan ya kasance sakamakon wasu cututtukan jima’i ne (STI) da sauransu. Wannan zai taimaka wajen magani gudun kada a yi ciwo daban, magani daban. Akwai yiwuwar sai an sha magani, ko allurai gwargwadon tsanantar wannan ciwo, sai a nemi shawarar kwararru a kan wannan a asibiti. A wayar wa jama’a da kai a kan illar cunkoso da kazanta da kuma matakan cimma wannan tsafta. Za mu ci gaba insha Allah. |
Shafin Gamji | Tafsirin Alkur'ani | Hadisai | Crescent International |